ZAKI

11

by @khadeejacandy

Kamar wacce akai wa kyauta makka yana na nufo gida farinciki ya cika min zuciya. Ina tafe fuskarta dauke da murmushi duk wanda ya kalleni ya san ina cikin farinciki a yau. Sallamar shiga gidansu Farida ma da karfi nai ta Mahaifiyar Farida na tsakar gida zaune tana gyara Alayyahu har kasa na risina na gaishe ta sai ta masa sama-sama sannan ta bawa banza ajiyata ni kuma na tashi na nufi kitchen da Nana take. Kwance na same ta kamar yadda na fita na barta. Kusa da ita na zauna ina washe hakora. 


“Nana na samo kudi har dubu takwas”


Dan dagowa tai ta kalleni cike da mamaki.


“Ina kika kudi har haka, bara ki kai?”


“A'a ai ba zan sake yin bara ba, sanadin raban nan aka kade Lukman, bana ma marmarin sake komawa bara, wani gida naje na ce musu zan yi musu aiki, amman sai sun fara bani kudi sannan na fara, na fada musu cewar Mahaifiyata bata da lafiya”


“Kuma suka yarda suka ba ki?”


“Matar ba ta yarda ba, mijin ne ya ba ni”


Hannu ta shafa kaina tana murmushi. 


“Allah ya miki albarka, wannan kalubale da kika fuskata tun a yanzu da kurciyarki Allah ya tallafa miki ya baki wanda zai mutunta ki ya zame miki gata”


Kasa amsawa nai a fili saboda kunya, sai a zuciyata na amsa da Amin.


“Nana ina takardar msganin take sai naje na siyo”


“Ban zo da takardar ba, komai a can ya bar asibiti”


“Kai amman ban jidadi ba, yanzu ya zamu yi kenan?”


“Ataa ki daina dorawa kanki damuwa da wahalar da kanki a kaina”


“Idan ban miki ba wa zan yi ma, ba ni da kowa a yanzu sai ke, idan na rasa ki ban san iya halin da zan shiga ba”


Na fada idona tab da hawaye. Sai tai murmushi tana ta kallona cike da kauna. 


“Ko asibintin za mu koma?”


“Asibiti babu komai sai cin kudi, kara ma kije gurin masu magani ki siyo abunda ya sawwaka, sauran kudin ki siyo mana abinci da su”


“Amman maganin chemist anya zai yi kuwa?Ai kara dai mu koma asibintin zai fi”


“Ataa na gaji da zaman asibitin nan, kuma wannan kudin idan ma muje karewa zai yi”


“Ko ya kare indai kin samu lafiya ba matsala ba ne”


“Aa kara dai mu ci abinci da su zai fi mana”


“Amman Nana rashin sha maganin zai iya janyo miki matsala fa”


“Da muje a kashe kudin ba a samu biyan bukata ba kara dai mu san mun saka a ciki, tun da kika fita ba ki ci komai ba, ni ma da nake nan ban cin ba, magani ma ai ba yayi sai da abinci”


Gaskiya ta fada, sai dai ni na fi damuwa da ciwonta fiye da abincin, na san kudin ba zai isa maganin duka ba.

Ta shi nai na fita daga dakin cikin rashin jindadin duk farinciki da murnar da na ke sai suka koma ciki. 

 Wani shagon provision na nufa na siyo mata biredi da madara da gwangwanin suga, ni kuma na siyo ma kaina gari da gida da suga sannan na dawo gidan, wannan karon Maman Farida ba tsakar gidan, hakan yasa ni jindadin wucewa na shigewa inda Nana ta ke na mika mata ledar sannan na fito da dauki kofi biyu da ruwa na koma dakin, ita na fara hadawa da ruwan sanye sannan ni kuma na hada nawa garin na saka suga na sha, yadda take fisgar biredin tana sai ka rantse da Allah ta shekara bata ci abinci ba. Tausayinta ne ya lullube, an cire mata koda daya dan zalinci, ga yunwa tana fama da ita babu mai bata sai Allah, dan ya tafi ya barta a garin nema yafiyarta. Tabbas ba zan taba manta Doc Asim ba, ba kuma zan taba yafe masa ba, sanadinsa na kwana a cell, na rasa kanena, ga mahaifiyata a halin da ba zan iya juye ganinta a haka ba. 

