Chapter - upset
by @maidambu41
_....ZAYN MALIK....✿_
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
Mai_Dambu
CHAPTER-6
*Wow wannan shafin naku ne Maman Twins na taskar Khadijah Candy, Sister Bilqis na Fitilar MD Maman Hajiya na Fitilar MD wato Waɗannan mutane uku suna sheke min walwala ta da kiran Jikan Hajjos dan haka ba zan iya fitinar Hajja da jikanta ba idan zaku iya ga fili ga me doki 🥰🤌🏽❤️*
Lokacin da Zayn ya kammala secondary a lokacin Aunty Rukayya tayi haihuwan farko, ai kuwa ba karamin shagali aka yi ba a sanin ta mijin ta da abokan aikin shi ne sai yan uwa yan Nigeria da suke Boston, sai gashi an yi mugun shagali domin dai Zayn me jama'a ne, kuma ta gansu ba yaran musulmai ba ba yaran turawa kiristoci ba, ana gobe suna aka kawo hajjah tsakani da Allah ya ji haushin kawo ta domin yanzu zata hana shi sakat. Ai kuwa ranar da suka zo dake ita da Mama ne sai AUNTY Fatimah kin kwanan gidan yayi sai washi gari ya shigo daga shi sai gajeran wando dake a karon farko da ta fara ganin shi da gajeran wando kenan. Sake baki tayi tana cewa.
"Innalillahi yau naga ikon Allah Zainu gane da gajeran wando kamar me shirin tsalleke wuta?"
Zuwa yayi jikin Maman shi ya ce mata.
"Welcome to Boston Mama na, bari gayawa Friends dina su san mama na tazo"
"Haba Malamina waye ya shiga tsakanin mu dan nasan akwai masu bakin ciki da zaman mu" cikin sakalci da shagwab'a ya ce Mata.
"Matar karfe kawai nasan baki zo sunan nan dan kome ba, sai dan ki hanani sakat " ya fada yana wani nodding kan shi.
"Inji wani dan kusun uwan? Ni zan dami Zainu na? Kawai abinda ya dame ni wannan gajeran wandon ai bai yi ba kowa ya ganka yasan babu Allah a cikin lamarin ka"
"Hajjos kina nufin na zama mutumin banza kenan? Shi kenan gara naje na fada teku na mutu" zubur ta mike tana daura dan kwalin Super wax dinta tana kokarin da kusa da shi.
Cikin kwantar da murya ta ce mishi.
"Ayya ba haka nake nufi ba, kawai ija nufin kaf cikin garin nan babu na Allah irin ka." Murmushi yayi sannan ya ce mata.
"Toh zauna bari na shirya "
"An tafi intermission kenan?" Inji Aunty Rukayyah da ta fito ta cab'a kwalliya sosai.
"Wow Auntyna kin yi kyau You look adorable bari na haura na yi wanka"
Haurawa yayi sama yayi wanka ya shirya cikin wata dakakiyar shaddar da tayi mugun mishi kyau, kasancewar shi fari ne, sai ya saka dark blue ya murza hular shi me suna tangaran sai wani daukar idanu take tsabar ta samu k'aro, tayi wani d'as akan shi gwanin ban sha'awa.
Takalmin shi ta kamfanin Nike ce asalin fatar crocodile aka yi amfani da wurin made din shoe din har cove, haka ya fito wani kato da shi, yana murmushi ya kalli Hajjos wacce ta rangad'a gud'a kamar ba tsohuwa ba, a duniya idan tana da wani mafarki taga Zainu ya fito cikakken Hausa fulani, kara mishi kwarjini yake.
Murmushin gefen baki yayi sannan ya ce mata.
"Matar ina son ki"
"Tafi can mugulmamme nan kayi ta min iyayi kamar na zagi uwaka da Ubanka dan banza kato me kamar da kututturen bushiyar kuka"
Kallon ta yayi yadda ta gwatsile shi lokaci guda. Murmushi yayi sannan ta fita abin shi, ba laifi gidan ta cika babu abinda ya d'aga hankalin Hajja irin yan matan turawan da suke bin Zayn kamar jela.
"Ke Talatu anya yaron nan ba zamu koma da shi gida ba? Kin ga wata yarinya can zolo-zolo tana bin shi kamar wutsiyar shi!"
