10
*ƘADDARARREN AL'AMARI*
© *Rahma Kabir*
Mrs MG
Wattpad @Rahmakabir.
10
Bayan sun zauna a bisa tabarka a nan tsakar gidan, Muslim ya kalli Safna cike da kulawa.
"Anty ina kika hadu da wa'innan Matan?"
"Sun zo wajen hajiyar da nakewa aiki ne shi suka rage min hanya."
"Amma anty gaskiya ba mutanan kirki bane ji kayan jikin wannan mara dan kwalin, ni basu kwanta min ba"
"Kai muslim meyasa daga ganin su zaka yanke musu hukunci? babu kyau mummunar zato, bana son haka kuma ai musulmai ne, daga yau bama ga su ba karka kara kulla haka a ranka babu kyau"
"Anty Kiyi hakuri insha Allahu bazan sake ba, yanzu ya zamuyi da kudin nan kinga ran nan kawu yayi fada sosai akan abinda muka yi da kudin da aka baki"
"Karka damu zan aje kudin duk ran da yazo zan nanu masa sai mu nima shawarar yadda za muyi dasu, nasan zai fahmce ni, sannan ma yanzu muna da sauran kayan abinci ai"
"Hakane Allah ya mana jagora"
Duk suka amsa da Ameen.
***** *****
Washe gari
Haka safna ta shirya da wuri ta tafi aiki, tana isa ta samu suma basu dade da bude shago ba, ta gaishe da hajiyar ta amsa fuska sake cike da fara'a, tana kara jin kausar Safna a ranta, lallai ta kara tabbatar da cewa ita haske ce a rayuwarta.
"Safna ai yau daga ni har ke bamu ga ta zama ba, yanzun nan zamu tafi kasuwa dan yi miki siyayya, kisan Haj. Najwa bata son kazanta dole zaina siya miki kaya masu kyau da tsada, ita duk haka yakewa ma'aikatanta akwai kirki, in dai kika kwantar da kai zaki samu alkhairai sosai a gunta"
Murmushi kawai safna tayi dan ko a jiya ma ta tabbatar da kyautar Najwan data basu dubu goma, dan haka babu musu suka yankaya karuwar central.
Kamar yadda Najwa ta sanya NEPA su maida wutarsu Safna haka kuwa aka yi, dan karfe tara na safe da mintuna suka dira a kofar gidan, basu tsaya yin sallama ba suka soma kiciniyar hada guntuwar wayar da tayi saura wacce da jimawa duka yanketa suka jona da wata mai kyau suka dane falwaya suka mayar musu da wuta, nan take hasken kwan dakinsu dana tsakar gida ya kawo, Muneera ta tashi sai tsalle take tana fadan yeee an kawo wuta, shi kam Muslim da gudu yayi kofar gidan dan ya ga nepan, yana fita ya tsaya yana kallonsu suna kokarin sanya lada a bayan mota, bai yi wani mamaki ba dan dama jiyan anyi komai a gabansu, sai dai shi tun jiya ya kasa samun natsuwa da haka hankalinsa yaki kwanciya dasu Najwa, haka ya dawo gida jiki a sabule ya shiga jero Addu'an Allah yasa ba yan yankan kai bane suke son cutar da Antynsu.
Mutanan unguwa kuwa ba karamin mamaki suka sha ba ganin NEPA sunzo takanas dansu mayar da wutan su Safna, nan take suka fara gasgata rade radin zargin da akewa Safna akan ta fara bin maza, Wanda jiya ma akan idan wasu ta sauka a motarsu Najwa, nan fa hira ta barke a unguwa, Matan dake cikin gida suma labari ya ishe su, kowa dai yana fadar albarkacin bakinsa, wasu ma cewa suke maraici babu abinda baisawa, sannan su da aka bar musu tabiyyar kansu a hannunsu babu mai kwabawa ai dole hakan ya faru, sun gama kokarin safnar da tuntuni bata balle da iskancin ba sai yanzu. Maganganu dai marasa tushe, ranar watan maganar su Safna ya kama a unguwar, d'ai d'ai kun mutane ne masu fadan abin kirki akansu da yabon halinta.
