02
Mafarin ko wace Rayuwa numfashi da jini ne, ne numfashin da nake fitarwa ne ya tabbatar da cewar a raye na ke. Sai dai bana iya tantance yadda nawa numfashin yake a yanzu, domin surkinsa da wani kalar iska ne mai dadi shaka. A take na bude idona sai na hango gurin da mutumen yake tsaye kamar anyi ruwa an dauke domin babu alamarsa balle shi din yayi batan dabo bat kamar be taba wanduwa a gurin ba. Wata kila yaji tsoron fuska ta ne dake da bakin gawayi ko kuma rufen idon da nai ya tsorta shi, shiya saka yai hanzarin barin gurin.
Samun kaina nai da murmushin kaina saboda tsoron dana ji, na Lumashe ido ina shakar kamshin turare mai shiga har cikin kwakwalwa ya samawarda natsuwa ga marar ita ga mai ita kuma ya dada masa.
Na risina na dauke kudina da suka zube ina dariyar kaina, domin sai a yanzu abunda nai yake bani dariya na fashe gilashin motar mutane saboda mai motar ya watsa min ruwan kazanta a jiki, wata kila ma ba shi yai ba.
Lokacin dana hango mahaifiyata tana a gaban murhu sai farinciki da jindadi ya lullube ni, domin ba kasafai zaka zo ka tarar an dora girki a gidanmu ba, mun fi siyen garin kwaki mu jika ko muyi kwado (Datu) da kuli mu ci, idan wadatar tai mana yawa muna siyen kanzon tuwon dawa ko na shimkafa mu aje muna ci, hakan yasa na iya sarrafashi ta ko wace siga, idan nai jalof dinsa sam ba zaka ci ka dauka cewar kanzo ka ci ba har sai idan na fada. Ban saba shiga gidanmu da sallama ba, dan haka yin sallamar be dame ni ba sai kawai na karasa gurin mahaifiyata ya kai hannu na bude tukunyar dake kan wuta ina fadin.
“Nana me kike dafawa”
Ba shiri ya yada murfin sakamakon wani azababen zafi da naji a take yan yatsuna sukai ja, sai dai ganin taliya yasa ni manta zafin dana ji duk kuwa da irin halina na raki sai wani farincikin ya kara baibayeni har na hade yawu. Ina son taliya sosai musamman dafuwar masu kudi ba irin tamu ba da sai an sauke muke saka yaji da magi wani lokacin ka gishiri kawai za mu saka mu ci.
“Taliya ce nake dafawa”
Ta bani amsa itama fuskarta dauke da far'a.
“Ina kuka samu kudi?”
“Bayan fitarki Maman Maryam ta aiko mana da ita”
Na yi dariya ina saka hannuna a kwagirina dake kuguna na ciro duk kudin da nai na mika mata, ban san na rage ba balle har na cire wani abu ko da kuwa ina da bukatar siyen wani abu ne, har sai idan Nana ta dauka da kanta ta bani. Gaba daya kudin da nai a yau ba su wuce dari uku da yan canji ba, daman ba ko wace rana ce jumma'a ba.
“Wai Ataa ina kake zuwa baran ne? Kullum kudin da kake samowa be wuce wanda za si abinci da safe ba, da rana haka muke wuni babu komi a ciki inda ba Allah ya kawo mana wani abun ba”
Na yi shiru domin ban san me zan fada mata ba, tana da gaskiya a lokacin da take baran tana tara kudi mai yawa har ma ta siye wani abun ta aje, tsabanin yanzu dana hanata kuma ni bana iya kawo abun kwarai domin ni ba baran na ke ba.
“Nana kin san ni ban iya baran sosai ba, kuma bana son zuwa gurin manyan motoci ba”
“Ka gani Ataa ka cire wannan girman kan, ka raba kanka da girma kai ka ba dan kowa ba, idan za ka dage ka yi bara ka dage domin shi ne komai na mu”
Fada take min amman dariya nake, saboda yadda take kirana namiji kamar yadda take yi ma ko wace mace idan kuma namijin ne sai ta mayarda shi mace, domin ita har yanzu hausarta bata gama fita ba. Sai itama tai dariya domin ta san abunda nake yi ma dariya.
