02
Arc. AKRAM TAHIR ALI
*ƘADDARARREN AL'AMARI*
© *Rahma Kabir*
Mrs MG
Wattpad @Rahmakabir.
*02*
Akram d'ane a gurin Alh. Tahir Ali Kubau Former Governor na jihar Kaduna, kuma mai riƙe da Muƙamin Senator a yanzu, Asalinsa Mutumin Zaria ne daga ƙaramar hukumar Kubau. Matansa biyu da Yara hudu, Uwar gidansa mai suna Haj. Zainab Yaranta biyu Babban shi ne Akram, sai Auta Fatima suna kiranta Teema. Sai Amaryarsa Haj. Aisha itama tana da Yara biyu, Aisha ce Babba suna ce mata Humaira, sai Auta Ameena suna kiranta Meena.
Akram yana da shekara Talatin a duniya, yayi karatu a Ƙasar England ya karanta Architecture. Akram Mutum ne mai sauƙin kai bai ɗauki kansa ɗan wani ba, yana da company nashi na kansa mai suna A.T.A PAINTINGS & BUILDINGS COMPANY, sai dayan kamfanin Mahaifinsu KUBAU SHOES & BAGS TRADING COMPANY, duka shi ne CEO wato president na kamfanin duk wasu ma'aikata suna karkashin ikonsa ne. Akram mutum ne mai ilimin Addini dana Zamani babu ruwansa da Mata kuma baya shaye-shaye, abu guda ne ya koyo a England zuwa club dan shaƙatawa shi da Abokansa.
Teema tana da shekara Ashirin da daya, ita ce mai tashen rawar kai, duk wani wurin rawa da club sun san da ita bata jin magana, sai dai duk rashin jinta bata shaye-shye ko bin Maza, tana karatu a KASU tana karanta Biology.
Humaira shekarunta Ashirin da Shida Mace ce mai shuru-shuru bata da hayaniya ta kammala Karatunta na Mass com tana aiki a tashar NTA Kaduna. Mislika ce kuma Ma'abociya Addini halinsu ɗaya da Ahmad bata ɗauki kanta komai ba.
Meena tana da shekara ashirin da biyu, halin guda da Teema duk rashin ji tare suke yi, ita ma tana karatu a kasu tana karanta English, 200level duk suke, kuma suna kama sosai da Teema kamar yan biyu da yake da Abbansu suke kama.
Wannan sune Familyn Former Governor Tahir Ali Kubau kuma Senator mai ci a yanzu. Suna rayuwa a katafaren gidansa dake Unguwar Rimi Shehu Crescent, ƙaton gida ne mai ɗauke da filat uku a ciki da gate biyu, na Hajiya Zainab (Umma) shine farko sai na Alhaji Tahir Ali (Abba) shine a tatsakiya kuma nashi gidan sama ne mai hawa ɗaya, sai na Hajiya Aisha (Mami) shine na ƙarshe. Gidan Abba akwai haɗin kai da ƙaunar juna babu wani mugun kishi a tsakanin Matansa, in ba ka sani ba baza ka iya tan-tance ƴan ɗakin Umma ko Mami ba saboda a tsakuɗe suke, duk da ko wacce part dinta daban a gidan. Yaran sun taso Kansu a haɗe yake duk da akwai ban-bancin halayya amma suna Girmama junansu da ƙaunar juna.
Alh. Tahir yana da kannai biyu, Alh. Kamalu shi ke bi masa, yana zama a garin Abuja, yana aiki a ma'aikatar pension, matarsa daya Haj. Maryam, yaranta biyu, Umar shi ne babba dan shekara ashirin da takwas, fannin kasuwanci ya karanta, yana aki a nan kamfanin su Akram shi ne CFO (chief financial officer) duk wani abinda ya shafi kudi, banki, checks da duk abin da ke shigowa company a hannunta yake. Sai Aneesa wacce take tsarar Meena tana karatu a nan abuja 300level mass com.