**** ****
Haj. Hauwa tun jiya ta zo Kaduna ta sauka a shahara hotel dake cikin malali, dan ta yarda da tsaftarsu duk zuwa a nan take sauka. Cikin sauri ta kammala shirinta, sanye take cikin doguwar rigar leshi dinkin buba saita tane kanta da gyale ta sanya farin tabarau fuskar nan sai keshi take ta dauki hand back dinta ta fito rike da key din dakin, ta samu drivern daya tukota tunda Abuja tace yaje ya huta ta amsa key motar tayi gaba abinta, unguwar Abakwa ra nufa gidan Malam, bata dauki dogon lokaci ba ta isa tare da yin parking ta sauko, sai wani cuna hanci take saboda warin kwatan dake kofar gida daya noshi hancinta, haka dai ta daure ta shiga, Halima tana ganinta ta washe baki tana yi mata lale, fuska ba yabo ba fallasa ta amsa tare da tambayar ko malam na nan.
"Ai kya bari ki zauna ki sharuwa ko"
"Ba zama ya kawo ni ba nazo ne kan zancen 'yata"
"To matsiyaciya ai dama sai kin nuna halinki, to gani na fito muje daga nan sai na danka miki 'yarki a hannu mu rabu"
Cewar malam yana fitowa daga makewayi ya aje buta, bata tanka masa ba sai taja guntun tsaki domin in da Sabo ta saba da cin zarafin da malam yake mata, sai dai abin mamaki bata iya tanka masa saboda mugun kwarjini yake mata, sum sum ta fita daga gidan tana cika tana bacewa, shima yafi bayanta yanata sababi, mota ta shiga shima ya zauna gefen ta suka wuce state cid.
Suna isa suka bukaci magana da dpo da case din su Seema ke hannunsa, sunyi sa'an samunsa domin shima yazo kan batun shigar da maganar kotu dan Akram ya matsa akan hakan, suka shiga wani wadataccen office duk suka zauna, dpo ya koro musu bayanin laifin da aka kama 'yarta dashi, gaba daya sun girgiza musamman malam da ya cika da mamaki har yake tunanin yaushe ta soma haka? Dan sam bai kula da wani sauyi a tare da ita ba in banda yawan sauya sutura da Seeman take yi, kuma bai tambayi ba'asi ba saboda yasan uwarta itace ke kashe mata kudi. Ita ma haj. Hauwa tasha mamaki sai dai ko dar bata ji ba na tsoro, a ganinta in kudi na aiki to zata fito da 'yarta ta samu ta dauketa gaba daya kowa ma ya daina ganinta, burinta da yawa akan Seema, so take tayi karatu mai zurfi ta yadda zata shiga gomnati a dama da ita sosai ta zama mai fada a ji, sannan ta aura mata hamshakin mai arziki ta yadda rayuwarta zai bunkasa ta buwayi kowa.
Haj. Hauwa ta nisa tace cike da gadara.
"Yallabai ni dai ina so a kawo Karshen maganar nan, a rufe case din ko nawa ne zan biya"
Dpo yayi murmushi kasaita.
"Hajiya ba zan iya komai akai ba domin yan Matan da ta yiwa haka yayan babban mutum ne a kasar nan, dan haka ki a dana kudinki zai miki amfani wajen samo mata lawyer"
"Uhum kar muyi haka da kai, ko kasan cewa ni Matar ministan kudi bace? Abba turaki"
"Ina ganinki na shaidaki domin lokacin yana raye kun fancama, sai dai kuma ki sani wannan bashi zaisa aki hukunta 'yarki ba, domin laifi ne babba, sannan ma wanda ya bani wannan case din a yanzu ya fiki arziki da komai, bana tunanin zaki iya ja dashi"
"Mutsssss, koma waye bai isa ya ja dani ba, ni ce nan Haj. Hauwa, dan haka ka kira shi ya zo nan mu hadu duka muyi magana"
Dpo Auwal yayi wani kyataccen murmushi domin yasan Akram mutum ne mai taurin kai da zafi, musamman in mutum ya nuna shi wani ne a lokacin yake kaskantar dashi, dan haka ya san zai yi maganin tunkahon ta, ba musu ya daga waya ya kira Akram. Yana office tsaka da aiki sai ga kiran dpo cikin hanzari ya dauka suka gaisa kana dpo yace.
