ZAKI

04

by @khadeejacandy

Misalin goma aka shigo da ita tiyata amman basu fito ba sai karfe uku da wani abu na dare. 

Anyi mata tiyata cikin nasarar Allah da iyawarsa, saidai a halin da naga mahaifiyata sai na kara matso da maraicin mu kusa ni da Lukman. A wani dakin mai kyau aka ajeta kamar matar wani babban mutum ko kuma wata hajiya, a jikinta an manna mata wasu na'urori har a hancinta a wani abu mai kamar kwanfuwuta nake kallon tafiyar numfashinta, sai dai tana kwance a gurin kamar gawa jikinta babu tufafi sai wani zanen asibiti da aka saka a lulluba mata. 

Ina tare da ita har asuba ban runtsa ba, gani nake kamar zata iya farkowa ta bukuci wani abun ko da yake babu komai a tare da ni wanda zata iya ci ko ta sha, lukman ne kawai ke ta bachinsa hankalinsa kwance. 

 Misalin takwas da rabi likitan ya shigo cikin shiga ta kananan kaya da rigar likitoci a samansu fuskarsa a sake yana ta min murmushi kamar mun saba. 


“Ina kwana?”


Na gaisheshi cikin girmamawa. Sai ya amsa min kamar be gane ni ba, ba kuma kallon rashin ganewar bane, wata kila sai a yau ne yake tantance irin hallittar da Allah yai ta kyau mai daukar hankalin mace balle kuma namiji. 


“Miye sunanki?”


“Aisha amman ana kirana Ataa”


“A nan kuka kwana?”


Ya tambaya yana kara tantance kyawun surar jikina. 


“Eh”


“Ayyah ban sani ba ai da na kawo muku abun shimfida ko kina da shi”


Na girgiza kai alamar aa a cikin yanayin dake nuna dukan hankalina da damuwata tana gurin mahaifiyata ne. 


“Da gaske baki da kowa a nan Nigeria? Ku yan nijar ba naga akwai wadanda suke da yan'uwa a nan ba?”


“Ni ba mu da su, ba a mu da kowa a nan”


Na fada masa cike da gundira da tambayoyinsa. Sai naga yayi murmushi kamar wanda jin hakan yai masa dadi, sai ya saka hannunsa aljihu ya nufi mahaifiyata yana dubata. 


“Ki samo riga ki saka mata da zanen da zai iya rufe kafafunta, na bada a siyo mata maganin dubu dari da bakwai manyan magunguna ne masu tsada yadda mahaifiyarki za tai saurin jin sauki kuma an mata allurar bayan na mata sai nai mata operation na cire mata dafin macijin”


Wani irin dadi ne ya lullube ni sai na rasa ta inda zan fara masa godiya, hawayen farinciki suka cika ido har naji kamar na dauke shi na hade, a rayuwata ta duniya tunda Nana ta haife ni ban taba karo ko ganin mutum mai tausayi da jinkan masarasa irinmu ba kamar wannan likitan. 


“Na gode Allah ya biyaka ya saka mata da alheri, Allah ya daukaka asibitinku Ya saka maka da aljanna ka taimaki rayuwata sosai ba zan taba manta ka ba”


Murmushi yai yasa hannunsa aljihu ya ciro kudin da za su kai dubu goma ya miko min. 


“Ga wannan, ki je ki siya abinci ki yi duk abunda kike bukata, kuma idan mahaifiyarki ta farka ki kirani karki bata komai”


Wannan karon addu'ar gamawa da duniya nai masa, domin a tunani ita kan aljannah da duniyar duka ya sameta, domin mutum mai taimako mai share hawayen masara shi Allah yai masa alkawarin aljanna kamar yadda Annabi yace shi da mai taimakon maraya kafada da kafada za su shiga aljanna da shi. Babu abunda nake hangowa sai matarsa tabbas tayi dacen miji domin samun miji mai taimakawa al'umma har su yi masa addu'a ta yi babban dace. 

Bayan ya fice ne na kama hannun Lukman muka fita zuwa gida, sai dai abunda na tarar a gidan sai yafi tada hankalina fiye da ciwon mahaifiyata. Yar bukkarmu ce aka hankade can gefe aka cire kwannon da maihaifiyata ta saka domin zagaya yin fitsari ko ba haya, kayan abincinmu da tufafinmu an watsar da su can gefe gaba daya an watsar da komai. Tsaye nai ina kallon yadda kayan idona cike da kwalla, ba komai yasa ake mana haka ba sai rashin, rashi kuma na kudi saboda talaucin da yake tare da mu da kuma rashin kowa a kusa da mu. Lallai muhalli babban abu ne, da ace haya muke ko mallakinmu ne da wani be isa ya wulakanta haka ba saboda kawai mun raba a gidansa dan mu zauna. 


“Ataa waya maka mana?”


