01
*ƘADDARARREN AL'AMARI*
© *Rahma Kabir*
Mrs MG
Wattpad @Rahmakabir.
2020
*_Bismillahir Rahmanir Rahim_*
_Duk kan Godiya ya tabbata ga Allah Ubangijin mu, shi kaɗai ne ba shi da Abokin tarayya. Tsira da Aminci su k'ara tabbata ga fiyayyen Halitta Monzon tsira s.a.w, tare da Ahalinsa da Sahabbansa._
_*Alhamdulillah da Allah ya k'ara bani dama na zo muku da sabon littafina mai suna ƘADDARARREN AL'AMARI.*_
*Gabatarwa*
_Wannan littafi k'agaggen Labari ne, domin mu ilmantu kuma mu d'auki darussan dake ciki. Idan labarin yazo d'aya da labarin ki/ka to ku yi min Afuwa. Labarin yana k'unshe da kalubale, tsantsar tausayi, rikici, damuwa, wahala, ƙunci, rashin ƴanci, cin zarafi, rikitacciyar soyayya.
*Gargad'i*
_Ban yarda ayi afmani da wani b'angare na wannan labarin ba ko kuma satar fasaha, dan Allah a kiyaye_
*Sadaukarwa*
_Ga group d'ina Sirrin 'ya mace. WhatsApp._
*01*
Da misalin ƙarfe Huɗu da rabi na yammacin la'asar, rana ta yi sanyi iska na kaɗawa. Gidan Marigar Malam Ashiru ya kasance cikin unguwar talakawa, ɗan ƙarami ne yana ɗauke da ɗaki uku ciki ɗai-ɗai, guda biyu kwanan ya kwaye sakamakon iskar ruwan sama daya yaye su, ɗaya ne kawai mai kyau, sai toilet guda ɗaya yana haɗe dana wanka da bayan gida, babu kitchen sai duwatsu guda uku dake tsakar gidan da aka jera da alama nan ne madafa, sai rijiya daga gefe an sanya masa babbar taya da marfin fale-fale. Wasu yara ne su uku suke rayuwa a cikin wannan gida, zaune suke bisa wata yalolon tabarma a tsakar gidan, Babbar ita ce mai suna Safnah shekarunta sha takwas, sai mai bi mata Muslim ɗan shekara sha biyar, sai ƙaramarsu Muneera ƴar shekara sha biyu.
Mumira ce ta zabga hamma har sai da ta fidda kwalla saboda azabar yunwa daya addabi cikinta.
"Anty Safnah wai dan Allah yau mai zamu ci ne? wallahi ni fa yunwa nake ji, kuma ga shi ba mu da komai da zamu ci, ya kamata muje gidan Kawu Bala"
Muneera ta yi maganar tana shafa cikinta tare da runtse ido kwalla ya sauka kuncinta.
"Muneera ya kama ta ace zuwa yanzu kin saba da wannan yana yin da muke ciki, tunda ba yau muka soma wannan rayuwar ba. Kawu Bala yana iya ƙoƙarinsa a kanmu, shima ba ƙarfin ne da shi ba, dan haka bai kamata mu rika matsa masa ba. Kuna kallon yadda nake faɗi tashi wajen niman aiki, amma dana fara nake samun matsala"
Safnah ta bata amsa cike da damuwa a fuskarta.
"Anty Safnah ki rabu da Muneera ta sani take tambayarki ai, ni ina ganin bari naje na yi bara, ƙila mu samu abincin da zamu ci"
"Muslim karka fita, bari ni naje wurin mai saida abincin nan, inta aike ni ko na yi mata wanke-wanke kila ta bani abinci a madadin kuɗin da zata biyani, sai na kawo mana mu ci"
Safnah Tana kaiwa nan a maganar ta sai ta miƙe jiki a sanyaye, ta jawo wani koɗaɗɗen hijab a igiyar shanya ta sanya, sannan ta sanya silifas ɗinta wanda ya siɗe ya yi rami.
