Matsalar Mu A Yau

9&10

by @bintaumarabbale

MATSALAR MU A YAU!*

 _(Labarin Surayya)_


*NA*

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*

____________________________


*SADAUKARWA NE GA:*

   _(Surayya dee🥰)_



 Free pege

*9&10*

"Daga ina kike a cikin wannan daran."? Idonsa a tsaye a kanta yake mata wannan tambayar." Cikin rawar murya tace."Awara na siyo gurin Ummiyo." Yana ya mutsa fuskarsa Yabi awarar dake kasan gurin da kallo ya girgiza kansa da fadin." Shiga mota." Gabanta ne ya fadi tabi shi da kallo yana kokarin bude motar ya juyo ganinta a tsaye a inda take sai ransa ya 'baci tsawa ya buga mata da fadin."Tsayuwar me kike a gurin ko ba kiji abinda nace ba."


A sanyaye ta karaso gurin kamar zata fashe da kuka ta bude motar ta shiga sanyi da kamshi suka bakunce ta Tsaki yaja ya kunna motar suka bar gurin.


Tun daga nesa suka hangoshi zaune akan kekensa da alama ita ya fito nema gari yayi duhu ga dare.


Fuska a daure yace."Yanzu meye amfanin abinda kika aikata kin tafi yawo kin saka zuciyar mahaifinki cikin damuwa.


Hawaye ta share tace."Uncle nima wallahi ba'a son raina ba.'' shuru kawai yayi mata ya gyara parking ya bude motar ya fito 


Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka ta fito daga motar salo-salo take tafiya 


Malam yana ganinta tare da Nura sai ya sauke ajiyar zuciya ya zuba musu ido har suka karaso inda yake..........A tsoroce take kallonsa sai kuma ta fashe da kuka.


Malam yace." Ai kema kin san baki kyauta ba dole kiyi kuka Ya kalleshi da fadin."Nuraddin a ina ka tsinto ta."


Yace."Kan hanya na ganta tana tafiya ita kadai ga dare abin ya bani mamaki.


Malam Habu yace."Wallahi Yaudarar mu tayi ta fita wai ta kasa cin abincin daka kawo saboda tafarnuwa shine na bata kudi ta nemi yaro ya siyo mata wani abun shine fa tunda ta fita sai yanzu.


Girgiza kansa yayi yace."Malam a dinga kiyayewa yarinyar nan na ga alama tana da rawar kai dole a sanya ido a kanta kasancewar unguwar nan akwai marasa tarbiya ganinta tana yawo cikin dare zasu samu nasara a kanta.


Malam yace."Kwarai kuwa Nuraddin maganarka haka take insha Allahu zamu kula sosai nagode da kulawarka da abin arziki.


Yace."Babu komai malam yiwa kai ne na barka lafiya." Malam yace."To Allah ya bamu alkairi a gaishe da mutan gidan." Ya amsa yana kokarin barin gurin tace."Uncle nagode." Ba tare da ya kalleta ba yace." Okey. da sauri ya barsu a gurin idansu akan motarsa har sai da ya bar gurin sannan a sanyaye ta tura kekan suka shiga cikin gidan.



 Innah na tsaye a tsakar gidan suka shiga rai a bace tace."Wato Surayya kin zama mayaudariya ko." Tana kuka tace."Innah dan Allah kiyi hakuri wallahi gidansu Samira na shiga muna hira ban san dare yayi ba. 


Tace."Ai dama tunda naji shuru baki shigo ba nasan sai da kika je gurin nan yanzu ina awarar."? " Da sauri tace."A can gidan naci." Malam Yace."Habiba abar maganar haka Surayya ta kori gaba nima ba zan sake bari ta fita cikin dare ba tunda ba ta jin magana."


Tace."Baba don Allah kuyi hakuri wallahi banyi domin na 'bata muku rai ba." Babu wanda ya tanka mata dan Innah ma barin gurin tayi shima ya sauka daga keken ya rarrafa ya shiga dakinsa.


