ZAKI

13

by @khadeejacandy

Ya dade a gidan Momy zaune gaba daya jikinsa ya gama yin sanyi, yana ta jin kamar akwai laifinsa a cire mata kodar da akai, and if da laifinsa ya akai laifinsa ya shiga ciki bayan shi idan ma ba yanzu ba be tana ganin yarinyar ba, idan yai duba ta wani bangaren yana ganin cewar ba shi da laifin komai, shi dai kawai matarsa yake nemawa lafiya and shi be ce a cire da karfi ba. A masallaci yai sallah magariba sannan na ya dawo cikin gidan, jikin ba kwari kusan sai ya rantse shi be taba jin jikinsa a wannan yanayin, wata kila saboda ba a taba cutar wani a gabansa ba, ko kuma shi din be taba cutar wani da dukiyarsa ko da ikonsa ko karfinsa ba, sai wannan karon, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na fada masa cewar ba shi da laifi. 

Yana shigowa falon Sisters dinsa sika make kyam kamar babu wani abu mai numfashi a falon, ko wacce ta shiga natsuwarta, tsayawa yai kallonsu kamar yadda ya saba idan ya shigo cikin gidan domin lura da yanayinsa da kuma halin da ko wace daga cikin kannen nasa guda hudu suke cikin. 


"Ina Umar?"


Ya tambaya da irin fuskarka nan ta ba wasa. 


"Be dawo ba"


Duka su hudu suka hada baki gurin bashi amsa dan sun sani sarai baya son kyaluwa, Momy zata iya tambayarsu abu su tsaya tunani ko wani sha'anin kamin su ba da amsa amman ban da Aliyu baya daukar wannan shashancin a time din da ya tambaye ka time din zaka ba shi amsa, idan kuma kai kuskure wani abun ya fito daga bakinka kuma kai ne a matsala. Juyawa yai ya shiga dakin Momy sai ya same ta zaune saman carpet tana jan carbi. Guri ya samu kusa da ita a kasan ya zauna yana fiddo wayarsa.


"Dan waje bata Fulani ina ta tunani anya likitan nan Asim zai kyale ta kuwa?"


Dagowa idonsa daga jikinkin screen din wayar yai ya kalleta. 


"Ban gane ba?"


"Ina tunanin kamar ta jefa kanta a matsala ne, baka tunanin zai iya yi mata wani abun da nan gaba ba zata sake shaidarsa ba? Babban likita mai asibitin kansa kamar Asim ba zai dauki wannan matsalar ba, ba zai yarda ta karya masa aiki ba"


Aliyu yai shiru yana nazari. 


"Wannan abu be min dadi ba sam Wallahi, saboda ban jidadi abunda ya faru da yarinyar nan ba, duk kuwa da ban santa ba, amman na san irin zafin da ake akwai ace an cuce ba gashi baka da hali jan hakkinka"


Mikewa yai tsaye yana fitarsa numfashi a hankali ya ce. 


"Momy zan tafi gida, na san yanzu Rahma ta farka"


"To ka gaisheta"


"Za ta ji"


Ya juyo yana tafiyarsa kamar yadda ya saba har ya sauko kasa, ya nufi gurin motarsa yana shiga yai mata key ya dauki hanyar gidansa. Yana tafe yana tunanin abunda ya faru da kuma maganar Momy, he find himself in middle of tausayin Ataa da yarda cewa an zalince, every words of her yake tunawa da yadda take furta su, idan har ba zalince ta ba, ba zata iya daga hannunta ta mari babban mutun kamar Doc Asim ba, yadda ya lura da rashin tsoron da ke cikin idonta a lokacin da idanuwansa suke yawo a fuskarsa, ya tabbatar ko kashe Doc Asim zata iya yi a gaban kowa, and Momy was right ba lallai ne Doc Asim iya kyaleta ba. 


'Allah ya isa'


Haka maganarta ke ta dawo masa sabowa a kunne, ga wa zai isar mata, ga Doc Asim ko ga shi ko kuwa ga su dukansu? Haka yai ta saka tunani kala kala har ya isa gida, yai mamakin ganin Motar surikinsa a wannan lokacin, the first thing that come his mind is ko ciwon Rahma ya tashi ne, amman kuma idan ciwon ta ne ya tashi ai shi zata kira ba Daddynta ba. A bude ya samu kofar falon tun ka ya shiga yake jiyo muryar Alhaji Nasiru Gobir. Da sallama Aliyu ya shiga, surukinsa da wani yayan Rahma suka amsa masa, Rahma kan ko inda yake bata kalla ba. 