Idan zan yi tunani sai na rasa da wanne zan fara abubuwan duniya sun taru sun min tsaye a raina, har wani zafi na ke jin kirjina yana yi idan ina tunani, na rika jin zuciyata kamar zata fasa kirjina ta fito. 

 Bayan mun gama na dauki kofunan na kai waje na wanke na aje mata a inda na gansu, ashe ta hangi lokacin da na aje sai ganinta nai ta fito rai a bace tana ta masifa wai mun taba mata kofi kazamai da mu, a kan idona ta dauki kofunan ta wilgar bayan gidan, na ji zafi sosai amman ban nuna mata ba, domin fadanta akan gaskiya ne, ni na taba mata abu da ban taba ba da bata min wannan maganar ba. 

 Kitchen da muka raba na koma na dauko duka kayan wanke wanken na fito da su tsakar gidan, na je na siyo omo na debo ruwa a rijiyar gidan na zauna na wake su tas, na dauka na kai kitchen din wanda zan iya cewa dakinmu. Sannan na fito rike da soson wankanmu na dibi ruwan a robarmu na shiga bandakin tsakar gidan nai wanka, na wanka jiki sau uku sannan na saka ruwa na dauraye na fito fes da ni ni kaina har wata ni'ima na ke jin tana shiga jikina. Ban ssmu na shafa mai ba saboda yanayin garin da zafi, sai kawai na saka daya daga cikin tufafin da na ke ji da su, na dauki bakin dankwalina nai nikab da shi sannan na saka Hijab sama na duka inda kudin sukd na dauki naira dari na dan hawan acha6a, domin akwai tazara a tsakanin unguwar mu da tasu. 


“Nana zan tafi”


“Yau za ki fara aikin?”


“To Allah ya taimaka ya tsare a dawo lafiya”


“Amin, ki aje wannan kudin muna cin abinci da su, idan na samu wasu wadanda suka yarda nai aikin yamma sai na rika zuwa ina musu kin ga idan an ban kudi sai na hada da wannan mu koma asibitin”


“To Allah ya nufa”


Duk maganar da nai mata da hausa nai ta ita kuma sa ta maida min da yaren da tafi kwarewa akai wato buzanci. Sai da nai mata sallama sannan na fita, ban yi nisa sosai na samu mashin na tara na hau yana sauke ni na bashi hansi ya karba ya wuce ni kuma na buga kofar gate din a hankali. Mai gadin ne ya leko yana ganina sai ya fito gaba daya. 


“Baiwar Allah lafiya”


“Lafiya kalau, ni ce wacce na zo neman aiki dazu kuma suka ce sun dauke amman sai naje na shirya”


Wani kallo yai min tun daga sama na har kasa, nasan kallon baya rasa nasaba da bakin kyallen da na saka na rufe fuskata, wata kila yana munanamin zato ne.


“Bari dai na fara fada musu tukuna”


Haka ya barni tsaye a gurin ya koma ciki, ba dauki dogon lokaci ba sai gashi ya dawo ya bude min gate din. 


“Ance kin shigo”


“Na gode”


Na fada ina saka kafata cikin gidan, sai a yanzu ne nake kara kare masa kallo babban gida ne da za ayi iya kiransa da aljannar duniya, ko a harabar gidan kadai aka barka zaka sha kallo tun daga kan furanni da kuma manyan motocin da ke gidan, ko wace kofa an kawata ta da furanni. A inda na naga sun fito dazun na na bi stairs din na isa gaban katuwar kofar mai kyau na yi knocked a hankali, shiru ban ji an bude kofar ba, hakan yasa na sake knocked, nan ma shiru ba a bude min ba, sai da na yi na ukun sannan aka soma motsa kofar aka bude. Mijin matar ne ya bude min yana sanye da kananan kayan, bakin wando da jar t-shirt, fukarsa kamar ta kullum babu alamar murmushi ma balle kuma ayi zancen dariya. 


