Burin masoya

Part 2

by @kwalisa

          ***

Ta shigo da sallama a hankali ta nemi kujera ta zauna cikin jin nauyinshi ta gaishe shi ba tare da ta dubeshi ba, ta zubawa jar dardumar da ta mamaye xan madaidaicin xakin idonta, akwai manya kujeru bakwai sai wata qatuwar kanta cike da littatafain addini birjik kala-kala.

Abdul ya dubeta cikin wani salo ya yin da ita ma ta kai idonta kansa suka yiwa juna murmushi, Abdul ya ce “Ashe haka kike da jin kunyar tsiya?” Bata ce komai ba sai xan murmushi ya ci gaba “Za ki yi mamaki na ko? Na san wallahi na sha giyar qaunarki na bugu sosai, ban tava ganin abinda ya shigar min rayuwa, zuciya da jini ba tamkarki, kasa haquri na yi yau nace bari in yi kasada da qundubala, inyi shahada domin irin yadda qaunarki take azabtar dani bana iya bacci ko kaxan, ga idanuna sun bushe sun qone, qaraf daga samun barci ko yaushe ina cikin yinwa da qishirwa qaunarki sam na kasa control xin zuciyata a kanki, idan har ban xora idanuwana a kanki ba, wallahi ji nake tamkar na mutu na huta da baqin cikin da zan shiga a rana” Ya sassauta murya yace.

“Don Allah Fauziyya ki ji qan rayuwata tabbas ubangiji ya jarrabeni da tsananin qaunarki, wanda ba zan iya misalta ta a yadda nake jinki a raina ba, don Allah ki ce kina qaunata”.

Ta yi shiru zuciyarta tana bugawa da qarfi kamar zata keto qirjinta ta fito, halitaccen ciwonta ya soma tasowa yana mamaye zuciyarta lokacin xaya ta dinga fidda numfashi a hankali anan take ta xago kanta ta dubeshi idanuwanta suna cike taf da qwalla ta cije bakinta ta kasa furta komai, Abdul ya taso a hankali ya zo kanta ya tsaya ya tsura mata ido yana kallonta, zuciyarsa cike da karayar rashin samun nasara, a take ya ji hawaye yana sulmiyo mashi akan fuskarshi a hankali ya sulele ya tsugunna a gabanta ya zuba mata idanuwanshi haxe da girgiza kanshi a hankali ya riqe gefen hijabinta cikin raunananniyar muryarshi ya furta “Ba kya qaunata ko Fauziyya?” A hankali ta ji gabanta ya faxi ta tuno da alqawarin data xaukarwa kanta da hanzari ta yi fatali da wancan tunanin nata sannan ta kalli Abdul a hankali ga mamakin ta sai taga yana hawaye , yanayin fuskarshi kaxai ya isa narkar da tata zuciyar, ta ji wani bala’in tausayinshi itama bata san sanda wani siririn hawaye ya sulalo mata ba, cikin rawar murya irin ta mai tsananin tausayawa ta ce “Ina qaunarka kuma na amince da kai” Ta yi shiru tana dubanshi shima ya saki murmushin sannan ya goge hawayenshi da gefen hijabinta ya kalleta da yin murmushi ya ce “Na gode Allah ya saka miki da alheri, Allah ya mallaka min ke a matsayin matata ta har abada, don Allah ki ce amin koda a zuciya ne” Yana kallonta ta sunkuyar da kai sannan ta ce “Amin” a hankali ya yi ‘yar dariya jin daxi ya koma kan kujera ya zauna yana cike da farin ciki fal a ranshi a hankali ya furta “Allah ya sakawa Abban ku da alheri dattijon qwarai gaskiya yau zan yi isashen bacci dana daxe ban yi shi ba, na gode Fauziyya” Ta miqe tace.

“Zan koma gida kaga dare ya yi” Shima ya miqe ya tsaya a gabanta yana kallonta, har taji ‘yar kunya hakan ya sa ya yi murmushi yace “Allah bana gajiya da kallonki, ina haqiqancewa jininki aka xebo aka gauraya da jinina ko?” Ya dubeta a cikin qwayar idonta cikin jin kunya sosai ta sunkuyar da kai tana murmushi da haka suka yi sallama, sai daya rakata har cikin zauren gidan ya ga shigarta cikin gida sannan ya fito ya haye babur xinshi motobi sabo fil ya tafi cike da farin ciki da gamsuwa da abar qaunarsa.

