Rumanah (Zabin Iyaye)

14

by @shooly84

...Rumanah🕊️

 (Zabin Iyaye)







©️ Aisha Machika







*Page~14*






Dan Allah Ramanah ki tashi naji ana raɗa mani a kunne, lokacin dana dawo daga doguwar sumar da nayi, na buɗe ido a hankali ina salati, Saraki na zaune kusa dani yana riƙe da hannuna, ganin na buɗe ido yace yawwa kin tashi? Sannu Ummu, na kalleshi sosai da gani yasha kuka bana wasa ba, sai dai ban san kona halin dana shiga bane ko kuma na zubewar cikin shi.


Ina nake Saraki? Asibiti ne Rumanah, waya ce ka kawoni asibiti? Haba Rumanah kamar dai ina da tabin hankali kina wannan halin zan tasaki naita kallone? 


BuÉ—e Ć™ofar da akayi ne yaja hankalinmu wajen, Dr Ni'ima Y.F ce, ta zo inda nake kwance tana faÉ—in masha Allah Dr ta farfaÉ—o, nayi murmushi tace ba dai kijin ciwon komai ko? Na É—aga kai, Saraki ne ya tambayeta, ya ya Dr? 


Taja kujera ta zauna, a sakamakon bincike ciki yana nan bai zube ba, ya dai ja baya ne dan ba zata haihu nan da wata shidda ba sai ya maida kwanakin shi saboda jini data zubar da yawa, amma fa yana under risk sai kunbi a hankali dan anything can happend, dan inta ƙara shan wani abu ko yin wani abu dan zubar dashi ina tabbatar maku zai bi rariya.


A kula ayi a hankali, ko wane abu mai nauyi ko motsa jiki da Ć™arfi kai hatta damuwa da faÉ—uwar gaba suna iya sawa ya fice, ta maido da hankalinta gareni, ina mamaki Dr Rumanah, ke kau ta yaya za kiyi yunĆ™urin zubar da ciki bayan yana da uba? Saraki ya bata amsa, Dr wata Ć´ar rigima muka yi da ita, shi ne tayi wannan aikin, tayi murmushi tace wauta ce kinji Dr Rumanah? 


Dan Allah ina baki shawarar kada ki ƙara kinji?


Nayi É—an murmushi bance komai ba, tunda baki jin wani abu bari in rubuta maki drugs kuma kinsan yadda ya dace kisha ba sai nayi maki bayani ba, tayi mana sallama ta fice.


Har muka dawo gida ba wanda yace komai tsanina da Saraki, dan ciki dai tabbas ya sake karya doka zan cireshi fit daga mahaifata, mun iske Jamila tayi abincin dare, sannan ni kuma ta dafa mani abu mai ɗan ruwa-ruwa yadda zai man daɗin sha, ina ɗaki kwance ya shigo, cikin sanyin murya ya fara magana, Rumanah ban taba zaton rashin ƙaunata ta kai haka ba a zuciyarki.


Kinsan da sani duk duniya bayan iyayena da ƴan'uwana babu wanda nake ƙauna sai ke, sai kuma wannan cikin dake gareki, Rumanah ba tausayi da imani kwata-kwata cikin zuciyarki, koni ɗin ba jininki bane sai haka, nace Saraki duk ba rashin tausai ya kawo haka ba, dokar daka karya ce, bari kaji konan gaba ka sake yin haka zan cireshi.


Ya kallan wai kina zaton tashi nayi da son raina? Baba Sarki ya kirani ta waya yana son ganina da sauri, ni kuma ganin baccinki yayi nisa yasa nayi tafiyata, amma dan Allah kiyi haƙuri ba zan sake ba, oho maka ni dai na gaya maka.


Tun lokacin kulawa ta musamman nake samu daga Saraki, dan yanzu ma kusan É—akina yake zama, ganin yarda yake riritani kamar kwai yasa Jamila soma canza hali ta hanyar nuna kishinta a fili, daga baya ma ta koma Jamilarta Ć´ar gidan Ibrahim Ningi, ba ragi balle raguwa, rashin mutunci da rashin kunya suka dawo, dama Ć´an magana sunce *HALI ZANEN DUTSE...*


>>>>>>>>>>>>>


Allah ka bamu ikon bin Allah da iyayen mu sau da ƙafa Amin, cikin watanshi goma amma bai yi wani girma sosai ba dan ina da tsayi wanda ya taimaka ma cikin bai girma sosai ba, tun ina sa ran ganin haihuwa yau, gobe, jibi hardai na cire rai, sai tsabar lalaci da bacci.