Gurin ya samu kusa da ita ya zauna yana kallon Alhaji Nasiru Gobir wanda fuskarsa ke dauke da damuwa.


"Rahma ta fada min abunda ya faru, daman ta fadawa mahaifiyarta tun a waya, wannan wace irin yar iskar yarinya ce marar tarbiya haka?"


Aliyu ya juyo gefensa ya kalli Rahma sai kuma ya sake kallon mahaifinta ya ce. 


"Ba ta fada maka abunda akai wa yarinyar ba?"


"Ko ma mi akai mata ai ba mu muka ce ta siyar da kodarta ba, irin talakawan nan da kake gani Aliyu ba su da komai a ransu sai hassadar nai arziki, idan suka ganka da arziki ji suke kamar su kashe ka su kwashe dukiyar, shiyasa tsakaninmu da talaka aiki kawai mu biyashi, wata banza a banza bata isa ta shigo har cikin gidanki ta fada miki maganar banza ba, watan ma kuma talaka!"


"Daddy har da kai ta ciwa mutunci, wai a gidanka ta raba ka koreta ni da kai duk ba musan darajar talaka ba"


"Zan sa a binciko yarinyar da iyayenta sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne"


Duk abunda ake Aliyu ba ce uffan ba, har Daddy yai musu sallama ya fita, a lokacin ne Rahma ta tashi ta nufi dakinta, shi kan sai da yaji tashin motar surukinsa sannan shima ya mike tsaye ya bi bayan Rahma. Gaban madubi ya same ta zaune tana cire dankunnen da ke kunnenta, kusa da ita yaje yai mata kissing sannan ya zauna gefen gadon yana kallonta.


"Miyasa za ki kira Daddy ki fada masa maganar da bata kai ta kawo ba?"


Da mamaki ta kalleshi 


"Wannan abun ne be kai ya kawo ba? Yarinya karamar yar talakawa kamar wannan ta fada min magana son ranta ka ce be kai ya kawo ba? Aliyu ka san me kake fadi kuwa?"


"Amman ai zalintar ta akai? Yanzu kuma sai ki fadawa Daddy bayan kin san zai iya daukar wani mataki?"


"Amman mu muka zalince ta? Daman can matakin na ke son ya dauka shiyasa na kira shi na fada masa, tun da kai ka kasa komai sai ma rike min hannu da kai dan kar na dake ta"


"Sanadinmu aka zalince ta, kodar mahaifiyarta aka cire Rahma aka dasa miki? Kuma kike tunanin ba zatai wani hargagi na huce haushinta ba?"


Juyo tai gaba daya ta kalleshi da kyau. 


"Kana magana Aliyu kamar ba kai ba? Lafazin da ke fitowa daga bakinta yana karantar da ni cewar ba kai ne ba?"


Hannu ya kai ya kama hanyayenta ya cigaba da mata magana a hankali kamar yadda yake mata dazun. 


"Dear, zan iya juye yi wa mutum komai amman ban da zalinci, an riga an cuci yarinyar nan, kuma kodar nan an dasa miki ita wannan kadai ya isa yasa jin tausayinta waya sani ma ko mahaifiyar ta mutu"


"Tausayi Aliyu? Tausayi? Tausayi fa ka ce? Mi mukai mata da har za mu ji tausayinta? Mu muka zalince ta ne? Akan mi zaka yarda da yarinyar daka soma gani cikin kwana biyu, saman da likitan daya saba yi maka aiki shekara da shekaru? Ban taba ganinka cikin wannan yanayin ba Aliyu, ba ka taba ce min na ji tausayin wani ba, baka taba ce min kana tausayin wani ba, wanin ma talaka irin wannan yar shekara a gidanka"


"Ba tausayinta nake ji ba, ina kallon abunda akai mata ne a matsayin zalinci, and be dace ki saka Daddy a wannan maganar ba, zai iya unkura yi mata wani abu sanadinki, ni fa na yarda da wulakanta kowa na ci mutunci kowa kuma na kyama ci kowa amman ban yarda karfin iko ko dukiya su saka na zalinci wani ba, ba zan iya da hakkin wani a kaina ba"


Kai ta girgiza masa tana murmushi irin mai ciwon nan idonta na cika da hawaye. 


