25&26
MATSALAR MU A YAU!*
_(Labarin Surayya)_
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE🍒*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*
____________________________
*SADAUKARWA NE GA:*
_(Surayya dee🥰)_
FreePege
*25&26*
"Hajia Babu Fadila kwata-kwata a cikin tsarin rayuwata bana sha'awar auran zumunci dan Allah ki janye wannan kudirin naki." 'Bata fuska tayi tace."Babangida kaifa yanzu ba yaro bane ka kai matakin aure har ka wuce shekaru talatin da biyar ba kadan bane duk sa'onin ka sunyi aure amma kai kana zaune ko sha'awar auran ma ba kayi wai shin ko dai baka da lafiya ne."?
Girgiza kanshi yayi cike da damuwa yace."Hajia shi aure lokaci ne ki daina damuwa sannan ni lafiyata lau kawai lokaci ne beyi ba amma tunda kinyi magana yanzu zan fara duba matar aure amma inaso ki janye maganar Fadila dan kwata-kwata bana sha'awar auranta.
Tace."To shikkenan tunda kace haka yanzu zuwa wane lokaci zaka kawo min matar auran naka." Shuru yayi yana nazari tace."Kayi shuru kai nake saurare.'' Yace."Ki bani lokaci zan duba." Murmushin takaici tayi tace."Babangida wannan itace damarka ta karshe idan baka kawo min matar aure ba to babu shakka Fadila ce uwar 'ya'yanka."
Mikewa yayi babu walwala a tare dashi yayi mata sallama ya fita ta bishi da kallo tana girgiza kai tabbas idan ba tayi masa da gaske ba to haka zai ta zama babu aure duk ga abokanansa da 'ya'ya amma shi yana zaune.
Koda Maigidan ya dawo ta sheda masa hukuncin data yanke sai ya nuna farin cikinsa yace."Fadila yarinya ce mai tarbiya da nutsuwa kuma 'yar uwarsa ce akan ya fita ya dauko wata to gwara ya aureta.'' Cike da farin ciki tace."Nima abinda nayi tunani kenan sannan kuma zumuncinmu da 'yar uwata zai kara karfi." Alhaji Sabo yace."Kwarai kuwa Allah ya tabbatar da alkairi.'' Ta amsa da ameeen ya Allah.
*BAYAN WATA BIYU*
Shahid ya siya min waya kamar yanda ya fad'a kuma duk abinda ya samu yana rawar jiki zai kawo min hidima babu irin wacce ba yayi min Innah ta dinga bala'i tana fadin ita ta gaji da wannan shashancin bata neman fitina sai kawai na yanke shawarar a duk lokacin da Shahid ya kawo min wani abu bana shiga dashi gidan gidansu Samira nake 'boyewa wasu muyi amfani dashi wasu kuma mu siyar mu kar'bi kudin mu kashe.....Magulmata sukaje suka kai wa mahaifiyarsa gulma da irin facakar da yake min da kudi.
Iya Mari ta fusata ta kumbura yana shiga gidan ta rufeshi da fad'a ta inda take shiga ba tanan take fita ba yace." Iya Mari kiyi hakuri ki daina wannan fad'an maganar aure tsakanina da Surayya tayi nisa domin Baba ya sani kuma sun tsayar da magana da Babanta yanzu ana jira nan da shekara daya lokacin za tayi Candy sai a daura aure.
Ajiyar zuciya ta sauke tace."To yanzu naji magana ai na dauka babu wata tsayayyar magana a tsakaninku kake kashe mata kudi a banza.
Girgiza kansa yayi yace."Akwai magana mai karfi a tsakaninmu.'' Tace."To Allah ya sanya alkairi yanzu sai ka tsagaita dayi mata hidima ka fara kokarin gyara gurin da zaku zauna.
Yace."Inna Mari da inaso na fita na kama haya ne." A fusace! tace."Ashe baka da hankali Shahid yanzu duk girman gidan nan ka rasa gurin zama a cikinsa babu inda zakaje a cikin gidan nan zaka zauna kamar 'yan uwanka." Yace."To shikkenan Innah haka za'ayi." Abinci ta bashi ta zauna sai fada take masa shi dai abincinsa kawai yake ci yana gyada kansa inda sabo ya saba da masifarta.