Saraki kuma har yanzu zaman mu na nan irin na da, Jamila ce dai zaman ya canza, dan ko kaɗan bata ƙaunar ta buɗe ido ta ganni gidan, ni kuma ko a zani na dan nafita son barin gidan, da yau Saraki zai ce Rumanah jeki na sakeki toh da na fi kowa murna.


Koda yaushe naje wajen Baba Sarki aikin kenan inyi haĆ™uri in haihu, Iyalle kam bata taba ceman komai ba, nasan ido ta sa mana nida Salihu Baba Sarki, Saraki ya katseni daya shigo, sallama kawai na amsa mashi, yayi tsaye kaina, Rumanah bacci zakiyi koko inje inda zani? 


Kamar ince baccin zanyi amma sai naji tausanshi, dan yanzu kwata-kwata bana barinshi zuwa aiki sosai, yana nan ya tare a wajena, da naga cikin ya wuce munzalin cirewa sai na tsiri cewa zansha abinda zai kashe yaron ya fito babu rai, Saraki ya zaci da gaske nake, ni kuma ina haka ne dan kawai bana son ganinshi yana hutawa ko yana cikin walwala.


Rumanah magana nake kinyi shiru, na ɗan kalleshi ta gefen ido, kana iya zuwa inda zaka, ya duƙo ya sumbaci kumatuna sai na dawo my wife, nabi ƙofar daya fita da kallo, agogo na kalla naga 4:51pm, falo na fito insha iska saboda na gaji da zaman ɗakin, kan doguwar kujera na kwanta bacci mai daɗi ya ɗaukeni na minti talatin kafin inji wani wawan duka a cikina.


A firgice na farka saboda wani irin juyawa da cikin yayi ya cure waje ɗaya kuma, Jamila ce tsaye kaina riƙe da ƙugu tana man kallon sama da ƙasa, tace sannu ɗiyar gwal, aikinki kenan daga bacci sai bacci waike mai ciki, toh yau ba zanyi abinci ba tunda ba akanki aka soma ciki ba, ina jin ta amma ba damar tankata hannuna dafe da cikin wanda ke motsi da wata irin a zaba.


Magana nake maki kin wani dafe ciki, inkin tashi ki haihu a yau ba ruwana ni, ta sake ɗaga hannu zata sauke a kaina karaf Saraki ya riƙe, cikin wani mummunan tashin hankali ya dinga yarfa mata mari a duka kumatunta biyu kafin yasa ƙafa yayi balli da ita ta tafi zuuuu sai jin tim kake a jikin bangon falon, ni da ita muka ƙwalla ƙara lokaci ɗaya.


Ita dai ta jin zafin buguwa ne ni kuma wata irin ƙullewa marata tayi kamar zata tsage, surata Saraki yayi zuwa cikin mota kai tsaye asibiti ya wuce dani, bayan gwagwarmayar awa uku na haifi ɗana namiji tubarakalla! Yaron kamar kaki Saraki yayi sai dai ƴar kamata da ba'a rasa ba, ganin komai lafiya taran dare aka bamu sallama, kai tsaye gidan Baba Sarki ya wuce dani ya dire ma Iyalle, farin ciki kam ba'a cewa komai wajensu Baba Sarki nan da nan Iyalle ta ɗora ruwan wankan jariri dani kaina.



Kafin suna duk ƴan'uwa kowa ya zo, mazan tare suke da matayensu da ƴa'ƴansu, su kuma matan yara ne kawai, gaskiya naga so da ƙaunar baby wajen ƴan'uwa kamar ba'a taba haihuwar baby ba a gidan sai na Saraki, ranar suna anci ansha yaro yaci sunan Al'amin zabin yaya Nuraddeen.



