Matsalar Mu A Yau

27&28

by @bintaumarabbale

MATSALAR MU A YAU!*

 _(Labarin Surayya)_


*NA*

*BINTA UMAR ABBALE🍒*

*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION🤝🏻*

____________________________


*SADAUKARWA NE GA:*

   _(Surayya dee🥰)_


FreePege

 *27&28*

Diriricewa nayi na fara inda-inda! ya buga min razananniyar tsawar da ta kusa sa fitsari ya kufce min murya na rawa nace."Uncle ka dube ni da kyau wallahi bana shafa man bleaching ni tun asali haka kalar fatata take.


Ya tsira min ido da bacin rai a fuskarsa yace." Don Ubanki! makoho zaki mayar dani kome."? Jin zagin daya kurma min yasa jikina ya mutu sai na sunkuyar da kaina hawaye na nema ya 'kwace min.....Ya cigaba da cewa." Kin raina Allah har kike rantsewa dashi ko."? Uffan ban ce ba sai kokarin mayar da hawaye nake. Yace."Zaki fada min wanda yake siya miki man bleaching ko kuwa."?


Murya na rawa nace." Babu kowa ni haka skin d'ina yake." Da azama! ya mike nayi saurin kallonsa gabana na faduwa naga ya dauko bulalar Uncle Bash. Da sauri na mike Tsaye ina zazzare ido jikin bango na makure Jikina hawaye kuwa kamar an kwance famfo murya na rawa nake bashi hakuri.


Rai a bace yace." Zaki fad'a min ko kuwa."? Hanci na shaqa cikin inda-inda nace."Saurayina ne sunansa Shahid." Ido ya tsira min. Nace."Wallahi da gaske nake shine yake siyo min kayan kwalliya." Babu sukuni yace."Ashe har kinyi girman da zakiyi samari."? shuru nai tare da sunkuyar da kaina ya girgiza kai cike da takaici yace."Babu mamaki tunda kina tare da wad'annan yaran marasa kunya zakiyi abinda yafi haka to wannan shine na farko shine kuma na k'arshe kada ki kuskura ki kara shafa man bleaching ki bar hallitar da Allah yayi miki  komai ba'ki da muninki ba zaki rasa mai auranki ba rashin wayo da dubara shine yake cutarku kuyi ta shafe-shafe saboda wai ku samu mazajen aure to wannan ba dabara bace  saboda haka ki kiyaye ni wallahi daga yau kada ki sake shafa man karin haske idan kuma kika sa'bawa umarnina sai nayi miki mummunan hukunci."


Cikin mutuwar jiki gami da dana sani nace."Uncle kayi hakuri don Allah insha Allah ba zan kara shafawa ba."


Hanya ya nuna min da hannu alamar na tafi....Da sauri na sanya takalmana nayi gaggawar fita daga ofis din.


Can bakin band'akuna na hangosu a gurfane hannu a sama fuskokinsu a idon rana da saurin gaske nayi nufin sanja Hanya wata 'yar ajinsu Samira ta gan ni ta nunawa Uncle sunana ya kira na dawo da baya yace."Zo don ubanki ki shiga cikin 'yan uwanki." Tamkar na kurma ihu! saboda bakin ciki naje nasa gwiwata a kasa tare da daga hannuwa sama kamar yanda sauran sukayi.



Ranar nan mun galabaita mutuka mutum kusan bakwai suka tada aljanu Uncle Bash ya rabu dasu sukayi suka gama suka tashi Sai da aka tashi sannan Uncle Bash ya kyalemu muka tafi gida tun daga ranar kowa ya kiyaye saboda Uncle ya tsananta da yawa ya hana bleaching ya hana zuwa da waya bayan haka ya kafa dokoki masu tsauri  yanzu karatu muke sosai babu wasa dan idan ka sake aka samu wani kuskure ta gurinka to kashin ka ya Bushe gurin Uncle Bash.


****

Muna daf da zana jarrabawar Nyco Shahid yazo min da wata magana raina a bace nace."Kaga Shahid ni don Allah ka kyale ni naji da abinda ya dame ni jarrabawa ce a gabana kai kuma kazo kana min wata magana nifa ko nayi Candy ba aure zanyi ba karatu zan cigaba dashi.


A sanyaye yace."Haba Surayya ya zaki karya alkawari kuma. Kada fa ki manta shekara guda mukayi dake a kancewa kina gama secondary za'ayi maganar aure amma yanzu sai ki sanja magana.


D'auke kaina nayi ina kallon hanya ni sam ba wannan damuwar ce a gabana ba burina kawai Uncle yace ya sona da aure. Yace."Surayya kinyi shuru baki ce komai ba alamu ya nuna kin amince na turo da sadaki  na.


