ƘADDARARREN AL'AMARI

11

by @rahmakabir13

*ƘADDARARREN AL'AMARI*


© *Rahma Kabir*

     Mrs MG


Wattpad @Rahmakabir.


11


Ranar laraba


Kotu.

Duk kan wa'inda ake bukata sun hallara, Akram gaba daya dasu Teema suka zo harda Anty Meemi da Abida sai umar yayanta, iyayensu dama tuni Akram ya labarta musu komai sun yi na'am da hukuncin daya dauka, sai suka ce su ba sai sunje kotun ba. Bangaren Haj. Hauwa kuwa daga ita sai wata kawarta ko malam yaki zuwa, cikin kwana biyu ta rame tayi baki abin duniya ya gama cude mata, ta raina kanta da lamarin Akram. Haka su Seema an zo dasu tare da tawagarta duk sunyi wani iri wahala sosai ya bayyana a jikinsu, bangaren Aisha ma ta zo tare da babanta sai wata kawarta wacce su Seema suka yi komai akan idonta dan tayi shaida, haka ma dpo Auwal ya zo tare da jama'arsa, suna jiran shigowar alkali, kotun babu mutane sosai domin Akram yabukaci da kar ayi gayyar jama'a ayi a bun cikin sirri. Alkali yana shigowa suka mike ya zauna kafin kowa ya zauna, Maga takarda ya tashi ya gabatar da takardan kara, nan Alkali ya bawa lawyer damar fara gabatarwa, haka aka fara shari'a tare da gabatar da shedu wanda ya tabbatar lallai su Seema sun aikata laifin da aka kamasu akai, bayan an gama gabatar da komai alkali yayi rubuce rubuce ya dago tare da gyara mazaunin farin tabaronsa ya soma magana a nutse.


"Kotu ta saurari kara tare da bayanai ta kuma yarda da gamsassun shaidu wanda ya tabbatar da laifin wa'inda ake kara, dan haka a doka ta kasa shafi na 112 kotu ta yankewa su Seema zama a gidan kaso na wata shida tare da aiki mai tsanani, sannan zasu biya tara na miliyan bakwai na bata suna da suka so yi ga wanda suka kawo kara"


_(Wannan hukunci a kotuna na yanke shi ba tsarin dokar kasa bace, kawai dai nayi kintace ne na fadi haka saboda yadda labari na zai tafi min yadda nake so, ban tsaya dogon bincike ba dan kar ya cinye min lokaci, da fatan kun fahimce ni)_


Sai ya buga sandarsa ya mike court duk jama'a suka mike suna yin magana kasa kasa, aka fito da su Seema tana ji tana gani aka hanata ganawa da mahaifiyarta, da kuka wiwi aka fita dasu aka sanya su a motar da za a wuce dasu gidan yari, Haj. Hauwa ta fashe da matsanancin kuka da kyar kawarta ta lallasheta sai ta rage sautin kukan sai hawaye ke bulbula tana sharewa da hankacif, haka duk suka fito daga kotun. Su Akram ko murna ne fal cikinsu ya yiwa dpo Auwal godiya sosai kana suka isa parking space, zasu shiga mota Haj. Hauwa ta cimmusu ta rike marfin kofar motar, Akram ya kalleta ido cikin ido tare da kayataccen murmushi a fuskarsa.


"Da kyau Akram, ina taya ka murnan kayi nasara a kai na, amma ka sani wutar bata mutu ba, mu zuba ni da kai"


Sai ta wuce tana wani irin shu'umin murmushi wanda ita kadai tasan ma'anarsa, a wannan lokacin Akram yaji tausayin ta sai dai ko kadai baiji tsoron furicinta ba domin ya dogara ga Allah, sai ya shige mota, Amir ya zauna gefensa Umar a bayan seat, su Teema suka shiga motar Meemi zasu je gidanta, sai da Akram ya ja musu kunne ya ce zai aiko driver karfe biyar ya dauke su zuwa gida.


Su Teena suna isa gidan Meemi suka barke da hirar Kotu ko wanne yana fadar albarkacin bakinsa, Meemi ta sanya mai aikinta data dafa musu abinci sai ta wuce dakinta danta rage kayan jikinta, Abida itama sai ta mike zata bi bayanta Teema ta ce.