"Hajiya ai ba wani abu bane kinsan nan basu damu da haka ba, dan yanayin su da namu da banbanci"
"Toh ai shi kenan idan ke baki kishin danki ni kakar shi ina kishin sa, kuma yanzun zan musu magana su bar bin jikana domin kika ganin wancan zilaziyar idan ba ayi da gaske ba zata iya turmushe min shi yaro karami"
"Yaro karami??!!" Suka tambaye lokaci guda. Wani Uban fuska Hajja ta saka wallahi sai ka rantse da Allah ba ita tayi wannan maganar ba.
Mikewa yayi tare da shiga kitchen din Aunty Rukayyah ta dauko muciya, ta nufi hanyar waje.
"Hajja don Allah kar ki je, wallahi kawayen shi ne" inji Aunty Rukayyah.
Kamar an ce ta kai idanun ta, kawai ta hango yar budurwa ta kai hannun ta kafadar shi tanar da mika mishi glass cup suka cheer.
"Innalillahi wa'inna illahi raju'un, kuce min sun gama lalata min shi, dubi yadda take mishi magana tare da daura hannu a kafadar shi " ta fada kamar tana
"Hajiya umma wallahi ba kome bane a nan Kinga dukkansu yara ne" kallon Mama tayi da tayi magana duk da bata ji haushin maganar Aunty Rukayyah ba, amma Wallhi sai da taji haushin maganar Mama wani banzan harara ta watsa mata sannan ta ce mata.
"Ban da Allah ya dubi zuciyata ai nasan wallahi Auta da Rukayya ba zasu iya tarbiyyar Zainu ba, na fasa komawa kaduna kuyi tafiyar ku ina nan ina kallon yadda ake tarbiyyar a gidan nan"
"Eyye amma Hajiya wallahi kin ma toh " inji Aunty Fatima ta bar falon domin taji haushi ba na wasa ba,. Me yasa lokacin da suke London basu lalace ba, sai Zayn da yake namiji za a saka ido haka.
"Wato Rukayyah keda auta kamar ba amana kuka dauka ba, kun bar yaro yana ta kara kaina akan doyoyin masu jan kunne salon dare daya a samu daya ta Nishi fyade Allah na tuba ji yadda suke kallon shi "
Ba Mama ba ba Aunty Rukayyah Ba kamar su watse su bar ta ita ɗaya, sun san yanzun suna watsewa zata iya fashewa da kuka tace sun mai da ita mahaukaciya. Dan haka suka zauna har aka gama taron lafiya,.yana shigowa kuwa ta ce mishi.
"Zainu!"
"Na'am Hajjos "
Cikin kalar tausayi ta kalle shi sannan ta ce mishi.
"Ko xaka je kayi wanka domin doyoyin masu jan kunne ba tsarki ne da su ba." Kallon Mama yayi yaga hankalin ta yana kan news, Aunty Rukayyah kuwa tana feeder Baby dinta me sunar Hajiya dake mace ta haifa.
Zasu kirata da Widad.
Sai AUNTY Fatimah da take dinning table tana dariya,
"Hajjos zargina kika fara?" Ya tambaye ta cikin wani cool voice,
"Haba wane mutum inji mutuwa, gani nayi ai ba sallah suke ba, kai kuma sallah kake lokaci biyar kake kallon gabas me zai saka na zarge ka, sannan ita kanta rike sallah da cikata akan lokaci.yana kare mutum daga miyagun halaye da zunubai, kawai yaran ne basu da tsarki"
Sosai goshin sa yayi yana nazarin abinda zai yi dan Hajiya ta daina saka mishi ido har haka, wucewa yayi bai ce mata kome ba. Domin idan ya cigaba da tsayawa wallahi tsaf zai iya fasa ihu.
Ai kuwa har kusan goma na dare bata gan shi ba, yana can dakin shi.
"Auta ba zaka kira danka ya ci abinci ba ne?"
Share ta Uncle bashir yayi yana kurban shayi.
"Auta dan kaniyar ka ba magana nake da kai ba?"
"Toh hajiya ban san me ya haɗa ku ba, kuma kin san halin Zayn idan na tafi duba shi bai zama dole ya kula ni ba kawai ki je da kanki "
Ganin da gaske babu abinda ya dame shi yasa ta mike tana faɗin.
"Na gane wannan sharrin mahassada ne da suka shiga tsakanin mu Allah yana gani zan je na rarrashe shi " bata gama rufe baki ba sai gashi ya sauko yaci uban kwaliya zai tafi birthday party na kawar shi Anita wata yar india class mate din su ne.