“Ina wuni”


Be amsa min ba, sai kallon fuskata yake kamar nai son tantace abu, ni kuma nai tsaye a gurin cike da tsawalla, gabana sai faduwa yake ina jin kamar cewa zai yi ya fasa baya so. Sakin kofar yai ya juya ya koma ciki ya barni a gurin tsaye shi be cena shigo ba, kuma be ce min na tafi ba, ganin hakan yasa na yi tsaye agurin kamar an dasani, har sai da na ji muryar matar tana ce min na shigo. 

Kamar wata hawainiya haka na rika taka tile din mai tsantsi gudun kar na taba da karfi su ce na musu ba daidai. A kan wata babban kujera suke zaune tun na shigo falon daga ita har shi babau wanda ya kalleni balle ya ce min wani abu. Haka ma zauna a gurin kamar daman sun biyana dan na zo na zauna gabansu ne. 


“Ke anya macen kwarai ce? Miyasa kika rufe fuskarki?”


Matar ta fada tana min wani kallon uku saura kwata. 


“Ba komai, na fi jindadi idan na rufe fuskar ne shiyasa na rufe, ina da konuwa a fuskar ne”


Ta tabe baki. 


“Bedrooms din mu za ki fara shiga ki gyara komai da nan falon sannan ki shiga kitchen ki gyara kuma ki wanke duka kayan da suke can sannan ki yi mopping ki saka mana turaren kanshi”


“To ina dakunan suke?”


Da yatsanta ta nuna inda yake har na mike tsaye sai kuma ya kira ni. 


“Keee ban da sata kar ki kuskura daukar mana wani a gida”


“Ban taba sata ba a rayuwa”


Na bata amsa cike da jin zafin furucinta.


“And secondly mijina baya son kallo, kuma daga yanzu tun bakwai za ki rika zuwa kina hada mana breakfast, kuma ki gyara gidan, kuma kullum ki wanke mana bathrooms din mu”


Tana fadar hakan sai na ga jikinta ya kalleta, ya kalli sannan ya sake kallonta. 


“Ban da girki, saboda shara da mopping kawai na dauke ta”


Yana fadar hakan ya mike tsaye yana wani irin kamshi turare mai dadi shaka ya hau sama, ni kuma na maida hijab dina baya na daure sannan na nufi upstairs din na soma takawa a hankali kusa da sai na ce wannan shi ne karo na farko da na taba taka stairs bayan wanda na taka a asibitin uduth, dakin farko na fara kai hannuna na tura kofar dakin, da alama dakinta ne, domin kayan mata da ke dakin suna da yawa ga gadon duk an tumurmuza shi kamar karamin yaro ya kwana kai. Bedsheet din na fara gyarawa sannan na linke kayan kayan da aje guri daban, na duba iya dubana ban ga tsinsiya ba da abun mopping ba. Hakan yasa na fito na sauko kasa can nesa da ita na tsaya.


“Ina tsintsiya?”


“Ni zan dauko miki na kawo miki?”


“Aa fada min za ki yi inda take na dauko”


A gurin ta bar ni tsaye har na kusan minti ashirin sannan ta ce.


“Tana can kofar baya ki je ki duba”


“Ina ne kofar baya?”


Sai da taja tsaki sannan ta bani amsa tana mikewa tsaye ta nufi upstairs. 


