ƘADDARARREN AL'AMARI

04

by @rahmakabir13

*ƘADDARARREN AL'AMARI*


© *Rahma Kabir*

     Mrs MG


Wattpad @Rahmakabir.


*04*


Suna isa gida suka tasa keyarsu part din Abba, sun same su zaune a falon kamar yadda suka barsu, Akram ya kaisu gabansu Umma suka tsaya tsamo tsamo kamar wanda suka fito daga cikin ruwa.


"Ga su nan mun gansu a hanya, da alama daga wani gun suka fito kuma duk alamun rashin Gaskiya ya bayyana a fuskarsu"


Umma ta mike tana binsu da kallo idonta ya kawo kwalla amma sai ta dake ta danne zuciyarta ta ce cikin daga murya.


"Yanzu kun kyauta mana kenan, ji irin shigarku kamar 'ya'yan da basa kallon gabas, ni dai badan nasan haihuwarku ba dana ce sauya mana ku aka yi, domin duk cikin zuri'an mu babu masu irin halinku duk kuwa da daular da muke ciki mun tsayu bisa tatiyyanku, Allah ya shirye ku"


Ta juya ga Akram.


"Ka musu duk hukuncin daya kamata karka raga musu"


Tana kai wa nan a zancenta ta wuce part dinta cike da kunan rai, su Teema suka kara fashewa da sabon kuka, basu da bakin magana tabbas dan sun gama tado fushin Umma, Humaira ta mike ta kallesu sama da kasa.


"Amma albasa bata yi halin ruwa ba Allah ya shirye ku"


Sai ta wuce dan ta nufi wurin aikinta dama rashin ganinsu yasa ta tsayawa a gidan, tana ta jajjada Addu'an shiriya ga yan uwanta.


Abba shima da yake daure musu yau ya nuna musu iyakarsu ya mike yana kallon Akram.


"Daga yau na danka kular shege da ficensu a hannunka, a da ina ganin zaku daina shiyasa nake shigar muku, amma tunda kunce kunnen kashi gareku to na zame hannuna daga yau duk abinda kuka yi a hukuntaku dai dai da yadda suka aikata"


Sai ya haura sama abinsa. Mami ma yau ba bakin magana dan haka itama bin bayan Abba tayi da yake itace keda girki, tana jin yau in ba a hukunta su ba zuciyarta ba zata ji dadi ba domin sun sata a damuwa. Akram ya zauna inda Humaira ta tashi ya fara magana cikin kasa da murya fuska daure, dama shi da zarar ransa ya baci a murya ake fara ganewa.


"Fateema, Ameena, yanzu kunfi son ku sabawa Allah sannan muma ku bata mana rai, ku gata ya zame muku hauka ko?, ku sani a kwai mutane da dama da suke son su taka matsayinku amma basu samu ba kuma duk da haka sun kasance masu godiyar Allah. Nasan cewa Abba da Mami sune duka daure muku kuyi duk abinda kuka ga dama ko, to ku sani wlh zan muku zargen da ba zaku taba iya kwancewa ba, kuma wannan shine last warning da zan muku duk ran da na kuma ganin rana mai kamar ta yau hmmm zaku sha mamaki na fiye da zatonku"


"Ai wlh nima zan basu mamaki ba kai kadai ba domin banyi zaton iskansu ya kai haka ba, kuma daga yau ba zaku kara tuka motocinku ba duk inda zaku sai dai driver ya kaimu kuma fita ta yanke sai zuwa makaranta kawai"


Cewar Amir yana hura hanci cike da masifa. Su Teema babu bakin magana sai hawaye da suke sharewa. Haka suka tasa su a gaba suka yi musu tatas har sai da suka gommaci duka da wannan fadar da suke musu, sunyi kuka da magiya da bada hakuri amma basu barsu ba har sai da suka kwashi kusan awa guda kana daga bisani suka sallame su suka wuce dakinsu dake bangaren Umma.


*****


Safna bata samu halin kaiwa su Muneera abinci ba saboda aiki yayi yawa dan runfar Haj. Uwale kullun cike yake da jama'a babu masaka tsinke, Safna ta tara abinci mai yawa a leda wanda in mutane suka ci suka rage sai ta juye a leda, shi zata kaiwa kannenta suci, duk da dai ita ta shi ta koshi saboda Haj. Uwale bata barin ma'aikatanta da yunwa, Safna duk tabi ta damu saboda ta san suna can cikin yunwa da kosawar dawowarta. karfe biyu ta wuce ta isa in da hajiya ke zaune ta tsuguna kamar mai rokar gafara.


