ƘADDARARREN AL'AMARI

9

by @rahmakabir13

*ƘADDARARREN AL'AMARI*


© *Rahma Kabir*

     Mrs MG


Wattpad @Rahmakabir.


09


"Hmmm aikin kenan, dama ke ce kika bata ta, to gwara kizo ki tattarata ki kwashe ta dan bazan iya ba, Allah ya gani nayi na zumunci, yau da Turaki yana raye duk haka ba zai faruwa ba domin nasan d'an uwana mutumin kirki ne"


Cewar Malam tare da kashe wayarsa cike da takaici. Haj. Hauwa taja tsakai.


"Aikin banza, dama uban waye yace ka dauketa"


Sai ta mike ta shige toilet danta kimtsa ta kamo hanyar Kaduna.


Asalin Haj. Hauwa yar jihar nasarawa ce sun hadu da Abba Turaki a wani taro na yan siyasa, abu kamar wasa suka kulla soyayya. Hauwa ta kasance mace mai shige shige tun tana budurwa, burinta ta samu kudi kota halin kaka, shiyasa duk lokacin da ake taron yan siyasa takan je ita da wata kawarta wacce ta taimaka wajen budewa Hauwa ido, iyayenta sun rasu tana zaune wajen kakarta, duk da haka bawai ta rasa gata bane domin kakarta macece mai kokarin niman na kanta saboda ta faranta ran jikarta tilo d'aya. 


Hauwa da farko ta amince da soyauyar Abba ne saboda taganshi da kudi sai da ga baya son shi ya kamata taji ba zata iya rabuwa da shi ba shiyasa ta amince da aurensa, sai ta watsar da rayuwar bariki data so sanya rayuwarta akai. Sunyi aure cike da so da kauna, Allah bai basu haihuwa ba har tsawon shekara goma, Abba Turaki yanata samun budi, dangin Abba suka matsa dole sai ya kara aure hakan ya tada hankalin Hauwa sosai, domin bata burin wata mace ta rabe su da sunan Matar Abba saboda daularsa suke ciki, shiyasa ta mike tsaye kullun suna zarya asibiti Wanda aka tabbatar infection ne yayi mata mugun kamu har yaso taba mahaifarta, likita ya daura ta akan magani tana sha, a haka dai har Allah ya bata cikin Haseema a wahalce har ta samu ta haihu, sai da ta samu matsala wanda ya haddasa aka cire mata mahaifa. Tun daga nan zancen kara auren Abba ya kare tun dama rashin haihuwar Hauwa yasa danginsa matsawa yayi.


Seema taga gata sosai a gurin iyayenta musamman Mahaifiyata da take ganin ita ce kadai rabonta na duniya. Allah ya yiwa Abba Turaki rasuwa tun Seema tana da shekara goma sha bakwai, mahaifiyata ta cigaba da rikonta sai dai matsalar da aka samu Seema duk abin da take so ko da abu ne mara kyau sai tayi babu mai kwaba mata, bata damu da islamiya tun tasowarta ta aje shi ta kama boko, ganin haka ne yasa Mal. Tijjani wan Abba yazo ya dauketa ya maudo da ita gidansa ganin Hauwa tana son bata tarbiyyarta. Duk da haka lamarin bai sauya zani ba domin Hauwa ta budewa Seema account tana tura mata kudi masu yawa tana kashewa a banza, a haka harta kammala secondary ta shiga university kasu, a wannan lokacin ta tada hankalin Malam akan dole a barta ta zauna hostel din makaranta, Malam ya hana ya nuna mata bata isa ba, ya kira Hauwa ya shaida mata, sai ta kira Seema ta lallasheta tare da yi mata alkawarin siyan mata gida a nan Kaduna ba tare da sanin Malam ba.