"Muslim in na fita ka rufe gidan, ka ja ruwa a rijiya ka cika farar roban cen ka kai mana ɗaki, zan dawo yanzun nan Insha Allah"
"Anty Safnah Allah ya tsare ya kiyaye hanya"
Muslim da Muneera suka haɗa baki wajen yin maganar lokaci guda.
******
Safnah, Muslim, Muneera Ƴaƴane ga Baffa Ashiru da Inno Aishatu, Asalinsu Fulanin Gombe ne, Malam Ashiru yana aikin gidan Gona a nan Kaduna, dalilin da yasa kenan ya dawo da Iyalinsa nan Kaduna tun Safnah tana ƙarama. Alhajin da Baffa Ashiru ya ke yiwa aiki, shi ne ya siya masa ƙaramin gida a nan Unguwar Badarawa.
Safnah ta yi saukar al-Qur'ani tun tana shekara sha Huɗu lokacin ta kammala Jss 3 zata shiga ss 1, a wannan lokacin ne Mahaifinsu ya rasu sakamakon ciwon sanyi da ya yi masa mummunar kamu, ya bar Mahaifiyarsu da karamin cikin wata uku.
*
Lokacin da cikin ya kai wata tara da kwana biyar haihuwa ya kama Inno cikin dare, maƙota su kawo ɗauki kafin a kaita Asibiti ta haihu da Namiji, yana fitowa Duniya nan take Inno ta rasu, zuwa safiya Yaron shima ya cika.
Tun daga wannan lokacin su Safnah suka shiga cikin rayuwar maraicin rashin Uwa ba Uba, Ƙanin Mahaifiyarsu Kawu Bala, shi ne kawai yake taimaka musu kuma bai da ƙarfi yana fama da Iyalinsa, dan shima aikin gadi yake yi, Baffansu shi ne ya sama masa aikin har ya baro Gombe da iyalinsa. Ya mallaki gida mai ɗaki ciki hudu, sai toilet sai kitchen, yasa ƴan haya a cikin biyu su suna maneji da ciki da falo. Haka yake kokarin taimakon su Safnah yaso ya dawo dasu gidansa amma matarsa taki yarda, a cewarta shi da bai da karfi nauyi zai masa yawa tunda suma haka suke rayuwa hannu baka hannu kwarya, basu ci sun koshi ba balle su bawa wani, da wannan hujjar ta hana shi mai do da su Safnah gidansa.
Can ƙauyensu kuwa Riga ce, babu wani mai ƙarfi da zai riƙesu suna fama da kiwo, Baffansu shi kadai ne a gun iyayensa kuma tuni suma suka kwanta dama, sai sauran dangi da suka rage masa. Ta bangaren Inno kuwa, Kawu bala ne kawai dan uwanta da suke uwa daya uba daya, mahaifinsu ya rasu sai mahaifiyarsu da take zaune a can riga, Baffa bala yana kumajin yaje ya daukota amma matarsa ta hana. Zaman su safnah a nan Kaduna yafi misu alkhairi da rufin asiri fiye da zaman rigarsu.
Safnah tun tana da ƙanƙanin shekaru ta cigaba da kula da Tarbiyyar Ƙannenta da taimakon kawu Bala, ita ke faɗi tashi akan abin da zasu ci, da gidan nan kawai suka tsira. Tun lokacin mutuwar Baffansu, Alhajin da ya kewa aiki ya kawo musu abinci bai sake waiwayensu ba. Safnah ta yi aiki a gidajen masu kuɗi da dama sai dai ko wani gida da irin matsalar data fuskanta har kawo yanzu. Kawu Bala shi ne ke taimakonsu da wasu abubuwa, wani lokacin rashi kesa baya iya musu komai, wata rana haka suke kwana basu ci komai ba, Maƙota sunyi nasu taimakon har sun gaji, hakan yasa Muslim ke fita bara zuwa unguwar masu hannu da shuni ya samo musu abinci, wata ran kuma Safnah ta fita zuwa shagunan masu saida abinci ta musu aiki su bata abinci ta kawo musu, a haka suke Rayuwa, batun Boko da Islamiyya tun rasuwar Iyayensu suka daina zuwa.