Lukman ya tambaya yana bata fuska kamar zai yi kuka, ban da jansa jikina na rumgume babu abunda nai domin ina jin idan har na bude baki nai masa magana kuke kawai zai fito domin shine cike a zuciyata. Waiga nai banga kowa ba, da alama ba aikin yau ba ne idan kuma har yau akai shi tabbas tun da farar safiya aka zo aka mana haka aka tafi. Bani da wani zafi daya wuce na share hawayena na shiga hada tarkacen mu ni da Lukman babu inda zan kaisu gashi ni kuma ban iya hada bukkar ba balle na sake yin wata, Nana ce ta iya hadawa ita kuma tana asibiti, ance zuciyata tana ga mai kudi idan aka masa abu sau daya ba za akara ba, domin zai dauki mataki wanda bashi da shi kuwa sai ayi ta maimata masa kuma ya shanye yai hakuri saboda bashi da shi, ganin babu inda zan kai kayan yasa na hada komai na je can cikin wani daki da yake a kangon gidan da ba a karasa ba na saka su ni da Lukman sannan na fito waje na samo duwatsu na hada murhu na dauki jaran bukkarmu na saka na aiki Lukaman ya siyo mana ashana da taliya da cefanen dafa taliyar. Ni kuma na wanke tukunyar da mike girki da ita sannan na gyara tarugu da albasa na nufi gidansu kawata Farida dan na jajjaga, da nai sallama mahaifiyarta na ji taki ta amsa min a zatonta rokin wani abun na zo kasancewar wani lokacin idan ba mu da ashana ko gishiri tana aikawa tace ta sammata, har take yawan cewa wai mun cika roko, ni ko a ganina duk wanda zai mika maka hannu yace ka bashi tabbatas oa fishi kuma dan kana da shi ne ake zuwa nema a gareka amman mutane da yawa ba su fahimci hakan ba. Sai da na karasa har bakin kofarta ina sallamar sannan ta amsa min na gaisheta ta amsa ciki ciki. 


“Dan Allah turminku za ara min zan jajjaga tarugu ne”


A tsaye ta bar ni a gurin na kusan minti biyar tana ta kallon arewa 24 a karamin tv ta sannan ta dago ta kalleni. 


“Gashi can gidan kin gama ki dauraye”


Ta fada min a cikin yanayin da ke nuna alamar bata son ara min kamar yadda take yawan yi min idan na zo nema abu, shiyasa bana son zuwa idan ba Farida ce a gidan ba ita ce mai min maraba wani lokacin har ta tayani dakawa duk kuwa da irin fadan da mahaifiyarta take mata na kin jinin abotarmu da take. Ni kuma babu wani gida da zan iya zuwa na roki abu kamar irin gishiri ruwa ko ashana ko daka wani abu kamar wannan gidan, domin duka gidanjen da suke kewaye da mu na manyan mutane ne, a ina zan iya shiga roko ayi min kallo banza wani gidan ma ko gate din su ka taba sai mai gadin yace maka basa nan saboda kawai anga yanayinka na masu bukata ne. 

Daf da zan gama jajjagen ne take tambaya wai ance maciji ya tsari mahaifiyata, ni kuma na amsa mata na kuma bata labarin yadda abun ya faru har ma da taimakon da aka mana a asibiti, sannan na kwashe jajjagen na wanke mata turminta kamar yadda ta bukata na yi mata godiya na juyo na fito. 

 Hura wutar na fara yi na dora tukunyar na zuba mai da sauran abubuwa a take saboda tsananin yunwar da nake ji, haka nai ta bankawa girkin wuta har ya dafu na zubawa Nana a wani kwanon mai murfi Lukman kuma na saka masa a nasa kwano na zubawa kaina, na kwashe saura a wani kwanon na rufe, sai na zauna na tisa abincin a gaba na kasa ci babu komai a zuciyata sai kewar mahaifiyata da tunanin ruguje mana bukka da akai, a take na nemi yunwar na rasa, kuka ya maye min gurbinta har sai da Lukman din ma ya fashe da kuka ganin yadda nake ta kuka. Abincin na aje na shiga ciki na daukowa Nana riga da zane na saka a jakar da kudin suke ciki na jira Lukman ya gama cin abinci ya wanke hannunsa sannan na dauki abincin Nana muka fito bakin titi na tari Napep muka shiga ni da shi muka doshi asibitin. 




ALIYU POV. 


Bachi Rahama take ta yi tun bayan sallah asuba har goma ta gota, a saman wani katon gado mai tsada da katifa mai kyau take kwance, ta lulluba da blanket mai laushi kamar kada, ta saba da hutu da jindadi haka take bachi har sai ta gaji dan kanta ta farka. 