"Magulmaciya ki jira mana ta fito zaki wani bita kamar bindi"


"Eh din sirri za muyi"


"Gulma dai" 


Cewar Meena, sai duk suka sanya dariya, Abida ta samu Meemi a daki tana kokarin kiran mijinta daya yi tafiya zuwa Lagos amma yaki shiga, sai ta zauna gefen godon tana mai sosa keya alamar akwai magana a bakinta. Meemi ta kalleta da kyau ta gama karanto komai dake tare da ita tasan baya wuce zanen Akram zata yi mata, dan kullun ita a duniyarta ba tada damuwa wanda ya wuce na Akram baya kulata.


"Ina jinki fadi zuciyarki" 


"Uhum Anty wlh Akram har yanzu baya kulani sai dawainiya nake yi da sonsa"


"Ai dama nasan zancen gizo bai wuce na koki, to ya kike so nayi masa kin san dai Akram ba lallai ya saurareni ba tunda nasha kawo masa maganar ki sai ya waske"


"Ni yanzu anty abinda nake so ki min ba shi zaki samu ba, ina so ki shigar da maganar wajen su Umma yadda Abba zai ji ayi maganar aurenmu kawai"


"Kai Abida wannan gaggawa ne ki bari mubi komai a hankali, baki gama karatunki ba fa"


"Anty ba ki san yadda nake ji bane, Allah in har na wuce wannan lokacin ban yi aure ba nan gaba bazan iya rike kaina ba shiyasa na kawo miki maganar"


Meemi ta kura mata ido, zuciyarta cike da mamakin wai Abida ce ke yi mata wannan bayanin saboda tsabar rashin kunya, sai ta nisa.


"Shikenan zan samu Ammi da maganar sai ta samu Umma suyi zancen"


"Anty ni dai don Allah kije da kanki ki samu Umma Allah ya gani a matse nake"


Meemi ta dankara mata mugun kallo


"Wai ko dai ke harija ce bamu sani ba?"


'Haba Anty inda ina daya daga cikin wancen mutanen ai da ban kawo haka ba zan balle, kawai dai aure nake so"


"Hmmm lallai lamarinki babban ne Abida wlh mamaki ma kike bani, ko kunyata ba kya ji kike gaya min aure kike so"


"Anty ba haka bane kin san ke ta wajena ce shiyasa bana boye miki komai"


To shikenan zuwa gobe insha Allahu zanje na samu Umma da maganar, Amma anya ba kya kallace kallacen film din batsa kuwa? Dan kin fara bani tsoro ma"


"Anty gaskiya ba zan boye miki ba ina dan tabawa danna rage zafi"


Tana kaiwa nan a maganarta ta fice da gudu tana dariya, sakin baki Meemi tayi tsoron Allah ya hanata magana, ai babu arziki ta daga wayarta ta kira Umma nan take, ta shiga gaya mata duk yadda suka yi da Abidan bata boye mata komai ba, Umma dai sauratenta take tana eh eh, bayan ta gama mata bayani ta daura da cewa.


"Umma na tsorata da lamarin yarinyar nan, ina ganin gwara a tado da maganar ayi kawai tunda nasan Akram ba zai ki jin maganarki ba, dan kar Abida ta dauko mana magana".


"Gaskiya ne Meemi anjima zan yiwa Abbansu magana a san abin yi"


"Zanzo gobe insha Allahu a kan maganar"


"To Allah ya kaimu, amma ina so mu bar maganar a tsakaninmu karki gayawa kowa, ni zan san abinda zan fadawa Abban su dan Akram dinma ai ya isa ya aje iyali"


"To Umma Allah ya shiga cikin lamarin ya tabbatar da Alkhairi"


"Ameen" 


Sai suka yi sallama. Meemi ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi sai ta fita zuwa falon ta same su.