Wannan shine dalilin rashin kwanan Seema a gidan Malam, sai dai tayi karya tace karatu ne ya kaisu dare shi ne ta kwana a dakin course mate dinta, bacin a gidan da Mamanta ta siya mata take kwana tare da sheke ayarta da kawayenta, babu mai kwabawa, Kuma anan kasu ta hadu da Aisha suka kulla abota, kasantuwar tasu tazo daya saboda imata Aishan yarinya me son rayuwa. Seema ta fara harkar kasuwancinta daga wasa sai lamarin ya zama gaske, wata rana sunje wani party da dare sai wani dan majalisa ya dauki kawarta Jidda suka kwana hotel, Jidda tayi musu photo a wayarta babu kaya jikinsu, irin dai suna enjoying moment din, washe gari ya biyata suka rabu ta nufi gidan Seema suka barke da hirar Party, ita Kuma Jidda saita shiga basu labarin irin yadda suka kwashi soyayya da dan majalisa har ta nuna musu hotonsu data dauka, Seema tana gani wani tunani ya fado mata sai ta tura hoton a wayarta ba tare da sanin Jidda ba. Bayan kwana biyu ta nimo number dan majalisan ta tura masa hoton a WhatsApp ta fadi makudan kudi take so in ya tura mata zata rufa masa asiri, hankalinsa tashe ya tura mata miliyan uku a account dinta, sai bayan sun gama take sanar da Jidda abinda ta aikata, Jidda tayi mamaki sosai domin dan majalisan bai sanar da ita ba, shima kuma zuciyarsa ta gama gaya masa Jidda ce ta yi masa haka shiyasa bai nima number dinta ba. To tunda wannan lokacin Seema ta samu sana'a sai dai bata yiwa manya sai matasa yan mata yayan masu kudi, a ganinta wannan zaifi kawo mata kudi.


***** 


Da yamma


Safnah basu tashi daga gurin aiki ba sai gabda magrib, kasantuwar ranar lahadi suna samun jama'a sosai. Haj. Uwale tace dole sai ta bita gida ta gyara mata daki domin yau ta fito bata yi wa dakin komai ba, ba a son ran Safnah suka tafi ba duk da tasan ta ajewa kannenta abinci kafin ta fito Amma bata kaunar yin dare a unguwar rimi saboda tsoron abinda ya faru da ita rannan dan bata manta ba. Suna isa ta soma shara kafin nan ta yi mopping ta wanke bayi, har kusan sallar isha'i bata kammala ba sai sauri take ta gama ta samu ta wuce gida.


Haj. Uwale tana zaune tsakar gida bisa babbar tabarma yan mata sun kewayeta kamar yadda suka saba sai hira suke zubawa. Sabira ce ta rugo cikin gidan da gudu daya daga cikin yan mata gidan tana haki ta tsaya gabansu Hajiya.


"Uwar manya yau kinyi babbar bakuwa domin Haj. Najwa ta faso tana kofar gida yanzu motarsu ta tsaya"


Haj. Uwale ta mike a zabure tana rera guda cike da farin ciki domin tasan ganin Najwa, watan samun kudinta ne ya tsaya. Nan take ta hura usir da yake makale da key din dakinta, wanda duk lokacin da Babban abu zai faru takan kira mutanan gidan dashi suna ji zasu hallara su fara jera layi, dama tun yamma ko wacce zata tsala wanka wasu su sanya kananun kaya wasu kuma atamfofi ko leshi sannan su sanya turare ko ina suka gilma kamshi ke tashi, kadan ne daga ciki suke yin sallar magrib da isha'i sai su kara gyara fuska, wanda kuma kururuwar shaidan yayi tasiri akansu bama sayin sallar.


Hajiya tana hura usir din gaba daya yan matan suka soma fitowa daga daki, wa'inda ke bisa tabarman ma duk suka mike suka shiga jera layi sun kai kimananin su goma sha shida, wanda wasu sun yi tafiya wasu kuma sun fice da alhazawansu. Safna tana ciki tanata hidimar ta bata san meke faruwa ba saboda hayaniyarsu bata gane komai sannan ma ba wannan ne a gabanta ba domin har ta fara sabawa da ganin rayuwar gidan, kasantuwar tana kyamar haka yasa bata damuwa da lamarinsu ita dai burinta kullun Allah ya kawo mata mafita ta samu wani aikin ta bar wannan kazamin gida. 