 A lokacin Aliyu na falo zaune saman wata lallausar kujera rike da kofin tea laptop a saman ciyoyinsa yana duba yanayin yadda aikin gas din kamfaninsu na Abuja yake tafiya. Sanye yake da short jean da farar vest, a gabansa wani katon tv ne mai dauki da farar baturiya tana watso labarai a channel din Al Jazeera. Wayar ce dake silent tai haske sai dai be lura ba, domin ya cire ringing din, baya so hayaniya ko kadan that's why he choose Abuja a gurin aikinsa to because its a quiet place for him, ko da wani meeting din ne ya taso wanda yasan za a iya hayaniya da cece kuce sai ya tura abokinsa Umar. Be lura da kiran ba har sai da ya gama abunda zai yi ya juya da zimmar aje laptop din sai ya hango wayarsa tana haske, hannu ya kai ya dauki wayar ganin Doc Asim yasa shi sauri picking. 


“Hello Doc”


“Ranka ya dade ina ta kira baka dauka ba”


“Yeah ina wani aikin ne, sai yanzu na lura”


“Na kira na maka albishir ne cewar an samu Kidney din”


Kofin tea dake hannunsa ya aje ya mike tsaye da sauri cike da farinciki marar misaltuwa har ya saka shi kin yarda da maganar da Doc ya fara masa sai da ya sake tambaya duk kuwa da yasan be taba masa karya ba. 


“Doc are you serious?”


“Wallahi da gaske nake, gani nan ma gurin Alhaji abunda muke tattaunawa kenan”


“Wow gani nan zuwa”


Yai saurin waje wayar ya nufi bedroom dinsa cike da farinciki, labulayen dake fuskarta gadon ya bude sai ga hasken rana yana haske gadon kasancewar gaba daya gaban dakin glass ne. Jin hasken rana yasa ta lunkumewa cikin blanket tana bata fuska, sai ya zauna bakin gadon ya yaye blanket din ya dagota.


“Dear wake up yau ranar farinciki ce”


“Ba yau na ke birthday ba sai next month”


Ta fada ba tare data bude idon ba. 


“Ba maganar birthday za ki yi birthday cikin koshin lafiya In-Sha-Allah, Doc Asim ya kirani ya fada min yana gurin Daddy suna tattaunawa an samu Kidney din”


Ba idonta kadai ta bude ba har da baki da da hancinta duk a bude suke jin wannan daddan labarin, da sauri ta kama hannayensa. 


“Dear da gaske”


Ya gyada mata kai yana kallonta da cat eyes dinshi sai ta rungume shi da sauri ta fashe da kukan dadi. Dan murmushi yai kadan ya shafa bayanta. 


“Congratulations Dear you save me”


“I said i would”


Ya fada yana dagota daga kirjinsa yana share mata hawayenta. 


“Tashi ki shirya zan kaiki gidanku ni kuma na wuce gurin Daddy na gana da likitan naji yadda za ayi”


“I love you”


Ta fada tana kuka, sannan ta daga daga jikinsa ta sauka ta shiga bathroom ta sauka cikin kankanen lokaci ta fito shima ya shiga yai ko daya fito har ta shirya, shima be dade gurin shiryawa ba dan ya matsu ya hadu da likitan.


“Idan munje can zaki karya promise?”


“Promise”


Ta fada tana saka bakinta cikin nashi, musanyar yawu sukai halshenta da nashi suka hada auratayya sannan ta sake shi ya rika hannunta suka fito tare. A tare suka sauko kasa hawayen farinciki tana cika idonta, har ya bude mata motar ta shiga sannan ya zagaya ya shiga ya yai mata key tun kamin yai horn mai gadin ya bude masa gate suka kama hanya gidan Alhaji Nasiru Gobir. 

 Cikin kankanen lokaci suka isa gidan nan ma horn daya yai aka bude masa gate, tun kamin yai parking Rahama ta bude motar ta fita ta shiga cikin gidansu da sauri, shi kan sai da ya faka motar sannan ya fito ya rufa mata baya. A falo ya sameta tana zaune kusa da mahaifinta.


“Daddy naga kamar kana cikin bacin rai”


“Wallahi wasu wulakantaccin mutane suka shige min a gidan da nake ginawa a Clapperto road, ance sun janyo har macizai suna shiga gidan, amman na ce a korasu”


Hannunsa ta kama. 


“Daddy kar wannan ya dame ka yau rabar murna ce na Doc Asim ya kira wai an samu kidney din”


“What”


Gaba daya suka amsa har kanenenta suka taso ta sauri suka rumgume ta suna ta murna. Alhaji Nasiru ya kalli Aliyu irin kallon ganin kima da kauna ta suruki da surukinsa. 


“Mun gode sosai Aliyu Allah ya saka da alheri”


“Karka damu Alhaji aikina samawa Mamata lafiya ko ta hali yaya, zanje gida san na samu ganawa da likitan”


Daga haka yai musu sallama ya fito ya shiga motarsa ya dauki hanyar family dinsu wato gidan Alhaji Garba Fayau...