8
*ƘADDARARREN AL'AMARI*
© *Rahma Kabir*
Mrs MG
Wattpad @Rahmakabir.
08
Haj. Hauwa ta saki wani guntun murmushi.
"Akram meye haka? ina ce ka dade da waye a wannan duniyar tamu mai cike da ababen dadi, kai da kayi rayuwar a kasar waje ai nasan kasan komai. Dan Allah ka bari mu jiyar da juna dandanon dadinmu, kar kayi wasa da damarka. Wlh tun ranar dana ganka a wannan videon naji na kamu da sonka tare da tsantsar shawarka, shiyasa nayi dubarar shirya maka gadar zare akan kwangila domin kazo gareni"
"Kinyi babban kuskure domin Akram ba zubin irin ki bane mai budurwar zuciya, ina tsoron Allah kamar yadda nasan zatinsa yake a ko ina, bazan ci amanar tarbiyyar iyayena ba sannan ba zan sabi Allah ba saboda in gujewa azabarsa. Ina miki fatan shiriya, amma daga yanzu ki tabbatar da kin goge shafin sani na a duniya, ki manta da sunana domin ba zaki taba samun abinda kike nima a gareni ba har abada"
Yana gama fadar haka ya matso ya dauki key motarsa ya sanya a aljihu tare da wayarsa, ya zo zai rabe ta ya wuce, Haj. Hauwa tayi saurin kamo masa hannu tana son jawosa jikinta, Akram yayi wani kyakkyawar zabura ya fincike hannunsa kana ya sakar mata lafiyayyan mari a kuncinta yana mai huci kamar tsohon zaki, ta dafe kuncin tana kallonsa cike da tsoro, nan take idanunsa suka yi jaa ya zaro su waje yana wurga mata wani irin mugun kallo.
"Akul hanunki ya kuma taba jikina, wallahil azeem saina yi kasa kasa dake kuma babu abinda kika isa ki min. Banza mahaukaciya wacce ta kulla kawance da shaidan"
Ya kare maganar yana dukan kansa da tafin hannunsa, domin tayi matukar kure bacin ransa, ya girgiza kai tare da karonto Azubillahi... A ransa kana ya juya akalarsa yayi gaba ya barta cike da tsoro gami da mamakinsa. Sai da taga bacewarsa kafin ta samu damar dauke ajiyar zuciya, ta fada kan cushing jabar kamar wacce lakka ya kare mata.
"Wallahi kayi kadan, ko da zanyi yawo tsirara sai na sameka kuma saina juyaka na mai da ka tamkar bawa na, Da ni kake wasa, ka tabo ruwan dafa kanka"
Yayi maganar a fusace, gaba daya zuciyarta ta dagule ta rasa ina zata sanya ranta taji sanyi.
Akram yana fita daga gidan ya shiga zuba gudu kamar zai bar garin, sai da yayi nisa sosai kana ya sauka kan hanya ya dafe kansa cike da kunan rai, ji yake dama hawaye zai zubo masa ya samu sanyi a zuciyarsa, ya ji dama yayi mata dukan mutuwa kila daga kansa ba zata kuma kula wani d'a namiji ba, yaji ya tsani duk wani social media musamman Instagram da mutane suka mai da shi duniyarsu, in har baka yi kai baka waye ba. Mutane sun mai da kansu kamar wawaye sun aje addini sun dauki rayuwar yahudawa, sun daina kishin kansu balle na matansu, su yad'a duk abinda suke ciki na yau da kullun babu sirrin domin duniya tasan su wasu ne, sun dauki hakan wata duniya ce ta wayewa, bacin halaka ce a bayyane suke jawota da hannunsu.
_Wani Malami mai hikima yana cewa wayewa iskanci wanda ya waye dan iska, ma'anarsa na fadar haka shi ne duk wayewar da mutum zai yi bata addinin musulunci ba, to wannan wayewar ta zama na iskanci_
"Yanzu da Amir bai sanya video na ba babu yadda za ayi ta ganni har shaidan yayi mata kururuwa akai na. Na yarda a cikin kaso tamanin cikin dari waya ita ce ummun aba'isin yawan fasadi da yawan aikata ayyukan alfasha. Musamman yadda manyan mata da maza suka daukeshi hanyar samuwar abinda suke so dan wanyewar sha'awarsu. Kuma su iyayen wasu ne, duk da girma ya kamasu hakan bai sa sun koma ga Allah ba. Tir da wannan rayuwa mara tushe Allah ka fisshe mu tsaka mai wuya ka kare mu da bata bayan shiriya, Allah kaine mai kariya ka kareni daga aikata aikin dana sani"
Yana gama wannan addu'an ya tada motarsa ya wuce gida cike da tunani iri iri a zuciyarsa.