"Alhamdulillahi Zainu malamina zoka ci abinci "
"Hajjos na koshi xan tafi party ne dai an jima zan dawo "
"A wannan tsawon daren ko tsoron dare baka yi idan kayi gamo fa?"murmushi yayi yana faɗin.
"Uncle Insha Allah 12:30 zan shigo "
"Ok Son Becareful "
"Insha Allah " ya fada yana barin gidan.
"Bashir wannan shine tarbiyya?"
Hajiya ta tambaye shi ran ta a matukar bace,
"Hajiya rayuwar nan da banbanci da Nigeria Zayn baya bin mata, baya shaye-shaye, baya sata Hajiya idan na cika takura Wallahi hukumar kare hakkin Yara da mata zasu iya bashi mugun yancin da zai dame mu, yanzu haka na gama kome na shi na shiga jami'a kawai Monday xai fara domin yan uzurina ne ya sa bai fara ba"
"Ba shi nake son sani ba, wani irin yanci me haka mara Kasafi? Zan mai da shi Kaduna yaje gabana yayi karatun shi akan Idanuna!"
"Toh Hajiya" ya fada Mata, sannan ya shige study room din shi, kafin Zayn ya dawo ya gaya mishi yadda zai yi da Hajiya dan wallahi ba zai iya asarar kudin shi ba.
Bai san a inda ya bar ta take zaune ba sai da ji kukan Baby Amal, sannan ya fito ya ga ta zubawa kofar gidan idanu.
"Hajiya ba zaki kwanta ba? Zayn zai dawo fa." Kwafa tayi tare da nufar dakin da suka sauka. Ta same su suna barci.
Har ta hau gadon ta fa ta kwanta can ta tashi ta fasa musu kuka kamar wacce aka daura mata mari, ai babu shiri kowa ya tashi ya zauna.
"Hajiya umma me aka miki?"
"Wayyo Allah na, Wayyo Zainu na" abinda tayi ta fada kenan ta hana kowa kwanciya dole Uncle Bashir ya dauki key mota ya fita a daren ya nufi gidan su Anita yana zaune ya harde daya akan daya, ya sai fama yake da zokar wiwi.
"Mr Malik zaka iya tashi muje" yarda mandular yayi domin lokacin bai yi kaurin suna ba, ya mike tana hura bakin shi, sannan ya wani b'ata rai kamar bashi ba, zuwa yayi ya ɗan rungume Anita sama sama, sannan ya wuce bayan sun yi magana ya nuna wani abokin shi zai bata sakon shi.
Tunda ya shiga motar ya wani ƙara b'ata rai, kamar an mishi wani abu kalmar nan ta Hausa da ake cewa.
Taburman kunya nad'e shi da haka Zayn yayi tare da cin wani uban magani kamr wanda aka aiko mishi sakon mutuwa.
Suna isa gidan uncle Bashir ya ce mishi.
"Hajiya umma ta ce zata mai da kai Kaduna, sannan na gama kome ya za ayi kenan yanzu ita ce ta saka kuka a dawo mata da jikan ta."
Kallon Uncle bashir yayi kafin ta bude motar ya fita abin shi, yana shiga gidan ya same ta a dakin ita dasu Aunty Rukayyah da Mama, takaici ta hana Aunty Fatimah fitowa.
"Zainu na" ai kuwa ta fashe da kuka, zuwa yayi gaban ta ya zauna tare da zuba mata ido, cikin nutsuwa murmushi yayi sannan ya ce mata.
"Muje ki kwanta" babu musu ta mike yana gaba tana bayan shi har cikin dakin, ya gyara mata wurin kwanciyar. Sannan ya zuba mata ido yana kara nazarin ta kafin yasan me zai gaya mata, a hankali ya ce mata.
"Hajiyata! Kwanta ki huta idan Allah ya kai mu gobe sai muyi magana"
"Zainu ina cewa ba zaka tafi ka bar ni ba?" Ta tambaye shi tana matsar kwalla.
"Ina nan har gari ya waye " ya zauna a wurin har tayi barci bai matsa ba, yana zaune a gaban ta, tana barci ya ja mata mayafi ya lullube ta, sannan ta koma ya zaune a bakin gadon yana kallon ta, yana tuna tun kankantar shi Hajiya bata iya barci idan har yana ciwo ko yana jin rigima, bai da abinda zai biya Hajiya da shi har tayi nisa.
"Ko zaka tafi ka kwanta ne?" Mama ta tambaye shi tana shafa kan shi a hankali, d'ago kai yayi yana kallon ta sannan ya ce mata.
