ZAYN MALIK

Chapter 7

by @maidambu41

_....ZAYN MALIK....✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

  

       Mai_Dambu

CHAPTER-7

*Allah ya saka da alkhairi naji dadin yadda kuka amshi labarin nan 😍🔥🤌🏽*

Wani b'ata rai yayi domin ya fara gajiya da halin Hajiyar shi.

"Hajiya wallahi bayan ke da Mama ban tab'a kallon kowa da wata fuska ba, Hajiya iya yarda da kika min shi ne garkuwa na, idan baki yarda dani ba waye zai yarda dani? Hajiya ina gaban ki ne domin na gaya miki gaskiya bana karya, domin bana tsoron kowa sai Allah hajiya tsoron wani bai saka nayi karya duk duniya abu daya nake yi shine ina shan wiwi ban gaya miki dan ko d'aga hankalin ba sai dan ki gane cewa bana wuce iyakar Ubangiji, shima wiwi zan rabu da shi while Time"


Hawaye ne ya zubo mata cikin tsannanin kaunar shi ta ce mishi.

"Me zai saka naki yarda da bawan Allah irin ka? Me zai saka na juyawa maganar ka baya, Allah ya san me yasa ya shirya a rayuwar yaron da bai san kome ba sai iyayen shi kayi farin cikin abinka" ta fada tana shafa kan shi, duk cikin jikokin ta Allah ta daura mata kaunar Zayn shine bai tab'a daukar abinta domin ya cuce ta ba, idan yana son abinta kai tsaye yake dauka, kuma akan idanun ta, Zayn hatta uban shi bai cuta ba balle uwar shi.

Dan haka tun daga Kuruciyar shi ta taso ne da kaunar halin shi, mijin Sadiya ya tab'a mata duka, lokacin yazo hutu wallahi yaron nan ya bishi har inda yake ya damfara shi da kasa, ya kuma d'ago shi ya ce mishi.

"Ahalin idan suka zubda hawaye ji nake kamar ana sheka min ruwan tafasheshen dalma, idan suka yi dariya ji nake kamar an min bushara da aljanna ya zaka ji idan na karya kafarka na bar ka tayi jinyar ka, wawa me dukan mata kawai." Wai a lokacin bai gama secondary school ba kenan yanzu da zai shiga jami'a yake nan

Wa shi gari ya dauki Hajiya da Mama da Aunty Fatima suka tafi sayayyan tsaraba.

Tun a hnya Hajiya ta fara kokarin takolo shi.

"Zainu wadannan mutanen suna cin abinci kuwa? Don Allah dubi wancan yarinyar ta saka takalmi kamar me shirin tab'a gajimare, anya da kashi a jikin su?"

"Hajiya akwai mana kamar ke haka suke ji fa"

"Kai rabani da shiga uku fitar takaba da molo, yau ga duniya karen ma abun yawo ne cikin gari Zainu anya akwai masalatai a garin nan?"

Juyawa yayi ya kalle sannan ya ce mata.

"Hajajju akwai mana." Ya bata amsa.

"Hajiya yaushe kika fara aikin jarida bamu da labari?" Inji aunty Fatima.

Juyawa tayi ta ce mata.

"Zainu kaji yar Uwarka tana cin mutuncina idan isuhu da kuluwa suka haife ni bani kuma magana"

Danne dariyar shi yayi har sun kusan zuwa mall din ta hango wata tsohuwa sanye da hill cikin mamaki ta ce.

"Zainu ita wannan bata tsufa bane? Yau naga duniya a inda ake cinta da tsike salon ta fadi ta karye ta bar Yara d jikokin salatin amada."

"Hajiya amma cewa kika yi baki kuma magana" wani irin bata rai tayi sannan ta ce.

"Da ubana idan na kuma magana suna na ba hali Dubu ba" a hankali ya shiga parking spaces da yake mall din, sannan ya bude motar suka fito.

"Ikon Allah yau naga duniya Zainu ai nan mutum ya shimfida taburman shi ya kwanta kaga wai wurin ajiye mota ne, gaskiya nasara bai yi ba!"

Bai ce mata kome ba can tace mishi.

"Zainu da alamu ana son farraka mu, idan na koma zan aiko maka da kaikaiyi koma kan mashikiya ya kashe duk wanda zai shiga tsakanin mu"


"Kisan kai? Hajiya rai ne fa" ya fada mata suna tafiya.

"Toh meye a cikin shi ni da za a raba ni da kai fa"

Ta fada tana bata rai ita nan da gaske raba ta za ayi da jikan ta, kuma duk wannan maganar da take na za a shiga tsakanin su ba da kowa take ba sai da Mama, ita kan murmushi take dan Hajiya bata mata abinda zata ji haushi ba, ita kanta da take uwar Zayn tana wallahi ba zata nunawa Hajiya kaunar Zayn ba, domin tun yana tsumma Hajiya babu inda bata kai shi wurin masu magani ba, na Hausa da na Yarbawa, har na iyamurai da Gwari da nufawa sai da ta kai shi, gashi lokacin yayi mugun farin jini duk yaran gidan babu farin fata irin shi, haka tayi tai ta sawa ana mishi lauhula maganin baki, tun Zayn na wata shida ta bashi dadauri wani hadin itacce marasa iyaka wanda yake sawa yaron taurin kai da fada kamar me ga ƙara lafiya kamar an mishi wahayin lafiya, tun yana dan karamin shi yake buga yara da kasa har yau gwara ma yanzun da ya girma. Baya fada sai dai yana tare da ahalin shi baya kaunar dukkan abinda zai tab'a su.

