FreeArewaPen original
Matsalar Mu A Yau
- 1views
- 15chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample 路 1&2
MATSALAR MU A YAU!* _(Labarin Surayya)_*NA**BINTA UMAR ABBALE馃崚**MANAZARTA WRITES ASSOCIATION馃馃徎*____________________________*SADAUKARWA NE GA:* _(Surayya dee馃グ)_*FreePege1&2* Cikin nutsuwa take tura keken guragun da yake zaune. a hankali ta fito dashi kofar gida ta tsaya tana kallonsa da idanuwanta da suke cika da ruwan hawaye. Cikin kulawa da tausayawa yake kallonta ya sauke ajiyar zuciya cike da jarumta yace."Surayya nace ki daina kuka duk da yanzu yamma ce idan na fita Allah ba zai hana ni abinda zan siya miki littatafan makaranta ba saboda naga kin damu yasa na yanke shawarar fita ko Allah zai sa a dace."Hannu tasa ta share hawayen idonta tace."Baba Tausayin ka nake ji wallahi baka da koshin lafiya kawai ka koma gida ka zauna na hakura."Girgiza kansa yayi da murmushi a fuskarsa yace."Surayya ai tunda na fito ba zan koma ba sai na fita dama can ala dole nake zama a gida tunda yanzu naji kwarin jikina sai na fita watakila Allah yasa a dace."A sanyaye tace."To shikkenan Baba bari na tura ka bakin titin." Girgiza kansa yayi yace."Aa kin san bana so kina bina bakin titin nan wasu mutanan basu da uziri."A shagwabe tace."Na sani Baba yau d'aya ka bari na tura ka." Murmushi yayi yana girgiza kansa yanzu duk wanda zai ganshi da yarinyar tana turashi sai ya dauka bara sukeyi yasan bai wuce a bashi sadaka ba amma tunda Allah yasa yana iya sarrafa hannayensa to babu abinda zai gagareshi a yanda Allah ya halliceshi a haka yake so ya cigaba da bashi kwarin gwiwar sauke nauyin iyalinsa zuciyarsa a tsaye take sam bashi da kasala da nuna cewa shi din nakasashshe ne dole jama'a su taimaka masa.Idan yaga 'yan uwansa nakasassu suna yawo kan titi na suna bara da maula ransa yana baci mutuka shiyasa shi ya d'aura d'amarar neman halalinsa tunda Allah ya bashi rai da lafiya to nakasarsa ba zata hanashi aiwatar da komai na rayuwarsa ba.Cikin nutsuwa take turashi suna hira sai murmushi yake yana amsa mata. Wani matashin saurayi ya tare musu hanya.Surayya ta 'bata rai ta kallashi da fadin." Bawan Allah menene haka zaka tare mana hanya."Shahid murmushi yayi yasa hannu ya sosa sumar kanshi ya d'an risinar da kai da fadin."Baba barka da yamma." Malam Habu ya amsa kadaran kadahan sam irin wad'annan samarin basa burgeshi yafi san nagartattun mutane su nemi auran 'yarshi.Shahid ya jefe ta da kallon kauna yace."Surayya ya kwana biyu."? Gabanta ne ya fadi da sauri taja tsaki ta yi saurin tura keken suka barshi a tsaye a gurin. bayansu yabi da kallo yana murmushi shi dai Allah ya sanya masa kaunar yarinyar a cikin ransa.Suna kokarin karya kwana ta hango maigadin gidan...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.