ƘADDARARREN AL'AMARI

07

by @rahmakabir13

*ƘADDARARREN AL'AMARI*


© *Rahma Kabir*

     Mrs MG


Wattpad @Rahmakabir.


07


Safna ta fashe da kuka mai ban tausayi, ba tayi zaton zargin da mutane ke mata ba kenan sai yanzu da kawu yake maganar, shi ya kasa fahimtarta inaga sauran mutanan gari. 


"Ja'ira ki bani amsar tambayata kin tsaya kina kukan da ba zai fissheki ba"


"Kawu aiki na samu a rumfar Haj. Uwale mai abinci dake nap club, wanke wanke nake yi sai aike a wata zata biyani dubu hudu"


Tayi maganar tana share hawayenta, Kawu bala yadan yi Jim kadan kana ya sausauto daga fushinsa.


"To a ina kika samu kudin da kika siyo muku abinci"


"Wani ne ya bani sadakansu wai yaji ance mu marayu ne"


Safna ta samu kanta da shirya wannan maganar domin bata san ya zai dauka ba in yaji ainahin musabbabin abinda ya faru, kuma bata so su Muslim su sani, Anan ma kawu ya sauke ajiyar zuciya.


"Shikenan gobe in Allah ya kaimu kafin ki tafi ki biyo ta gidana muje tare naga gurin aikin naki danna tabbatar, danku 'ya'yan yanzu ba komai zaku ce a yarda nan take ba, kuma ki kara kiyayewa ki rike mutuncinki, ga kannenki nan duk abinda kika yi shi zasu koya, Allah ya muku albarka ya kawo mana Karshen wannan talaucin"


Duk duka amsa da Amin.


"Dama siyayyar salulin wanki da omo nayi muku gashi can ki adana, ga dari biyar ki rike a hannu dan siya muku abin bukata"


Safna ta amsa cike da girmamawa.


"Allah ya kara rufa asiri da budi na Alkhairi mun gode Kawu"


"Yauwa ni zan tafi sai kin zo, sai ku rufo gidan"


Da to tabi bayansa tana kara masa godiya kana ya tafi, ta rufe kofarsu tare da jingina jikin kofar tana mai sauke ajiyar zuciya da jimamin irin zargin da ake mata. Safna ta runtse ido ta bude tana mai cewa.


"Akwai Allah, da kai na dogara kaine mai wanzar da komai ka kara kareni daga sharrin zamani da shaidanun mutane"


Muneera data biyo bayanta bata sani ba taji ta amsa da.


"Ameen anty Allah sai ya saka miki"


Tace tana mai turo baki cike sa jin haushin abinda Kawu yayi musu. Safna ta saki guntun murmushi ta kama hannunta ta shiga yi mata wasa, da dariya suka karasa cikin gidan.


******


Washe gari 


Safna bayan sun karya ta kimtsa ta bar kannenta a gida ta wuce gidan kawu, ta samu matarsa a tsakar gida tana shara, tana ganinta ta daure fuska, Safna ta gaisheta ta amsa cikin fada.


"Lafiya, kuma me ya kawo ki da safen nen? dan ku in mutum ya ganku sai yaji gabansa ya fadi dan ba alkhairi ke kawo ku ba sai dai kullun a baku"


"Inna wurin Kawu nazo zamu je da shi wajen dana fara aiki"


"Ato yanzu naji dama dama, da na dauka kin zo da zancen babu ne a yi muku. Malam! malam!!"


Ta kare maganar tana kiran Kawu wanda ya amsa yana kokarin sanya rigarsa ya fito. Yana ganin Safna ya saki fuska.