"Ban taba yin wani abu ka ce ban yi daidai ba sai yau, ban taba daga hannu da sunan dukan wani ba ka hana ni sai yau, wani be taba fada min mummunar magana a gabanka ka kyaleshi ba sai yau, na fahimcin inda ka dosa Aliyu, ta wanke fuskarta kaga tana da kyau tana da fari tana da gashi na fahimta..."


Mikewa tai tsaye zata fice daga dakin tana share hawayen da suka zubo mata, sai yai saurin rumgumeta ta bayan ya dora kansa saman wuyanta. 


"Ba kyau ba ne matsalar, ina auna irin halin da na samu kaina ne a lokacin da aka fada min cewar za ki iya rasa ranki idan ba a canja miki koda ba, na ji tsoro sosai Rahma, kullum fargabata kar na rasa ki, na shiga damiwa sosai wanda hakan yasa na fadawa Doc Asim ya samu ko koda ta nawa ce zan siya, amman ban san cewa zalintar wata zai yi ya kawo min ba, ni kenan da nake tsoron rasa mata ina ga ita da take tsoro rasa mahaifiya tana da daraja ga yayanta Rahma ko da kuwa talaka ce"


"Babu ruwanmu da rayuwar wasu, abunda muke so shi muka samu, whither ya zalince ko mu muka zalince ba matsala ba ce, tun da mun samu abunda mu ke bukata, Aliyu bana son na sake jin maganar yarinyar pls"


Juyowa yai da ita ta yadda zata fuskance shi irin fuskartar da zata famince ko wace kalma da zata fito daga bakinshi. 


"No ba haka ya dace ba, idan har ba mu bata hakurin zalincin da akai mata ba, be kamata ba, be kamata mu kara mata da wani abun ba, Daddy zai iya yi mata wani abu, and maybe Doc Asim ma ba zai kyaleta ba"


Kallonsa take tana ta kokarin fahimtarsa amman sai ta kasa, zuciyarta nata raya mata cewar Aliyu ya fara son yarinyar nan ne, hawaye ne suka shiga nata zirya ta fasa cewa komai, ganin hakan yasa shi saka bakinsa cikin nata ya tsotse bakinta tas sannan ya matso da ita baya suka zauna bakin gado ya rumgume ta. 


ATAA POV. 


Tunda aka tsayar da maganar zuwa aikina Abuja na fara koyon wanka akai akai kamar yadda Maman Salma ta fda min cewar Abuja ba a kazanta, baa gulma ba a wasa duk abunda ya kai mutum shi yake yi, wani lokaci a rana sai nai wanka biyu ma, wankin baki kuwa ba a magana, akai akai na ke saka gawayi ina wanke bakina gudun kar na je ace yana wari, yadda na ke ta jin labarin Abuja a gurin Maman Salma sai ji duk na gagara na je kamar wacce zata je wani guri gurin jindadi ba aikatau ba. 

Sai duk wannan zumudin da murnar da nake idan tuna cewar zan tafi na bar Nana sai hankalina ya tashi na ji babu dadi, duk kuwa da nasan cewar ina bukatar aikin, kuma idan har na daure nai na san zan samu kudi kuma, kudin za su mana amfani sosai. Sai kullum Nana cikin nuna bata son tafiyata take, tana ta ganin kamar idan nai nisa da ita zan dawo na tarar ta rasu ne. 


Ana saura kwana biyu mu tafi Abuja kamar yadda Maman Salma ta fada mana, na shirya ni da Farida na raka ta bayan unguwarmu gurin kitso, ba mu dawo da wuri ba, kasancewar mun tararda mutun hudu suna jiran kitson, ga shi idan muka hadu da Islam mai kitso abun ba dama gurin fira da dariya, muna hanya ana kiran sallah la'asar muna tafe muna fira har muka iso gidan sai dai yadda na tararda gidan wan wulgar mana da kayan dakin Nana ya sa ka gabana faduwa, a tunanina ko mahaifiyar Farida ce tai mana haka domin bata son zaman mu a idan, yana daya daga cikin abun ya saka na ke son na samo kudi ko dan mu tashi mu bar mata gidan.