****
Ganin yanda wasu da cikin 'yan ajinmu suka manta da abinda ya faru yasa nima na dauko White scret d'in dana siyo na fara laftawa a jikina da fuskata cikin ikon Allah sati guda fuskata tayi haske nayi ta murna ina jin dadi sai dai duk shafawar da nake a hannuwa da kafafu na ba suyi haske ba. Nace."Samira bana so fuska tayi haske jiki ba'ki kamar wata 'kazama.''
Dariya tayi tace."Sai a hankali ai kedai ki cigaba da shafawa ai baki da matsala tunda kina da Shahid." Murmushi nayi nace."Samira wallahi Shahid mugun tausayi yake bani sai ci masa kudi muke alhalin ba sonsa nake ba.
Tana dariya tace."Rabu da shashasha mara wayo kawai ai wasu mazan sune suke janyowa kansu suna da kudi iyayensu basu isa suci ba sai 'yan mata ni wallahi bana tausayinsa.
Nace."Allah ya kyauta dai kwana biyu bamu waiwayi Uncle ba yau mu rubuta masa text mai zafi."
Tace." To shikkenan me za'a rubuta."? Wayar na kar'ba daga hannunta ina murmushi lumshe ido nayi tare da saukar da ajiyar zuciya na fara rubuta text din ina jin wani zazzafan feelings a tare dani.
Bayan na gama rubutawa na mika mata wayar a sanyaye nace "Karanta." Ta karba da sauri tana dubawa.
Ta kalleni da mamaki a tare da ita tace."Ke Surayya ki goge wasu abubuwan kamar bai dace ba." Harararta nayi nace."Dallah ki tura masa ni babu abinda zan goge.'' Murmushi tayi tace."Surayya kenan wallahi ni abin ma dariya yake bani.
Tsaki naja nasa hannu da niyyar kwace wayar ta janye da fadin.'' Bari a tura masa tunda kince ba zaki goge ba." Ajiyar Zuciya na sauke lokacin da naga text din ya tafi nace." Tashi muje mu sayi abinda zamu ci." Wayar tasa a jaka ta mike muka bar gurin.
Lokacin da ya karanta text din sai da tsigar jikinsa ta tashi abinda ya kwana biyu bai Ji ajikinsa ba ya tashi Sha'awa mai tsanani ta tayar masa hakika text din ya tayar masa da hankali mutuka......Ga abunda yake rubuce a text din.
_Assalamu alaikum Habibi ina fatan kana lafiya to Allah yasa haka ameeen. Nice dai wannan mayyar mai nacin sonka da begenka ba zan gaji da fad'a maka cewa kai d'in kaine rayuwata dan kai aka hallice ni shiyasa yau nake so na tabbatar maka da cewar kaunarka da sha'awar ka su zasu zama ajalina Jiya nayi mafarki muna bargo daya muna rayuwar aure kana cikin biya min bukata na farka daga bacci yanzu haka ina cikin mawuyacin hali cikina sai ciwo yake mara ta tana ciwo Breast d'ina suna bukatar agaji daga gurinka tun asubah nake kwance ina murkususu saboda sha'awarka Mylov my heartbeat kayi wani abu a kaina kada na rasa rayuwata._
*Daga S-R-Y*
Cikin mutuwar jiki ya mika hannu ya dauki wayar text din yake nanatawa.......Da sauri ya mike yana bin harufan da kallo *S-R-Y* yau dai sai yayi binkice akan al'amarin.
Ya jima yana mamakin abin *S-R-Y* Yana nufin Surayya ya tsirawa kasan kafet ido yana nazari da tunanin akan yarinyar a iya tunaninsa yarinyar bata da wayon da za tayi wannan shaid'ancin yafi zargin wata Surayyan ba ita ba amma dai zai tsaurara binkice akan al'amarin.