“Idan kin ga dama ki duba ta can”


Inda ta nuna min na bi na je na bude kofar dake gefen falon, sai ga ni a wata karamar haraba, kusa da gen hannu nasa na dauka da bokitin na nufi fomfon dake kallon kofar na kauna na wanke bokitin sannan na fito, tsaye nai a falon inata tunani inda za samu omo na ko man wanki na zuba a ciki. Ganin bata fito ba yasa na bar ruwan a nan na koma da Tsintsinyar bedroom dinta na share shi tsaf na kwashe na na fito da datti sai kuma na rasa inda zan zuba, gashi ba ta fito ba balle na tambayeta, a dole na aje ta jikin kofa na koma dayan bedroom na share na gyara komai sannan na sauko kasa na share falon har karkashin kujera na shiga kitchen na share na hada kayan wanke wanke guri daya, a kusa da tab na samu omo sai naje na zuba a cikin ruwan mopping din na koma dakin na mopping sannan na shiga bandakin na wanke na dawo falon nai mopping na goge ko'ina sai kuma na koma kitchen din na wanke kayan cin abincin bayan na gama nai mopping din kitchen din sannan na fito na zauna a falo ina kare masa kallo a pop kadai na san ba kananan kudi aka kashe ba, balle kuma irin manyan kayan alatun kawata falo da aka cika falon da su. Ko agogon falon irin wanda na ke gani a tv ne. 


ALIYU POV. 


Yana shiga dakin Rahma ta biyo shi tana fadar ita bata yarda da wannan yarinyar ba shi ru yai be ce mata komai ba, yai kamar be ji ta ba sai latsar wayarsa yake.


“Ka ji, ni fa ban yarda da ita ba, jiya ta shafa wani a fuska ta zo nan duk baki yanzu kuma ya saka nikab”


Sai a lokacin ya dago ya kalleta. Kamar zai yi magana sai kuma yai shiru ya sake mai da hankalinsa gurin wayar. 


“Kana jina fa”


“Mi kike son? Ke kika damu a samu mai aiki ai”


Ya fada ba tare ya kalleta ba, sai tai fushi tana mikewa tsaye yai saurin riko hannunta ya dawo da ita kusa da shi ta zauna. 


“Kin cika son saka bacin rai a zuciyarki Dear, kuma kin san matsalarki, idan mai aikin ce ba ki so ai sai ki koreta kawai”


“8k din da ka bata fa?”


Yai murmushin kasaita yana kallon goshinta.


“Ai kyauta na bata ba dan aiki ba”


“Aa gaskiya sai dai tai mana aikin one month sai mu koreta, dama dai ba ka ba ta kudin ba”


Kara matsawa yai kusa da ita yasa duka hannyensa ya rike fuskarta. 


“Idan na ga mutum cikin rashin lafiya, ina tausaya masa sosai, saboda na san zafi da ake ji, musamman idan mutumen nan makusancin ka ne, na auna kaina a matakinta, kin tuna lokacin da muke ta yawon neman lafiyarki?”


“Waya sani ita ko karya take, wata kila ma muguwa ce shiyasa take rufe fuska”


Be sake ce mata komai ba ya kwantar da ita kirjina ya cigaba da latsa wayarsa. After like one hour ta ďaga daga jikinsa ta sauko downstairs ganin Ataa zaune tana kallo ya bakanta mata rai sosai domin ba kowa take son yana morewa da abunta ba.


“Kin gama sharar ne da kika zauna kina kallo”


Ataa ta juyo da sauri jikinta har ba ri yake ta kalleta. 


“Eh na gama tun dazu na share ko'ina na gyara”


“To daga yau karki sake rufe mana fuskarki, idan ba za ki iya bude fuska ba ko zauna a gidanku ba yadda za ki zo ki cutar da mu ki tafi ba tare da mun ha fuskarki ba”


“Wallahi ni ba na cutarta kowa”


“Ai ba za a iya ganewa a fatar ba ki ba, shiga dayan dakin ki wanke bathroom din kuma ki gyada dakin”


Tana fada mata sannan na nufi kitchen dinta dan tabbatar idan kayan sun wanku. 


ATAA POV.


Daukar tsinsiyar nai na hau sama a doshi dayan dakin wanda na ke saka ran shine dakin mijin, ciki tsoro da fargaba nai knocked, sannan na ja baya kadan na tsaya ina ta jiran ace min na shigo amman shiru, sai hakan yasa ni jin babu dadi, daga fara aikina a yau na fahimci daga matar har mijin kamar ba su san darajar dan adam ba, wata kila kuma saboda na kawo kaina ne, ni da kaina ina nema shiyasa suke wulakanta ni oho. Na fi karfin minti talatin a tsaye bakin kofar sannan ya fito yana ta kamshin turare, har wani matsawa yake kai ya ra6o ta kusa da ni ya sauka downstairs. 