Daga haka na samu na shashantar da maganar na tashi na dauki fassashiyar butar mu na zagaya a inda muka killace na wanke fitsari sannan na fito na saka sabulu na wanke fuskata mai bakin gawayi nai alwala na shiga bukkarmu. Ban samu kanena Lukman a bukkar ba hakan ya tabbatar min da cewar yana islamiya kenan. Iyakar kokarin da nai na canja tufafin jikina ne na saka wasu sannan na soma rama azahar kamin na dora da la'asar. Ba tozarci ba, ni kadaina ina shakkar sallah da muke a bukkarmu domin na taba ji a lokacin da nake zuwa makaranta ana cewa Allah baya karba sai mai tsarki sai dai ban iya banbancewa ba tsarki na fitsari da janaba ko kuwa tsarki irin wannan na tsabtace daki. Babu wanda zai iya zama dakin mu yai minti biyar a ciki saboda zarnin fitsarin Lukma da kuma na kayan daudar da suke bukkarmu ga tarin kwanoni marasa marafe da kuma tarin gwangwayen da Nana take tarawa wai idan suka kai buhu uku zata siyar.
Ina sallamewa kunnuwana suka sato min muryar Lukma dake fadin.
“Nana kin dawo gurin baran?”
Juyo nai da sauri ina kallonsu daga inda nake zaune, daga ita har kanena basu san ina yi ba.
“Nana bara kike zuwa?”
“Ataa idan be je bara ba, da me zan dafa taliyar nan?”
Daga can gaban murhun ta amsa min kai tsaye. Wani abu na ji ya tsaya a kirji wanda ya saba tsaya min a duk lokacin da mahaifiyata taje bara.
“Amman Nana na fada miki zan rika yi ba”
“Ba inda kake zuwa kake zuwa (Nake) kai wani guri kake tafiya dabam”
Na turo baki baki ina bata fuska. Har tai girkin ta gama ni fushi nake ta yi dan taje bara sai dai hakan be hana ni cin taliyarba, sai dai ni sai da naje na siyo man kuli na zuba sama da yaji sannan abun ka da mai kwadayi baki baya son ba dadi.
Washe gari ma kamar ko wace rana sai da haske rana ya leko bukkarmu sannan na farka daga bachi, a maimakon na tashi sai na kara dunkulewa cikin wani tsohon zanen gado wanda rabinsa ya gama yagewa (Barkewa). Bana jin yau zan tafi aikin dana saba zuwa da sunan bara, inda har zan je nai abunda zai kare mutumcin mahaifiyata ita kuma ta zaga baya idona taje bara banga amfanin zuwan nawa ba. Dan haka ban fito daga bukkarmu ba sai kusan tara da rabi duk da kasancewar babu agogo a bukkar balle na iya ganewa sai dai a yadda na auna tara tayi ko ma ta dan gota. A lokacin ne na dauki butarmu na zagaya can nesa da bukkarmu a wani fili da aka ware ban san me za ayi da shi ba, a nan na saba yin ba haya ta a duk lokacin da bukatar hakan ta kamani, domin a wacan gurin da muka zagaye da kwano da sunan bandaki idan mukai ba haya a ciki sai mun kwashe mun kai can nesa mu zubar a kullum ni kuwa zubarwa ne yake bata min rai, na zabi nai nesa da bukkarmu nayi bahayar a inda aka tana da domin yin wani abu.
Bayan na gama na dawo na saka kasa na wanke hannuna sannan na saka sabulu, sai kuma na dora da alwala sannan na shigo dakin nai sallah asuba. Da yaren buzanci mahaifiyata ta fada min cewar na dauki waina mai kuli na ci na tashi muje bara.