******    ******


Safna cikin kwana biyu ta sauya daga fatarta har zuwa suturunta, sai dai bata yadda ta rika sanya shegun gyalen da hajiya ta siya mata ba sai dai hijabanta take sanyawa, tun ranar lahadi da suka je kasuwa Hajiya tayi mata siyayya sosai washe gari saloon ta kaita tasa aka gyara mata kai gashin nan nata yayi fes dashi sai kamshi da sheki yake, ita kanta safna ta ji dadin haka domin har wani iska take ji na musamman yana ratsata, ita kanta hajiyar ta yaba da sumanta dan Allah ya wadatata da suma sosai har gadon baya, daga nan takaita wajen wanke hakori aka wanke mata so suka kara fitowa fes bakin sai kamshi suke, tasa aka wanke mata kafa duk kaushi kaushin suka tafi, har wajen gyaran jiki ta kaita akayi mata gyara na musamman fatanta tayi kyau da haske, cikin kwana biyu safna ta sauya duk halittarta ta asali ta bayyana kyawun ta ya fito sosai, duk inda ta girma sai kamshi domin wasu mugayen turaruka hajiya ta siya mata na kamfanin oriflame sannan ta siya mata humra masu kyau da kamshi asalin na 'yan maiduguri, kwata kwata ta daina aiki sai dai taci ta sha yamna nayi hajiya ke sallamarta.


A jiya talata Baffa Bala yazo gidan dan dama ya samu labarin an sanya musu wuta, wannan karan baizo da fada ba ya saurari bayanin Safna yayi na'am. Sai ya amsa kudin da Najwa ta basu tace zai musu siyayya, Safna tace ya raba kudin biyu ya dauki rabi shima yayi siyayyar gidansa, yace sam ba zai dauka ba su sun fishi bukata haka ya tafi tare da yi musu nasiha. Duk da ya gamsu da bayaninta amma ya dauki alwashin zuwa wajen hajiya uwale dan ya ji ainahin zance. 


Haka kuwa aka yi yau da safe ya wuce rumfar Haj. Uwale yayi sa'a ta zo, tana ganinsa ta gane shi suka gaisa cike da girmamawa, nan Baffa ya Koro Mata bayanin abinda ya kawo shi nan hajiya ta tabbatar masa da hakane tare da wasu bayanai da zaisa ya kuna gamsuwa da sabon aikin da safna ta samu, ya nuna murnansa sosai a kai kana yayi sallama da ita, dubu biyar haj. Uwale ta bashi, Baffa da kyar ya amsa danma tayi ta rokonsa daya amsa, hala ya tafi yana godiya tare da mamakin kirkin hajiyar. Baffa shi ba irin mutanen nan bane masu son duniya, daya san irin sana'ar da hajiya uwale zata daura Safna a kai, da wlh bazai yarda ba daga ita har kudinta basu ishe shi kallo ba.


Safna ko da tazo gurin aikin Hajiyar bata sanar da ita Baffanta yazo ba, haka ta ce ta zauna cikin shago bata balas bata ragas sai dai taci ta sha, a haka har yamma ta yi. Koda lokacin tashi yayi hajiyar sai tace tare zasu gidanta dan tana tunanin yau ne zata damkata hannun Matar da ta zata yiwa aiki, Safna bata Musa ba ta bita gida ta dauki tsintsiya zata yi mata shara, hajiyar ta hanata ta hada mata ruwan wanka mai zafi tare da wasu turaruka a ciki tace ta shiga bayi tayi wanka, ba musu ta shiga tayi ta fito, hajiyar ta bata wata doguwar riga ready made maroon color safna ta saka tayi mata das a jiki kamar ba ita ba, tasa ta ta yi kwalliya, safna powder kawai ta shafa sai kwalli da man baki, ta daura dan kwali saita sanya hijabinta data cire.


"Ohh ni uwale, yarinya sai kace ba yar zamani ba, ai wannan ba kwalliya bace kuma dole ki aje hijab din nan gyalen kayan zaki yafa" 


"Hajiya ki bari haka Dan Allah, ni hakan tafi min"


"To shikenan bazan takuraki ba in kinje gidan Haj. Najwa dole zaki daina wannan kauyencin. Samu guri ki zauna kafin tazo"


Safna ta zauna bisa dadduma tana jiran a kira sallar isha'i ta tashi ta gabatar, ita kuma hajiyar ta fice zuwa tsakargida dan ta zauna a fadarta su cigaba da chapter.