Haj. Najwa ta shigo cike da kasaita sanye take da wando jins pencil blue wanda ya matseta sannan sai ta sanya vest dark pink babu ko brazia a jikinta, ana ganin tsinin kan dukiyar fulaninta daga cikin rigar kasantuwar a tsaitsaye suke, kanta yasha kitson attachment manya all back, jelar gashin sun zuba a bayanta, siririya ce tana da matsakaicin tsawo sannan akwai hips sosai, ba zata wuce shekara ashirin da biyar ba a duniya. sai wani irin sihirtaccen kamshi ke tashi a jikinta. Haka ta shigo gidan tare da wasu yan mata biyu suna biye da ita a baya Billy da Ma'u, daya ta sanya domuwar riga dayan kuma riga da siket na leshi, suke rike da jakar Najwa da kuma wayarta. Najwa ta soma bin layin yan matan tana kallonsu daya bayan daya tun daga sama har kasa, wata ma saita sanyata ta juya taga mazaunenta harta matsa kota matsa dukiyar fulanin, a haka ta gama duba yan matan ta isa gaban haj. Uwale ta tsaya tare da kama hannunta ta baya. Hajiya ta shiga yi mata kirari tana murmusawa cike da isa ta na kada kai kamar kadangare.


"Ina godiya Uwar manya. Ina Bilki yar fara?"


Cewar Najwa a hankali cikin natsuwa, hajiya ta bata amsa da cewar.


"Ranki ya dade tayi tafiya zuwa binnin tarayya tare da wani Alhajinta"


"Dama tana Hulda da maza?"


"Eh kin san sana'ar biyu ce in hagu taki sai a goma dama"


"Hmmm kice gaba daya yaran gidan haka suke"


"Eh to kusan hakan ne tunda kinsan bariki komai ma tab'awa ake yi"


"Da kyau. Amma ki sani gaskiya ni bana son wanda suke mu'amala da maza, dan haka zan baki aiki ki samo min matashiyar yarinya wacce take sabuwa a wannan Harkan, domin yan matan gidan naki babu wacce tayi min, zan baki million daya in har kika yi min kyakkyawar kamu"


Haj. Uwale ta shiga rera guda cike da tsantsar farin ciki ji take kamar ta samo mata ta bata kudinta, ta shiga yi mata godiya kamar zata kwanta mata. Abin takaici Haj. Uwale ta kusa yin jika da Najwa amma saboda rudin duniya bata hango ma kanta haka, sai ma idonta daya rufe take ganin yanzu ta soma cin duniyarta da tsinke. Najwa ko babu abinda take yi sai murmushi, suna cikin wannan yanayi ne sai ga Safna ta fito sanye da hijab zata wuce gida, ta karaso gaban hajiya ba tare da ta tsaya fahimta abinda ke faruwa ba ta ce.


"Hajiya zan wuce na gama komai"


"To Safna kije waje ki tambayi Ubale mai mashin shi ne zai kaiki gida" 


"Nagode Allah ya kara girma"


Tace cike da murna dama tana ta tunanin yadda zata samu abin hawa. Saita rabe Najwa ta wuce ita kuma Najwan ta bita da mayen kallo tun daga fuskarta har bayanta data tunkari kofar fita. Cikin izza tace


*Hajiya a kira ta" 


Tayi maganar tana nuni da hannun akan Safna ta ke gabda ficewa, cikin sauri Hajiya ta kira Safna ta juyo da sauri cikin sassarfa tazo ta tsaya gabanta.


"Yauwa mage kiranki nan" 


Tayi maganar tana nuna Najwa. Safna ta juya tana kallon Najwan sai da taji gabanta ya fadi domin shigar dake jikinta yasata jin wani iri tare da nima Addua shiriyar Allah a zuciyarta, ita kuma Najwa ta shiga kallonta tun daga sama har kasa saita maida dubanta ga Hajiya.


