12 and 13
[6/30, 8:26 PM] Rahma Kabir: *ƘADDARARREN AL'AMARI*
© *Rahma Kabir*
Mrs MG
Wattpad @Rahmakabir.
12
Safna bata ganshi ba dan hankalinta yana wajen wasu samari da yan mata da suke rawa, Najwa tana ganin Akram ya nufosu ta kauda kai tana jiran taji yau da wanne yazo? dan da wuya su hadu a gurin ba suyi rikici ba, yana isa gunsu ya finciko Safna cikin kidima ta juyo suka yi ido hudu, tana ganin shi ne ta zaro ido cike da tsoro a fuskarta, Akram ya kare mata kallo.
'Tabbas ita ce'
Yace a ranta, hannu ya daga ya kifa mata kyakkyawar mari wanda yasata ta gigice tayi baya, Su Najwa suka mike a zabure hakama su Amir suka mike suka zo gurin cike da mamaki, mutane suka koma kallonsu domin wannan marin da yayi mata ya jawo attention dinsu.
Akram kake ko wa ka fita daga cikin tsabgata, me tayi maka da zaka mari yar mutane?
Cewar Najwa cike da masifa,
Banyi dake ba dan haka kija tsastsamar jikinki a nan. Ke kuma uban me kike a nan cikin dare? ko kin dauka ban gane ki bane
Ya kare maganar kan Safna cikin zare mata ido, hawaye ya gama wanke mata ido tsananin tsoronsa ya shige ta sai ta girgiza mata kai dan ta kasa cewa komai.
Ba dake nake magana ba? Me ya hadaki da wannan fasikar iyalan shaidan? Ko kema yar hannu ce kin gama bata jikinki ta tatse ki?
Safna hanjin cikinta suka kada ta girgiza kai a lamar A'a. Bai kuma cewa komai ba sai hannunta daya kama ya kwace jakar Najwan ya aje akan table, ya ja hannunta suka yi gaba kowa yana kallonsu baki sake cike da tsantsar Mamaki, Najwa tayi wani makirin dariya.
Wannan karan karya kake ka rabani da ita wlh, sai nayi maganinka sai kasan ka shiga gonata. Hey guys muje kawai.
saita dauki jagarta ta mikawa Billy suka bi bayan su Akram, Su Amir dai sun kasa kyakkyawan motsi sai dai suka bisu da kallo.
Auwal muma mu wuce kawai tunda uban gayya ya siya fadar da babu ruwansa
Cewar Amir cike da jin takaicin Akram.
Akram suna isa parking space ya bude mota ya je fata a mazaunin baya shi kuma ya koma mazaunin driver ya figi motar a guje kamar zai tashi sama. Suma su Najwa Motan suka shiga suka wuce gida cike da haushi, Amir ma motan Auwal suka shiga ya je ya sauke shi a gida su kuma suka wuce. Akram yana isa junction din katuru ya samu guri yayi parking.
Ya fara magana a kausashe.
Wai ke wace irin yarinya ce da kike da kunnen kashi, kwakwalwarki kamar ta dabba ba kya lissafi ko, yanzu iyayanki saboda son duniya zasu barki a hannun wannan shaidaniyar kina mata aiki. To wlh ina mai miki gargadin karki yadda na kuma ganin fuskarki tare da ita, ke bama ita ba inna kara ganinki a unguwar mu saina karya ki.
Kayi hakuri wlh dama yau na fara aiki a gunta daga...
Rufe min baki shashasha kawai fita min a mota kan in rufe ido
Da sauri safna ta dago suka hada ido ta mirro gaban mota, ya galla mata mummunar harara jikinta yana rawa ta fita a motar kafin tayi masa godiya yaja galas dinsa ya figa a guje. Safna ta sauke ajiyar zuciya tare da yin hamdala a zuciyarta da Allah ya kawo Akram cikin rayuwarta. Haka ta tari napep ta wuce gida cike da tunani iri iri sai maimaita sunansa take yi a zuciya, ko kadan bata ji haushinsa ba face wani farin ciki daya lullubeta. Shima gida ya wuce cike da jin takaicin kansa daya damu akan rayuwar yarinyar da ko sunanta bai sani ba.
***
Akram da Najwa a kwai jikakkiyar tsama a tsakaninsu, hakan ya faru ne akan dalilin kanwarsa Humaira.