"Muna zamanmu Malam zai janyo mana masifa, ai bari ya dawo sai ya san matakin da zai dauka tun wuri dan ni ba zan yarda da zaman mutanen nan a cikin gidan nan ba, wannan iskanci har ina?"


Irin kalaman zagi da na ji suna fitowa daga bakinta ya saka na fahimci ba daga ita har ba ne. Da sauri na nufi dakin da Nana take ciki sai na sameta ta zaune tana kuka.


"Lafiya Nana miya faru?"


"Wasu mutane ne suka shigo cikin gidan nan suna nemanki, aka nuna musu ni saka ce na fada miki karki sake zuwa ki fadawa Rahma wata magana marar dadi, idan kika sake sai sun wulakanta ki, wacece Rahma kuma?"


Ta karasa tana tambaya ta. 


"Matar da ta koreni aiki ce"


"Fada kuka yi?"


"Kawai dai mu samu dan sabani ne, ta ce talaka ni kuma na fada mata bakar magana"


"Ataa dan Allah ki kama kanki, kin ga dai ke ba yar kowa ba ce, kar ki janyo mana wata matsalar muna neman abunda za mu ci"


"In-Sha-Allah ba zan sake ba, wacan din ma kuskure aka samu"


"Ina son ki min alkawari idan kin je Abujar nan, duk abunda za a miki za ki yi hakuri ki hade, ba za ki saka shi a ranki ba"


"Na miki alkwari Nana"


Na fada ina sakar mata murmushi. Sannan na tashi naje na waje na dauko duka kayanmu tare da Farida na dawo da su dakinmu, ni da Farida muke ta zagin masu kudi da irin wulakancinsu, Mahaifiyarta kuma nata shigar musu wai idan ban musu wani abun ba ai ba za su zo har cikin gida su mana haka ba. Ni dai ban ce da ita komai ba, ni da Nana muna ta jiran tsammanin idan mahaifin Farida ya dawo ya kore mu ya ce mu bar masa gida, amman be kore mu, kirana kawai yai ya tambayi ba'asi sannan yai min jan kunne akan gaba kar na yarda irin hakan ta kara faruwa, na jidadin yadda yai mana daman sanin darajar talaka sai talaka dan'uwansa, ko da yake wasu talakawan ma basu san darajar talakan dan'uwansu ba kamar Maman Farida. 

A daren taliya na dafa mana, muka ci ni da Nana sai da muka koshi nas sannan muka kwanta bayan mun kashe kyandir din dake haska mana dakin duk dare, yau ma kamar yadda na sabawa kaima da tashi da wuri na tashi sai dai bayan na yi sallah asuba na koma na kwanta tun da bana aikin komai kuma ina da bukatar bachi. Ko da na farka ranata fito ko'ina kusan duk wani abun da ake saidawa na kari kama daga koko ko waina sun kare a lokacin sai dai na yamma idan anyi, dan haka na dimama sauran taliyar da muka raga ni da Nana jiya mu ka sake cinta da safe. Sannan na shiga nai wanka na fito na shirya cikin yadinmu na gado na rufe kaina kamar yadda muka saba yi idan zamu je bara, wannan karon har da gashin kaina na saki ya sauko har gurin mazaunaina, sannan na dauki dubu daya a cikin yan kudi da suka rage mana dan na siyo takalmin zuwa Abuja domin takalmina sun cinye daga kasa. 


"Ki siyo mana tuwon ruwa daga can (bula) da kuli da zogale sai mu yi kwado"


"To Nana sai na dawo"


Na amsa ina saka kafata na bar gidan, misalin sha biyu na rana na kama hanyar kasuwar yar murna, domin bana son zuwa tsohuwar kasuwa ko sabowa saboda cinkoson mutane, alhalin ba wani abun kirki zan siya ba, a kafa na tafi duk kuwa da irin nisan da ake akwai amman ina jin kamar hasara ne na biya kudin achaba bayan muma muna da bukatarsu, kara dai idan zan dawo sai na hawo achaba ko Napep na dawo shi ma idan na rago canji. 


Abun ka da wanda ya so tafiyar kafa, kuma gwanim tafiyar nan da nan na isa kasuwar murna, wata karamar kasuwa ce wance za a iya kiranta da unguwa ma domin mutane da yawa suna da gidaje a cikin kasuwar ba kamar sauran kasuwani ba. Daga bakim titi ma tsaya na siye takami na roba sai da natsaya na gwada wandanda suke yi ma kafata sannan na biya kudin dari shida da hansi, murna ta cika min zuciya domim rabon da na saka talkami mai tsada kamar haka har na manta duk talkamin da zaka gani a kafata ko dai an bani ne ko kuwa wasu sun gaji da amfani da su ne sun jefar na tsinta na gyara ina sakawa, kusan ma sai na ce ko a lokacin sallah da ake siyayya ni ba asiya min sabon kaya ba balle wani sabon takalmi. Bayan na bashi kudin na shiga cikin kasuwar na siyo abunda Inna ta aike ni sannan na fito na tsaya titi jikin wata mota ina jiran wasu motocin su gama wuce saina tsallaka na koma ta dayan bangare na hau Napep da naira hansin din da suka rage min. Ina kokarin tsallakawa wata motar na kokarin parking kusa da wance na ke tsaye sai ji nai motar ta ture ni da karfi har sai da na fadi zaune. Lambar motar kawai na kalla na gane cewar mutumenan mijin matar nan, wani abun isa yaga ya kade mutum amman ba zai iya fitowa ya duba waya kade ba, waya sani ko da gangan ya kade ni. Unkura nai na tashi na nufi inda yake na daki gilashin motar da karfi sai ya sauke gilashin yana kallona da cat eyes dinsa.


"Me na maka za ka kade ni? So kake ka kashe ni? Wulakancin da ka tura aka mana a gida be wadatar da kai ba, sai ka kade ni? Kai wa wane irin mutum ne? Kana son matar ka kasa cire kodarka ka bata sai da kasa a zalince mu aka cire aka dasa mata, kuma yanzu dan tsabar zalinci na yi magana shine zaka aiko har gida a ci mana mutunci a wulakanta mu? Hakan bw maka ba yanzu kuma ka ganni zaka nemi wulakanta ni?"


"Ba a nuna ni da yatsa"


Shine kawai abunda ya fada yana hakimce cikin motarsa yana kallona ido cikin ido kamar ba da shi na ke masifar ba, ba dan cewar na ji maganar ba da sai na rantse ba daga bakinsa ta fito ba. Ni sai a yanzu na lura da cewar na nuna shi da yatsa din ma, a maimakon daya sai na saka yatsuna biyu na nuna shi da su. 


"Saboda kana wa? Mai arziki? Mai arzikin da ba zai iya zuwa gida da ko naira ba? Mai arzikin da bai iya komai da duniyarsa ba sai zalinci? An nuna ka ka yanka ma idan ka iya, bana tsoronka kai da muguwar matarka da mugun likitan nan, babu tsoronku babu kaunarku ko kadan a zuciyata"


Ina gama fadar hakan na tofa masa yawu a motarsa na koma inda nake tsaye, na tsallaka titi ina ganinsa yana ta kallona har na tari achaba na na hau, shi da mutanen da suka fahimci fadanmu. Sam babu tsoronsu yanzu a zuciyarta ko kadan, sai ma tsanarsu da nai har na isa gida zuciyata zafi take saboda bacin rai. Sai dai ban fadawa Nana ba, kuma ban nuna mata cewar wani abun ya faru ba, ina shiga na shirya mana tuwon ruwan na gyara zogale na kwada mana muka ci, sannan na cigaba da shirye shiyena a yar ghana must go dita da na siyo sabowa. 

Bayan sallah isha'i muka kwanta ni da Nana, sai da na tabbatar ta yi bachi sannan na taso na baro mata dakin na zauna a tsakar gida cikin farin wata ina ta kallo taurari kamar mai kirgasu, tunani a zuciyata lallai ba dan talauci ba babu abunda zai nisanta ni da mahaifiyata. Kukana nai ni kadai babu mai bani hakuri har nai na gama sannan na wanke fuskata na koma dakin na kwanta amman bachi ya kasa daukata, sai na juyo da fuskata kusa da ta Nana ina ta kallonta kamar ance idan na tafi ba zan dawo ba. 