          **

Cikin xan taqaitaccen lokaci Abdul ya mamaye, xaukacin ‘yan uwanta kowa da kowa ya san Abdul irin tsananin damuwa da nuna qaunarshi a gareta yasa Fauziyya ta dinga tausaya mishi a hankali tausayin ya juye qaunarshi, don haka ta sakankance da shi ta rungumeshi da gaskiya, tayi ammana tare da cikakkiyar gamsuwa da shi, Abdul bashi da wani buri kamar ya buxe idanunshi ya ganshi tare da Fauziyya a kusa da jikinshi, a kullum zancen shi kenan na cikar burin masoyi.

Haka zalika ya xaukarwa kanshi hidimominta kala-kala, kullum suna cikin jayayya da ita akan irin wahalar da yake yi akanta akan sun yi yawa, hakan yana bala’in vata masa rai, qarshe ma idan ta fiye matsa mishi akan maganar fushi ya yi da qyar take samo kanshi ya huce.

Baban su ya yi iyakar duk bincikenshi akan Abdul da mahaifinshi,ma sha Allahu ya samu dukkan cikakken sakamako da shaida mai kyau kamar yadda ake buqata dukkan mutum na qwarai.

Yawaita wahalhalu da hidimomin da Abdul ya ke ne yasa Babansu ya yi kiranshi ya tsawatar mishi, Abdul marairaicewa Abban Fauziyya ya ce “Baba in har abinda na yi bai savawa shari’a ba ina ganin ban yi laifi ba, domin duk abinda na yiwa Fauziyya ina yi mata daidai qarfina kuma na tabbata ban faxi ba, domin qaunarta a raina wani abu ne daga rabi izzati, sannan mutuncinta da darajarta gareni ta isa na yi ninkinki ba ninki abin da ya fi haka ma domin ta cancanci hakan daga gareni”.

Abban Fauziyya yace “To Abdul na ji hanzari ka amma abinda zan nuna maka anan shi ne wasu abubuwan ka ragesu idan Allah ya sa ta je gidanka to ko mene ne sai ka yi mata domin haqqinta ya koma kanka, bana son kuma tun yanzu ka saba da irin wannan tarbiyar”.

Abdul ya ce “To, na gamsu da bayaninka na gode Allah ya qara girma”.


A cikin watannin su na shida Abdul suka shiga cikin watan azumi Abdul ya dinga tsananta addu’a akan Allah ya cika masa burinsa na mallakar Fauziyya, yana cikin farin ciki da nishaxi da kwanciyar hankali duk sanda ya je wajen Fauziyya, sai ya dinga yi mata magiya kenan, akan ta bashi dama a zo yin maganar auren su, ita kuwa sai ta marairaice tace ya bari zuwa xan lokaci kaxan su sake fahimtar junansu hakan yakan xaga hankalinsa sosai a ranar da qyar yake barinta ta tafi gida ya dinga damunta da sambatu buguwa da tsantsar shauqin begenta, wani lokacin idan yana rarrashinta har qwalla yake fitar mata abinda ta tsana ta gani kenan, a qarshe ta yi masa alqawarin bayan sallah ya turo magabatanshi akan maganar aurensu.

Ranar jajibirin sallah Abdul ya zo sai da ya turo yaro da wata qatuwar leda, Ummi ta ce Maimuna ta kai xakin Abban Fauziyya ta ajiye a can, sannan Fauziyya tana kicin tana aikin miyar sallah, Ummi tace ta je ta faxa mata Abdul ya zo, sai data xan vata lokaci saboda jin nauyin Umma, Umma da kanta ta shiga kicin tace “Ke ba kiranki ake yi ba? Kin bar mutum a zaune yana yana jira ai ba daxi” Bata ce komai ba sai ta fice taje ta wanke hannunta da sabulu ta koma xaki ta sako wata atamfa koriya England.

Saboda waxan can akwai warin hayaqi a jiki, da yake xakin babba ne, sai ta xauko wani siririn koren gyale ta yafa akanta ta xan shafa turare kaxan, yadda sai ka je daf da ita zaka ji qamshinsa ta fice can wajen Abdul.