"Wannan tayi min dari bisa dari, sai dai zan baki kudi da zaki gyara min ita na tsayin kwana biyu zuwa uku, zanzo na dauketa"


"An gama Hajjaju mutan Abuja"


Najwa ta mika hannunta baya alamar nata bukatar jakarta, da Sauri Billy ta mika mata. Ta ciro kudi rafa guda biyu yan dari biyar biyar kimanin dubu dari ta mikawa Hajiya ta amsa hannunta yana rawa.


"Wancen alkawarin zaki ji alert ta account dinki, sai kuma in na dawo daukar ajiyata"


Hajiya ta soma zuba godiya tana yiwa Najwa kirari, ita dai Safna tana kallon ikon Allah bata fahimci komai ba. Najwa ta juya ita da mutanenta suka wuce, Hajiya ta kalli Safna.


"Gobe in Allah ya kaimu kizo da wuri zamu je kasuwa kin samu sauyin aiki, zaki koma gidan wannan Matar da aiki. Da fatan ba zaki yi min gardama ba"


Safna ta murmusa ta yiwa hajiyar godiya kana ta wuce. Tayi murna da hakan koba komai zata bar zuwa wannan kazamin gidan, tayi kuma alkawari duk wahalar aikin zata yi shi in dai zata damu rufin asirinta.


Tana fita Billy ta kwala mata kira dake tsaye jikin mota, Safna ta isa gurin ta.


"Yauwa shiga mu rage miki hanya ko"


Tace tana yarfe hannu tare da jefa mata wani shu'umin kallo, Safna bata yi musu ba tace to, Billy ta zauna a mazaunin baya ita da Ma'u sai ta umarci Safna ta shiga gaba kusa da Najwa da yake ita ke tuki, ba musu ta shiga ta zauna suka wuce.


"Inane unguwarku?"


Cewar najwa.


"Badarawa layin fulani road"


"Ok sai ki rika yi min kwatance dan ban san unguwar ba"


Safna tace to ta shiga kwaranta mata a haka har suka isa cikin layin zuwa kofar gidansu Safna, Najwa tayi parking Safna ta fito tana yi mata godiya, Najwa sai ta fito ita ma ta ce.


"Muje na gaisa da mutanen gidan" 


Ba musu Safna tayi musu jagora suka shiga, ganin ba wuta Najwa ta kalleta.


"Ya naga gidan naku da duhu? kuma ko ina da hasken wutar lantarki"


"Da jimawa aka yanke mana sai dai muyi amfani da kendir" 


"Ok ina iyayenki naji gidan shuru?" 


"Sun rasu daga ni sai kannena biyu muke rayuwa a gidan"


"Ayya sorry ko, karki damu da kin fara aiki dani komai zai yi muku dai dai, zaki samu alkhairi sosai a guna in dai kin yi min biyayya"


Safna ta ce to, lokacin su Muslim suka fita daga daki suna bin su da kallo da yake akwai hasken farin wata, a tsorace suka gaishe da su Najwa suka amsa cikin sakin fuska. Najwa ta daga wayenta ta kira wani babban ma'aikacin NEPA ya dauka suka gaisa kana ta koro masa bayani akan tana so a zo a mai da wutan su Safna ko nawa ne zata biya sannan kar a kara yankr musu wuta, za kuma ta tura masa da tukuicin kudi mai tsoka. Cike da murna ya amsa mata sannan ya tambayi layin da sunan gidan.


Najwa ta cewa Safna.


"Ya sunan gidanku"


"Gidan marayu uku duk wanda aka tambaya sai nuna masa"


Sai Najwa ta ba shi amsa kana suka yi sallama. Ta ciro dubu goma ta mikawa su Muneera dasu sha sweet sai suka ki amsa, saima kallon Safna da suka yi in ta basu umarni. Safna ta ce.


"Hajiya ki barshi mun gode" 


"Ba ke na bawa ba, kannena na bawa sai dai ko in sun raina saina kara musu"


"A'a sunyi yawa ne ba rainawa suka yi ba"


Cewar Safna sai tasa Muneera ta amsa kudin suna godiya, sai su Najwa suka wuce su Muslim suna binsu da kallo.


Rahma ce

#follow

#vote

#comnent

#share