Kafafunta taje ta wanke ta nemi guri ta zauna kan tabarma ita kadai abin duniya yayi mata yawa gabadaya ma yunwar cikinta bata damunta kamar yanda ta damu dashi da soyayyarsa hanyar da zata shigar da kanta gurinsa kawai take tunani ita kanta fa tasan ta daukawar kanta dala da gwaron dutse tasan  sai tsananin rabo guy zai aureta sabida yafi karfinta ta kowane fanni zuciyarta ce kawai take kokarin kaita inda yafi karfinta.


Da tunanin Uncle Nura bacci ya dauketa ita kadai a tsakar gidan sai gefin Asubahi ta farka a firgice ta shige daki ta kwanta tana jin wani irin tsoro a cikin ranta.


***

Bayan sati daya  ita da Samira suka shirya wasika mai zafi mai cike da kalaman soyayya irin na rashin kunya ta karbi wasikar tasa a cikin jakarta tana addua Allah yasa a dace.


Niqab tasa ta rufe fuskarta ta samu yaro ta bashi wasikar da fadin "Idan ka shiga gidan ka bawa maigadi kace wai ya bawa Uncle Nura." Yaron ya karbi wasikar sai da taga fitowar yaron sannan ta bar gurin da saurin gaske.



Da yamma ya fito cikin kayan shan iska maigadi ya gyara masa kujera da littafansa a nutse ya mika masa takardar da fadin."Ranka ya dade ga sako dazu wani yaro ya kawo."


Ta cikin farin gilashin dake idonsa yake kallon takardar kafin yasa hannu a nutse ya karba..Maigadin ya dan risina da fadin."A tashi lafiya. Hankalinsa na kan takardar ya daga masa hannu.


Ya jima yana nanata karanta wasikar yana kuma mamakin tsagerar yarinyar data turo masa da ita.

 

_Assalamu alaikum Masoyi na farin cikin na abin alfahari da tunkaho na ina sonka ina sha'awarka saboda kai din cikakken namiji ne da kowace mace za tayi sha'awa a duk lokacin da zanyi tozali da kai nakan shiga halin damuwa da tashin hankali bayan azababben feelings da yake damuna a sakamakon kallonka nakan rasa kuzari na kullum buri na na kasance a matsayin matarka na gan ni kwance a faffadan kirjinka hakika duk dare ina kasancewa tamkar zautacciya saboda Sha'awarka don Allah ka kar'bi soyayya ta wallahi baka fi karfina ba zan iya maka."_

  Daga masoyiyar ka

      *S-R-Y*


Abinda yake rubuce kenan a jikin wasikar.....Tsaki mai karfi yaja ya sake bin wasikar yana karantawa tare da tunanin daga inda take.....Lokacin da yazo gurin _Baka fi karfina ba wallahi zan iya maka_ Sai kawai ya fashe da dariya irin wacce ya jima beyi irinta ba hakika duk yarinyar data turo masa wasikar nan ta kai ta kawo kuma fitinanniya ce wato yanzu zamani ya lalace 'yan mata na rashin kunya har da maganar da bata dace ba.


Takardar ya ninke ya bude tsakiyar littafin dake hannunsa yasa babu shakka zai cigaba da nazari da tunanin daga inda wasikar ta fito.


 



Pls Share👏🏾






 _*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_

*****

*****

*BINTA UMAR ABBALE*


*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE  KU NEMI WANNAN NUMBER......._*

*22790899076*

*HAJIA FATIMA MUSA  (MOMMY NIJAR)*





 *MAR'ATUS-SALIHA*

_(Itace Cikakkiyar Mace)_


*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*

1- Maganin Sanyin mara

2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba

3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa

4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba

5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa

6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa

7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)

8-Maganin Basir mai tsiro

9-Maganin Basir mai kulle ciki

10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)

*11- Maganin Karin Ni'ima

12- Maganin K'iba mai kyau

13- Maganin Cikar Nono (Breast)

14- Maganin Hips

15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!

16- Maganin Matsi mai kyau

17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba

18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)

19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba



*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*

*****

*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*

Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp