12
A gidan ta wuni ita da mahaifinta da sauran yan'uwanta suna ta tayashi murnar birthday kowa na kalla fuskarsa dauke da farinciki,kamar wadanda aka yayewa damuwa har abada. Sai da yamma mahaifinta ya fita ya barsu a cikin gidan suna ta shagalinsu. Duk iya shagalin da akai da ciye ciye da akai Ataa na waje zaune ita kada kamar yadda Rahma ta umarce da zama waje, sai misalin sha daya na dare ta fito cikin gidan baya ta yi waya da Aliyu ta fada masa ba zata iya driving ba ya zo ya dauke ta.
Ko da ta fito Rahma na kwance a balcony, matsawa tai ya saka fada ta dan musgune ta kadan ita kuma ta farka a girgice sannan sai ta jefa mata dari biyu
“Tashi ki je gidanku”
“To”
Ta fada tare da saka hannun ta dauki kudin ta gyara Hijab dinta ta kama hanya. A gurin Rahma tai tsaye har Aliyu ya iso da motarsa harabar gidan ya faka. Sannan na soma takawa a hankali ta karaso inda yake, fito yai daga cikin motar ya bude mata front seat ta shiga ta zauna ya rufe ya koma cikin motar yai nata key ya danna horn aka bude musu gate.
Lokacin daya hau titi ya fara tafiya sai ta kwanto jikinsa, shi kuma ya kai hannunsa yana taba kanta da yake ji da zafi.
“Kina jin rashin lafiya ne?”
“Eh”
“Since when?”
Ya faka motarsa gafen titi ya juyo yan fuskantar da kyau.
“Dear miyasa kike wasa da lafiyarki ne? Ba ki san lafiyar ki tana da amfani a gurina ba? Tun yaushe kika so ma jin zazzabi”
“Da yamma nan, yanzu ne ya fi min sosai”
Wayarsa ya ciro ya kira Doc Asim bugu biyu ya dauka.
“Doc same ni gida yanzu, jikin Rahma ya tashi”
Yana fadar hakan ya kashe wayar ya jana motar @360 suka iso gida, ba su yi minti ashirin da isa ba sai ga Doc Asim ya iso, tana zaunen falon kusa da Aliyu ya tambayeta abunda ta ke ji ta fada masa ya bata magani, sannan Aliyu ya rika ta suka shiga bedroom ya kwantar da ita, bakin gadon ya zauna kusa da ita yana ta kallonta kamar mai auna hawa da saukar numfashinta, har bachi yai gaba da ita, sannan na taso ya fito daga dakin shi ma saboda kiran wayar da Mama Fulani tai masa ne, saukowa yai kasa yana amsa wayar. Yadda fuskarsa take sake duk kuwa da irin tashin hankalin da ke ransa na ciwon matarsa, amman ka ga murmushi a fuskarsa ka san mai kiran yana da muhimmanci gare shi.
“Aliyu ka yafe kowa ka kyale mu ko?”
“Na isa Mama? Ai ko zan yafe kowa ban da uwata matukar ina neman albarka”
“To ya gida ya matar ta ka?”
“Gida kalau surukarki kuma tana nan yau jikin ya soma tashi”
“Subhanallahi fatar dai da sauki”
“Da sauki ta samu bachi ma”
“Masha-Allah Allah kara lafiya, zan je Dubai gobe, ba lallai idan na je can na kira ka ba, fada min abunda kake son na siyo maka da matarka”
“Ni dai perfume na ke so, ita kuma ki siyo mata duk abunda kika ga ya dace”
“To shikenan, a gaishe ta idan ta tashi”
“Zata ji thank you Mama”
“Allah maka albarka”
Daga haka tai hanging. Shi kuma ya tashi cikin rashin kuzari ya nufi kitchen, tea ya hadawa kansa ya dawo saman kujera ya zauna ya kunna tv for like ten minutes ya tashi ya koma dakin matarsa.