Sai kuma kanwarsu Haj. Rahma wacce take zaune a nan kaduna, mijinta babban dan kasuwa ne mai suna Alh. Ghali yaransu biyu babbar ita ce Halima wacce taci sunan mahaifiyar su Alh. Tahir suna kiranta da Meemi ta girmi Akram da shekara biyu, ta yi aure da mijinta mai suna Sameer, tana da yara biyu Najeeb da Irfan. Sai kaninta Amir yana da shekara ashirin da tara, shi ne shakikin abokin Akram komai nasu daya hatta karatun su tare suka yi a kasar England, kuma kwas dinsu daya, sannan a kamfanin Abbbansu Akram yake aiki, Amir shi ne COO (chief operating officer) a kamfanin, duk wani shige da fice na company sai anbi ta gunsa kuma shike daukar duk wani bayanai yana turawa ceo Akram wato president din company, tare suke gudanar da komai, Amir shi mutum ne mai barkwanci da son wasa sabanin Akram da kullun yake miskili baya son yawan magana. Umar kuwa akwai surutu da yawan son mata shiyasa sam basa shiri da Akram.
_Wannan shi ne tarihin Akram a kataici_
*****
Akram ya isa gida ana kiran sallar magrib, side dinsa ya wuce yayi wanka ya sanya brown din jallabiya ya fito zuwa masallaci cikin sauri, Humaira ce ta kwala masa kira wanda yasa dole ya tsaya ta karaso cikon sauri tana haki.
"Yaya Akram Meena da Teema sun fita tun dazu basu dawo ba, kuma mun kira wayarsu a kashe shine Umma tace nazo na duba in ka dawo na fada maka"
"Amma yaran nan ko, ina suka ce zasu"
"Gidan anty Meemi, tun wurin karfe biyu suka fita saida Umma taja kunnensu"
"Je ciki kawai bari naje masallaci zan shigo yanzu insha Allah"
Daga haka ya wuce masallaci zuciyarsa cike da tunanin irin hukuncin da zai zattar musu.
Bayan sun idar ya nufo gida direct side din Ummansa ya wuce, yana shiga ya isa gun dinning domin baya jin zai iya wata moruwa har sai cikinsa ya ji dumin abinci. Ya bude food warmer yaga tuwon semi miyar kubewa danya kore shataf na mangyada sai miyar stew a wani warmer din daya ji naman kaza sai kamshi ke tashi, kwad ya hadiye miyau saboda ya tsinke, sai ya zuba ya soma ci. A haka Umma ta same shi taja daya daga kujerun dinning ta zauna tana kallonsa.
"Akramu ka dawo baka nime ni ba ko baka ji sako na gun Humaira ba?"
Akram ya dago kai yana murmushi.
"Ummuna sannu da gidan da fatan na sameku lafiya, kiyi hakuri yunwa ce ta hanani sakat shiyasa nace inna kammala sai na zo'
"Lafiya lau muke, kuma na tabbar yanzu haka baka ci lunch ba, ina jan kunnenka kar ulcer ta kama ka fa"
"Zan gyara insha Allah, Ummuna meyasa ake barin yaran nan fita ne any how?"
"Gidan Meemi suka ce zasu kaga ba zan hana zumunci ba. Kasan saboda in yarda da fitan nasu ko mota basu dauka ba suka bi napep, na kira wayansu shuru, sai Meemi na kira tace wai sun fito tun kafin magrib, kaga ya ci ace sun dawo tunda ba nisa tsakanin malali da nan"
Bai iya bawa Umma amsa ba ya dauki wayarsa ya yi dailing number Meemi, bugu biyu ta dauka.
"Anty Meemi wai ina su Meenal suke? bana son karya ki fada min magana guda daya ta yadda zan cigaba da ganin girmanki"
Meemi ta nisa tare da gyara zama.
"Haba Akram ka bari mu gaisa mana"
"Ina wuyi yasu Irfan? shi kenan munyi gaisuwar, yanzu bani amsata"
"Hmmm Allah ya shirya mana kai, to su Meenal sun ce zasu birthday din wata kawarsu, in suka fadawa Umma ba zata bari su fita ba, kawai dai dan ka cika ni da magana ne da ba zan gaya maka ba dan nayi musu alkawarin hakan"
"Ato in kin boye suka lalace kannanki ne"
Yana fadan haka ya kashe wayar, Meemi taja guntun tsaki.
"Kana da matsala Akram baka taba yiwa mutum magana mai dadi, Allah ya kyauta"
Tace a fili tana mai mikewa ta shige dakinta.
Akram ya mike bayan ya kora ruwan swan ya kalli Umma da duk taji hirarsu da Meemi ya ce.