Najwa 'ya ce a gurin ambassador Ishaq da mahaifiyarta mai suna Sabura, su biyu suka Haifa Najwa ce babba sai kaninta Najib wanda ya kasance baida cikakken lafiya sicker ne shi, hakan yasa iyayen suka je aka gwada genotype dinsu aka tabbatar musu jininsu duk AS ne wannan dalilin yasa suka hakura da haihuwa aka juya mahaifar Haj. Sabura. Najwa ta taso cikin rayuwar turai domin kusan rayuwarsu a Italy suka yi shi inda mahaifinta yake ambassador kasarmu nigeria, Najwa kasantuwar babu ilimin addini a rayuwarta shiyasa ta koya munanan dabi'u wanda a ganinta dai dai ne, tun tasowarta take mu'alama da mata bata taba saduwa da namiji ba sai mata yan uwanta tun bata kware ba har ta zama gwana a harkar. Retired da mahaifinta yayi shine silar dawowarsu Nigeria suka sauka a Abuja, mahaifinta ya cigaba da kasuwancin saida motoci inda yake da company mai suna N.N motors wato sunan yayansa ya rada sunan companynsa. Najwa ta yi karatu a can Italy inda ta hada degree a fannin computer science, ko da ta dawo nan bata damu data yi aiki ba kuma mahaifinta yanada hanyar sama mata. Sai dai sun bata ta da kashe kudi bata san babu ba a rayuwarta, tun dawowarsu ta cigaba da harka da mata tunda ta dandana bakar fata sai taji sunfi turawa dadi haka take sakin kudi a duk lokacin da ta samu yarinya dan cikar burinta.
Najwa ta hadu da Billy da Ma'u a wani club suma yayan masu kudi ne duk mazauna Abuja, haka rayuwarsu take duk uwa ba kwaba kaka ba tsanani, tunda suka hadu suka fara harka wanda Najwa ta basu kudi mai yawa a matsayin sadakin aurensu haka suka amince suka zama mata ita kuma miji, najwa bata yarda suna kula kowa ba sai ita kadai dan mace ce mai kishi, wanda bata sani ba suna yin harkansu da mutane a waje ba tare da sani ba.
Wata rana najwa tana kallon tashar NTA sai tayi kicibis da Humaira tana gabatar da labarai aiko nan take zuciyarta ta biya, hakan yasa ta sa aka yi mata bincike a kanta har da number ta samu, tun daga lokacin ta shiga matsawa Humaira tare da gaya mata manufofinta a kanta, tana tura mata hotunan tsiraicinta ta WhatsApp hakan ya tsorata Humaira sai ta yanke shawara gayawa akram, koda ya ji bai tsaya bata lokaci ba yaje police state yayi karar najwa, suka je suka kamata wanda har saida commissionern yan sanda ya shiga maganar, anan aka yi sulhu aka shiga tsakaninta da Humaira, wannan ne ya kawo dalilin tsamanta da Akram duk in suka hadu sai sun yiwa juna abin da zai bata ransu, musamman Akram daya matsawa rayuwarta baya bari tasha ruwa in dai suka hadu.
*******
Bayan kwana biyu
Safna tun ranar da abin nan ya faru saita yi karatun ta natsu, tayi tunani mai zurfi akan najwa wanda ya tabbatar mata da lallai akwai abinda take nima a gunta dan maganar da Akram yayi akan ko itama ta bata ta tatseta ne yake ta dawo mata a rai. Har gidan Baffa taje ta labarta masa komai, salati yayi yana mamakin lamari, ya shiga tsinewa haj. uwale sannan ya gargadi Safna akan karta sake zuwa wajenta tunda abin haka ne, sannan yace ta zauna a gida kafin ta samu wani aikin.
Yau kimanin kwana biyu kenan bata je shagon uwale ba ta natsu a gida, da yake sunada abinci sai bata damu ba ta fara tunanin samun wani aiki, su Muslim sunyi ta tambayarta dalilin da yasa bata zuwa aiki sai dai ta basu amsar hajiyar ta koreta ne bisa wani laifi da tayi mata.
Bayan sallar magrib
Suna zaune a tsakar gida sai gasu Najwa sun shigo gidan cike da isa, a zabure Safna ta tashi tsaye jikinta sai rawa yake dan a yanzu babu abinda tafi tsoronsa irin Najwa, sai yanzu ta tabbatar da tayi kuskure data bari suka rage mata hanya har suka san gidansu, Najwa ta karaso Billy na biye da ita a baya dan yau basu zo tare da Ma'u ba, su Muslim ma duk tsayawa suka yi suna kallonsu. Najwa ta karasa har ciki dakin su ta tsaya tana kare masa kallo sai yatsine baki take, Safna ko gezau bata yi ba balle tayi niyyar bin bayan Najwan, billy ta kalleta.
Ki bi bayanta mana karki bata mana lokaci
Safna ta kasa ce mata komai saita nufi dakin zuciyarta yana dukan uku uku, gani take in ta shiga zata yi mata wani mugun abu, tana shiga ta tsaya nesa da ita suna kallon kallo, Najwa ta matso, Safna tayi baya da sauri, sai tayi murmushi ta cigaba da matsawa safna tana baya harta cimma bango, Najwa ta isa har jikin bangon ta dafa da duka hannunta tasa safna a tsakiya, sai ta runtse ido tana karanto duk Addu'an daya zo bakin ta.