ATAA POV.
ban taba auna rashin imani da tausayin irin na matar nan sai yau, ta ba a gidan zan kwana ba amman ta kyale ni na zauna a waje bata ba ni abinci ba na wuni da yunwa ta bar ni a haka, yanzu kuma sha dayan dare ta ce na kama hanyar gidan, gashi ko abun hawa babu, tsoro da fargabar abunda zai same ni, wa zai tare ji a hanya barayi ko masu cin zarafin mata duk be dame ta ba, saboda kawai ina nema a karkashinta, shi kenan dan ina talaka ba ni da gata, ni fa ya ce kamar kowa ba daga sama na fado ba, amman saboda ba ni da shi ina talaka a yau an sake ni karfe goma sha dayan dare na kama hanyar gida. Ban samu a abun hawa ba, a kafa nai ta takawa ina ta addu'ar Allah ya kai ni gida lafiya. Ko da na isa unguwar babu mutane sosai domin daya saura na dare. A bakin kofar gidan na tsaya nai buga kofar ba a dade ba aka bude min, babu wuta a lokacin dan haka mahaifin Farida ya haske min fuska da fitila.
“Ataa ke ce cikin daren nan? Ina kike je?”
“Gurin aikin ne, muka fita ba mu dawo ba, sai yanzu”
“Ina kuka je?”
“Gidan iyayenta”
Sai ya bude min kofar na shigo yana ta kallona kamar be yarda da ni ba, sai da na shigo cikin gidan na hango Nana tsaye rike da bango tana kallona lokacin da na karasa kusa da ita sai na rasa me zan ce mata, na sani dole hankalinta ya tashi rashin ganin na dawo, gashi babu mai mata wata hidimar sai ni. Rikata nai muka koma cikin dakin sai da ta fara zama sannan na zauna kusa da ita na fada mata dalilin dadewar da nai ban dawo ba.
“Da wani abun ya same ki a hanya fa?”
“Nana matar nan da na ke yi ma aikin yar mai kangon gidancan ne wanda ya kore mu, ina ganin gaba daya danginsu basa da mutumci ko kadan”
Na fada cikin muryar da ke Nun a gajiye na ke ga kuma yunwa da na ke ji rabon da na saka wani abu a cikina tun karin safe da na sha koko da kosai. Sama-sama mu kai fira da Nana ta nuna min rashin jindadinta na dadewar da nai a can sannan muka kwanta ni da ita.
Yau ma kamar jiya na tashi da wuri saboda matar nan ta fada min na rika zuwa tun karfe bakwai na safe, na san idan na tsaba lokaci wani abu zai iya biyo baya, waina na siyowa Nana ta karya sannan na fito na wanke kwanon da ta ci na maida na janyo ruwan rijiya na yi wanka na saka doguwar rigata ta atamfata kodaddiya, ban damu da saka dankwali ba, na fita waje na daddaka bakin gawayin na shafa a fuskata, na saka Hijab dina na fito na leda dakin Maman su Farida na gaisheta sannan na saki labulen dakin har na kama hanyar fita sai ga Farida ta fito sanye da uniform din makaranta tana cewa na tsaya mata.
“Har kin shirya zuwa aikin tun da safe haka?”
“Wallahi matar da na ke aiki gidan ta ne bata da mutunci ko kadan, tace na rika zuwa bakwai kin ga idan na tsaba zata iya korata gaba daya”
“Gaskiya kan bata da mutunci, tun da har zata rike ki ki kai karfe daya na dare sannan ki dawo, ni wallahi da za ki biye ni da kin yarda maman Salma ta sama miki aiki a Abuja, acan take samawa mutane kuma Wallahi albashi mai tsoka”
“Kai anya Farida zan iya zuwa har Abuja? Kin ga Nana ai bata da wanda zai kula da ita sai ni”
“Amman ai dan neman lafiyarta da abincin ta za ki yi, kuma idan ya wadace ku ya kamata ki dauke ta kuje har garinku ki nemi danginku, zama a nan babu kowa a tare da ku ba zai amfana muku komai ba”
“Nima ina tunanin haka, amman na fi son sai Nana ta samu lafiya tukuna”
“Allah ya bata lafiya, nawa ne suka dauke ki aikin?”
“8k ne”
“8k mi zai miki? Ai wannan kudin zai iya karewa a abinci kawai, gaskiya kara ma Abuja nan ance can fa irin manyan gidajen nan har 30k 50k ana bawa mutum, kin ga da kin hada na wata uku ai ya isashe ki”
“Da gaske Farida”
Na tambaya cike da kwadayin tabbatar da zancen nata.
