ƘADDARARREN AL'AMARI

06

by @rahmakabir13

*ƘADDARARREN AL'AMARI*


© *Rahma Kabir*

     Mrs MG


Wattpad @Rahmakabir.


06


Humaira tana isa sashin Akram ta shiga buga masa kofa, Akram da barci ya fara kama shi ya tashi da sauri ya zo ya bude kofar, ganin Humaira ce sai ya saki murmushi.


"Lafiya zaki zo kina buga kofa cikin Daren nan? ai da sai ki kirani a waya in Umma ce ta aiko ki, bana so kuna gilmawa cikin huduwan daren, kin san ba mu ka dai muke rayuwa ba saboda yanzu lokacin da aljanu suke yin nasu hidimar"


"Yaya Akram" 


Ta kira sunansa hawaye na sauka a idonta, ganin haka yasa ya tabbatar ba lafiya ba, juyawa yayi cikin falonsa tabi bayansa, Sai duk suka samu waje suka zauna. Akram ya tambayeta me yake damunta. Humaira ta gyara zama ta shiga koro masa labarin duk abinda taji su Meena suna magana akai, Akram ya mike a zabure kamar an tsikareshi, innalillahi... kawai yake ambata a bakinsa. 


"Abinda ake kujewa yaran nan kenan basa ji, muna zaman mu lafiya zasu dauko mana masifa. Humaira tashi kije karki nuna musu kin ji komai, ni bari na je yanzu dole ne a yiwa abin tufka da wuri kamin a watsa mana mutuncin gidanmu"


Humaira ta yi masa sai da safe kana ta wuce sashin Umma. Akram kuwa fita yayi zuwa part din Mami. 


Yana shiga ya wuce dakin Meena bako sallah ya fada ciki, fuska daure har wani jaaa yayi saboda Bacin rai, dukansu suka mike tsaye babu inda jikinsu bai rawa a zuwa lokacin sun san cewa Seema ta gama yada hotunansu, in ba haka ba to me zai kawo yayansu a irin wannan yanayin, Akram binsu yayi da kallo domin alamun rashin gaskiya ya bayyana a fuskarsu, sunyi tsuru tsuru kamar mage a kwali, girgiza kai yayi ya matso gabda su.


"Ku bani wayoyinku kuma duk ku ciresu a key"


Meena da teema suka kalli juna duk zuciyarsu tana wani irin harbawa kamar zai faso kirjinsu. 


"Nace ku bani"


Yayi maganar cikin daka tsawa, jiki na bari suka cire wayoyin a key suka mika masa hawaye nabin kuncinsu kamar famfo.


"Wacece Aisha?"


A wannan lokacin sun gama firgita, kafafunsu ba zasu iya daukarsu ba sai suka zube a kan guiwowinsu suna mai fidda kuka mai tsananin sauti wanda har falo za a iya jinsu. 


"Yaya Akram wlh sharri suke mana bamu aikata komai ba"


Cewar Meena cikin kuka.


"Na atambaye ku me kuka yi ne? Kawai ku gaya min wacece Aisha"


"Kawarmu ce school dinmu daya, ita ce muka je birthday dinta"


Cewar Teema. 


"Ok, fito min da number dinta da adrashinta"


Ya mikawa Teema wayarta da sauri ta amsa ta fito da number din tare da yi masa kwatancen gidansu Aishan.


"Good, naji duk abinda kuka tattauna sannan ina mai gargadinku karki fadawa wani, ni zan dauki mataki, sannan na haramta muku fita har sai komai ya dai daita"


Gyada masa kai suka yi suna hawaye, yayi ajiyar zuciya rai ba ce ya fice daga dakin ba tare da ya kuma magana ba, su Teema suka kara rushewa da sabon kuka babu mai lallashin wani, dana sani ya gama cike zuciyarsu har wani zazzabi ne yake barazar ka masu, haka suka kwanta bisa gado ko wacce ta ja gefe suna jimantawa kansu wannan *K'addararren Al'amari*.


****


Safnah tana isa gida ta samu su Muneera suna zaune a tsakar gida Muslim yana yi mata tatsuniya. Yadda ta gansu ya tabbatar mata da babu yunwa a tare dasu, da gudu Muneera taje ta rungumeta tana yi mata oyoyo.


"Anty Safnah tun safe baki dawo ba sai yanzu duk mun damu" 


"Allah sarki Munee aiki ne ya min yawa kuyi hakuri ban kawo muku abincin rana ba"


Sai ta taja hannunta suka zauna a tabarma Muslim yana yi mata sannu da zuwa ta amsa tana mai shafa kansa.


"Na san kai ne kayi bara kuka samu abinci ko?"