Karfe takwas da Rabi Najwa tazo tare da kawayenta, tana shigowa duk yan matan suka natsu cikin takun kaisaita ta shigo har tsakiyar gidan, haj. Uwale ta mike tare da yi mata kirari Najwa tana murmushi cike da basarwa.


"Fito min da ajiyata sauri nake"


"An gama ranki ya dade"


Sai ta shiga kwalawa Safna kira, cikin sauri ta fito tana amsawa 


"Yauwa maza zo ku wuce ga hajiyarki ta zo"


To tace tare da sanya flat shoe sabo da hajiyar ta bata ta sanya, tazo cikin nutsuwa Najwa tana kare mata kallo. Safna ta gaishe ta a ladabce bata amsa mata ba saita jawo hannunta ta kama tare da danka mata jakarta ta ce.


"Beauty muje"


Safna hakan nan taji gabanta ya fadi sai dai bata kawo komai a ranta ba suka wuce tana binsu a baya rike da jaka najwan, Hajiya Uwale ta rakasu da guda sai murna take. Suna fita mota suka shiga Najwa a back seat tare da Safna sai billy mazaunin driver Ma'u a gefenta, haka suka tafi. Wani katon wurin shakawata suka nufa dake can cikin anguwar rimi wanda wurin ya tara yayan manya kala kala maza da mata, wuri ne na musamman da aka bude don shan shisha da kuma kayan maye da sauran abubuwan jin dadin rayuwa, an kashe kudi sosai a gurin sai dare gurin yake cin kasuwansa dan ba a bude shi da rana, kuma gurin a yadda aka yi shi ba kowa ne zai fahimci wurin jin dadi bane don a boyayyen unguwa aka yi shi, gate dinsa biyu ne kafin a shiga sannan akwai manyan security a gurin, sannan kafin ka shiga sai ka nuna gate pass dan tun rana mutane ke booking tru online sai a turawa mutum ticket a phone dinsa in zai shiga shi zai nuna. 


Suna isa security suka bude musu gate dan dama sun gane motar Najwa basa tsayawa duba gate pass dinta, suka yi parking a gefen inda ake aje motoci duk suka fito suka kutsa kai cikin wurin Safna tana biye dasu a baya da zambadeden hijabi kamar matar malam tana rike da jakar Najwa, wannan karan shigar mutunci suka yi dukansu, dogayen riguna ne a jikinsu sun yane kai da gyalen kayan. 


Akram, Amir, Umar, Auwal, sai wani abokinsu Fahad suna zaune a gefe, katon tabur agabansu kujerunsu ya zagaye table din duk kansu da tukunyar shisha a gabansu, babu wanda aka sanyawa kayan maye a ciki sai flavor masu kamshi domin su sam baya shaye shaye sai dai suna mu'amala da shisha sosai muaman Akram da Amir da sukayi rayuwar turai, in dai suka je club abinda suke sha kenan suyi nishadi sannan suke zuwa gida.


Takun takalmar su Najwa yaja hankalinsu Akram suka waiga dan suga ko su waye, Akram yana ganin Najwa ce yayi dogon tsaki ya juya ya cigaba da abinda yake, Amir ya kwashe da dariya.


"Mutumina ga fa Najwa abokiyar tsamar ka"


"Amir bana so kabar kawo min zancenta"


Murmushi kawai duk abokansa sukayi suka sauya hira, Najwa ta gansu itama sai ta ya mutse fuska ta kauda kai gefe ta wuce ta samu wurin zama dai dai setting su Akram, duk suka zauna Safna dai tsayawa tayi Dan bata yi mata izinin zama ba, kamar ance Akram ya dago kai sai idonsa ya sauka kan Safna, sosai ya bude idonsa danya zai tabbatar ita dince daya taba kwata hannun yan daba, nan take zuciyarsa ta tabbatar masa domin fuskarta ta zauna a idonta ba zai taba mance ta ba, a zabure ya mike ya nufi gurin.


_*yawan comment yawan rubutu*_


Rahma ce

#Follow

#comment

#vote

#share