Ni da ake kwana arba'in na wankan gida a koma gidan miji, amma ni yau watana uku a gidan kenan, tunda na gama wanka na koma aiki na, watarana idan naga dama intafi da Al'amin, idan kuma na tuno É—an Saraki ne wajen Iyalle nake barinshi, ba wani zan can bashi nono ko ina gida sai naga dama, su Iyalle basu taba ceman komai ba, balle uban É—an, kullum dai zai zo ya É—auki kayanshi ko ina yake zuwa da shi Allah kaÉ—ai ya sani.


Biyar da rabi dai-dai na taso aiki yau daga asibiti sakamakon rashin marasa lafiya, ban iso gida ba sai shidda, tunda na shiga da motata farfajiyar gidan na soma jin kukan Al'amin, na kalli motocin wajen banga ta Saraki ba, sai wata sabuwar ƙatuwar G.M.S Royal blue tanata sheƙi a sauran hasken ranar daya rage, sai kuma motar Yaya Muhammad, nace Saraki bai zo ba yau kenan, aikau na shiga uku da faɗan Ya Muhammad.


Ina yin sallama a falon, idona Ya Muhammad ya fara gani yana riƙe da Al'amin wanda keta tsala ihu, sai Saraki zaune kusa da Iyalle duk sunyi shiru suna kallon Al'amin, jikina ya fara rawa ganin irin kallon da Ya Muhammad ke mun, a haka naje inda yake, kyakkyawan mari ya sauka akan kuncina kafin inji ya sako man Al'amin a hannu, cikin tsananin bacin rai ya fara magana.


Rumanah yaushe kika zama ƴar'iska ne? Irin taki rayuwar kenan? A'a yau dai kai ka fara ganin haka, kullum nan take barinshi taja mota zuwa aiki, inji Iyalle kenan take faɗi itama cikin takaicina, taci gaba da cewa idan taga dama tun safe sai dare zata dawo, ya kalli Saraki da kanshi ke ƙasa yace kai kuma baka iya mata magana kana kallonta? Saraki dai shiru ya yi, ya dawo kaina, toh bari in gaya maki yanzun nan zaki tattara komatsanki kibi mijinki gidanki, idan kinga dama ki kashe yaron da uban yaron gaba ɗaya saboda rashin ƙauna, ni wuce ki bani waje yarinyar banza kawai.


Ina rirriga Al'amin hawaye na sauka idona na shiga É—aki, na zauna kan gado ina ba Al'amin nono ina kuka, a falo kuma Ya Muhammad ya ci gaba da sababinshi, ina gama bashi na kwantar dashi domin ya samu bacci, kayanmu na soma haÉ—awa still kuka nake, a haka Saraki ya shigo, ban kalleshi ba ya zauna wajen Al'amin, har na gama haÉ—a kayana ba wanda yayi ma wani magana, na shiga toilet in É—auro alwallar sallar magriba da naji an soma kira, koda na fito ba Saraki ba akwatin kayanmu sai Al'amin kwance kan gadon.


Na idar da sallar ba É—auko Al'amin na fito, falon ba kowa na shiga É—akin Iyalle na isketa zaune kan dardumar sallah, na durĆ™usa Ć™asa na fara magana, Iyalle dan Allah ku yafe mun duk abinda nayi maku, ni kam har yanzu bana jin son Saraki a raina, wallahi ina zaune da shi ne saboda Baba, ta É—ago kai tana kallona, magana É—aya zan maki Rumanah, ki rinĆ™a kula da wannan yaron, haƙƙinshi kike É—auka na rashin bashi kulawa, hakan zai sa ya taso babu shaĆ™uwa a tsakaninku, kinfi kowa kuma sani muhimmancin nonon uwa, dan Allah ki rinĆ™a kula kinji? 


Ummu ni bana ganin laifinki akan irin zamanki da Saraki, kowa yasan dole aka maki, abinda nake so dake kawai shi ne ki yawaita addu'a idan zamanku alkhairi ne Allah ya sanya maki sonshi, idan kuma babu Allah ya kawo sanadin rabuwarku, Ummu haƙƙin maraici babban abu ne, wasu basu damu da cin zarafin marayu ba, ke marainiyace a garemu, har abada ba zamu taba takura rayuwarki ba, yanzu tashi kije kada yaita jiranki, na miƙe jikina a mace, Baba Sarki bayanan balle muyi sallama koda na fito banga motarshi ba sai Sarakin jingine jikin G.M.C ɗin nan, ban tanka ba na isa da kanshi ya buɗeman ƙofa na shiga.