“Wallahi haka Maman Salma ta ce min”
“Ai ba zuwan ba, kin ga dama ace Lukman yana da rai dazan samu sauki wanda zai kula min da Nana amman yanzu bata da kowa ai sai ni, ita kanta ba zata yarda na tafi ba”
“Gaskiya haka ne, amman indai ina nan ni kaina ai zan iya kula da Nana kin sani, ko da ba zan cire mata kewarki ba zan rage mata shi, ko ba zuwa aiki ba ai dole wata rana za ki yi aure ki tafi ki barta, ko da yaki kin ki bari ma aga fuskar na ki kullum sai boyo kike”
Na yi murmushi ina kallonta a yayinda muka kawo a hanyar da za mu rabu.
“Farida kenan, ni ban taba kawo wa kaina tunanin aure ba, ban taba lissafa kaina a cikin matan da za a iya aure ba”
“Saboda?”
Ta tambaya cike da mamaki. Sai na sake yin murmushi a karo na biyu na ce.
“Ba ni wannan lokacin da zan tsaya na yi fira da wani namiji ba, kullum tunanina ina abinci zai shigo, yanzu kuma tunani ina kudi za su shigo na nemawa Nana lafiya, bayan haka maza basa son yarinyar da bata da arziki a gidansu, sun fi son aure yar masu kudi ko mai rufin asibiti, amman irina idan aka ce za amin aure na san daga ni sai tabarma za a kaini, wanda na san hakan zai iya janyo min wulakanci da kankanci a gurin mijin da yan'uwansa”
Kallon hawayen da suka cika idona ta tsaya yi sai ta rumgume itama idonta cike da kwalla.
“Za ki yi aure kawata, In-Sha-Allah za ki auri mutumen da zai dauki dawainiyarki har da ta Nana ma, na saka ki gaban mota yai ta yawo da ke a garin nan”
Na sake ta ina yar dariyar zancenta.
“Farida kenan, wa zai yi mace irina haka? Mace da batai boko ba, bata waye ba, bata iya komai ba sai bara da roko a titi? Babu wanda zai so auren makaskanciya”
“Ataa karki yanke kauna daga rahamar Allah, dan jarrabe ki a haka ba shi yake nufin ba za ki samu jindadi a gaba ba”
“Na sani, kawai ina duba yanayin rayuwar ne, duniyar ta canja ba kamar da ba ne, ke dai ki tafi makaranta kar ki yi latti”
Daga haka muka rabu ita ta wuce makaranta ni kuma na kama hanyar zuwa gurin aikina, ina ta kwadayin zuwa makaranta amman ba hali, lallai karatu da samun wanda zai tsaya maka ka yi karatun gata ne.
Ina tafe ina ta sake sake na har na isa, yau kan ni kaina na san na yi rana zuwa domin a kafa na zo kamar yadda a jiya din ma na dawo a kafa duk kuwa da irin tazarar da ke tsakanin unguwar mu da ta su. Sai da nai knocked gate din sau biyu sannan aka saka bude min gate din na gaishe shi kamar yadda na yi jiya sannan doshi cikin gidan, na yi mamakin tararda kofar falon abude wata kila wani dalilin ne ya saka suka bude kofar. Ni dai na shiga da sallamata duk da nasan ba za a amsa min ba, haka kuwa akai domin mai gidan nan na hakince saman cushion amman be amsa min ba duk da idonsa na kaina har na karasa tsakiyar falon na gaishe shi nan ma be ce min komai ba. Ban damuwa ba, domin a tsakanin jiya da shekaranjiya kawai na fara sabawa da halinsa da dabi'unsa, matarsa ta fda min baya son yawan kallo, sai dai na lura shi din yana da kure mutum da ido har ka soma tsarguwa sai kuma ace wai kai ba zaka kalleshi ba, lallai masu kudin nan akwai su da rashin adalci da takura rayuwa. Abu na biyu na lura baya son yawan magana kuma yana da kyama sosai fiye da matarsa, ga kamshi a duk inda ya wulga ko ya zauna, kamshin turarensa ne ke yiwa mutum sallama tun gabanin shi yai maka, akwai kwarjini sosai idan kana kallonsa, haibarsa tana fitarta da siffar zatinsa da ainahin kyauwunsa, ban taba ganin murmushinsa ba, a tunani murmushi kamar ba zai yi ma fuskarsa kyau ba, duk kuwa da kasancewar yana cikin sunnar Manzo na, sai dai nana jin wannan miskilin ya ta6a ďa66aka sunnarsa ta murmushi balle kuma har ta kai shi ga yin dariya.