_Asalinsu kenan a takaice_
******
Safnah ta isa shagon Hajiya Uwale mai saida Abinci ta tsaya gefe a rakuɓe kamar mara gaskiya, Hajiya Uwale ta fito daga shago tana kwalawa ɗaya daga cikin ƴan aikinta kira, Safnah ta risina ta gaisheta.
"Umm Hajiya yau akwai aike ko wanke-wanke nayi miki?"
Tace tana kunshe baki a Hajibi kamar mai jin tsoron yin magana.
"Safnah ke ce da yammar nan? aiko babu wanke-wanke Ma'aikatana sun gama sai dai aike in zaki iya zuwa"
"Eh ki bani zan iya zawa"
"To bari mai Napep ya gama ɗaura kayan a mota, Unguwar rimi zaki gidana dake Fulani road, wannan kayan zaki kai mai napep in ya sauke ki sai ki sanya min su a ɗaki, saiki wuce gidan dan yau ko sauran Abinci banyi ba amma ga Naira Ɗari biyu, Ɗari kiyi kuɗin mortar dawowa Ɗarin kuma kici Abinci"
Safnah ta amsa kuɗin hannunta na rawa, "Nagode Allah yasa kifi haka"
"Amin ƴan mata ina son kwazonki sosai, gobe kizo sai ki fara aiki nan dan na lura kin iya wanke-wanke mai kyau" tayi maganar tana murmushi.
"Nagode, Hajiya nagode, Allah ya jikan Mahaifa" tace murya na rawa alaman tana son yin kukan farin ciki.
Mai Napep ɗin ya ɗauketa da kayan suka nufa gidan Hajiya Uwani. Safnah tana ta kallon hanya da motoci masu wucewa yadda zata gane hangar koda wata ran Hajiyar ta kuma aikota. Suna isa Mai Napep ya sauke kayan ya juya akalarsa ya wuce, Safnah ta shiga gidan da sallama wasu Mata ta gani duk sunyi ɗaurin ƙirji suna shan rake a tsakar gidan babu wanda ya amsa mata sallamar, sai da ta gaishe su tukuna suka amsa a daƙile, ta tambayesu ɗakin Hajiya Uwani, ɗaya daga ciki ta nuna mata ɗakin da ya ke rufe an jawo ƙofa ba tare da an sanya kwaɗo ba, "nagode" tace sai ta wuce ta tura ƙofar ta shigar da kayan kana ta jawo ƙofar tayi musu sallama ta nufi yanyar fita, ɗaya daga ciki tace.
"Hajiya da yaje-yaje ko ina ta samo mai suffar mayu haka oho? amma fa Yarinyar tana da kyau, tana kilewa zata zama kaya"
Tsaki ɗayar taja "Daɗi na dake kin fiye gulma..."
Haka Safnah ta fice ba tare da taji ƙarashen zancensu ba, tana nazarin maganar amma ta gaza gane me suke nufi, bayan ta kawo bakin titi ta tari Napep ta gaya masa inda zata yace
"ɗari da hamsin"
Zaro ido tayi cike da mamaki "Dan Allah Malam zan baka Naira ɗari"
Da kyar ya yarda zai kaita a hakan.
Sun kamo hanya gosilo ya ritsa dasu sanadin wata mota data lalace bisa kan titin, ga yamma tayi kowa na haramar zuwa gida kasantuwar ƙananun motoci sunfi yawa a wurin saboda Unguwa ce ta masu hannu da shuni.
Arc. AKRAM TAHIR ALI. Matashin hamshakin mai kudi, yana ɗaya daga cikin wanda gosilon ya ritsa dasu a hanyar, tsaki yaja tare da dukan sitiyarin motar, Abokinsa Amir da suke tare ya kyalkyale da dariya.
"Haba Abokina meye na wani ɓata rai in kayi haƙuri yanzu gosilon zai saki mu wuce"
"Amir ba zaka gane ba wallahi wata yunwa nake ji, kasan yau ban samu halin leƙa gida ba saboda cikowar visitors, Lipton ne kawai a cikina tun safe"
"Kaima da gan-gan kake zama haka, ni ina zan iya, ɗazu restaurant naje naci na ƙoshi, ya kamata ka kiyaye dan kar ka kamu da ciwon gembon ciki"
Tsaki Akram yaja ya cire farin tabarau dake idonsa ya ajiye a gefe.