"Safnatu"


"Naam kawu ina kwana"


"Lafiya lau, muje da sauri kafin lokaci ya kure. Ke Jimmala bari naje na dawo yanzu"


"A'a malam sallameni kudin cefane ba zan iya jira ba, dan ba abin mamaki bane ka wuce aiki daga can ka barni da sakekken baki"


"Haba Jimmala bani nace miki zan dawo ba, dan Allah ki daina wannan zancen. Ke Safna muje"


"Ai malam nasan hali ne"


Murmushi kawai yayi ya wuce, Safna tana biye dashi a baya.


Har runfar Uwale suka je ya gaisa da ita kana ya Koro mata bayani, hajiya ta tabbatar masa da Safna tana aiki agun. Dan ta rike zuciyarsa ma har dari biyar ta bashi da zai tafi, da farko yaki amsa sai daga baya ya karba yana godiya, ta kuma sanya aka zuba masa abinci a take away ya tafi yana yabawa da kirkinta, har cikin ransa bai zargi komai akanta ba, sai farin ciki yake Safna ta samu aiki mai kyau da zata taimakawa kansu shima zai huta daga wasu hidimoninsu dan dama ba karfi gareshi ba, da tunani iri iri ya tafi gida. Safna kuwa ta yiwa hajiyar godiya tare da kara ganin kirkinta da jin son aikin a ranta, sai ta wuce ta fara aiki gadan gadan.


*****


Akram da sassafe yayi shirin zuwa Abuja ya kira Amir a waya suka tattauna sosai akan matsalan su Teema, kana daga bisani yace ya bar masa komai a hannunsa sai washe gari lahadi in ya dawo, da haka suka yi sallama. Yaje ya yiwa iyayansa sallama sannan ya kara garganin su Teema, kana ya fito ya shiga mota driver ya jashi tare da escort dinsa, can rigasa suka nufa wajen jirgin kasa, bayan sun isa driver ya fita ya siya masa ticket a fanni mai tsada kana ya dawo, minti ashirin da zuwansu jirgi zai tashi Akram ya shi ga su kuma suka juyo zuwa gida. 


*

Bangaren Aisha kuwa, DPO Auwal ya kira mahaifinta yazo sunyi magana da safen suka sallameta, saboda bincike ya nuna bata da hannu a ciki sai dai sun bayar da cewar duk lokacin da aka bukaceta zata zo, ta kuma amince, sannan sun gargadenta karta sanar da kowa maganar hasalina sun amshe wayoyinta kafin suka wuce. Dpo Auwal ya sanya yaransa sun shiga bincike cikin sirri wanda har zuwa lokacin babu wani labari akan Seema sai dai sun samu tabbacin bata garin tayi tafiya a bakin wasu mutanan unguwarsu.


*****   *****


Abuja


Akram sun isa lafiya inda yana sauka yaga driver gidan Baba Kamasu yana jiransa, da sauri yazo ya amsa briefcase din hannun Akram ya wuce gaba ya bude masa gidan baya ya zauna, kana ya koma mazaunin driver ya tuka suka wuce gida. Bayan sun isa Akram ya fito rike da jakarsa yana shiga babban falon gidan Abida ta rugo da gudu har zuwa gabansa kamar zata rungumeshi dan murna.


"Oyoyo yaya Akram" 


"Ke dai Abida har yanzu ba zaki girma ba ko? halinku guda dasu Teema" 


Ya fada da murmushi a fuskarsa. Mama ce ta fito daga dakinta tana cewa.


"Lale marhabun da bakon kaduna"


Akram ya karasa cikin falon Abida na binsa a baya, duk suka zauna Akram ya gaisa da mama ta amsa cike da murna itama.


"Da fatan zuwan namu ne bana Babanku ba? Dan nasan kai sai aiken Alhaji Babba kake zuwa gidan nan"


Da yake sunan sa take karan babansu Akram kenan, Akram ya sosa keya.


"Zuwan naku ne duka"


"To madallah mun gode, tashi kaje dakinka ka kimtsa sai kazo ka karya" 


Da to Akram ya mike ya wuce da yake yana da daki a gidan hakama su Teema, su Abba ma Baba Kamalu ya ware musu nasu sashin koda sunzo gidan duk suna da masaukinsu. Abida ta bishi a baya kamar wata jela, yana shiga dakin tasa kai itama, Akram ya juyo yana kallonta.


