Rumanah (Zabin Iyaye)

13

by @shooly84

...Rumanah🕊️

 (Zabin Iyaye)







©️ Aisha Machika







*Page~13*







Tunda safe nayi fitsari na zuba a kwalba, bakwai na safe sister Aina'u ta zo na bata taje tayi mani gwajin ciki, asabar ce ba aiki dan haka Saraki na É—akinshi kwance, haka nan cikin dauriya na haÉ—a kalacin safe, ma'aika sun É—auki nasu, kofin tea ne a hannuna ina juya shi na kasa sha saboda tunanin amai, Jamila ko har tayi nata ta shirya ta tafi gidansu sai yamma tace zata dawo.


Ina nan zaune Saraki ya fito sanye da Ć™ananan kaya, bai kalleni ba balle insa ran zai man magana, dan dama yanzu ya dawo da miskilancin shi, idona na kanshi, ya buÉ—e flacks É—in kunun gyaÉ—a sai naga yayi saurin rufewa ya zuba ruwan zafi, tea ya haÉ—a ya sha da bread, raina ya baci sosai domin da Ć™yar na dama mashi kunun dan rashin son Ć™amshin gyaÉ—ar, amma shi ne yanzu ba zai sha ba, bana iya shiru sai naji dalilin rashin shan, nace Saraki kunun ne baiyi maka ba? Ba tare daya kalleni ba ya bani amsa, bana ra'ayin sha ne yau, saboda me? Haka nan, Saraki kasan ko yarda akayi na dama shi? 


Ya kalleni a wulaĆ™ance, ina ruwana da yarda kikai, ko nace dole ki dama ne? Zuciyata tayi mani zafi kamar inyi mashi rashin kunya, wata zuciya ta haneni domin koba mijina bane amatsayin yaya na yake, nayi murmushin bacin rai nace maganar bata bacin rai bace Saraki, daga yau in kana da buĆ™ata sai ka rinĆ™a gaya mani, miye duniyar? Masu karin magana ma cewa sukai daga duniya sai KADUNA, ina kai aya wayata tayi Ć™ara, ganin sister Aina'u na É—auka na sanya a kunne ina faÉ—in hello! Yaya dai Aina'u? 


Tace Congratulation Dr, kina É—auke da ciki 13 weeks kenan, nace what! da Ć™arfi ina zaro ido, ta sake maimata mani abinda tace, nayi mata sallama na aje wayar, kaina na dafe da hannu biyu ina wani irin kuka na takaici, a ruÉ—e Saraki ya taso ya dafa man kafaÉ—a yana tambayar lafiya Ummu? Ko wani ne ya mutu? 

 

Nayi mashi banza, yace kinsan fa bana son ganinki cikin damuwa wai lafiya, na bige hannayenshi ina faɗin ni ka kyaleni bayan kaje ka haɗani da bala'i, hankalinka ya kwanta tunda kayi man ciki, da ƙarfi cikin mamaki yace ciki Rumanah?


Kai na godema Allah da wannan ni'imar daya bamu, na galla mashi harara, dama ka wani daina murna dan zubar da shi zanyi...what ya faɗa yana man wani irin kallo, wallahi kada kiyi wannan kuskuren, zan mugun saba maki, ai sai ka zo ka hanani, sanda ma zan zubar ka sani ne, ya miƙe tsaye kina iyayin duk abinda kike so amma banda zubar man da ciki, ya shige ɗakinshi ya barni nan.


Ashe da Baba Sarki yaje ya haÉ—ani, bayan la'asar sai ga wayar Baba Sarki yana nema na yanzu, nasan dai maganar cikin da nace zan zubar ce, zaune nake gaban Baba Sarkin yana man nasihohi da kawo man misalai, duk dan yasa jikina yin sanyi, ni kuma jinshi kawai nake dan duk matsalar da yake kawo mani na sansu, tashin farko na sanya mashi kuka.


Ni gaskiya Baba bana iya haifa ma Saraki ɗa, ni gaba ɗaya ma auran ya isheni, Baba kayi man alƙawarin rabamu idan nayi watanni, to ai yanzu nayi su, Baba yai shiru yana kallona kafin ya sauke ajiyar zuciya yace ina sane Ummu, amma baki son inga ɗanki dana Saraki a duniya Ummu?


Ina so mana Baba amma ba tare da Saraki ba, toh naji yanzu dai ki haƙura ki haifa mashi wannan ɗan, bayan kin haihu sai na raba maku auran, kinga yanzu idan kika zubar kamar kinyi kisan kai ne, da lallashi da ban baki Baba Sarki ya samo kaina na amince.


Koda na koma gida Saraki na falo zaune, Jamila dai ta shige ɗaki tunda bata wuce takwas zuwa da rabi a falon, banyi mashi magana ba na wuce, ina shiga ɗaki ya biyoni, dan Allah Rumanah kiyi haƙuri ki bar cikin nan, wallahi duk abinda kika ce inyi maki zanyi inde zaki haƙura, nayi mashi banza kamar ba dani yake ba, yayi magiya da lallashi nayi shiru, sai naga ya fara zubar da hawaye na kalleshi da mamaki wani ɗan tausayi ya gitta cikin zuciyata.