Koda suka shiga mall ɗin ya mata sayayya nan ma kawai sai da aka kusan kai ruwa rana ita da Aunty Fatima, kafin ta hakura da magana, shima tayi shiru ne dan Zainu ya ce mata.

"Hajiya ba girman ki bane kula Aunty Fatimah ita Damuwar ta, ta haɗa kafada da ke ne bayan kin wuce ajin ta." Kallon Aunty Fatima tayi ta dauke kai dan bata son Aunty Fatima ta kuma niman renata.


Haka suka gama yana lallaba ta, har suka dawo gida, dafe goshin sa yayi domin yau yasha fama da hajiya.

Wa shi gari guduwa yayi Uncle Bashir da kan shi ya dauke Hajiya suka tafi yawon bude idanu,basu dawo ba sai bayan la'asar likis, suna dawowa Hajiya tayi tsalle ta dira.

"Ni yau ba zan ci shinkafa ba kamar wata mara galihu da Ubana Isuhu ba zan ci ba"

"Toh Hajiya Kiyi hakuri shinkafar tuwon ce ta kare na manta ban gayawa Maman Zayn ta tawo min da shi ba."

"Ai fa sai dai ku ci wallahi da Ubana ba zan ci ba, duk abinda za ku yi sai dai kuyi"

Wato ita dai Hajiya wannan da Uban ta ba zata ci ba ya zame mata kamar wani rantsuwa idan ya buga shi toh wallahi ba zata yi abu ba, dan sai ta yi wallahi tayi abu amma idan tace da Ubanta Isuhu bazata yi ba, toh fa ba zata yi ba sai dai Zainun ta ya karya mata rantsuwar ta ta hanyar rarrashi. Dan haka Aunty Rukayyah ta kira uncle Bashir ta gaya masa shi kuma ya kira Zayn ya gaya shi, kamar baya zunduma ihu haka ya shiga tambyar, ya samo African restaurant, can wajen Boston shi da abokin shi da su Anita suka tafi, ya sayo mata kusan dalar amurka dari uku da wani abu, yana kawowa bai yarda da je gidan ba yasan rike shi zata yi dan haka ya tura mata dan makotan su William. Koda Aunty Rukayyah ta juya mata tuwon miyar kubewa kallon tuwon tayi kafin ta kalli Aunty Rukayyah ta ce.

"Ya ga tuwon kamar sakwaran shege? Ji don Allah abu tikirkir kamar an jefe dan banza gaskiya a dumama min tuwon nan idan naci haka zai zauna a cikina ba zai narke ba."

Ta fada tana ture tuwon, Mama ce ta dauka ta nufi kitchen da shi tana me juyewa a tukunya.

"Gaskiya wallahi shi yasa nake son Tabawa domin kaf masu girkin da Talatu take nimowa babu irin tabawa, Matar nan ta san kan duniya a girki"

"Hajiya yau kuma tabawa kike yabo nan kikace an kawo ta dan ta kashe ni ne da cika yaji da gishiri a miya!"

"Toh zugazigi ban san kina yi ba sai kin rufe ni da duka mutum da bakin shi ba za a bar shi yayi magana ba, yabon ta nayi ai ba zagin ta nayi ba kodan na.kira suna uwar ki ko? Zaki nuna min feleke har da su kaza a cin danko toh ɗan uban mutum na fada tabawa an daukota ne dan ta kashe ni"

"Allah ya huci zuciyar Amaryan Zainu Malami"

Wani dauke kai tayi tana faɗin.

"Salon kinibibi nayi magana a fini a baki, toh wallahi ba a fini a tsumma ba, ba kuma za a nuna kwarkwata ba. Aikin banza idan ma dan tuwon da kika gani ne yawun ki ya tsinke toh da Ubana ba zan ba yar ba, idan na bayar shegiya Uwata ta haife ni"

"Hajiya Umma meye na zagi Allah ya baki hakuri ba dai tuwo bane ci abinki idan kika cinye zamu dawo daidai, abinda wani yaci shine rabon ka wanda kaci kashi ne"

"Rukayyah kina jin Fatsuma tana gaya min maganar banza. Wallahi idan na kwana a gidan nan ba Isuhu da Kulawa suka haife ni ba."


"Fatimah bana son haka hajiya kiyi hakuri."

Aunty Rukayyah ta fada tana hararan AUNTY Fatimah.

"Ni da gidan dana ana nuna min iko gara na bar gidan nan ai na jima da sanin kaf cikin jikokina Zainu ne kawai zai rike ni dan haka zan bar gidan Bashiru na kama haya;"

"Kiyi hakuri Hajiya " Mama ta fito sa Abincin ta, ya Juye mata a bowl.