Gurin da na dauki tsitsiya jiya na nufa na dauka tare da mopper na nufi kitchen, can na ke ra'ayin na fara gyarawa tun da na ga shi yana zaune a falon, waya sani ita ko bata tashi bachi ba, balle na gyara bedrooms. Ina cikin aikina na ji tsayarwar mota a harabar gidan, sannan na ji sallama da muryar da na ke kyautata zaton kamar na san mai ita, sai da na gyara kitchen din tsaf sannan na riko tsintsinyar ya fito daga kitchen da zimmar gyara dinning area da falon idan magajin izzar ya tashi.
Arba idanuwa sukai da mummuna mutum wanda zan iya kiransa da bakar jaddara, da bana son na sake saka ta a idona har a bada, Doc Asim ne sanye da suit ya dora labcoat sama yana zaune akan kujerar da ke fuskantar wacce Rahma take zaune ita da mijinta...
Bana bukatar na tambaye abunda ya kawo shi gidan, kasancewarsa likita, da kuma yanayin da naga Rahma na tabbatar bata jindadi, sai dai ina tabbacin ba su san ko waye Doc Asim ba, shiyasa har suka kira shi har cikin gidansu, akwai yiyiwar ya sake samun damar sake cutarsu kamar yadda ya cutar da ni. Kallonsa kawai da na ke ina jin kamar naje na shakeshi ya mutu.
“Ke lafiya kika tsaya kallon mutane ba za kije ki yi aikin ba?”
Rahma ta daka tsawar data saka ni dawowa hayyacina. Sai mijinta yai saurin rike hannunta yana alama da tai shiru kar ta wahalar da kanta gurin magana.
“Karku yarda da wannan mutumen Wallahi azzalumi ne macuci, mugu wanda ba zai taba gamawa lafiya ba”
Da sauri Doc Asim ya dago yana kallon inda nake tsaye da mugun mamaki, da alama sai yanzu ya san da tsayen da nai jikin kofar.
“Wacece wannan?”
Ya tambaya yana kallon Mai gidan da ke kallona shi da matarsa.
“Ba ka gane ni ba?”
Na fada kana na saki tsintsiyar hannuna na juya na koma kitchen din na cire Hijabina abun ka da marar dankwali sai gashi na sauko har gadon bayana, na zuba omon da ke gurin na wanke bakin fuskata na juyo na fito a fusace na karasa har kusa da inda yake zauna na nuna masa fuskata.
“Ka ganene yanzu? Bayan ni wace yarinyar ka cuta? Bayan ni wace macen ka sani mai kama da ni?”
Miyewa yai tsaye ya wanke min fuska da mari.
“Ba ki da hankali ke kin taba ganina ne?”
Tasss na mayar masa da martanin marin da yai min cikin zafin rai, duk da kasancewar ya girme ni a shekaru da jiki.
“Na mare ka da hujja sai ka samu damar sake saka yan sanda su kulle ni a cell kamar yadda ka sa aka min saboda ina talaka”
Yadda muryata take fita kadai ta isa ta karantar da kowa irin daci da dafin bakincikin da ke raina, ga wasu zafafan hawaye da suke sauko min, ina yi ma Doc Asim wani irin kallo mai guba. Mamaki ya hana shi motsi sai sakin baki da yai yana kallona, Rahma ce ta mike tsaye.
“Ke ashe baki da hankali ba ki da tarbiya? Za ki daga hannu ki mari babban mutum mai daraja kamar Doc Asim? Kina yar talaka?”
“Ba yin kaina ba ne talaucin, ke ma da Allah ya zabi a gidan masu arziki ba yin kanki ba ne, ba wata gwaninta kikai wa Allah ba ya zabe ki ya bar ni, saboda kawai ina talaka ba shi yake nufin ni ba mutum ba ce, a gurin ki Doc Asim yake mai daraja amman a gurina konanniyar ashanar bola ta fi shi, zan fi jindadin sunan mutuwa fiye da sunan wannan azzalumin, ganin bakin duhun zai fi min ganin wannan mutumen”
Na fada ina nuna shi da yatsana, mamaki ya cika Rahma, mijinta kuwa kallona kawai yake sai kuma ya kalli Doc Asim kamar mai son tantance abu. Doc Asim ya jinjina kai yana kallona yai kwafa.