 Be ba ni izinin shiga ba, dan haka ba zan shiga na taba wani abun da zai iya zan min matsala ba. Haka nai tsaye a gurin na kasa sauko kuma na kasa sai duk na ji na tsawwala, wani kankanci da bakincikin suka kwankwaso min kofa, na tabbatar da a ce yar wani ce ni da ba za su bar ni a gurin tsaye ba, za su nuna min kyama ba. Suna min duka wannan saboda ina talaka kuma na raba jikinsu ina neman taimako. 

Da gaji da tsayuwar ne na sauko kasa cike da fargabar abunda za ta ce min da Kuma irin kallon da mijinta zai min.


Tana zaune kan kujera ita kadai tana waya, da alama wayar tai mata dadi sai kyalkyalar dariya take tana buga kafa kasa, ni dai kallonta kawai na ke, irin rayuwar jindadi da take ciki ta burgeni ga ta cikin farinciki abunda na ke ta marmarin samu amman ya gagara, zaunawa nai kasa tile har ta gama wayar sannan na ce


“Be ce min ya na shiga ba, ni kuma ban shiga ba, gudun kar na shiga ya zama laifi”


“Ya ce baya son ki gyara masa dakinsa”


“Yanzu zan iya zuwa gida kenan?”


“Idan kin ga dama”


“Na gode”


Sai na nufi inda na dauko tsintsiyar na maida, sannan na dawo na dauki dattin sharar na fita da ita daga gidan gaba daya, can karshen layin unguwar n samu wata bola na zuba ta a ciki sannan na dawo na aje shi a inda na dauke shi na yi mata sallama ban jira ta amsa ba, na kama hanyar gata zuciyata na mugun kuna kamar an dora ta ka ce garwashin wuta. 

 Ina tafe ina ta tunanin kamar ba zan iya jure aiki a gidan ba har na tsawon wata daya, saboda yadda na fahimcin hayyarsu da dabi'unsu ba kamar na kowa ba ne, sai dai idan ban yi aikin ba kudin su fa? Ai dole na biyasu bayan kuma na riga na taba wani abu daga ciki kuma ina da bukatar kudin. 

 Kamar yadda aka kai ni dazu haka wani mai achaba ya dawo da ni na bashi naira hansi sannan na shiga gidan, ina yin sallama Farida ta amsa tana wanke wanke, fuskarta da far'a kamar kullum ni ma na yi kokari aron murmushi na yaba a fuskata duk kuwa da kasancewar shi a kusa da ni. 


“Har kin dawo? Nana tace min kin samu aiki?”


“Eh na samu, yau na fara”


“Allah ya taimaka, wane unguwa?”


“Nasarawa”


Na bata amsa ina shiga inda Nana take, wanann karon a zaune na same ta ta saka dayan hannunta ta dafe gefen cikinta tana hawaye. Da alama ciwon ne ya taso mata domin ba abu kadan ke kasa nana yin hawaye ba musamman ciwo. Kusa da ita na zauna na rafka uban tagumi ina ta kallon saukar hawayenta, ban san abunda zan yi ta samu lafiya ba, ban zan zwa zan kaiwa kuka ya saurareni ba, Doc Asim ya zalince mu zalince mai tsanani kuma na kai kararsa aka kasa kwatar min hakkina suka kasa bani gaskiya saboda ina talaka shi kuma yana mai arziki. Sai wani numfashi take wahalce ni kuma na kasa ko motsawa daga inda na ke zaune balle nai nata sannu yadda take hawaye haka ni ma na ke hawayen, kashi ya hade min goma da shirin can ba dadi nan ma ba dadi. 