“Ni bana son zuwa bara Nana”
“Sai ka je, gaba daya zamu je”
Haka na turo baki na bata fuska sosai kamar zanyi kuka, amman hakan be saka ta kyaleni ba, har sai da na ci wainar ina ta fushi daya kasa boye kyawon fuskata, har sai ta na dauki bakin gawayi da mai na shafe fuskata da shi sai gani na fito wata mummuna kamar ba ni ba.
“Kin fi son ki shafa bakin gawayi kullum a fuskarki kamar wata dodo”
Mahaifiyata ta fada da yaren buzanci, daman can tafi kowa tsarguwa da shafa gawayin da nake domin yafi min kwanciyar hankali da lamana. Ko ba komai hakan hana sa ana min kallon kazama wanda ba karamin kariya yake min ba, na san da ace yan iskan mazan da suke unguwar za su ga ainahin yadda fuskata take wata kila da ace cikinsu wani ya keta min haddi....
Cikin rashin maida hankali na saka tufafin jiya masu kama da farin lela na yafa bakin gyale kamar yadda yawancin buzaye suke yi, mahaifiyata kuma ta yafa fari wanda ya gama dafewa ya canja kala saboda tsufa da kuma lalacewa. Lukman ya dauka yar robar ruwansa da kuma ta bara kamar yadda ya saba Nana kuma ta dauki ghana must go dinta ni kuma na daura jakata (kwajiri) a kuguna sannan na dauko wani tsohon gidan sauro ya rufe a saman bukkarmu a daidai inda kofar dakinmu kana na dauko wano (Langalanga) na rufa a gurin kofar kamar yadda muka saba idan za mu fita unguwa. Nana na gaba ita da Lukman suna firarsu abun shawa'a ni kuma ina baya ina kallonsu har muka isa gaban manyan shagunan da suke gawon nama inda manyan motocin masu kudi suke tsayawa siyen abu. Kamar yadda muka saba a can baya lokacin da muke baran ni nakan tafi gurin wata motar dabam Nana kuma ta tafi gurin wata dabam ita da Lukman idan mun fita tare da shi, idan kuma gida muka bar shi to ni da ita a tare zamu rika bin motoci ko kuma mutanen dake shiga cikin shagunan.
Ba ma magana sai dai mu muka hannu mu marairaice fuska kamar za mu kuka ta yadda mai ba mu zai dauka ba mu da sama balle kasa ya taimaka mana.
Haka muka wuni a gurin muna ta mikawa mutane hannunmu idan ya fito daga mota ko zai shiga wani shago har muka tara da dan yawa, duk abunda mahaifiyata ta siya sai ta aiko Lukman ya kawo min na ci. A haka muke har yamma tai daf da zamu tafi gida na hango wata motar a fake da sauri na nufi motar a zatona akwai mutane ciki sai da na isa sai naga babu kowa a ciki sai dai gilashin motar a sauke yake. Ina juyowa sai naji na bugu mutum, da sauri na dago kai sama ina kallon wanda na buga din, dogo ne mai faffadan kirji mai tsananin fari ga kwarjini da haifa, duniyar kamshinsa ta tunatar da ni cewar shine dai mutumen dana fasawa mota a yanzu ma ji nai na zama wata yar tsuntsuwa, yana ta kallona da fuskarsa mai dauke da walwala kuma ba walwalar ba, ba kuma ra a kira shi da rashin walwala ba, amana dai ba yabo ba fallasa a bayyana yake kana kallonsa kasan abu ne mai hawayin ya dabbata Sunnar murmushi a addininsa. Kwalla nake saboda ainahim zatin fuskarsa da nake kallo, ba hawayen kyawonsa ne ba, ba kuma na rashin far'ar fuskarsa ne ba, na tsoro ne irin wacan tsoron daya kamani jiya a lokacin dana hangoshi tsaye yana kallona, banbancin wacan karon da wannan a jiya fitsari nai yau kuma kwalla ne a idona na tsoro da fargabar abunda zai min. Lokaci daya naji an fisgoni wanda hakan ya bani damar sauke numfashin da ban san ina rike da shi ba sai a yanzu.