“Ni kika mara? Sai kin yabawa aya zakinta, ni ban sanki ba ban san inda kika fito ba amman sai na nuna miki ko wanene ni”
“Babu abunda zaka nuna wanda ban san shi ba, na sanka na san zalincika tun har ka iya cire kodar mahaifiyata ba tare da saninta ba, saboda kawai ka maida ni zahila marar galihu, ka sa na saka hannu kai mata aiki ka cire mata koda, kuma kasa aka kulleni a gidan yan sanda saboda na nemi hakkin mahaifiyata, to wane zalinci zaka nuna min da ya wuce wannan? Idan kashe ni kaka son yi, to mutum baya mutuwa biyu, domin ni na dade da mutuwa tun daga lokacin da kasa mahaifiyata ta rasa lafiyarta, sanadin haka na rasa kanena, to me zaka min yanzu? Duk abunda kake jin zaka iya yi kaje kai, ba a duniya za a tabbata ba, akwai kiyamar Allah zata tsaya, kuma ni da kai za ku amsa ko wace tambaya daga Ubangiji...”
Na karasa ina fashewa da kuka tare da juyawa da zimmar zuwa na dauki tsintsiyar na cigaba da aikina, sai naji muryar mijin matar nan yana wata irin magana mai rikitarwa.
“Kardar kodar da aka dasawa Rahma take magana....?”
Juyowa nai idona na hawaye na nuna Rahma.
“Kodar Nana ka sakawa wannan matar? Matar da mahaifinta ya koremu a kangon gidansa saboda mun taba a gidan? Matar da mahaifinta be san daraja talaka ba? Matar da mahaifinta yasa a ka wulakanta mu? Ita ka sakawa kodar talaka? Talakar ma wacce ya wulakanta? Ka cuce ni ka cuci nana Allah ya isa tsakanina da kai, da kai da duk wanda yasa kuka aikata min wannan aikin ba za ku ga da kyau ba, Wallahi Allah ba zai barku ba”
Na fada cikin daga murya iya kar karfina, sam na manta da a gidan wani mai kudi nake, yau duk wani tsoro da fargabar gudun laifi ya fita a raina, daga Rahma har mijinta da Doc Asim yau kananan mutane na ke kallonsu kuma azzalumai.
“Uban waye yace ki siyar? Akan mi za ki rika fada mana magana son ranki cikin gida? Ubana sa'arki ne da zaki rika saka ko a maganar ki?”
Rahma ce ke wannan maganar tana matsowa kusa da ni, har ta ka hannu zata mare ni sai mijinta yai saurin rike duka hannayenta ya matsar da ita jikinsa yadda ba zata iya ko da kwakwaran motsi ba.
“Talauci ba hauka ba ne Rahma, kuma ba kaskanci ba ne, jarabawa ce daga Ubangiji, ba kuma zan sake yarda marar sanin darajar dan adam irinki wacce ta more da kodar mahaifiyata ta sake wulakanta ni ba, kin ci riba da ni tun da nayi aikin kwana biyu a karkashin ki, amman ba za a koma ba, ya zama na karshe, sai dai ki wulakanta wata amman ba ni ba, kuma tun da har kuka zalinmu lafiyar nan da bata yi amfani komai a jikinki ba”
Ina kawai nan na nufi kitchen din a fusacw na dauki Hijab dina na saka na fito fuuuu na fice daga gidan kamar iska. Kan kace kwabo har na kai gate na bude na fita raina na min mugun zafi zuciyata na ciwo sosai. A rayuwata ban taba ganin mutane masu son kai da tsantsan zalinci kamar likitan nan da mutanen nan ba, babban bakincikina sun ci riba da ni na aikin da nai a karkashinsu, wanda hakan ya fi komai yi min ciwo.
Tun da na kama hanyar gida sai na nemi kukan zuciyata da na ido na rasa, wani karsashin da karfin zuciya dana ruhi suka rufe ni, na jaddawa kaina nemawa Nana lafiyata ta rayu ko dan bakincikin masu son ganin bayanta, a yau na gane ba kuka na ke bukata a yanzu ba, lokacin kuka da bakincikin abunda ya faru a baya ya kare, wannan lokacin na fuskartar gaba ne da inganta rayuwata da ta Nana, na yarda abunda ya tafi baya dawowa amman abunda be zai zo za a iya tarbarsa gabannin ya zo, zan jure ko wane kalar wulakanci da cin zafi daga duk wanda zai iya zama dalilin samun lafiyar Nana.