Wani banzan kallo na watsa masa da fadin " Aa ni kada ka turo kowa na fada maka ba yanzu zanyi aure ba sai nayi degree. "


Murmushin takaici yayi yace."Surayya kenan kin san wahalhalun karatu kuwa? ko kina da wanda zai tsaya miki."?


Cikin Izzah! Nace."Eh Ina dashi ba kowa bane face Uncle Nura." Shahid ransa ya 'baci kishi ya rufe masa ido yace."Nasan zai tsaya miki kiyi karatu tunda shine Ubangidanki ai ina da labarin duk irin hidimar da yake muku  to ina rokon Allah yasa karatu kawai zai tsaya miki kada yace zai aure ki."


Naji kamar ya soka min wuka a makoshi ido jawur nace."To idan yazo zai aure ni don Allah ka hana aikin banza kawai."


Ya fusata mutuka yace."Ni kike zagi Surayya ashe dama baki da kunya  To wallahi sai na rama abinda kikayi min kuma sai kun biya ni hidimar da nayi muku.


Nace."Shahid duk abunda kayi mana babu wanda ya saka kai kayi niyya don haka babu wani abu da zamu biya." Girgiza kai yayi yana hura hanci ya dauko wayarsa daga aljihu yana danne-danne.................Malam ne ya karaso gurin akan kekensa ganinsu a tsaye cikin 'bacin rai yasa yace."Ina fata dai lafiya."? Hawayen fuskata nagoge na shige gida ba tare da nace komai ba. Ya kalli Shahid din da fadin." Me yake faruwa ne."? Shahid na hura hanci yace." Malam ina ganin girma da mutuncin ka amma yarinyar nan tana so ta janyo maka bacin rai." Malam yace."Kayi hakuri kayi min bayanin abinda yake faruwa.


Shahid ya sauke ajiyar zuciya yace............Tsaf ya kwashe duk abinda yake faruwa ya fada masa. Malam ransa ya b'aci  yace."Kayi hakuri kaji ko Surayya bata isa ta mayar dani 'karamin mutum ba kamar yanda mukayi magana da ita shekara daya data wuce ta tabbatar min da cewa kai ta za'ba a matsayin abokin rayuwarta to alkawari yana nan babu gudu babu ja da baya kaje ka cigaba da shirye-shirye." Shahid cike da farin yace."Nagode sosai Malamai Allah ya kara girma.'' Malam ya amsa da ameeen ameen ya tura kekensa domin shiga cikin gida.....Shahid kuwa cike da karsashi da kuzari ya bar gurun.



 Ban ta'ba ganin bacin ran Malam ba sai yau  yana shigowa gidan ya rufe ni da fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita. Ya cigaba da cewa"To baki isa ki mayar dani k'aramin mutum ba wannan yaro ke kika amince da auransa muka zauna da mahaifinsa mukayi magana sai yanzu kuma da aski yazo gaban goshi sannan zaki bijire to baki isa ba wannan aure sai an anyi shi."


Cikin kuka nace."Ni wallahi bashi nake so ba Malam kada kayi min auran dole." Innah ta bude baki tana kallona tace."Yanzu ke baki ji kunyar fadar wannan maganar ba."?  


Hanci na shaqa cikin dashewar murya nace."Innah ai kema kin san gaskiya a cikin al'amarin nan ina Shahid yaga sana'ar da zai iya aurena bashi da aiki sai buge-buge yak........Gwa'be min baki tayi tace."Ashe kin san bashi da sana'a amma idan ya kawo miki abin duniya kike kar'ba kina washe baki a gidan uban wa yake samo kudin."


Malam yace."Duk abinda zakiyi sai dai kiyi ba zaki mayar dani k'aramin mutum ba." 


Da sauri na mike na shige daki na fad'a saman gado ina kuka Wallahi ba zan ta'ba amincewa da wannan al'amarin ba ta yaya ma za'ayi nayi rayuwar aure da wani namiji ba Uncle ba na riga na sanyawa raina auransa insha Allahu sai Allah ya cika min burina.



Washe gari a makaranta na zayyanewa Samira duk abinda yake faruwa jikinta yayi sanyi tace."Surayya da zakiyi hakuri ki auri Shahid din watakila shine alkairi a tare dake tunda dai kinga duk wannan abun da kike akan Uncle be san ki nayi ba."


Cikin 'bacin rai nace."Samira kada ki 'bata min rai don Allah wannan wace irin banzar magana ce nifa na fad'a miki koda Allah bai bani nasarar auran Uncle ba to wallahi ba zan auri Shahid ba saboda haka kima daina wannan maganar."


Tace."To shikkenan Allah ya za'ba miki abinda yafi alkairi." Na amsa da ameeen da fadin." Ina fatan kinzo da wayar ki."