"Amma dai kin ji abinda Mama ta fada cewar nazo na kimtsa"


"Uhum yaya Akram zan ta yaka kimtsawan ne"


"What? ina wasa dake ne? maza bace min da gani" 


Ya yi maganar cikin tsare gira, Abida ta zumburo baki tana gunguni ta fita a dakin, Akram yaja guntun tsaki.


"Rashin hankinta iri daya dana su Teema"


Yace yana mai zame kayansa dan ya shiga toilet ya watsa ruwa. Abida ta samu Mama a falo tana cin gamani.


"Da kyau, kinyi halin rashin wayan naki ya koro ki ko? Ya min dai dai, wannan rawar kan naki babu inda zai kai ki garama ki nitsu, dan Akram ba irin Umar da Amir bane"


*Uhum Mama wlh sonsa ne ke fuzgata har nake yin haka"


"Na dai gaya miki ki shiga taitayinki, so ba hauka bane, sannan in banda abinki Akram namu ne aurenku da shi ai kamar zane ne akan dutse, ki daina sama kanki damuwa kuma ki natsu da wannan rawan kan"


"To Mamana na san zaki min komai akan haka"


Ta fada tana yar dariya.


"Tashi kije ki shirya masa abin kari saura ki ta bare baren jiki harki zubar"


Abida ta mike tana dariya ta wuce kitchen. Tun tana karama bata san so ba Allah ya daura mata soyayyar Akram, ita dai yana matukar burgeta musamman yadda ya keda miskilanci da kuma jan aji, hakan yasa ta kwazzabawa kanta cewa lallai bata da miji sai shi, tun tana boyewa har mahaifiyata ta sani, wanda zuwa yanzu kusan duk dangi sun fahimci haka, sai dai har yanzu babu wanda yace wani abu akai duba da yanayin da Akram yake nunawa na rashin kula a gareta, ita ke kidanta take rawarta.


*****


Bayan sallar magrib Baba ya dawo suka hadu a nan falonsa suka gaida da Akram, kana ya isar masa da sakon Abbansa wanda dama akan wani kasuwanci ne da suka fara yi tare, na fitar da danyen dimond da matsinta suke samunsu a kasa da cikin teku, su Abba suna siya hannunnsu sai su fitar dashi zuwa kasar Dubai suna saidawa da tsoka, wanda Alhamdulillah Allah ya sanyawa abin albarka har shi Baba ya bude babban office anan cikin Abuja. Har misalin sallar isha'i suna tattaunawa daga bisani suka rankaya zuwa masallaci. Bayan sun idar da sallar Akram yayi sallama da Baba zaije yaga wasu abokan hundar kasuwancinsa ya dawo, Baban yayi masa Addu'a kana ya ce ya amsa key din daya daga cikin motocinsa a gurin Mama ya tafi dashi, Akram yayi godiya kana ya wuce.


Tun a hanya ya kira Haj. Hauwa ya shaida mata inda zadu hadu, nan ta kawo masa uzurinta akan tana da baki a gida, sai ta bashi hakuri daya zo gidan ta ya sameta, bai so haka ba amma ganin girmanta da yake yi yasa shi amincewa kana tace za ta tura masa address da haka suka yi sallama, ta tura masa da text din adreshinta. Akram ya juya akalarsa zuwa gidanta, minti ashirin ya dauke shi zuwa gidan yayi hon mai gadi ya bude masa ya shiga yayi parking, ya fito ya jingina da motarsa ya tura mata sakon yana gidan. Minti biyar ta sanar da shi ya shigo, Akram ya wuce ya shigo babban falon gidan ya zauna akan Cushing yana hira da Amir a WhatsApp. 