A kullum idan zanje gida ina zuwa da kasala da jin gajiyar tafiyar, amman a yau na isa gida da karfi kamar daman can ban yi tafiyar ba, ban yarda Nana ta fahimci komai ba, na shiga dakinta na zauna ina ta kokarin yin far'ar da take ta zo min.
“Lafiya kika dawo da wuri haka Ataa?”
“Nana sun koreni daga aikin”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, sun kore ki kuma? Me kikai? Mun shiga uku”
“Ba mu shiga uku ba, kuma da yardar Allah ba za mu sake shiga uku ba, ina tunanin ma kamar wata hanyar zata sake bude mana?”
“Kamar ya? Yanzu ina za ki sake samun wani aikin”
“Farida ta fada min cewar Maman Samawa tana samawa mutane aiki a abuja, kuma a can ana biyan kusan 30k ko sama da haka, kin ga cikin wata biyu ko uku na hada kudin maganinki”
“Aa ni ba zan yarda kije can nesa ba, ban san iya abunda zai iya samunki ba, kuma nan wa zai kula da ni idan ki ka tafi?”
“Farida ta min alkwarin kula da ke, idan har za ki iya hakurin ciwon nan na ki zauna asibiti na tsawon wata biyu, zaki iya hankurin rashin ganina na wata daya, idan na samu lokaci sai na zo na ganki ni dai amincewar ki na ke bukataka kamin nai ma maman salma magana, ina son lafiyarki Nana, sai da lafiyarki zan iya neman dangina, hankalina kuma ya kwanta, dan Allah ki amince Nana”
Na fada ina kama hannayensa sai naga yanayinta da fuskarta sun canja.
“Ko daga nan zuwa wani gurin za ki je, ina jin tsoro Ataa sai naga kamar ba za ki dawo ba, bana son ki zo yi ta wahala da gawa waya sani ko ba zan kai wani lokacin ba”
“Da ba zaki kai wani lokacin ba, da baki rayuwa bayan wannan lokacin da akai miki tiyata ba, kuma babu wanda yasan rayuwa da mutuwar wani sai Allah, kina karya min guiya, ki rika nuna min cewar zamu rayu ni da ke ko da mu kai muka rage a duniya, dan Allah Nana ki barni nai wannan jihadin, ki bar ni na samun wannan faricikin da ladar”
Magangannun nai ta mata ina lurar da ita har na samu ta aminta duk da kasancewar ba ta so haka ba. Bayan sallah azahar na ja Farida muka kama hanyar gidan maman salma da shiga mu kai sallama muka gaisheta, sannan Farida ta koro mata da bayanin da ke tafe da mu, wani abun mamaki da jindadi sai tai murna da hakan har take labarta mana cewar daman ana neman mai aikin a wani babban gidan masu kudi da ke Abuja, sai dai tace ba zata yi komai ba har sai ta zo gurin Nana ta ji ta bakinta dan tabbatarwa, ni kuma na ce mata na yarda ta zo su yi magana, sallama muka mata muka kamo hanyar gida wani dadi ya lullube ni na soma yarda da cewar kukana ya kusa karewa...
ALIYU POV.
Zai iya rantsewa a rayuwarsa be taba haduwa da wata mace yar talakawa mai karfin zuciyar da ta iya tsaya gabansa ta fadawa Rahma magana son ransa ba sai yau, for the first time yau wata ta ciwa Rahma mutunci ya kasa yin komai, har yanzu fuskarta yake gani irin kyau da haiya ta yai arba da shi a fuskarta a yau ko a mafarki be ci karo da macen da kallonta ya saka shi faduwar gaba ba sai yau. Kalamanta da ďai-ďaiya suke masa yawo a kunne, kalma zalinci ita kalma ta biyu daya tsana bayan talauci, yes he's rich and he know be zama dole ya taimaki kowa da dukiyarsa ba, amman yai wa kansa alkwarin ba zai taba yarda dukiyarsa ta saka ya zalinci wani ba, ko da kuwa talakan daya kyama ne. Yasan yadda lafiyata take da muhimmanci tun daga lokacin daya fara neman ta matarsa yana jin tsoron rasa ta a ko wace dakika ita kadai da take a natsayin matarsa hakan yasa shi fahimtar Ataa wacce ita kuma take zancen mahaifiyarta.