"Eh Ant, ganin baki dawo ba shine naje nayi bara, yanzu haka babu wata yunwa a tare damu"


"Allah yayi muku albarka"


Safnah ta fada hawaye ya cika mata ido amma sai ta shanye saboda karta sanyasu a damuwa, yaran suka amsa da Amin. Nan ta shiga kirga kudin da Akram ya bata wanda ta damkesu a hannu kamar za a kwace mata, kudin yan dubu dai dai ne har kimanin dubu goma sha biyu, wani irin ajiyar zuciya ta saki zuciyarta cike da mamakin yawansu, wani irin farin cikine ya kuma rufeta ganin kudin ta samesu ne ta halal,vtunda kyautansu aka bata ba tare da ta sabi Allah ba, Muslim ya kasa hakuri ya tambayeta cikin zakuwa.


"Anty ina kika samu kudi haka?"


"Muslim daga Allahu rabbil ka'abati na samu, wani mutum ne ya bani sadakarsu yanzu da zan dawo gida, kila yasan muna bukata tunda da yawan mutane sun san mu marayu ne" 


Safna ta boye musu komai domin basu kai munzalin da zata yi musu sharing irin wannan maganar ba dan a yanzu kota gaya musu tada hankalinsu zata yi.


"Eh eh Anty kila yasan mu marayu, Allah ya saka masa da gidan Aljanna"


Cewar Muneera data katsewa Safna tunani, sai ta fadada murmushinta tace.


"Lamarin Allah kenan yafi kagan misali Allah ya kara rufa mana asiri, ya bamu kariya da taimakonsa, ya shiga cikin lamarinmu ya kuma jikansu Abba"


Gaba daya suka hada baki suka amsa da Aamin jiki a sanyaye.


***      ***


Washe gari


Da misalin karfe takwas na safe Safna ta aika Muslim yaje shagon Yusha'u mai shayi ya siyo musu ruwan bunu da biredi harda madara, mamaki sosai Yusha'u yayi amma ganin yanzu yana yawan ganin gilmawan fitanta yasa ya dai na mamaki, babu abinda ya zo masa a rai face safnan ta fara koyan rayuwar bariki ne kamar yadda yake jin rade radi gun mutanan unguwar, tunda since yanzu inta fita tun safe sai dare take dawowa. Haka ya sallameshi zuciyarsa cike da maganganu. Muslim ya dawo gida Safna ta hada musu shayi suka sha tea da buredi na marmari, bayan sun gama tace duk su shirya zasu kasuwa. Cike da murna suka yi daka tsami da sauya kaya kana suka rankaya zuwa kasuwar sati dake kusa dasu dan siyayya. 


Haka suka isa kasuwan Safna ta shi yi musu siyayyan kayan abinci, manja da magyada, sabulun wanki dana wanka harda takalma silifas ta siya musu kana suka rankawo gida niki niki da kaya da sauran canji, sai duk suka zama abin kallo da suka shigo unguwarsu, haka suka shiga gida fal farin ciki a tare dasu, lokacin kusan karfe tara da kwata, haka nan Safna ta aiki Muslim ya siyo musu ice na hamsin da kalanzir din hamsin, bai bata lokaci ba ya dawo nan da nan Safna ta daura musu girkin rana dafadukan taliya na manja burinta tayi saurin gamawa ta wuce gurin aiki, duk da zuciyarta tana hasasho mata barin aikin duba da hatsarin dake ciki, amma bata gama yanke shawara ba tukuna sai addu'an Allah ya zaba mata mafi alkhairi ya kare ta daga sharrin abin ki. Ba ita ta kammala aikin ba sai misalin karfe goma, haka tayi wanka ta shirya gudu gudu ta wuce duk da ta san yau dole Hajiyar tayi mata fada, amma ta dauki alwashin yi mata bayanin abinda ya faru jiya dan ta sassauta mata lokacin tashi.


Bayan ta isa ta samu Haj. Uwale a cikin shago, Ta gaisheta hajiyar ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, kafin ta fara mata mita Safna tayi saurin soma yi mata bayani.


"Ummm jiya wasu yan daba suka tareni wlh da kyar nasha wani mutum ya taimakeni, to gudun dana yi shine ya haifar min da ciwon jiki shiyasa ban samu zuwa da wuri ba kiyi hakuri. Kuma dan Allah ina rokan Alfarma ki ragemin lokacin tashi zuwa gida saboda kar su sake bina"


Hajiya bata ce komai ba saima binta da tayi da kallo tana nazarinta, can ta nisa ta ce.


"Allah ya kyauta gaba, zan yi kokarin sama miki mai mashin din da zai rika kaiki gida kullun, domin ina son aiki dake"


"Nagode nagode hajiya Allah ya saka da Alkhairi"


"Ameen, tashi kije ki kamawa dije wanke wanken"


Safnah ta mike da sauri ta fita cike da murna tana kara hango kirkin Haj. Uwani, dama tsoronta karta ki saurarenta kota koreta. Hajiya ta bi Safna da kallo ta saki wani shu'umin dariya.


'Yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka, ai tunda kika shigo fadata tofa kinyi sallama da bariki dan saina mayar dake babban jari na'


Tace a zuciyata tana mai hango wani daula nan gaba da zata riski kanta a ciki, domin tuni bokanta ya tabbatar mata da cewar Arzikinta yana tattare da taurarin Safnah. Haj. Uwale ita ce ta aika su Abbati dasu bawa Safna tsoro dan yadda zata samu hanyar da safna zata fara kwana a gidan, saboda dama su yaranta ne suke yi mata aiki akan duk mutanan da suka so kawo mata raini.


*****


Akram da sassafe ya kira Amir a waya yace yazo gida ya same shi, ba musu ya shirya cikin sauri ya iso gidan suka zauna a part dinsa, ya zayyana masa komai dake faruwa bai boye masa ba, Amir gaba daya tsoro da mamaki ya gama bayyana a fuskarsa.


"Yanzu me kake ganin za muyi?"


"Aisha zansa yan sanda su kama, ta hakane za a samu damar kama Seema da sauran yaran aikin nata"


"Hakan za ayi yanzu muje can headquartern yan sandan sai mu yiwa dpo bayani"


Da wannan shawarar suka fita a motar Akram escort dinsa suna biye dashi a baya. Ko da suka isa, Sargent Bala yayi musu jagora zuwa office din dpo Auwal, sun same shi zaune yana ganin Akram ya mike tsaye fuska cike da murmushi. 


"Akramuuu, ashe rai kan ga rai"


Yace yana mika masa hannu suka gaisa duk suna dariya. Auwal abokin Akram ne tun secondary basu sake haduwa ba sai yau, haka duk suka zauna suka dan taba hira na yaushe gamo, daga bisani Amir ya jero bayanin abinda ya kawo su, Auwal cike da jimantawa ya tabbatar musu da zasu yi aiki tukuru dan binciko su. Haka suka yi sallama tare da musayar number waya sannan ya amsa contact din Aisha da wanda seema ta aikawa Teema sakon hotunan.


*****


Bangaren Seema tunda ta turawa su Teema hotunan, take tsumayen jin reply dinsu amma shuru, har zuwa yau da take tsammanin su kira ta. Kiran Meena tayi da sabon number din data turawa Teema hotunsu amma haka taji wayar a kashe, abin ya bata mamaki sai ta kira na Teema shi ta samu a kunne sai dai harta gama ringing ba a dauka ba, Akram dake zaune cikin office dinsu yana kallon kiran bai daga ba yana gama ringing ya daga waya ya kira dpo ya sanar masa nan suka tattauna kana sukayi sallama.


***


Zuwa yamma yan sanda sun samu nasarar Kama Aisha, a lokacin ta fito daga gidansu zata je cikin gari, basu yi wata wata ba suka kamata duba da Akram ya tura musu hotonta dake wayar Teema, shiyasa basu sha wuyar ganeta ba, haka suka sanya tayi parking suka tasa keyarta zuwa police station. 


Dpo ya shiga jero mata tambaya Wanda ta sani ta amsa Wanda kuma bata sani ba tayi shuru, a bakin ta suka ji bayanin Seema harda ainahin contact din ta da adreshin gidan iyayenta, dama ainahin gidanta da take zaune. Duk da haka basu sake ta ba suka sakayeta a bayan kanta tare da amshe duk wayoyinta.


***


Yau Haj. Uwale ta sallami Safna da wuri dan suna tashi daga shago tace ta wuce gida, hakan ba karamin faranta ran Safna tayi ba, sai ta kara jin cewa zata kara kaimi wajen aikin dan ta kula hajiyar tanada tausayi. Safna tana shiga gida taji yo Kawu Bala yana balbale masifa ta in da yake shi bata nan yake fita, jikinta sanyi kalau ta karasa ciki da tunanin me yasa shi yin fada haka, tunda take dashi bata taba ganin haka ba. Kawu bala yana juyowa ya ganta sai ya fara zaginta.


"Yauwa dan ubanki zonan, abinda nake ji a gari gaskiya?"


"Kawu ina yini"


Ta gaishe shi ba tare da ta amsa tambayarsa ba.


"Ban yini ba, na ce ban yini ba sha sha sha, Safna ace ina yabanki sallah ki kasa alwala"


"Kawu meya faru ne, dan Allah kayi hakuri?"


"Safna wato kin zabi duniya fiye da lahira ko, ba zaki kiyi hakuri ki amsa maraicinki ba sai yawon ta zubar, to bari kiji rayuwar bariki babu riba sai faduwa, da ki jawo min magana gwara na tattaraku na maidaku can riga ayi miki aure"


"Kawu ni ban fahimci meke faruwa ba"


"Uwaki nace shaidaniya, sam baki halin iyayenki nagari ba. Wai ma dan ubanki ina kike zuwa tun safe sai dare kike dawowa? Kuma uban waye ya baki kudi kika siyo muku kayan abinci? Barin ku gidan nan ku kadai bawai yana nufin na baku lasisin zuwa iskanci bane fa" 


#Rahma ce

#Follow

#Vote

#Comment

#Share

Please.