"Ummm Hajiya zanje gida in dawo"


"A'a lokacin tashinki bai yi ba ki kira sai na sallameki, ko kin gaji da aikin ne ba zaki iya ba? Bana so tun yanzu mu fara haka dake ki kiyaye"


"To insha Allahu Kiyi hakuri"


Tana gama fadar haka ta mike jiki ba kwari ta koma mazaunin ta. Can gida kuwa su Muslim sun jita shuru sai ya yanke shawarar zuwa bara dan ba zasu jure yunwan ba, kokon da suka sha ya gama fita a fitsari suna bukatar abu mai nauyi, haka ya bar Muneera ita kadai a gida ya shiga unguwar masu hannu da shuni na s.m.c ya soma bara, cikin nasarar Ubangiji ya samu sauron tuwon shinkafa miyar kubewa busasshe harda nama, duk da dai miyar tayi tsami haka ya dawo gida cike da zumudi ya samu Muneera kwance lamama akan tabarma tana nishin kukan yunwa, da sauri ya isa gareta ya aje kwanan tuwan ya dagota.


"Yi hakuri auta gashi na samo mana tuwo, wanko hannunki kizo muci"


Guntun murmushi tayi masa dan ta kasa iya furta komai haka ya dibo musu ruwa suka wanke hannu kana suka soma cin tuwon a tare ba tare daya raba musu kwano ba, duk da tsamin miyar basu ji ba burinsu su cika kundunsu su samu salama.


**

Bayan sallar Magrib.


Safnah sun kammala aiki komai sun ajeshi a mazauninsa an rufe shago, Haj uwale ta sallami sauran yaran ta kalli Safnah tare da mika mata karamar jakar buhu.


"Ke kuma muje gida inna kallama dake sai ki tafi ko"


Idon safnah ya kawo kwalla tana son yin magana amma tana tsoron kar tayi laifin da zata koreta, haka ta amsa ba um ba um um suka hau napep ya wuce dasu gidan hajiya dake unguwar rimi. Suna shiga Hajiya ta umarceta data gyara mata daki Wanda yake ciki daya amma yada da girma, shinfide yake da tiles, sai babbar katifa dake kwance a kasa, ga kayan kallo sai karamin kitchen a ciki da bayi. Haka ta yi shara ta gyara gado tare da yin mopping bayan ta gama ta dauro alwalar sallar isha'i domin ana ta kira a masallaci. Haka ta gabatar da sallah data idar ta fito ta samu hajiya a taskar gida zaune bisa babbar tabarma yan mata sun kewayeta suna hira da shewa ga wasu dandali maza da mata a can gefe kowa yana sha'anin gabansa, jikin safna yayi sanyi sosai a zuciyarta ta fara hango mata kalar rayuwar gidan Haj. Uwale, haka ta cije ta karasa kusa dasu ta risina kana ta ce.


"Hajiya zan tafi na gama komai"


"Au ni bana manta dake ba, ga wannan dari biyu ne Kiyi kudin mota sai gobe in Allah ya kaimu ki zo da wuri dan akwai aiki sosai"


Ta amsa kudin tana cewa to tare da yi mata sallama sai ta wuce ta fita, yan mata dake gurin duk suka bita da kallo wata daga ciki ta ce.


"Hajiya ina kika samo yarinya haka mai danyen jini gata da kyau duk da dai alamu sun nuna tana cikin bukata"


"Hmmm wlh kuwa marainiya ce a haka ma ita ke kula da kannenta shiyasa na dauketa aiki, daga bisani kuma naga ya kamata na daurata akan network yadda zan samu alkhairi a dalilinta"


"Amma hajiya da baki yi haka ba tunda yarinya ce, mu ko kinga mune muka kawo kanmu ki duba maraicinta" 


Cewar wata babbar mace Kawar hajiyar,


"Ke rabani babu maraya sai rago, kin ga gwara na koyar da ita niman na kai, nan gaba sai kiga ta dalilinta ina kama hatimin nasara da kyau ina juyawa, manyan kasa suna sintiri a kofar gida na"


Sai duk suka kwashe da dariya wasu harda tafi. Haka suka yi ta tattaunawa.


Safnah ta fito taga kofar gidan cike da juma'a maza da mata sai bushe bushen taba suke da sholi, tsayawa tayi tana kallonsu cike da ta'ajibi, babu wanda yabi ta kanta sai da ta bata kusan minti goma kafin taja kafafunta da suka yi mata nauyi tana ayyana barin aiki da hajiya a ranta, sai dai wani bangare na zuciyarta yana tunatar da ita bata da mafita sai wannan aikin, a haka ta yi nisa a tafiya ta, rashin jin hayaniya ya dawo da ita tunani nan ta gane cewar ta baro arean jama'a ta fado layin da ba mutane, ga karancin hasken wutar lantarki, saita kara sauri domin tabar unguwar ta isa babban hanya da zai sadata da abin hawa. A haka wani napap ya kunno cikin layin da gudu ganin haka yasa Safna ta tsaya tana sa hannu da su tsaya a tunaninta mai adaidata ne, haka suka tsaya a gabanta sai taga duk maza ne sun cike motar, gaban tane ya fadi amma ta dake ta hadiye miyau ta ce.