Haka sukai tsaye a falon bayan fitar Ataa har na tsawon mintuna talatin ba tare da kowa ya ce uffan ba, daga Aliyu har Rahma da Doc Asim dake ra sake saken yadda zai kare kansa. Rahma jiran take mai kare yace wani abu tun daga lokacin da Ataa ta fada mata ba daidai ba, amman bata ji yace komai ba, sai ma rike mata hannu da yai a lokacin da zata mareta. Aliyu kuma yana ta jiran abunda zai fito daga bakin Doc Asim amman ya kasa magana kamar an daure shi.
“Kodar mahaifiyata ka cire aka sakawa Rahma ba tare da sanin ba?”
Doc Asim yai saurin kallon Aliyu.
“No karya ta ke yi? Ita ta siyar da kodar da kanta, zan iya nuna maka shaida ma, ita ta siyar da kanta”
“Mi zai saka tai maka karya? You know what na yarda da komai amman ban yarda da zalinci ba, ban yarda na zalinci wani na kuma na kwanta nai bachi mai dadi ba, dan ina neman lafiyar Rahma ban ce ka zalinci wata ba, na fada maka ka nemo wacce zata saida zan biya ko dala dubu nawa ne, amman ban ce ka cire ba tare da sanin mai ita ba”
“Amman Dear ai yace siyarwa tai...”
“Silent”
Ya fada sai dai ba cikin daga murya ba, tare da dagawa Rahma hannun wacce ke kokarin kare Doc Asim da nuna abunda yai ba dai-dai ba ne.
“Ka bani amsa da saninta ka cire ko ba da saninta ba”
“Ni ban san wannan yarinyar ba”
Shine kawai abunda Doc Asim ya fada ya dauki akwatinsa ya fice a fusace har gumi na karyo masa idonsa su yi ja alamar ransa ya bace sosai. Yana fita Rahma ta kalli Aliyu sannan ta nufi upstairs cikin bacin rai da zazza6in da da ke kokarin rufeta. Zaunawa Aliyu yai saman cushion yana ta auna irin zalincin da akwai wa Ataa idan har ta tabbata Doc Asim ya cirewa mahaifiyarta koda ba tare da sani ba, mikewa yai tsaye ya bi bayan Rahma a bedroom dinta ya same ta zaune bakin gado tana waya be san me ta fada masa ba, kuma be san da wa take wayar ba, sai dai yana alamar kuka da hawaye a idonta, saurin fisge wayar yai ya kashe kiran sai ya kashe wayar gaba daya, ya zauna kusa da ita.
“Kin sani idan kina ciwo bana son kina wani dogon motsin, za ki yi street kanki ne kawai”
Kallonsa tai da duba mai mai ma'anoni da yawa idonta har ya fara ja.
“Miyasa zaka yarda da yarinyar nan ka karyata likitan da ya shekara biyar yana maka hidima?”
Be ce mata komai ba, ya kai hannunsa ya share mata hawayenta sannan ya rika fuskarta da hannayensa biyu yana mata magana a hankali yadda hankalinta zai kwanta.
“Za mu magana daga baya, for now ina son ki kwanta ki huta, and promise me za ki yi bachi?”
Ta dauke kai tana hadeye yawu. Sai ya jata zuwa kirjinsa ya rumgume, ya dan kishingida da gadon yana ta kallon sillin kamar mai tunani. Ya dauki awa daya a haka sannan ya soma jin sauka numfashinta mai zafi alamar bachi ya dauke, sai ya kwantar da kanta saman fillo ya lullube ta da blanket ya mike a hankali ya fita daga dakin dare da jan kofar dakin a hankali.
Fitowa yai daga cikin gidan gaba daya, tun kan ya karasa gurin motarsa ya danna key motar ta bude, yana shiga yai nata key tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate din yana daga masa hannu, ko kula shi be yi ba ya dauki hanyar gidansu wato gurin Momy, as usual idan babu Nasir ko Mama Fulani a kusa da shi Momy ce abokiyar shawararsa, ko da ma suna nan wani lokacin ya kan kirata a waya ya shaida mata, yau ma yana da bukatar fada mata abunda ya faru yaji nata tunani. He arrived in time a daidai lokacin da Momy ta kara Daddy ya shiga mota tana tsaye tana kallon yadda mai gadin gidan yake rufe gate, sai ta ya sake budewa da sauri jikin har bari yake, ashe Aliyu ya hango tafe. Murmushi tai domin ta san a duk duniya Aliyu kadai ya isa ayi masa haka a gidanta, baya danna horn sau biyu kuma bayana son jira saidai a jira shi, idan kana son kaganin bacin ransa ka kwada bata masa lokaci ko kuma saka shi jira na rashin dalili.