“Ni kadai na san irin zabar da na ke sha a kan ciwon nan, ni kadai na san yadda zafin ciwon nan yake min, ni kam da ma na mutu wata kila da na fu samu sauki fiye da haka”


Cikin murya kuka ta fadi haka da sauki kasa-kasa. Hannu nasa na share hawaye na daga inda na hango kudin da na bata dazun na dauka na fito jiki ba kwari na je bakin titi gurin wata pharmacy, na fada masa yadda ciwon yake sai ya ba ni magani kusan dubu uku da dari bakwai na dawo jiki na rawa na balla na bata na shafawan kuma na shafa mata, sai na koma ta bayanta na rumgumeta na fashe da kuka marar sauti, ji na ke kamar ace ina wata dama zan iya nema mata lafiya ta warke ita kadai ta rage min idan ta tafi ta barni ban san halin da zan shiga ba. 

Na dade rumgume da mahaifiyata sannan na saketa ta kwanta, ni kuma na goge fuskata na fito tsakar gidan ko za a samu sassaucin abinda na ke ji a zuciyata. Da na fito sai Farida ta dasa min wata sabuwar fira dama akwai da yawan magana, a nan take labarta min cewar mahaifinta ne ya ce Nana ta dawo nan ta raba ta zauna tun da mai wacan kangon gidan ya koreta gashi bata da wani gurin zama. Ni kaina nasan indai Farida ba to ko sai mahaifinta, domin mahaifiyarta ba zata taba yarda tace ta zauna a gidan ba. 


Bayan sallah magariba na dauki kudi da kwano na siyawa nana tuwon masara da miyar yauki domin shine mai yar nasiha ba kamar shimkafa ba mai tsada, ko da na shigo na tarar ta samu sauki sosai tana zaune saman dankwalinta da tai sallah. Gaba na saka ta na cilasta mata cin tuwon ita kuma ta ki ta ci ala dole sai ni na fara ci, a dole sai na ci sannan ita ma ta ci na kawa mata ruwa ta sha, sannan muka gabatarda Allah isha'i muka kwanta a gurin da mutum ba zai iya mike kafafuwansa ba straight ba. 

  


***   ***   ***

Da wuri na farka gudun kar nai lattin zuwa gurin aiki, bayan na ayi alwala ita kuma na samo mata kasa tai taimama ta yi sallah asuba, cikin kudin na dauka naje na siyo mana koko da kosai da suga na kawo muka karya sannan na shiga bandaki nai wanka da ruwan sanyi duk da kasancewar akwai sanyin safiya da be gama sauka ba. 

 Bayan na fito na saka wasu tufafi, daman can shafa mai be dame ni ba bayan cikin tsarina wankan ma gudun kar suce ina wari da ba zan yi ba. Haka na shirya cikin wata kodaddiyar atamfata na sake kwaba gawayi kamar ranar na shafa a fuskata, tun da sun ce na daina saka nikab sai na saka bakin gawayin da na saba sakawa duk kuwa da irin kazantar da suke ganina da shi. 

  Yau ma sai da na dauki naira dari a cikin kudin sannan na saka Hijab dina na yi ma Nana sallama na fito na shiga dakin Maman su Farida na gaishe ta ita da mijinta shi ya amsa da far'a sabanin ita da ko kallon kirki bata min ba, wata kila tana ganin kamar mun takura tane mun zauna mata a gida mun hana ta wali a yadda a gidanta. 

Yau ma achaba na hau na fada masa inda zai kai ni, ba aje ni ko'ina ba sai bakin gate din gidan na mika masa kudinsa na sauka, ina kokarin yin knocked gate din sai na ga an bude shi gaba daya, ashe mai gidan ne zai fita sa na raba gefe sai da ya fice sannan na shiga ina mikawa mai gadin gaisuwa bayan ya amsa min na nufi kofar gidan wato kofar babban falon da zai sada ka da cikin gidan gaba daya. Da nai knocked din kofar sai na zauna kusa da kofar dan nasan ba yanzu zata bude min ba, haka nai ta zama a gurin har mai gidan ya dawo ya faka motarsa inda sauran motocin suke ya fito fuskarsa da Annuri da haifa ya nufo kofar ya saka keys din hannunsa ya bude. 