“Yana son ya shiga motarsa kin tare nasa hanya Ataa”
Nana ta fada tana rike da hannuna, ji nai na dawo duniyar mutane mai cike da hancin iska. Da hanzari mutumen yai saurin cire jacket din jikinsa ya bar t-shirt saboda na dan shafe shi kadan lokacin da mahaifiyata ta janyo ji domin na bar jikin motarsa, cike da kyankyami ya bude boot ya saka jacket din ya rufe ya dawo mazaunin gaba ya zauna yana goge hannunsa da tissue paper saboda ya rika rigar dana shafi gefenta kadan.
Sai a yanzu na gane, wato duk tsayin da yake yana kallona na jiran na bashi guri ya shiga motarsa ne, amman ba zai iya yi min magana ba, wata kila maganar wahala take masa ko kuma yana kyamar furta kalmar kauce na shiga motata ga mace iri na ne....
Ni dai da kallo na bi motar sai a yanzu na lura da number motar ita ma ZAKI ne rubuce a jikinta, sai dai wannan motar ba irin wacan bace ko a kala balle a kama.
“Miya saki kuka?”
Na na ta tambaya da yaren buzanci tana nuna hawayen fuskarta. Sai na saka hannu na share na bata amsa da hausa ina turo baki kamar wata shagwa6a66iya.
“Tsoro na ji”
Dariya tai Lukma ma yai min dariya ni kuma na kara turo bakin kamar zan cireshi gaba daya...
Sai da aka fara kiran sallah sannan muka dawo gida, a yau ma yar kullum ce sai da na wanke fuskata sannan na rama sallar da ake bina kana nai sauran, Mahaifiyata akam ba a magana domin sallah bata dame ta bayan sallah asuba bana jin tana wata Sallah sai idan ta kama. Lukman Nana ta aika ya siyo mana gari da sugar muka jika muka sha, ni kuma na roki Nana naira hansin a kudin dana samo ta bani na siyama kyanwata kifi na bata, tana ci ina shafata ina murmushi ina sonta sosai domin Allah ya saka min son kyanwa musamman wannan da muka sabu wani lokacin har fita nake da ita idan zan je wani gurin.
Washe gari ma haka na farka raina fes zuciyata kal kamar yadda na saba farka a ko wace safiya ta Allah duk kuwa da irin rashin da muke da shi. Sai dai yau ta sha banban, dan kekasa kasa nai na ki yarda na bi mahaifiyata da taga bana son zuwa sai ta kyaleni a bisa sharadin zan je inda na saba yi nai ba tare da ita ba. Bayan ta fita nima na shirya na shiga kangon gidan nan na dauki kayan aikina na kama hanyar Flyover din Alu. Ina isa na fara aikina na wanki mota a biyani, idan na hango manyan motoci na fi saurin zuwa na wanke musu domin sun fi baka kudi tsabanin na direbobi da wasu sai dai su wuce su barka ma ba tare da sun baka komai ba, wasu kuma su samma maka abunda ya samu.
Wata fara mota mai bakin gilashi na zubawa mai na fesa mata ruwa ina gogewa kamin traffic ya sakesu, bayan na gama na dawo ta gaban gilashin motar ina jiran mai ita ya sauke gilashin ya bani wani abu, A hankali aka zuke gulashin motar sai fuskar mutumen nan na jiya da shekaranjiya ta bayyana, a maimaikon ya bani kudina sai ya miko naga an zuro min hannu.
“Ba ni wayar da kika sata?”
Hannun na mace ne haka zalika muryar ma ta mace ce, sa tsakanin ba ni wayar da kika sata da kallonsa fuskarka da nake sai na rasa wane yafi wani razanar da ni, duk kuwa da kasancewar ba ni yake kallo dan da alama ni din ma ban isashe shi kallo ba, traffic kawai yake jiran a sake ya ja motarsa...