Tana ta kallon dan na ta har ya faka motarsa a inda ya fi masa soyuwa a harabar gidan sannan ya fito fuskarsa ba yabo ba fallasa kamar kullum ya doshi inda mahaifiyarsa take, yadda yake takawa sai ka rantse da Allah takun kasaita ne da nuna isa, alhalin haka tafiyarsa take, kamshin turarensa na ta sanarda zuwansa tun kan ya karaso kusa da ita. Zai da ya rage sauran taku shida zuwa bakwai tsakaninsa da ita sannan ya dabbaka sunnar nan ta murmushi wacce ta kara mishi kyau da haifa.
“Na ga Daddy ya fita yanzu har mun gaisa da shi ma”
“Eh yana ta sauri za su je meeting”
Haka suka jero ita da danta suka shigo cikin falon suna wannan hirar. Saman cushion ta zauna tana nuna masa dinning.
“Ga ragowar breakfast can idan zaka ci kanenka suka raga”
Ya dan yamutsa fuska yana murmushi dan yasan zolayarsa kawai Momy take.
“Momy kin san ai bana cin ragowar kowa ni, ina Sisters”
“Duka suna school”
Ajiyar zuciya ya sauke wanda yasa Momy sake dubansa.
“Wani abun ne?”
Ya jimm na wani lokacin sannan sannan ya kalleta a natse ya ce.
“Momy kin san kwana ki ina ta neman mai aiki ko? Sai ga wata yarinya ta zo gidan neman aiki.... ”
Tun daga lokacin da Ataa ta zo gidan ya jera mata labarin har ya isa zangon da ya fi rikitar da shi. Da mugun mamaki Momy ta kalli.
“Kuma ba ka ji komai a ranka ba Dan wajen Fulani? Ba zuciya da jini ne a kirjinka ba? A zalinci wata ta dalilinku har ka tsaya neman hujja?”
“Amman ni ban ce a zalince ta ba?”
“Miyasa da aka kawo maka kodar baka bincika daga inda ta fito ba? Akan me zaka zuba kudi mai yawa ka ce a samo maka kodar? Ba kayi tunanin ganin kudin zai iya saka Doc Asim aikata komai dan ya samu kudin ba? Ai da tun farko ka samu mai kodar ka yi magana da ita da bakinka, yanzu ga shi ka raya matarta kana cikin farinciki, ita kuma ka jefata a damuwa da bakinciki? Ka ji tsoron addu'ar wanda aka zakinta, kuma ka ji tsoron Allah ya isa, domin idan bata bi jikinka ba, tana bin dukiya da kaddara”
Lumashe ido yai ya bude yana fusar iskar bakina a hankali.
“Ka tuna lokacin da aka ce maka Rahma zata iya rasa ranta idan ba mata wano dashen kodar ba? Ka tuna? Ka auna ka ji ya yarinyar nan ta ke ji? Ita da mahaifiyarta ce, kamar ni ce ko Fulani aka cirewa koda ba tare da saninka ba? Idan ka gano me zaka yi?”
“Zan yi duk abunda zan yi na kwato muku hakkinku”
“To sai aka samu akasi ita yar talakawa ce, bata da wannan ikon bata da wannan gatan, mahaifiyar tana raye ko ta mutu babu wanda ya sani, wane hali suka shiga bayan wannan babu wanda ya sani, ina jiye maku tsoron abunda ta zai biyo baya, amman gaskiya an zalinci yarinyar nan”
“Momy kin san inna sani ba zan zalince ta ba, na yarda bana kula kowa amman bana zalintar kowa?”
“Ka bude zuciyarka kai tunani... Na san kana son matar ka kuma zaka iya komai akan samun lafiyarta, amman ina son na fada maka wani abu, ka ji tsoron addu'ar wanda aka zalinta, kuma ka ji tsoro mutumen da zai ce ya barwa Allah Allah shine zai isar masa, hakan yana nufin babu komai tsakanin shi da kai Allah ne zai wakilce shi ya fidda masa hakkinsa akanka.....”
Kallon Momy yai zuciyarsa cike da tsoro da be taba jin irinsa ba, jikinsa yai mugun sanyi, tsoron abunda zai biyo baya kamar yadda Momy ta ce yasa zuciyarsa rauni...