FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Official Khadeeja Candy ✍🏻 Author • Entrepreneur CEO, Khadeeja Candy Store ☎️ •- ***
Sample · 01
Carar Zakaran dake harabar gidan ne ya katse min dogon bachin da nake. A hankali na matsa fuskata dauke da murmushi domin ko kadan hakan be bata min rai ba, na daga hannuna a sama ina mika tare da kara watsakewa, kamar kullum yau ma bachin ya min dadi, ba dan gurin da nake kwanciyar ba, sai dan farinciki da kwanciyar hankali da natsuwa irin ta masu wadatar zuci data cika min zuciyata nake kwanciya da ita a kowane dare. Kamar wacce akai wa dole haka na bude manyan kuma lussasun idanuwana da suka rine suka sauya kala sakamakon dadewar da nai ina bachin. Akan farinciki na sauke idonuwana wato mahaifiyata wacce ke sanye da wani jan yade kodadden irin na talakawa kuma na gadonmu."Wainar ki ce take ci tun dazun aka aje miki" Da yaren buzanci mahaifiyata take muna min kyanwar dake kusada ni tana cin waina.Murmushi nai na kai hannuna na shafa kyanwar kana na shiga mata magana da yaren buranci. "Kin cinye min waina ko?""Ataa yau ba za ki je baranki ba ne?"Kanane ya tambaya, hakan yasa ni saurin tashi daga kwancen da nake, na fito daga cikin bunkar ina hamma ba tare dana rufe bakina ba, ba dan kuma ban san babu kyau ba, sai dan rashin kula da watsi da addini irin na mu na... Da hanzari na nufi wani dan guri da muka killace da kwano domin yin wanka ko kuma ba haya. Ba wanka nai ba domin wanka be dame ni ba duk kuwa da kasancewar na fi kowa tsabta a cikin gidan mu amman a hakan sai na kwana uku ban yi wanka ba. Fitsari kawai nai na fito da sauri na wanke fuskata da fassashiyar butarmu marar murfi, sai da na gama wanke fuskar sannan na nufi gurin da muke girki na dauki gawayin kara na saka a bakina na tauna na saka yatsana na wanke bakin na kuskure sannan na wanke kafafuwana na nufo bukkarmu da sauri tuna ban yi sallah ba yasa na dawo na dauki butar nai alwala na sake kowa bukkar wanda zan iya kiransa da dakinmu. Zanen dake daure a kirjina na cire na dauki riga da wando na wani shudin yadi mai kamar laile na saka na dauki hijab na saka nai sallah mai kamar asha ruwan tsuntsaye, wato da sauri domin cikin kannanen lokaci na yi na gama. Bakin dankwali na dauka na cire hijab din kaina na saka bakin dankwalin mai kama da karamin gyale na rufe kaina kamar yadda na saba ko kuma na ce muka saba.Na kai hannu na dauko madubi tare da gawayin dana daka na kwaba tare da man shafi a guri daya, tsayawa nai kallon kaina a madubin ina murmushin daya kara bayyanar da kyauwona har dimple dina suka bayyana, sai faman lumshen manyan idanuwana nake ina budewa. Abu ne da ya ke bayyane, bana bukatar kowa ya kalleni ya fada min cewar ina da kyau, kyau na hali ko na halitta kyau na jiki ko na fuska, ni kaina idan na kalli madubi kyawona tsorata ni yake, idan ba a kirani balaraba ba to ba za a cireni a jinsin india ba indiyawan ma sai an tona, hakika ni kaina na sa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.