Number ya kira yasa wayar a kunnansa....Lokacin muna kokarin shiga Class gabanta na faduwa ta nuna min. Naja hannunta muka 'boya a bayan bishiyo kar'bar wayar nayi nasa a kunnena amma banyi magana ba. Muryarsa ce ta doki kunnena na zabura! wayar ta kusa faduwa. shuru nayi jikina duk ya mutu.
Yayi gyaran murya da fadin."Surayya ko ba da ita nake magana ba."? Shuru nayi gabana na dukan uku-uku......Murmushi yayi sai naji wani yarrrrrr! na zube kasan ciyayi ina sake makale wayar a kunnena.
A hankali yace."Ina samun messages d'inki nagode kwarai kina wane gari ne."? Shuru nayi jikina sai kyarma yake...........Ya cire wayar daga kunnanshi yana dubawa yace."Surayya kina jina." ? Da sauri na kashe wayar ido jawur! na zuba mata ido. Tana dariya tace."Alhamdulillhi Nasara ta fara samuwa.'' A sarqe nace."Samira ina jin tsoron ya gane nice."
Tace."Ki cire tsoro kawata ai soyayya ba karya bace yanzu dai tunda har mun samu ya fara amsa mana sai mu sake zage dantse." Na mike ina karkad'e jikina nace."Gaskiya ne wallahi ba kiji farin cikin da nake ciki ba Samira nagode ke d'in 'kawar amana ce ina alfahari dake." Murmushi tayi tace "Muje kawai kada wannan masifaffiyar malamar ta shiga ajin.
Muna fitowa daga tsakanin ciyayi muka hangoshi can saman baranda da waya a hannunsa yana dubawa......Cikin sauri nace." Samira yi maza ki boye wayar hannunki ga Uncle can saman baranda.....Hannu na rawa take kokarin sanya wayar cikin jaka aikuwa ta fadi a gurin.....Cikin tashin hankali na kareta ta tsuguna da sauri ta had'e wayar tasa a jaka.
Duk abinda suke yana kallonsu kuma ya fahimci abinda suke 'boyewa abin ya bashi mamaki mutuka ashe duk tsaurin sa da jajurcewarsa akwai masu karya masa dokar makaranta Lallai sai ya kara tsaurara tsaro don ya lura masu bleaching sun dawo har da ita yarinyar da yake zargi duk da ba wani cikakken kallo yake mata ba amma ba haka ya san ta ba ita din baqa ce amma cikin kwanakinan ya ga fuskarta tayi haske lallai dukkaninsu zasu ci ubansu.
Sai da ya bari kowa ya sankankace ya saki jikinsa ya shedawa Uncle Bash abinda yake ayi Ranar litinin a gurin Assembly Uncle Bash yayi mana bazata gabadaya ya fito da mu mu kusan Talatin da bakwai aka taru a guri guda sai zazzare ido muke.
Ana tashi daga assembly ya tasa 'keyar mu zuwa ofis din mai gayya mai aiki.....Ni dai rasa bakin magana nayi ina jin sauran 'yan uwana suna ta surutai ko wacce tana kare kanta bakina ya mutu muna zauna muna jiran fitowarsa.
Tunda ya fito na kasa dauke idona daga kanshi yana sanye da kananun kaya wanda sukai masa mugun kyau as'usul kamar koda yaushe idonsa sakaye da farin gilashi ya dinga bin mu da kallo yana girgiza kansa wasu daga cikinmu har sun fara kuka suna bashi hakuri Uncle Bash yana tsaye a gefe da murtukekiyar bulala a hannunsa.
Babu walwala a fuskarsa da maganarsa yace."Wato kune gagararrun makaranta ko."? gurin yayi tsit!!! Ya cigaba da cewa." Anyi-Anyi daku ku daina abinda kuke amma saboda taurin kai kunqi shin wai don ubanku waye yake siya muku man bleaching ne."?
Kowacce tayi shuru yace."Na san dai da yawa daga cikinku samari ne suke siya musu ko ba haka bane."? Babu wacce tayi magana a cikinmu.