"Iyayen Seema sun zo in da hali kazo yanzu sun bukaci da su ganka"
Ok yace tare da saurin mikewa domin wani irin masifa ke cinsa, yana so ya sauke shi kwando kwando akan irin mugun tarbiyyar da suka bata, dan haka ba bata lokaci ya dauki key mota yana fitowa daga office dinsa yaci karo da Amir zai shi go.
"Ya ne sai ina kuma? ina sauri na sameka akan wani aiki"
"Auwal ya kirani akan case din su Teema, can zani"
"Aiko muje ayi komai dani"
Sai ya amsa key motar Akram din, shine ya tukasu suka wuce zuwa cid. Suna isa suka tambaya aka nuna musu office din da su dpo suke ba bata lokaci suka kutsa kai ciki, Auwal yana ganin su ya tashi tsaye cike da murmushi a fuskarsa su Haj. Hauwa Suna zaune sun basu baya, dan haka basu san ko suwaye suka shigo ba sai kada kafa take cike da izza da takama, malam ko yayi zugum yana karatun wasikar jaki. Muryan Akram da taji lokacin da suke gaisawa da Auwal ne taji wani damm kirjinsa ya buga, tabbas muryarsa ce sai dai bata kawo sune wanda za suyi maganar ba, wani irin nauyi taji wanda ya hanata juyawa amma harga arga tana cike sa tsantsar sha'awarsa har yanzu zuciyarta bata tsinke ba, dan har wani zut zut take ji a jikinta na sha'awar muryansa daya kamata.
"Ku zauna sune wannan"
Cewar dpo Auwal tare da zama shima, Akram duk suka zauna sai dai bai kai kansa gurinsu hajiya ba, sannan babu wata gaisuwa a tsakaninsu, malam sai zare ido yake dan daga ganin su yasan ba fa wasa. Auwal yace.
"To Hajiya gasu sun zo"
Cike da kasaita da nuna isa ta danne tsoro ta dago kai tsaraf suka ido hudu da Akram, sai ya kauda kai yayi kamar bai gane ta ba, sai Amir ne ya dan saki murmushi suka gaisa dan bai san yadda suka kwashe da Akram ba, dan yaki bashi labarin komai duk da yayi nacin yaji komai, Nan ta soma magana.
"Dama nasa ya kira ku ne akan muyi sulhu, Seema 'yata ce dan haka kuyi hakuri a janye zancen shiga kotu, nasan tayi laifi kuma insha Allahu zan rabata da garin nan gaba daya na kuma ja mata kunne"
Akram yayi wani irin kayataccen murmushi, har wani lumshe ido yayi dan tsantsar farin cikin dake fusgarsa, yayi matukar murna da Seema ta kasance 'yar Haj. Hauwa, yanzu ne ya samu cikakken damar da zai nuna mata ita kamar 'yar iska ce, cike da gadara yace.
"Ban yarda ba kuma ban amince ba, wallahi tallahi sai mun shiga kotu, Auwal yau nake so a shigar da kara gobe in Allah ya kaimu nake so mu shiga kotu a gama komai tunda an tattara duka shedu, bana so a bata lokaci, dan haka ka gaya musu su nima lawyer"
Sai ya mike yana dage gira cike da izza da rashin mutunci, Amir ya mike shima cike da jin wani iri da mamaki Akram, hakanan yaji a zuciyarsa zuwan da yayi Abuja lallai basu kwashe ta dadi ba, dan da business ta fada a tsakaninsu ya tabbatar Akram zai yarda a yi sulhu, zuciyarsa cike da tambayoyi da son sanin Amsa.
"Wlh baka isa ba kayi kadan, kai kwata kwata kwaya nawa kake da zaka ja dani, dole ne Ku tsaya ayi sulhu in har kana son mu wanye lafiya ni da kai"
"Haj. Hauwa tsakani na dake shege ka fasa, mu zuma mu gani kuma wlh bazan janye daga maganar dana yi ba dan ke ba kowa bace da kika isa dani, ai dama da wuya barewa tayi gudu danta yayi rarrafe, zan nuna miki ni dan halak ne bana yin magana biyu"
Sai ya fice.