“Ina kwana?”


Be amsa min ba, sai kallon fuskata yake ta yi wata kila yana mamakin yadda yau ban saka nikab dinba na sake shafa bakin gawayi, ni dai ban kalleshi ba domin matarsa ta fada min mijinta baya son kallo. Shi ya fara shiga sannan na bi bayansa na shiga kai tsaye na nufi gurin jiya na dauko tsintsiyar da mopper na fara gyara falon sannan na shiga kitchen na gyara, ban san a wane dakin ta ke kwance bana son na shiga ta ce na mata ba dai-dai. Sai kawai na nemi gefen kujera na zauna, ina ta jiran fitowarta shiru har bachi ya dauke ni a gurin ban sani ba. Can cikin bachin nawa na ji an watso min ruwa mai dumi hakan yasa ni farkawa a firgice, ashe ruwan tea da ke hannunta ta watsa min.


“Ina kwana”


Na mika mata gaisuwa kamar a rikice. 


“Ba ki yi bachi a can gidanku ba ne da za ki zo nan kina mana bachi? Ba aiki aka dauke ki ba?”


“Na gyara nan na gyara kitchen ina jiran ki fito sai na gyada dakunan”


“Miye a fuskarki kuma?”


Na yi shiru ban ce mata komai ba sai kawai ta tabe baki ta zauna a kan kujerar. 


“Shiga ki gyara min bedrooms dina”


“To”


Na amsa a ladafce sannan na dauki tsitsiyar na nufi dakunan na gyara na na dawo na dauki mopping na goge ko'ina na wanke bandakunan sannan na sauko. 


“Na kare”


Na fada mata bayan na maida kayan inda na daukosu. A gurin ta bar ni tsaye bata ce na tafi ba, ba ta ce na tsaya ba, har jikinta sauko hannunsa rike da agogon hannu yana kokarin sakawa.


“Kin tabbatar za ki iya driving da kanki? Idan ba za ki iya ba don't stress yourself zan turo direba ya kai ki”


Shine abunda ya fada mata, ita kuma ta girgiza masa kai. 


“Aa zan iya, wannan yarinyar za ta rika min kayan”


A gabana ya kai bakinsa a goshinta ya sumbace ta babu ko kunya, shi da kiss ni da jin kunya har na ji kamar kasa ta nutse da ni da kunya. Be yi minti talatin da fita ba ta hau sama ta bar a gurin a tsaye ina ta jiran saukowarta, sai da tai wanka ta shirya cikin wani lace mai kyau da tsada sannan ta sauko idonta sanye da katon bakin gilashi nan na mata. 


“Shiga dakina ki dauko min ledodi ki saka mota”


Abun ka da mai jiran umarni sai nai hanzari cira kafa na taka har dakin na dauko na kai gurin motar da ta bude na zuba su a baya, sai kuma nai tsaye ina jiran abunda za ta ce min. Bayan boot din taje ta dauko wani tawul ta miko min. 


“Shimfida wannan a baya sannan ki zauna karki shafa min dattin jikinki a mota”


Na saka hannu na karba cike da jin zafin furucinta, na shimfida kamar yadda ta fada sannan na zauna ita kuma ta shiga mazaunin direba tai ma motar keys, muka fita ba tare ni na san inda za mu je ba, nawa ido ne kawai ina ta kallon titi har muka isa wata kyakkyawar unguwa mai manyan gidaje, gida hudu muka wuce sannan ta danna horn mai gadin ya bude mata gate, a inda sauran motocin suke ta faka motarta ta fito sannan tace da ni na fito ya dauko mata ledodin, tana gaba ina bayanta har muka shiga cikin gidan. Alhajin nan mai kangon gidan da ya kore mu na hango zaune kan kujera yana dariya an zagaye shi suna ta hayaniya da alama wata wainar ake toyawa.


“Daddy... Happy birthday”


Hajiyar ta fada tana nufar inda yake, ban yi mamakin wulakancinta ba indai har wacan mutumen marar ganin tausayi ne mahaifinta.