Tace."Nazo da ita amma ki bari a fita break sai mu samu gurin da babu kowa muyi abinda za muyi." Nace."Ni don Allah bani wayar na shiga karkashin tevur nayi abinda zanyi."


Tace."Surayya kin san yanzu Malamar English zata shigo kuma kin san halinta bata da mutunci." 


Tsaki naja da fadin." Kinga Samira idan zaki bani waya ki bani wallahi kwana biyu da ban ji muryarsa ba duk wani iri nake ji."


Girgiza kai kurrum tayi ta dauko wayar a 'boye ta bani ni kuma na fakaici idon 'yan ajin da sauri na shiga karkashin tevur............Number shi nasa ina kokarin kira Malama Sa'adiyya ta shigo a maimakon na fito sai na cigaba da abin da nake.............Muryarsa ce ta doki kunnune yana sallama had'e da kiran sunana." 


Shuru nayi ina lumshe ido wani irin a zababben feelings ne yake taso min........"Assalamu alaikum Surayya ko ba da ita nake magana ba."? A firgice! na d'ago kaina sai kawai na hangi wucewarsa ta window  sai da wayar ta kusa fad'uwa daga hannuna saboda tsabar razana! Kafin ma nayi wani yunkuri ya shigo ajin.......Gabadaya kowa yayi tsit! babu mai kwakkwaran motsi. Har yanzu wayar na mak'ale a kunnansa yana magana idonsa tsaye a gurin zaman ta. Ganin babu ita a gurin sai ya gazgata zarginsa. cikin nutsuwa ya cire wayar daga kunnansa ya fara tafiya zuwa gurin......Samira tamkar ta saki fitsari a wando saboda fargaba da tsoro ni kuwa ta tsakankani nake hango zuwan shi sai kawai nayi saurin sa wayar a cikin  breziyya ta nayi kwance a 'kasan gurin  ina rike ciki had'e da birgima a gurin..........



*A taimaka da Shearing👏🏾*




 *MAR'ATUS-SALIHA*

_(Itace Cikakkiyar Mace)_


*Saboda yawan Tambayoyi gami da neman shawarwari daga 'Yan uwana mata ya sanya ni bude Group na mussaman domin wayar da kan 'Yan uwana mata akan abubuwan da suka damesu Mussaman A gidajen auransu👫 Matan aure da masu shirin aure su na amince suyi rigstar domin samun damar sauraran abubuwan da za'a gabatar a cikin Group din. Bayan haka akwai Magunguna na hausa masu kyau da Inganci!*

1- Maganin Sanyin mara

2-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba

3-Maganin Sanyi mai sa warin gaba da fitar da ruwa

4-Maganin Sanyi mai sa bushewar gaba

5- Maganin Sanyi mai hana Sha'awa

6-Maganin Sanyi mai hana haihuwa

7- Maganin Sanyi mai sa zafi gurin saduwar aure (sex)

8-Maganin Basir mai tsiro

9-Maganin Basir mai kulle ciki

10-Maganin Karfin Maza(Gurin Sex)

*11- Maganin Karin Ni'ima

12- Maganin K'iba mai kyau

13- Maganin Cikar Nono (Breast)

14- Maganin Hips

15-Maganin kurajen fata da hadin sabulai masu kyau da inganci!

16- Maganin Matsi mai kyau

17-Maganin Sanyi mai sa budewar gaba

18-Maganin kara karfin sha'awa da dade wa gurin (Sex)

19-Maganin Basir mai sa yunkuri da budewar gaba



*_Duk Zaku samu wannan magungunan Cikin farashi mai sauki Kuma babu algus da almundahana a ciki sai da mukayi binkice muka tantance sannan Kada kiyi kokwanto ko shakka akan ingantattun magungunan mu Insha Allahu idan kin gwada sai kin neme mu Hausawa suka ce siyan nagari mai da kudi gida Ga masu bukatar suyi rigstar da Group na MAR'ATUS-SALIHA sai suyi min magana ta WhatsApp da wannan number._*

*****

*1k Rigstar da Group din MAR'ATUS-SALIHA*

Accont.....0542382124.....Binta Umar gtbank....Idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp





 _*GA MASU BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP #400 VIP #600 ACCONT.......0542382124....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZA'A TURO AYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBERS ZAN FA'DI YANDA ZA'AYI*_

*****

*****

*BINTA UMAR ABBALE*


*_MUTANAN NIJAR IDAN KUNA BUKATAR LITTAFIN NORMAL GROUP DALA DARI VIP GROUP JAKKA DAYA KATIN AIRTAL KO ORANGE  KU NEMI WANNAN NUMBER......._*

*22790899076*

*HAJIA FATIMA MUSA  (MOMMY NIJAR)*