Shuru shuru har kusan minti goma bata fito ba, sai wata yar matsayar yarinya ce ta fito daga wani daki daga ganinta yar aiki ce. Tazo gabansa ta rusuna ta gaishe shi kana tace.


"Hajiya tace nayi maka iso zuwa ciki"


Akram ya mike ba tare daya ce komai ya bi bayanta. Wani karamin falo ne ta kai shi wanda yaji kayan alatu, inda ya zauna yarinyar ta shiga jera masa kayan ciye ciye bisa center table, tana gamawa ta fice.


Bagaren haj. Hauwa kuwa shegiyar ready made doguwar riga cream color ta sanya a jikinta, wanda yake shara shara illahirin surarta ya bayyana, daga ita sai pant da brezia a ciki, kanta yasha kitson shiku na attachment ta daure shi da ribom ta zubo da jelar gashin kafadarta, tasha mild make-up bakin nan sai shining yake da lips stick, ta sanya chewing gum a bakin ta tana tauna irin na gogaggun yan bariki, ta feshe jikinta da turaruka masu tsananin kamshi da tada sha'awa, ta kalli kanta a madubu tare da fidda siririn murmushi, ita kanta ta yaba da shigarta.


Haj. Hauwa fara ce kuma tana da dan jiki da tsayi sannan tana da kyau dai dai kwarkwado, zata kai shekara arba'in da biyar a duniya, amma da shike tana cikin daula da jin dadi shekarun nata basa nunawa a jikinta sai dai tsufa a fuska daya nuna kadan. Ta sanya flat shoe ta fito daga bed room dinta tana takun kasaita. 


Akram ya gundura da zaman falon domin tunda yake a rayuwarsa bai taba bin aiki ba balle har yaje a jirgashi haka yana zaman jira, haka yayita jan tsaki haushi duk ya ishe shi, dole ya cigaba da chart da Amir dan ya debe masa kewa, bai sha komai da yar aikin ta kawo ba domin baya bukata. 


Kamshin turarenta ya daki hancinsa wanda ya tabbatar masa da ta iso falon, amma baisa ya daga kansa ya kalleta ba, sai da ta iso tsakiyar falon ta tsaya tana kallonsa tare da yin gyaran murya. Akram ya dago kansa yana arba da ita yaji mummunar faduwar gaba. Auzubillahi... Yayi saurin ambata a zuciyarsa tare da saurin sunkuyar da kansa kasa, yana mai jin wani irin ciwon kai duba da irin karfin turarukan data sanya, wanda ciki harda na sihiri.


"Akram ya kake? Kayi hakuri na ajeka nasamu na sallami bakina ne sun tafi"


"Ok babu damuwa" 


Ya bata amsa ba tare da ya kuma kallonta ba, Haj. Hauwa sai ta isa kusa da shi ta zauna tare da daura hannunta kan nasa, wani shock ne yaji wanda yasa shi saurin mikewa tsaye yana mai komawa gefe cike da tsoro. Haj. Hauwa ta mike tana sakin masa wani shu'umin murmushi tare da girgiza jikinta dukiyar fulaninta suna rawa, Akram ya runtse ido saboda wani irin kululun bakin ciki da takaici daya dirar masa a zuciya, har lokacin ya kasa magana sai kallon kallon da suke yiwa juna, tana matsowa har ta cimmasa suna shakar zazzafar numfashin juna, ita na mugun sha'awarsa take fitarwa, shi kuma na tsantsar kiyayyarta yake fitarwa. Wani irin tsafka tayi masa tana kokarin hade bakinsu guri guda, Akram yasa karfi ya ture ta tayi taga taga zata fadi, amma sai ta yi na maza tayi saurin tsayawa da kyau, kana ta shiga jifansa da wani irin shu'umin kallo mai wuyar fassarawa.


#Rahma ce

#follow

#vote

#comment

#share

Please