Ta sameshi a xakin a zaune sanye da wata riga da wando na koren jins shima ya haxe sosai suka dubi juna suka yi murmushi. Abdul ya ajiye wani littafi mai kama da dary da yake dubawa a gefenshi, sannan ya tattara hankalinshi a kanta, ya kafa mata idanunshi a hankali ya furta “Gaskiya yau kinyi kyau, Allah ya bamu baby mai kyau da tsari kamar Mominta, don Allah ki ce amin ni gani nake yi ma azumin nan yaqi wucewa da wuri kullum a cikin lissafin kwanaki nake,don Allah Fauziyya ki tausaya min ki rage kwanakin nan, wallahi wallahi kullum ina cikin ximuwa rikicewa da fargaba da azabtuwa da begenki a dole na zama kamar mahaukaci. Na dami Alhajina da zancen ki shi da kanshi yana tausaya min, kullum dai zancen Fauziyya, ki yarda da ni qaunar da nake miki qaunace marar iyaka wanda ba zata tava qarewa ba har abada” Ya xan tausasa murya yace “Barina a kowane second ko qiftawar ido in ganki a jikina kina tare dani, domin a kowane runtsi idan na buxe idona, ko ina barci babu abinda nake tunani a cikin ruhina face na mallakeki a matsayin matata, na tabbatar da ana mutuwa a dawo duniya saboda farin ciki to wallahi ni na haqiqance zan iya mutuwa in dawo saboda tsabar farin ciki” Ya raunana murya cikin salon nuna qaunarsa qarara “Fauziyya” Ya raunana murya cikin salon nuna qaunarsa qarara “Fauziyya! Fauziyya! Fauziyya! Don Allah ki riqe ni ki rungume ni na daina shan wuya kin ji, domin qaunarki a gareni matuqar kika sakeni na faxi wallahi mutuwa tafiyen alheri, Fauziyya ki tausaya min don Allah ban san yadda zan yi da qaunarki ba a raina” Shiru ya sa tafukan hanayenshi ya kulle fuskarshi shi kaxai yasan abinda yake ji a ranshi, shiru babu wanda yace komai zuciyarta tana narke da tsananin tausayinshi, haqiqa zata iya kiran qaunar Abdul da wata jarrabace daga Allah ina ma yadda yake jin tsananin qaunarta haka itama take ji a ranta a game da shi? A yanzu ta daxa tabbatarwa tausayinsa ne yake daxa rinjayarta zuwa faxawa kogin qaunarshi zuciyarta raunananniya ce abu kaxan yakan bata matuqar tausayi harma ya sakata kuka, bare kuma irin kalaman da yake yi mata masu tsima zukata dole ne ta rungumeshi ta riqeshi ta tallafa masa, saboda matuqar ta barshi wallahi alhakinshi ma kaxai zai tambayeta. Bata Ankara ba sai ta ji hawaye yana fita idanunta itama sai ta samu kanta tana mai cike da tsantsar tausaya mishi ya daxa ya daxa fantsama ya mamaye dukkan zuciyarta, sai da suka xau minyina a haka sannan ta yi qarfin hali ta goge hawayenta da gefen gyalenta, cikin murya mai kyarma ta ce “Abdul kar ka tava tunanin zan iya yaudararka ko in canza ra’ayina gareka, ka tuna Abdul kaine zavina kai ne zavin mahaifina, zuciyata ta amince da kai a matsayin abokin rayuwa, insha Allahu zan kasance mai qoqarin gaske don kyautata rayuwarka da faranta maka zuciyarka, na amince da kai na amince! Da kai, na yarda zan riqi amanarka har abada kuma na sallama maka kaina, a gobe ma idan har ka shirya ka iya turo da iyayenka wajen Abbana”.

Ya xago idanunsa yana dubanta,idanunshi sun canza yanayi alamun kamar ya yi kuka ne, ya yi murmushi ya ce “Kin amince har ranki?” Yana kallonta ta xaga masa kai alamar ta amince, ya miqe tsaye ya xan shasshafa sumarsa sannan yace “Kin ban kyakkyawan guzuri yau,wanda zai tallafa min in yi barci da mafarkin kyakkyawan qwayar idanunki Fauziyya, ke ce amanar zuciyata” Ya zo wajen da take ya tsugunna a gabanta haxe da yi mata wani salon kallo idanuwanshi qasa-qasa a hankali yace “Ki faxa min wani abu dazan je in yi ta tunaninshi a raina” Cikin jin kunya ta yi murmushi taja gyalenta ta rufe idonta tace “Don Allah Abdul ka qyaleni haka nan” Ya yi ‘yar dariya ya girgiza kanshi yana duban yatsunta da suka sha qunshi ya yi jaja-jaja baqi-baqi akan farcenta a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya miqe yace “Shi kenan zan wuce gida, na gode yau gobe a yi min tanadi mai kyau” Ta yi dariya itama ta miqe tace “To sweet dream” ya yi sauri ya sha gabanta ya tsareta da idonshi yace “Repeat again muryarki kaxai tana kaxa min jinin jikina tasa na xauke wuta, ina jin daxin slow voice xinki, don Allah ki kuma faxa ko zan ji sanyi a raina”.

Ta rufe bakinta da gyale tana dariya, sai da ta ga ya shagala da kallonta sai ta shammace shi ta bi ta gefenshi ta gudu cikin gida da jin daxin da farin ciki. Zuciyarta tayi tas a ranar kwana ta yi da tunanin kalamanshi.

         **