Yanzu Saraki me zanyi maka kazo ka tasani kana kuka? Ya matso wajena jin nayi magana, Rumanah ki bar cikin kawai nake buĆ™ata, nayi dariyar mugunta, zan iya barinshi amma da sharaÉ—i, da sauri yace Allah na amince koma miye, kace fa Allah, wallahi Allah zanyi kinji na rantse, na kawar da kai, zan iya barinshi amma da sharaÉ—in duk abinda ciki ya sanyani kaima dole kayi, kamar me da me kenan Ummu? 


Misali na farko kaga idan amai cikin ya sanyani kaima dole ka taƙarƙare kayita kwara amai, ko naji ko baka ji, idan banson cin wani abu kaima zakaƙi ci, in banson ƙamshin abu zaka kiyayeshi, haka kuma idan ina son cin wani abu kaima dole kaci ko kana so ko baka so.


Sai na biyu, idan bacci zanyi kaima dole zaka kwanta kusa dani muyi tare har lokacin da zan tashi, idan yasa raina cikin ƙunci kaima naka ran ya baci, idan farin ciki nake kaima zaka yi, ka amince?


Yana man wani irin kallo yace Rumanah anya kina da hankali kuwa? Ta yaya za'ai i yi abubuwan da mace mai ciki zata yi ina namiji, kema kinsan ba zai yiwu ba, nace Allah ko? Tunda kaga ba zai yiwu ba nima ba zai yiwu ba cikinka ya zauna a mahaifata ba, zubar da shi zanyi bari ganin ka kai Ć™arata wajen Baba Sarki, ba abinda yayi mani kuma ba zai hanani abinda nayi niyya ba, yanzu dai ka bar mani É—aki kona na fara shirin raba kaina da wannan cikin, yayi shiru na tsawon wasu mintina, shikenan abinda kike so? 


Shikenan mana, to naji na amince zanyi zaki barshi ko? Yarda yayi maganar cikin sanyin murya ya sanyani dariya, nima na yadda zan barshi, yace man sai da safe ya fice, koda wai bai bani tausai ba, wanka kawai nayi na kwanta bacci.


Nasan wasu mutane zasu ji haushi na ko tsanata ko yi mani kallon bani da imani, amma ina ga wannan ba komai bane idan aka lura cewa bana son shi, mutumin da baka so komai kana iya yi mashi, kuma har abada ba zaka damu ka sashi ciki farin ciki ba, burinka kullum ka ganshi cikin baĆ™in ciki.


Ban taba tsammanin Saraki zaiyi abinda na ce ba, sai hashi yana kwatantawa dan baya haɗa awa bai shigo dubani ba idan yana gida, idan makaranta ne baya gajiya da yo waya, sannan ya kan dawo kafin ya tashi aiki, ni kuma gashi cikin mai laulayi ne sosai, yau ma ina toilet ina ta kelaya amai sai gashi ya shigo har cikin toilet ɗin, yana ganin abinda nake yasa babban ɗanyatsan shi a abaki wai dole sai ya ƙaƙaro amai, ganin abinda yake yasa ni dariya, na wanke bakina ina kallonshi, yace kin gama ne?


Na ɗaga mashi kai ya kamani muka fito, nace ya kwantar dani kan gado bacci nake ji, ya kwantar dani har da rufa, na kalleshi nace toh kai baka kwanta ba, Rumanah dan Allah ki yafe man baccin yau, ina da lacca sha biyun rana, na haɗe fuska nace duba nan Saraki, har yanzu ba cikin ba wai cirewa ya wuce ba, alƙawarin da kayi dole ka cika idan kana son ganin abinda ke cikin ya fito duniya.


Ya marairaice tare da langwabar da kai, da Allah fa na haÉ—aki Rumanah, na juyar da kai ina cewa fita kada ka dameni da surutu amma kada ka zargeni idan ka dawo ka iske ba cikin a tare dani, ya daÉ—e tsaye yana man wani irin kallo, ko kallon inda yake ban sake yiba balle inshi tausanshi, dole ya hawo gadon ya kwanta bayana, ni dai ban wani jima ba bacci ya kwasheni.


Na farka É—aya da minti biyar, ba Saraki ba dalilinshi, na fito falo ba shi, kai duk gidan ma babu shi, watakan wayo yayi man da yaga nayi bacci shi ne ya lallaba ya bar gidan, ashe ko baisan halina ba, cikin ko yanzu zan zubar dashi bari inyi sallah.


Allaurar zubar da ciki na danƙara ma kaina, sannan nasha magani kafin awa ɗaya jini ya fara zuba daga jikina, wani daɗi ya rufeni ganin buri na zai cika, sai dai kuma me? A zabanban ciwon ciki ne ya biyo bayan soma zubar jinin, nan na kwanta kan kafet ina muƙurƙusar a zaba.


Sunayen Allah kawai nake karantowa tare da duk wata ayar da ta zo bakina, ina cikin wannan halin Saraki ya shigo É—akina, a 

guje ya ƙaraso inda nake ya tallabeni yana salati, Rumanah lafiya? Na shiga uku kaddai ince cikin ne zaki zubar?


Rumanah! Rumanah!! Rumanah!!! 


Ya shiga kwaÉ—a mani kira, nikam tuni na barmashi É—akin ta hanyar somewa.



Toh gaskiya kuyita kanku dan ni dai kaÉ—an na typing yau atoh