*
Seema tun abin da ta aikawa su Teema a washe gari tabar garin ta wuce abuja, bata bari kowa yasan inda ta nufa ba, ta kama hotel tare da kashe duk wayoyinta sai ta bar sabuwar number din data siya wanda tayi amfani da shi wajen turawa su Teema hotunan su, ta kuma baza yaranta a nan Kaduna domin su kasance masu sanya ido ko da su Teema zasu mika lamarin ga yan sanda. Hankalinta kwance domin duk wani information da take so yana zuwa mata, sai dai har lokacin ba tada masaniyar maganar taje gun yan sanda, hakan yasa ta yanke shawarar shi cikin garin Kaduna a gobe Lahadi domin ta samu ta hadu da su Teema su biyata kudinta su karkare maganar.
****** *******
Washe gari
Karfe bakwai Akram yayi sallama dasu Baba in da Abida ta makale masa dole sai ta biyoshi tayi Hutu a gidansu, haka driver ya kaisu tashar jirgin kasa suka siya ticket suka shiga suka zauna. Haka ma ta bangaren Seema itama jirgin ta shiga wacce ta zauna a bayan kujerar dasu Akram ke zaune. Minti goma jirgin ya tashi sai garin Kaduna.
Suna isa dama driver da escort din Akram suna jiransu haka suka shiga mota gaba daya suka wuce gida. Bangaren Seema itama ta kira kawarta Jadda dan ta dauketa, tana fitowa itama ta shige motar Jidda duka wuce, motar tana tashin sautin music Seema tana kada kai kamar kadangare.
"Kawata ya labarin su Teema sunyi sending kudin kuwa? dan wlh na kosa mu wuce Dubai fa"
Cewar Jidda da ta maida hankalin kan titi tana tuki cike da kwarewa. Seema ta murmusa
"Abinda ya dawo dani kenan domin na kula yaran suna son suyi yawo da hankali na, tunda na tura musu hoton ba reply ba kira, ke har wayar Teema na kira basu dauka ba, dan haka zan shirya mana haduwa ta hanyar Aisha, zansa ta kirasu su zo"
"Amma ba kya ganin da akwai matsala?"
"Uhum ai kin san Aisha tsorona take, dan haka bana tunanin zamu samu matsala. Wai check point din menene wannan?"
"Wallah nima abin ya daure min kai, wannan check point din kusan duk hanyoyin ne aka sa"
"Yanzu haka wani Attajiri ne zai shigo garin, kin san Kaduna mahadace ta manyan yan boko"
"Uhum haka ne"
Cewar Jidda tana jan motar a hankali har suka isa gaban 'yan sanda da suke bincike, daga Jadda har Seema babu wacce ta kawo wani abi a ranta, domin sun san suna da ido a garin duk abinda zaije ya dawo game da harkarsu suna da masu gaya musu. D'an sanda DSP Jamal dake rike da waya a hannunsa ya sunkuyo da kai window yana kallonsu, wani irin shock ne ya kamashi domin fuskar wacce take jikin hoton kan wayarsa ya gani baro baro sai ya wayence yace.
"Yan mata daga ina?"
"Tashar jirgin kasa"
Cewar Seema cike da gadara.
"Ok bude bayan boot mu gani"
Yace yana mai wucewa bayan boot din danya duba, dayan dan sandan ya same shi a gun, nan suka magana kasa kasa, cikin zakuwa dayan yace yes sir. Suka koma jikin windon motar, dayan dan sanda ya bude kofar motar da Seema ke zaune,vdayan ma yaje gefen Jidda ya bude tare da cire key mota, DSP Jamal ya ce.
"U are under arrest"
Yana mai kama hannunta ya kafa mata ankwa. Cikin Seema ya kada tare da faduwar gaba tace cikin tsiea.
"Malam kamar ya? Wannan ai cin mutunci ne me muka yi muku? ni da yanzu na dawo daga tafiya"
Bai saurareta ba ya jawota ta fito daga motan ya tasa keyarta zuwa motarsu, Seema ta soma gaddamar shi, DSP Jamal ya daka mata tsawa ta shiga da sauri jikinta na bari, haka Jidda ma Sargent Aliyu ya taso keyarta itama ta shiga motarsu, Jamal yace Aliyun yaja motar su Jidda shi ka da sauran yan sanda suka ja motarsu sai police station. Hankalin Seema in yayi dubu to ya tashi, bata taba zaton haka ba zuciyarsa ta gama hasko mata su Teema ce.
Akram tun kafin su isa gida wayar dpo Auwal ya shigo wayarsa ya dauka, sun gaisa sannan Auwal ya sanar masa na sun samu nasarar kama Seema yanzu, cike da farin ciki Akram yayi masa godiya kana ya cewa driver ya tsaya a gefen hanya. Driver ya sauka suma escort dinsa suka tsaya, Akram ya kalli Abida.
"fita ki Shiga motar baya su karasa dake gida wani uzuri ya taso min yanzu"
"Kai yaya Akram ka bari mu isa tare mana"
Tace cikin shagwaba.
"Nace ki fita ko"
Yayi maganar cikin daga murya, Abida ta bude ta fita tare da yin gunguni taje ta shiga motar escort din a baya, suka wuce kana driven Akram ya juya akalarsa zuwa police station, Akram ya kira Amir da daya sameshi a can.
Dsp Jamal suna isa aka sakaye su Seema a bayan kanta, Dpo Auwal ya isa har dakin ya kare mata kallo tare da daure fuska.