"To wlh sai kaga matakin da zan dauka akan ka dan iskan yaro mara kunya"
Tayi ta sababi mara tushe, shi dai Amir ya bi bayan Akram wanda zuciyarsa ta gama tabbatar masa akwai jikakka a kasa, haka ma Auwal ya fahimci akwai wata matsala a tsakaninsu, Malam shima ya mike ya gyara mazaunin hularsa.
"To Hauwa kin ga dagan nan na cire hannuna daga lamarin 'yarki, wlh babu abin da ya shafe ita ta jawo kuma ya kare akan ta, in an shiga kotu duk yadda shari'a ta kama a yi mata ita ta jawo, daga nan ki tafi da 'yarki, in kin so ki rika zuwa muyi zumunci in kin ki ki karata can Allah ya hadamu da alkhairi"
Yana kaiwa nan yayi gaba ya barta da kukan zucci, zuciyarta har wani tafasa take. Dpo ya dauki takardunsa.
"Sai mun hadu a kotu"
Ya fice warsa, jiki a sabule ta mike lallai a wannan karan ta tabo ruwan dafa kanta, bata taba zaton a duniya akwai wanda ya isa ya ja da ita ba, domin tana ganin takai matakin data zama gagare, sai yau ta Gane cewar ashe da sauran ta.
'Lallai saina dauki mummunar mataki akan ka, wlh sai kayi dana sanin zuwan ka duniya, sai na wulakanta rayuwarka ko da zanyi yawo tsirara'
Tace a zuciya ta fice daga office din taje ta shiga mota ta fita a guje kamar zata tashi sama.
Amir kuwa ya yiwa Akram tambayar duniya nan akan abinda ya hadashi da Haj. Hauwa zuwansa Abuja, amma fir yaki magana karshe ma sai ya sanya karatun A-Qur'an yana saurare dole yasa Amir shuru cike da jin haushinsa.
Kamar yadda dpo yace daga nan high Court ya wuce ya gabatar wa alkali komai, Alkali ya dauki abin da mahimmanci musamman da yaji 'ya'yan former Governor ne aka yi haka, nan take ya tabbatar masa da ranar laraba jibi in Allah ya kaimu zasu zauna kotu akan case din, sai su hada komai zuwa gobe in Allah ya kaimu, a haka suka yi sallama.
Haj. Hauwa duk yadda taso da lamarin bata samu ba domin a ranar tayi yawo office din manyan kusoshin dake cikin jihar kaduna, tana karanta musu halin da take ciki da zarar ta furta sunan Akram da mahaifinsa sai su ce ba zasu ja da su ba lamarin babbane, haka har yamma tayi ta gaji ta wuce hotel din da ta sauke cike da tsananin kunci da tashin hankali, sai tsinewa Akram take tare da kudurta mugun nufi a kansa. Bayan tayi wanka ta natsa sai ta kira bokanta ta shaida masa komai, nan ya tabbatar mata da cewar zai yi iya kokarinsa dan ya lalata lamarin, da wannan maganar ta samu dan natsuwa a ranta.
Har zuwa washe gari tana ta zirga zirga dan samawa Seema lawyer, amma lamarin kamar hadin baki duk lawyer data je gunsa yana jin cewar su Akram ne suka kai kara tuni suke waskewa, wasu ma sun ji da ma case din ta fada a hannunsu sun zama lawyer din su Akram, sun san zasu ja kara dan ba karamin kudi zasu samu ba, tayi kuka kamar ranta zai fita kiri kiri aka hanata ganin Seema, da kudinta amma yau sunki yi mata magani, Akram ya kaskantar da ita a idon duniya, tayi alwashin saita lalata ruyuwarsa kamar yadda ya sata cikin kunci.
Su kuma Akram babu wasu lawyer da suka samu face lawyern gomnati da suka tsaya akan abin.
****** ******
Ranar labaraba
Kotu....
_________________
*Afwan sisters zaku jini shuru kwana biyu saboda nayi busy insha Allahu zan waiwayeku akan lokaci. Nagode da kauna tare adda'unku gareni Allah ya saka da Alkhairi ya kara so mara algush
*
Rahma ce
#vote
#comment
#follow
#share