"Kasan bana iya cin abincin waje saina gida, hakan tsarina ne"
Sai ya buɗe marfin motar ya fito, da sauri motar escort dinsa suka bude suka fito, Akram ya daga musu hannu alamar su dakata kana yayi musu nuni da hannu dasu koma, duk wannan abin da yayi bai juya ya kalkesu ba ta baya yayi musu nuni, da sauri duk suka koma cikin mota, shi kuma ya nufi zuwa tsakiyar hanyar daya kasu kashi huɗu, sai ya shiga bada hannu cike da salo mai burgewa, nan take Mutane suka fara masa tafi suna kuwwa, iya burgewa ya kai matuƙa wurin burge su, Amir ya fito ya shiga ɗaukar Akram a video camera.
Safnah da tun fitowar Akram a mota ta bishi da kallo domin ya gama tafiya da hankalinta, ya yi matuƙar burgeta ganin irin tsadaddiyar motar daya fito daga ciki ga kuma yanayin fatarsa data bayyana tsan-tsan hutu amma ya cire girman kai yaje yana bada hannu ba tare da damuwa ba.
'Dama ana samun masu kuɗi irin haka? da ganin alamu wannan Mutum ne mai sauƙin kai a cikin masu kuɗin' tace a ranta tana ƙare masa kallo.
A hankali hanya ta soma buɗewa, ganin hanya ya warware yasa Akram ya dakata da bada hannun ya dawo wurin motarsa yana mai sharce gumin daya karyo masa a goshi, ya bud'e motar ya zauna a mazaunin driver ya ɗauki farin kyalle yana mai share fuskarsa, ya kunna motar suka wuce.
Safnah tabi bayar motar da kallo, Akram kuwa bai san da ruwan halittarta a gurin ba. Safnah har suka isa Badarawa fuskar Akram ya kasa ɓace mata a ido ta yi zurfi cikin tunaninsa, mai Napep ya tsaya a bakin layinsu ya ce,
"Malama na kawo ko ba nan bane in da zaki sauka?"
Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin da ta ke yi, ajiyar zuciya ta yi ta sauka a napep ɗin ta ba shi kuɗinsa ta nufi gida.
***
Amir ya kalli Akram daya ɗaure fuska yana cin Magani,
"Wani lokacin in ka ɗaure fuska kafi kyau, Akram kaga yadda kayi kyau kuwa da aikin traffic, nayi maka video zan saka Update a Instagram mutane suga the youngest millionaire mara girman kai"
Tsaki Akram yayi.
"Kaifa ba kada aikin yi kana abu kamar ƙaramin Yaro, kasan dai ni ba boyayyen mutum bane zan ɓata mana rai muddun kasani a IG tom"
Ya ƙarasa maganar yana kwafa.
"Ai kaima Kasan sai na sanya in dai na faɗa, kawai haƙuri za kayi a ɗan baza hirarka na kwana biyu a Instagram, kila ka samawa su Umma suruka dan ya kamata ka bude mana kofar shiga daga ciki"
"Kai ka sani mara aikin yi, ba wanda na rikewa kafa duk kuje kuyi aurenku"
Ya ƙare maganar dai-dai yayi perking a ƙofar gate ɗin gidansu Amir.
"Fita min a mota zan wuce dan ina da abin yi"
Ya ce yana mai tsare gira. Amir ya fita yana yar dariyar shaƙiyanci ya ɗauki brief case ɗinsa da suit.
"Traffic Man ka gaida min da su Umma"
Tsaki Akram yaja ya figi motar a guje domin ya gaji da jin zolayar Amir, escort dinsa suna biye da shi, sai da yayi nisa kana ya saki Murmushi akan tunawa da sunan da Amir ya kirashi dashi.
"Amir kenan sarkin zolaya"
Ya ce a fili tare da kunna Radion mota yana sauraren labaren ƙarfe shida na yamma.
Rahma ce.