"Ke ce kike cin zarafin yan mata domin ki samu kudi ko? dama mun jima ana kawo mana case dinki bamu samu nasarar kama ki ba sai a wannan karan. Ki sani cewar kin tabo wuta dan wlh ba za muyi muki da sauki ba, domin muna da kwakkwarar shaida a kanki, kuma zamu mika ki kotu tare da yaranki"
Jidda ta fashe da kuka.
"Yallabai wlh ba ruwa na"
"Yi mana shuru yan iska kawai shaidanun yara"
Cewar Dsp Jamal. Seema ta yi guntun murmushi.
"A shiga kotun se me? Gani nayi sana'a ce nake yi kuma kowa da irin wacce ta amshesa"
Sargent Aliyu ya buga mata kulki a baki nan take ya fashe ya soma zuban jini, ya kara mata a kai nan dai ya rufe ta da duka yayi mata lilis, Dsp da dpo suka yi gaba abinsu suka barshi ya gama dukanta, ita dai Jidda tana gefe ta kame jikinta tana kuka. Seema kam saboda taurin kai ko gezau bata yi ba, fuskar nan bushe ko kwalla, domin a ganinta tana da hanyar da zata fidda kanta, domin tana da manya daga kusoshin kasar sannan uwa uba Mahaifiyarta da take mugun sonta, ta san ko kowa bai tsaya mata ba ita zata shiga ta fita. Sargent Aliyu bayan ya gama ya isa gaban Jidda ya shiga tambayarta sauran abokansu cikin rawar jiki ta shiga lissafo sunayensu tare adreshinsu. Nan ya sanyasu suka rubuta statement kana ya fito rike da bayanin daya dauka a gunsu ya kaiwa dpo.
Da Akram da Amir kusan a tare suka iso, sai suka hadu suka shiga office din dpo, nan ya zayyano musu bayanin komai, lamarin yayi matukar yi musu dadi nan suka sanya hannu tare da amincewa a kai maganar kotu daga bisani suka wuce gida.
Dpo ya kara sanya yaransa suka bazama kamo sauran yaran aikin Seema, sannan ya rubuta takarda ya aika gidansu Seema. Nan take kuma ya sanya aka fito da su Seema aka wuce dasu state C.I.D.
*
Zuwa yamma yan sanda sun samu narar kama yara biyu daga kawayen Seema, suma sun iza keyarsu zuwa state CID an sakaye su. Koda sako isa gurin baffan Seema cike da tsahin hankali ya isa gida ya samu matarsa Halima zaune, ganin fuskarsa kawai ya shaida mata ba lafiya.
"Malam da fatan dai lafiya naganka haka?"
"Halima babu lafiya, wai yan sanda ne suka kama Haseema yanzu haka suna state cid"
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, wannan wace irin masifa ce, wannan yarinya kullun cikin jawo mana masifa take. Me aka ce tayi?"
"Basu fada ba, takardar kawai suka aiko min da shi, wlh na gaji da lamarin yarinyar nan dole ne zan kira uwarta domin kuwa ba zan iya ba tazo ta dauketa kawai, dama tun farko abinda na guda kenan na rabata da ita ashe hakan ba zai sauya zani ba"
"Dama ai tuntuni na gaya maka tunda Seema ba jin maganar kowa take ba, yarinyar da zata fice daga gida tayi kwanaki a waje ba tare da munsan inda take ba, uwarta tuntuni ta gama bata ta, gwara ka maidata tun kafin ta gurbata mana 'ya'yanmu, Allah ya gani kayi na zumunci"
Humm kawai Malam Tijjani ya fada ya shiga lalubo wayarsa a aljihu ya dauko ya duba number mahaifiyar Seema ya danna mata kira harta gama ringing bata dauka ba. Ya kuma sake kira bata dauka ba, Malam yaja tsaki.
"Kinga ita tana can tana barci ni ta barni da bala'i, kullun cikin zullumi"
Yace cike da jin haushi.
"Allah dai ya kyauta malam, amma fa anbaro shiri tun rani, gwara ka yada kwallon mangoro ka huta da kuda"
***
Bangaren Mahaifiyaar Seema tana kwance bisa lallausar gadonta, tana chart ne da wani saurayinta wanda suke zancen haduwa da daddare sai kiran malam Tijjani ya shigo tana kallo bata dauka ba, daga bisani taja tsaki tare da cewa.
"In anga kiran ka bai wuce matsalar kudi ba, ai tunda kace zaka iya da Seema to gaka ga ita nan, ni naji dadin haka ma domin ina cin duniya ta da tsinke"
Sai ta danna number Malam bugu daya ya dauka, suka gaisa kana ya zayyono mata abinda ke faruwa, a zabure Haj. Hauwa ta tashi zaune nan da nan gumi ya cikata.
"Ni kam me Seema take son zama ne? Shikenan Malam ina nan zuwa anjima insha Allahu dan ba zan bari su nakata da duka ba, saboda 'yan state CID dukan mutuwa sukewa mutum. Ko nawa suke bukata zan bayar su sakar min 'ya"
#Rahma ce
#follow
#vote
#comment
#share