"naga a cike ya kuje kawai"


"Yan mata ki shigo mu rage miki hanya mana zai ishemu"


Daya daga ciki yayi maganar wanda alamu sun nuna a buge yake da abin maye, Safnah ganin zasu bata mata lokaci gashi a tsorace take dasu sai ta juya ta cigaba da tafiya ba tare da ta kara yin magana ba sai ta kara saurin tafiyar ta, ganin ta wuce yasa suka koma napep din suka bita, Safna tana jin sun biyo bayanta ta ari na kare gudu take suna binta ga layin mai shegen tsawo ihunka banza barinka hofi, haka suka sha gabanta da napep din suka firfito tare da adda da kwari da baka hakan ya nuna cewar yan daba ne, 


Jikinta ya soma rawa ga nishin gudu da take yi fishari ya matse mata mara cikin ta ya soma kugawa kamar ana hura wuta, sai gumi take hadawa kamar wacce ta hadiyi karfe, daya daga ciki ya nuna ta da adda.


"Ke dan ubanki har kin isa ki raina mu ana miki magana, sai in faffarke miki ciki babu uban da ya isa ya kama mu"


"Kuyi hakuri" 


Ta iya furtawa baki na rawa, wani daga ciki yace.


"Abbati rabu da ita kawai mu tafi da ita sai mu huta, kasan ina fama da kishin rashin Ladidi tunda ta tafi kauyensu ban sake kai ziyara Maji dadi ba" 


Sai suka kwashe da dariya, Safna ta fashe da kuka domin ta fahimci inda maganarsu ta dosa, haka ta gyara tsayuwa sai ta dai dai ci gefensu ta arce a guje sai duk suka rufa mata baya ogansu yana cewa.


"Karku bari ta tsare musu ku kamota" 


Sai ya shige napep din yabi bayansu, haka suke ta gudu kamar zasu tashi dama, ita kanta Safna wani karfi taji a jikinta duk gajiyarta taji ya tafi gudu take kamar na ceton rai, a haka ta kai Karshen layin ta sha kwanan wata unguwa dai dai kunnowar wata mota har ta kusa bogeta, mai motar ya ja ya tsaya da karfi itama kem tsayawa tayi dan ta sadakar zai bigeta, jin bai bigeta ba yasa ta dawo cikin hayyacinta ta matsa gefe ga yan daban sun tsaya cirko cirko suna haki tare da kallonta.


Akram ne a motar yaje gidansu Amir a kan hanyarsa ta komawa gida yana sauri dan Abbansu ya kirasa yana jiransa, yayi kicibis da Safnah, sai ya ja dogon tsaki tsaninan haushi ya turnike shi, ya bugi sitiyarin mota domin ya gano biyota suka yi, sai duk ransa ya kara baci, cikin sauri ya bude ma'ajiyarsa dake motar ya ciro wata karamar bindiga ya fito rike da ita dan wannan ne kadai zai iya kare kansa da shi. Ya tsaya jikin gabar motar ya zauna tare da gyara alburushin dake ciki, Safna tuni ta matso kusa da Akram ta ja ta tsaya dan ta tabbatar ta samu makafa, su Abbati ganin bindigar sai suka fara ja da baya suna kananun surutu, a haka ogansu ya cimmusu yana cewa.


"Ku auka masa mana ku kamota"


"Haba oga baka ganin bindiga ne a hannunsa"


"Matsoracin banza ka sani kota roba ne yake mana barazana"


Bai rufe maki ba Akram ya danna kunamar bindigar sama ji kake tasss domin su tabbatar bata wasa bane. Ai kafin kimtawan ido sun arce a guje hatta ogan nasu fita yayi a napep din ya ara a na kare. Abin ya bawa Akram dariya sai yayi murmushin gefen baki, kana ya tashi daga jikin motar yaje ya bude ya mayar da bindigar ma'ajiyarta kana ya fito ya tsaya yana kallon Safna cike da jin haushinta. Sunkuyar da kai tayi ta kasa cewa komai.


Bata an kara ba taji saukar lafiyayyen mari a kumatunta ya kara mata da rankwashi, a razane ta dago tana mai dafe kanta da kuncinta da duk hannunta, haka suka yi ido hudu yana mata kallon tsana da kyama yace a hasale...


#Rahma ce

#follow

#vote

#Comment

#share

Please