Tun kiran sallah fari na farka, domin maman salma ta fada cewar da na yi sallah asuba na zo mu kama hanya, ina sallah Nana na kuka har nai na gama, ina cikin yin addu'a aka buga kofar gidansu Farida na san ba zai wuce Maman Salma ba, a nan ni ma na fashe da kuka na kama hannayen Nana na rike ina ta shafasu a fuskata, Farida ta shigo dakin ta dafa ni tana ba ni hakuri. Sai na juyo na kalleta. 


"Ga Amanar Nana nan na baki, ki kula min da ita iya gwargwadon ikonki, ki yi mana gwargwadon abunda za ki iya, kin sani Farida ba dan talauci ba babu abunda zai nisanta ni da ita, tana da bukatata amman dole na tafi na nemo kudi. Dan Allah ki kula min da ita"


"Na miki alkwari Ataa zan kula da Nana In-Sha-Allah"


Na rumgume ta ina kuka kamar yadda ita ma take, sai kuma na sake ta ka saka hannayena na kama kafar Nana ina Shafawa. 


"Na yafe miki Ataa na yafe miki duk abunda ke tsakanina da ke, tashi kije Allah ya tsare ya kai ku lafiya"


"Amin"


Na fada sannan na mike tsaye ina kuka sosai na fito nai ma mamar Farida sallama da mahaifinta na karasa gurin Maman Salma sai wacce ke tsaye tana jirana, sau biyu ina waigowa ina kallon kofar dakin da Nana take, ina ta jin kamar kar na tafi na barta amman tafiyar ta zame min dole. Gidan Maman salma muka koma ta dauki kayanta a nan na gane cewar ba ni kadai zata kai ba, domin tare da yan mata shida muka kama hanyar Abuja bayan direba ya zo har gida ya same mu, da alama direbanta ne sun saba da juna ita da shi. 

Tafiya mukai ta yi, tun ina hawayen rabuwa da Nana har na soma wayewa, tafiyar ta fara ci min rai, a zariya muka tsaya muka karya sannan muka cigaba da tafiya mai isa, a takaice ba mu isa Abuja ba sai cikin dare... 


ALIYU POV. 


Yana rike da jarida a hannunsa amman ya kasa karanta komai, abunda Ataa ya fada masa jiya kawai yake tunani, wani be taba karfin halin fada masa magana mai zafi kamar ta jiya da Ataa ta fada masa ba, beside shi be san ya tura kowa gidansu ba, be ma san inda gidansu yake ba, and kadewar da yai mata ma bada gangan yai ba. Sai dai ko ba komai yadda take ta karfi hali ta burge shi, and yana da right din yi mata excuse tun da Azzalumi take ganinsa, kuma zalintarta akai? But waya tura wasu gidansu? Ko Doc Asim ne kamar yadda Momy take masa hasashen cewar zai iya cutar da ita? Ko kuwa mahaifin Rahma ne wanda shi ma yasan ba a zai kyale ba? Ko dai wanene he need to know ta dalilinsaba zai yarda sake zalintar kowa ba. Zaman da Rahma yai kusa da shi yasa shi dagowa daga dogon tunanin da yake ya kalleta yana kai hannu ya shafa gefen kafadarta. 


"Dear na gaji da garin nan, bana son mu sake neman wata mai aikin wani abun ya faru, kuma gidan nan zamansa da datti ni bana so kyankyami na ke ji"


Be ce mata komai ba, daman can ta san ba zai ce ba. 


"Ni mu koma Abuja kawai tun a can komai yi mana ake"


Ya aje jaridar hannunsa ya janyota jikinsa. 


"Ba yanzu ba"


Da mamaki ta daga kai ta kalleshi. 


"Saboda me?"


Shiru yai for like five minutes before ya bude baki ya ce. 


"We need to help her"


"Who?"


"Yarinyar da aka cirewa mahaifiyarta koda, zata iya shiga wani hadarin saboda mu, be kamata mahaifiyar yarinyar nan a jikinki ba, tana kallon mu a matsayin azzalumai, kuma ta rayu a cikin kallon zalintar za mu sake yi wani zai iya fakewa da mu ya zalince a again"


Wani irin zaranannen kallo tai masa kamar ya ce mata za a cire kodar jikinta ne a mayarwa mahaifiyar Ataa....