Yace."To yau idan akwai wacce ta shirya tayar da sarkin aljanu a makarantar nan ba zan fasa hukuncina ba." Ya kalli Uncle Bash da fadin." Bashir inaso da wannan bulalar ta hannunka ko wacce kayi mata ciki ashirin sannan ka kai su fuskar rana ka ajiye har a tashi.
"Uncle don Allah kayi hakuri wallahi mun daina don Allah uncle ka gafarce mu." Kujera ya nema ya zauna ya dora kafa daya kan daya babu fara'a ko ta kwabo a fuskarsa yace."Bashir ka fara aikin ka."
Uncle Bash ya murtuke fuskarsa ya gyara bulalar ta kan Samira ya fara ta dinga ihu! tana kokarin rike bulalar yana fuzgewa sai da yayi mata ashirin ciff! sannan ya fara laftawa ta kusa da ita.....Ofis din ya kaure da hayaniya da koke-koke da bada hakuri.......Ganin an kusa zuwa kaina sai hawaye suka kwace min na dinga sanya gefan hijabina ina gogewa jikina sai karkarwa yake......Ta gefan ido yake kallon duk abinda take ya dauke kansa tare da kokarin barin gurin.....Gurfana nayi gabansa murya na rawa nace."Uncle don Allah kayi hakuri wallahi ni bana bleaching haka kalar fatata take."
Ido ya tsira min fuska a had'e yace."Sakar min kafafu.'' Da sauri na saki dan ban san ma sanda na rike masa kafa ba.....Ofis d'insa ya bude ya shige abinsa.
Lokacin da Uncle Bash ya fara lafta min bulalar daskarewa nayi a gurin na takure jikina guri guda hawaye na zuba Uncle Bash a ko'ina duka na yake yi lokacin daya zabga min bulalar a kirjina na zabura da sauri na rike bulalar hawaye na karakaina a fuskata nace."Uncle Bash kayi hakuri ka dube fuskata da kyau wallahi sharri akai min bana bleaching. "
Ya fizge bulalar a zafafe! yace."Don Ubanki waye yayi miki sharri? ga zahiri nan fuskarki tafi jikinki haske sai naci ubanki yau." Ya daga bulalar zai zabga min na kurma wani uban ihu!!! na fad'i a gurin ina makyarkyata Uncle Bash ko a jikinsa ya zabga min bulalar hannunsa kan nonowana." Rintse idanuwa nayi ina kiran sunan Allah............... Hankalinsa a tashe ya fito ganinta a sheme a kasan gurin tana rike kirji sai hankalinsa ya tashi da sauri yace."A'ina ka dake ta ne."? Uncle Bash na huci! yace."Yallabai a jiki na doke ta kamar yanda na doki sauran 'yan uwanta."
Ya kalleni na sake lanjarewa a gurin ina janyo numfashi da kyar cikin kuka nake kiran wayyo kirjina zan mutu na shiga ukuna."
Hankalinsa gabadaya ya tashi ya kalleshi rai a bace yace."Ka doke ta a wani gurin da za kayi mata lahani ka san inda zaka dinga hukunci." Yace."Insha Allah za'a kiyaye." Hankalinsa a kaina yace."Kaje dasu ka basu horon dana ce." Da sauri ya amsa tare da kokarin barin gurin..........Ina kwance ina kallonsu ko wacce ta ta tashi tana matse fuska suka bi bayansa.
Ya kalleni da fadin."Tashi zaune." A raunane nace."Uncle ba zan iya tashi ba Kirjina ne yake zafi." Ya zuba min ido babu kiftawa. rintse idona nayi gabana na faduwa! maganarsa naji dab dani sai nayi saurin bude idona na ganshi tsugune a gabana ya k'urawa kirjina ido.....A zabure na mike zaune ina zazzare ido. harara ya watsa min da fadin." Kika ce ba zaki iya tashi ba." Shuru nayi ina kallonsa ya gyara fuska da fadin." Waye yake siya miki man bleaching...........!
*A taimaka da Shearing*
_*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_
*****
*****
*BINTA UMAR ABBALE*
*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE KU NEMI WANNAN NUMBER......._*
*22790899076*
*HAJIA FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*