"Wai wai! Sannun talatu kin ga yadda yake hayaki kamar an kara dafa shi, da an kawo abu kitikir kamar mugudumurki, bari naci kafin yan baƙin ciki su kwashe min kurwan shi "

Haka suka yi ta fama da hajiya a Boston kafin Zayn ya lallabata ta dawo Nigeria da sharadin duk hutu sai yazo, cikin matukar gajiya da halin ta ya ce mata.

"Toh naji "

*

Haka kuwa ya kasance sai dai a nan Kaduna ana yawan shi dakin Alhaji AbdulMalik Zain Malami ana mishi sata bai tab'a magana ba sai da Zayn ya dawo hutun shi na farko, anan aka shiga aka yi mishi wani satar renin hankali, kudi yazo da shi kusan miliyan talatin zai kai banki amma dare yayi dan haka ya saka a dakin shi.

Abun haushi haka aka dibi kusan miliyan biyu,

Koda yazo yana cigiyar kudin Hajiya Umaima tayi tsalle tace za ayiwa Muhideen sharri, abin ya mishi ciwo, yasan halin yaran shi kaf, musamman Zayn da baya kasar amma bai tab'a mishi sata ba, domin duk zuwan shi idan yazo da kan shi yake bawa Zayn ajiya kuma yazo ya karbi babu abinda ya samu kayan, sannan daga Samir Sagir, har Muhideen babu wanda yake son ganin cigaban shi, domin kiri-kiri yaran basu kaunar abinda zai saka ya cigaba, amma bangaren Zayn da kan shi yake gayawa Uban yadda zai kara fadada arzikin shi, yana yawan gaya mishi aikin gwamnati na wani lokaci ne amma idan yana da kamfani zai taimakawa Al'umma da kuma cigaban shi.

Dan haka baya zargin shi, gashi Hajiya Umaima ta birkice za a yiwa Yaran ta sharri, sai ya barwa Allah ya nemi kudin ya cika domin kudin ba bashi bane.

A haka Zayn ya gama kwanakin shi dake yana Jami'a, inda yake karanta biochemistry, bayan ya koma ne aka kama Muhideen sun shiga gidan wani Baban abokin su, sun kunduma sata, ai kuwa har gida aka shigo aka ɗauki Muhideen a gaban Uwar shi, tana ihu da kuka.sharri aka mishi aka tafi sa shi.

Dakyar aka fitar da shi domin har an tura shi gidan Yari, sai da Uncle Bashir yazo ya shiga case din, aka rufe sunan Muhideen, tun daga nan ne Hajiya Umaima ta kullaci Zayn tayi alwashin sai ta hana shi Moran kan shi sa duk wani na kusa da shi.

    Haka ya gama jami'a ya fito da first class.

Ya dawo, yai hutu tare da bude shafin iskanci da tsula tsiyar shi son ran shi, ganin haka Abban shi ya kuma tura shi ya karo master, dakyar ya gama domin a lokacin sam yake jin tsanar duk wani cigaban shi, sai da Umma tayi da gaske ta hana kan ta barci, ta shiga sakawa ana sauke mishi Kur'ani, da yanka dakyar ya nutsu domin yadda aka so ta lalace ba karamin abu bane sai ya kare da bin yan siyasa da jagalinyanci, ganin haka yasa ya samu Umma da maganar ya tafi aikin soja, lokacin baki daya shekarun shi shekarun shi ashirin da wani abu. Rimi Rimi

Akayi da Kuma ya tafi soja, kamar su gaske har ya tafi matar nan ta kasa hakuri ta fara cewa ita kan a dawo da shi ta fasa ya dawo haka aka yi ta fama da ita, har ya gama training din shi na farko ya tsalleke ya shiga ba uku, ganin kwazon shi suka tura shi sashin kwararru akan sinadirai na hada bom da harsashi. Yana dab da isa matakin da idan ya gama zasu bashi babban matsayi na me igiywa uku, kawai Hajiya ta sashi ya dawo, dan dole ya ajiye aikin soja ba wai dan yana ra'ayi ba, domin shima ya fahimci kamar nan ne ya dace da rayuwar shi, a can hukumar dakatar da shi domin basu yi niyyar rabuwa da shi ba, dan haka suka ce sun dakatar da shi duk lokacin da ya dawo suna maraba da shi.

Ganin Lokacin da Zayn ya dawo yasa Hajiya Umaima ganin ai koran shi aka yi a soja, dan haka tayi ta murnar.

Abun farin ciki har da. Habaici da mugun alkaba'i babu irin wanda bai gani ba, shi kuwa yace dan maganar mutane ba zai saka ya koma aikin soja ba, sai Hajiya da kanta tace ya koma aikin soja.

Ita kuwa tace ba zata tab'a cewa ba ya zauna suyi ta kallon juna, haka tafi musu da a tura shi aikin soja a kashe mata jika.

WANNAN SHINE LABARIN ZAYN DA HAJIYAR SHI..

#Paid