"Ummuna bari na cimma yaran nan kinji wai sunje birthday din kawarsu"
"Ya rabbi ka shirya min yaran nan, maza kaje ka taso min keyarsu, yan kanana dasu suna niman fin karfinmu"
"Ai Umma Abba zakiwa magana domin shine ya daure musu duk abinda suke yi, ita ma Ammi na taya shi"
Yana fadar haka ya wuce Umma tabi shi da Addu'a. Mota ya shiga ya dannawa Amir kira bugu daga ya dauka.
"Ka fito ka jirani a bakin gate gani nan zuwa"
Yana fadar haka ya kashe wayar. Amir yabi wayarsa da kalloyana jan tsaki.
"Mutum sai shegen son girma, ka wani kirani kamar d'anka kana bani oda, d'an rainin wayo"
Yace yana ciza lebensa na kasa cike da gajiyawa da halin amininsa.
******
Safnah tana shiga gida ta samu Muneera kwance bisa tabarma tana nishi da kyar, hawaye sai kwaranta yake saboda tsabar yunwa. Da sauri ta isa gunta ta zauna tana dagota ta daura kanta bisa cinyarta.
"Sannu Muneera, gashi na samo kudin da zamu siya abinci"
"Anty nima gashi nayo mana bara na samo sauran tuwo kin ganshi har kari uku"
Muslim ya ce yana shigowa cikin gidan ya samu guri ya zauna.
"Meyasa baka jin magana ne Muslim, sai da nace karka fita fa"
"Anty kiyi hakuri Muneera ce ta sani fitar dole dan naga sai nishi take. Ta shi ki fara ci kinji Munee"
Ya kare maganar yana kallonta, Muneera ta mike da kyar ta gyara zama jikinta na rawa ta jawo kwanon, zata soma ci Safnah ta dakatar da ita.
"Muneera bari Muslim yaje ya siyo mana ruwan bunun naira talatin mu fara sha yadda zai warware mana hanji, sai ka biya runfar Safara ka siwo mana tuwo na naira sitti sai ka siyo mana pure water na goma. Kayi sauri ka dawo muzo muyi sallah ko"
Minti ashirin ya dawo da Muslim gida ya same su a daki cikin duhu ba hasken fitila, da yake tuni suka yanke alaka da NEPA saboda basa bada kudin wuta, su da wutar NEPA sai dai su gani a bakota, torchlight dinsu kuwa da suke badawa ayi musu chargy a makota tuni ya lalace, kendil suke amfani da shi shima daya kare kafin su kuma siya sai sun wadatu da abinci ko kawu Bala ya kawo musu, sun riga da sun saba da zaman duhu.
"Anty ku filo waje cikin hasken farin wata na dawo"
"Muslim kayi sallah kuwa?"
"Banyi ba saboda lokacin da kika aike ni an shiga masallaci kafin da dawo an fito"
"Maza dibi ruwa a buta kazo ka gabatar da farali bana so kuna wasa da sallah"
Da to ya amsa ya ajiye sakon bisa tabarma dake shinfide yaje bakin rijiya yayo alwala, yazo kan tabarma daga gefen inda suke zaune ya tada sallah. Kafin ya idar Safnah ta zubawa Muneera ruwar Lipton ta soma sha ita ta tsaya jiran Muslim ya idar su sha lokaci guda. Yana idarwa ya matso kusa dasu ya gyara zama Safnah ta mika masa kofin data zuba masa Lipton ya amsa yana cewa.
"Nagode Anty"
Murmushi ta mayar masa ba tare da tace komai ba sai suka fara sha, bayan sun gama da Lipton suka fara cin dumamen tuwan da Muslim ya samo, suka ci suka koshi hade da tuwon daya siyo suka kora da ruwa, bayan sun kammala Safna ta kama hannun Muslim da Muneera suka hada murya suka soma karanto Addu'an bayan cin abinci.
_"Alhamdulillahil lazi ad'amani hazad da'am war zukunihi min gairi haulin minni wala kuwwa"_
Sai ta saki hannunsu suka shafa.
"Allah ya bamu na kullun kullun"
Cewar Muneera tana murmushi, da Ameen suka amsa kana safnah ta soma yi musu karin karatun littafin akdari da hadda suna amsawa, saboda kusan tanada haddarsa kuma babu haske balle ta nuna musu karatun a cikin littafin fiqhu.
#Rahma ce
#follow
#vote
#Comment
#share
Please