"A'a bana jin barci ne, mu yanzu lokacin hiran mu toh Hajiya ta hana ni hira, ba kome zan zauna na yi gadin ta "
"Allah ya yi jibanci al'amarin ka, ya kuma baka abinda kake nima ya baka hakuri da fasaha, ya baka ikon jure duk wata jarabawar da zata shigo rayuwar ka, Baby Allah ya baka abinda baka roko ba, ya kara maka akan wanda ka roka"
Murmushi Aunty Fatima tayi tana faɗin.
"Mama auta kawai kika sani?" Murmushi yayi yana mata gwalo, kafin suka shiga hira har suka kwanta, ya mike ya gyara musu bargon su, sannan ya dawo ya zauna gaban.gadon Hajiya tare da kwantar da kan shi a bakin gadon, hannun ta da yake daure a matashin ya daura saman kan shi. Sannan ya kwanta.
Lekowa uncle Bashir ya leko ya hango yadda suka kwanta murmushi yayi yana me ja musu kofar,
**
Washi gari
Duk sun fito ban da Zayn da tun sallah asuba da Hajiya ta gan shi, bata kuma ganin shi ba, yana sama a kwance. Sai jele take tana kallon sama, sai ta dawo ta zauna.
"Talatu Yaron nan lafiya yake barci haka? Gaskiya a duba min shi ba zan iya nutsuwa ba sai naji lafiyan shi"
"Hajiya ki haura saman mana" inji Aunty Fatima tana dariya,
"Ungo naki yar banza me kai kamar dutsen dala. Talatu maza taso min shi"
"Toh hajiya" inji Mama,
"Dan Ubanki idan baki tafi ba ai ita taje min yar banza da idanun kamar na tsohon kwaɗo"
"Allah ya baki hakuri"
"Idan kaya ne nad'e gammo ki dauka."
"Hajiya kiyi hakuri"
"Ban yi ba" ta fada a fusace,
Mama najin ta haura saman, tsayawa tayi a bakin kofar kafin ra murda yana kwance, dakin tsaf-tsaf kamar ba na matashi ba,.ko ina gwanin ban sha'awa babu abinda mace zata nuna mishi.
Bakin gadon ta zauna tana shafa kan shi, tare da kallon yadda yake barci.
"Allah ya kare ka da mugun ji da mugun gani"
"Amin Mamana" ya amsa mata tare da mikewa zaune yana murza idanun shi.
"Ina kwana Mamana"
"Da fatan ka tashi lafiya"
"Alhamdulillahi wancan matar ce ta taso ki ko?"
"Gidan ku Babana" mikawa yayi ya shiga ban daki yayi wanka kafin ya fito ya samu bata dakin gajeran wando ya saka sannan ya sauko kasa yana kallon Hajiya da take ta wani shan kamshi, wani dauke kai yayi shima ya wuce wurin abin karyawa ya zauna ya fara karyawa, yana idarwa ya kalle Aunty Rukayyah ya ce mata.
"Maman Baby Amal ina kwana? Aunty Fatima da fatan kin tashi lafiya?" Da gaya yaki gaida Hajiya,
"Dan Uban ka, ka tashi lafiya?" Ta fada tana kallon shi.
"Hajiya da fatan kin tashi lafiya, dama akwai magana ta dake, naji labarin kin ce zamu wuce kaduna wai haka ne?"
Rike baki tayi tana kallon shi.
"Zainu wani munafikin ne yake son farraka tsakanin mu?" Ta tambaye shi tana kallon Mama, wacce ta tura ta kira shi.
"Hajiya babu wani munafiki cewa kika yi uncle Bashir bai iya tarbiyya ba ko ba haka aka yi ba?"
"Zainu karka dauki maganar masu shiga tsakanin jika da kaka, ni bance haka ba, wai cewa nayi zan zauna nayi kwana biyu "
"Babu wanda ya gaya min kin ga can?" Ya nuna mata wani dan ƙaramin camera.
"Ina ganin kome, har zagin abokaina da kika yi ta yi. Yanzu don Allah idan abokaina suka ji wannan cin zarafin kin san abinda zasu miki kuwa?"
Yadda ta marairaice fuska zaka dauka da gaske a gaban shi aka yi kasa tayi da murya.
"Tunda basu ji ba ai sa sauki, kayi hakuri ban.wani d'aga hankali ba tunda wani sati zamu tafi shi kenan "
Cizon lips din shi yayi yana kallon ta baki daya yana jin shi very upset Kuma Hajiya ce take kara tunzura shi da kayan ciwon kai...