Cikin motar Al'amin na kwance kan cinyata, ni kuma na juya fuskata ina kallon hanya, lokaci zuwa lokaci ina É—auke ruwan hawaye da suke sauko mani, babu mai magana har muka isa, yana gama farkin na buÉ—e motar na fice, nayi sallama cikin falon Jamila ce zaune a falon, na É—an saki fuska ina faÉ—in Jamila kin ganmu sai yau kwaram ko?


Murmushin lebe tayi tace sannunku ya mutan gidan? Na miƙa mata Al'amin ga ɗanki bari naje na gyara mana wajen kwanciya, ina kallon irin riƙon sakarci da tayi mashi, na shige ɗaki kamar ban damu ba, abin mamaki ɗakin gyare yake kona ina ƙal, sai kawai na shirya mana kayanmu sannan naje na karbo Al'amin, yana kwance gefenta yana ta wutsil-wutsil ɗinshi nasa hannu na ɗaukeshi, nafa gode ko nace na wuce abina, wanka nayi mashi da ruwa masu ɗan zafi, sannan na sake bashi nono yayi dam, na gyara mashi shinfiɗa a gadonshi na yara tare da kwantar dashi, nima wanka nayi na gabatar da sallar isha nasa riga da wanko na bacci, rigar mai hannun shimi ce saboda shan iska.


Ina kwance wajen taran dare ina daĆ™ilar waya Saraki ya shigo, lokacin Al'amin baccin shi ya yi nauyi, wajen gadon Al'amin É—in yaje yana kallonshi kamar wata sabuwar halitta, sannan ya sumbaceshi ya baro wajen, kusa dani ya zauna ya yi shiru, can ya sona Ć´an kame-kame, Rumanah kinga sabuwar motata ko? Na ce hmmm...kawai yaci gaba jiya ta iso wajena dama nayi odarta da jimawa, tsuhuwar tawa kuma na saida na sai Honda civic, yayi shiru kuma can ya matso ya riĆ™e man hannu, na Ć™wace ya sake riĆ™ewa sai na Ć™yaleshi, Rumanah ban taba nuna maki irin murnar da nayi ba ta haifa man Al'amin, ko da yake tare mukayi rainon cikin tunda nima har laulayi nayi kamar mace, ya yi É—an tsaki gaskiya kindai Ć™wareni a lokacin amma bai hana in nuna maki godiyata.


Wani abu ya saka man a hannu, gashi nan gift ɗinki na haihuwa, key ɗin mota ce ford jeep, ya ɗanyi shiru tare da shigemun sosai ya rumgumeni gam a jikinshi yana saukar da munfashi a hankali, tunda ya soma magana ba abinda nace mashi, danni yau yayi man wani sukuku kamar ba namiji ba, jin yanata sauke numfashi akai akai yasa na ɗan janye baya, ya kalleni idanuwanshi sunyi jaa na girgiza mashi kai gabana yana faɗuwa ganin lokaci ɗaya yanayin shi ya canza, a hankali ya sake rungumata yana shafa kafin ya kwantar dani ya kashe wuta, abin mamaki nayi laƙwas kamar wani sihiri, jin abinda yake da niyyar yi yasa na motsa ina son tashi yai maza ya sake ƙwaƙumeni yana faɗin no Rumanah bai kamata kiyi man haka ba, nafi shekara fa banyi komai ba, kafin inyi wani abu ya lalubi bakina yana tsotsa hannayenshi na shafa duk inda suka sauka a jikina, hawaye kawai suka soma sauko mani dan koni nasan Saraki nada haƙuri babu yarda zanyi dole na amshi tayinshi.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>


Shekarar Al'amin ɗaya kenan, amma kamar ɗan shekara biyu ko uku, yayi girma da wayau tafiya da gudu ko ina, tun yana da wata sha ɗaya na yaye shi shikenan Saraki ya samu abokin yawo, aiki da shi ake zuwa masallaci ma haka, tsakanimu da Jamila dai ba wani canji yau daɗi gobe babu, har na fara tunanin gwanda Saraki ya saketa kawai dan bata da wani amfani wajenshi kada shiga haƙƙin yayi yawa.


Hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba ganin irin magungunan da nike sha na hana ɗaukar ciki amma sai gani da shi har wata huɗu da wasu kwanaki ban san dashi ba, bana yin al'ada sai ban damu ba ashe ciki ne ban sani ba, ba dama nace zan cire tunda yayi ƙwari dole na haƙura na barshi, farin ciki da murna kamar me Saraki yayi.


Ranar laraba ya kama aikin Jamila ne muna zaune mu duka a falo muna kallo, Saraki da Al'amin suna zaune kan kafet ya biye mashi suna wasa, ni kuma ina zaune kan kujera mai cin mutum É—aya, sai Jamila na kan doguwa, Sarakin ne ya kalleni yana tambayar Rumanah idan kin haihu wane suna zamu sa ma abinda kika haifa mace ko namiji? 


Nace Saraki sunan Al'amin zabina ne ko naka? Ka bari idan ba wani mai sha'awar suna sai ka sa wanda kake so, yace a'a gaskiya ba zan yarda ba, shikenan mutum da ɗanshi ba zai yi abinda yake so ba? Kada ka mance dasu Yaya dasu Aunty's duk ɗaya ne damu, suma idan sunsa sunan duk ƙaruwarmu ce tunda so da ƙaunar ya'yarnmu ya kawo hakan, yace toh bari dai inkai ki kiji, idan mace ce sunan Mami za'a saka mahaifiyarki wato Saudat, in kuma namiji ne zaici sunan Abdul-naseer.


Ban bashi amsa ba Jamila ta sako tata maganar, Saraki ban gane ba, kada dai ince Rumanah wani cikin gareta? Yace Ć™warai ma ko, wani abu ne? Ta miĆ™e zaune, a'ah da sake wallahi, shekaruna nawa a gidan nan, baka taba sauke haƙƙina dake kanka ba na mu'amular aure sai ita da tazo daga baya, ita ce mata a gareka ita ce mace mai ramin haihuwa, me kake nufi kenan? 


Nafa gaji da wannan wahalallen aure, banga abinda yake tsinana mani ba, ina budurwata amma zan tsofe a zaune ban gane komai ba, idan baka aure na toh ka sakeni inje masu sona su aura, koda yake duk wannan kilbabbar ce ta hanaka ganin ko wace mace da daraja, abinda ma ba sonka take yi amma ka nace saboda rashin zuciya, ni dai ba zan iya ba, cikin biyu zaka yi É—aya, saki ko aure zabi ya rage gareka.


Raina a bace nace, wai Jamila dukkan tada jijiyar wuyan me kike haka? Inde Saraki ne gashi nan duniya da lahira na bar maki shi sai ki kwata ki ci mu gani, amma ki sani na gaji da tozarcin ki da wulaƙanci dan bana ɗauka, Sarakin me da zaki tsaya kina babatu kanshi, daga yau sai yau wallahi kada ki sake gaya man ba daɗi saboda shi, idan ba haka ba wallahi zan...miƙewar da Sarakin yayi cikin bacin rai ya katseni, wajen Jamila ya nufa yana sakin huci yace, mu'amular aure dai kike so ta haɗamu ko?


Toh yau ko insha Allahu zan cika maki burinki, kinji na rantse da Allah yau sai nayi maki kaca-kaca yarda idan kika ga namiji zaki ruga da gudu dan tsirar da rayuwarki, yana gama faɗi ya duƙa ya sunkuceta ya nufi hanyar ɗakinta, ganin da gasken yake ta soma zillo tana kai mashi duka tana faɗin leave me alone, how dare you...bai saurareta ba ya shige ɗakin da ita, ni kuma na saki baki galala ina bin ƙofar da kallo, da shigarsu ba jimawa naji ta yanka wani irin ihu da yasa nayi saurin toshe kunnuwa na, Al'amin ya taho a tsorace ya lafe jikina.