Uhum me yasa kike tsorona haka? zuwa nayi na dauke ki ko kina tunanin zan rabu dake ne? To ki sauya tunani domin ni dake mun kulla ba kwancewa
Don Allah ki fita daga cikin rayuwata bazan iya miki aiki ba
Tayi maganar cikin rawar murya hawaye na bin kuncinta cike da tsoro.
Dama ai ba aiki za kiyi min ba, ina so ni da ke mu ci ribar juna, dan haka Safna ni sonki nake kuma da aure
A gigice safna ta dago ta kalli kwayar idonta na rashin fahimta.
Ban taba jin anyi haka ba ko kin manta ke mace ce,
Eh na sani kuma zamani ne yazo mana da haka
A'a ki sauya shawara ni bana cikin masu haka kema Allah ya shiryeki
Ta fada a fusace, nan take taji tsoron nata ya tafi Dan bata ga abin tsoro ga mai sabon Allah ba.
Uhum bari na kwatanta miki dadina na tabbatar ba zaki barni ba
Sai ta fincikota ta fada jikinta ta rungume tsam, safna taza tsandara ihu ta soma kokawar hada bakinsu guri guda, Safna ta dace hakoranta ta matsa bakin Najwa tana kokarin sanya harshen ciki ba hanya, da safna taga fa ba barinta zata yi ba sai ta sanya karfinta ta hankadeta baya, Najwa tayi baya zata fadi amma sai tayi na maza ta yi saurin tsayawa tana haki cikin daure fuska ta matso tare da fikawa Safna mari wanda yasa ta kusa faduwa, dagowar da zata yi Najwa ta fito da wani abu daga jaka ta fesa mata nan take ta zube a kasa a sume, Najwa sai ta fito da sauri tana fadan.
Billy ina magana da Safna sai ta fadi ta suma ina ganin dama ba tada lafiya zo mu kaita asibiti
Jikin su Muslim yana rawa suka isa dakin sukaga halin da take ciki ai sai suka fashe da kuka, Najwa da Billy suka shigo dakin suka shiga basu hakuri.
Kuyi hakuri bari mu kaita asibiti yanzu mu dawo tana bukatar ganin likita
Ku barshi kawai bari mu kira baffanmu
Kafin ku kira shi kuna so ta mutu ne, ku bari kawai mu kaita yanzu za mu dawo ku kwantar da kankalinku.
Babu yadda suka iya haka suka hakura su Najwa suka kama Safna suka fice da ita daga gidan suka sanya a cikin motarsu back seat, suka shiga da sauri suka wuce, sai da suka hau kan titi sosai suka tabbatar da sun bar unguwar billy ta waigo ta sakarwa Najwa murmushi.
Baby aikinki yayi kyau yadda kika san a film gashi mun sameta cikin sauki
Kin san ni duk inna so abu to ko ta wace hanya ce saina samu. Kulle ta zanyi a daki har sai ta amince zata yi rayuwa dani kafin zata samu kanta
Da kyau tawan
Haka suka isa gidansu dake malali quarters suka shiga da ita wani kayataccen daki suka kwantar saman gado suka fito suka rufe da key. Su Muslim suna jiran dawowar su har kusan sha daya na dare amma shuru, sun dukufa cikin tunanin ko jikin ne yayi tsanani, haka suka kwana barci barawo ya sace su cikin matsanancin damuwa.
***** ******
Washe gari
Safna bata farka ba sai takwas na safe, a gigice ta tashi zaune tana kallon kanta da kuma dakin da take ciki, wani firgitaccen ihu ta saki tana matsanancin kuka. Su Najwa suna falo suka jita da sauri suka nifo dakin suna budewa suka ganta sai ihu take tana fadin wayyo Allah. Najwa ta saki wani dariya mai sauti sai ta daure fuska.
Ke yi mana shuru, an gaya miki zaki ci bulus ne na barki, to bari kiji gwara ma ki natsu ki amsa tayi na in ko kin ki bake ba fita daga gidan nan har abada.
Wlh karya kike shaidaniya nafi karfinki Allah saiya min maganinku kuma ki sanya a ranki dana zama irinki gwara naga mutuwata.
Dariya kawai Najwan tayi saita fice, billy ta dire mata tire din abinci ta juya zata fita safna ta taso da gudu zata biyo su aiko billy ta yi saurin fita da dannawa kofar key, Safna ta zube a kasa jikin kofa tana matsanancin kuka.
Su Muslim ganin har washe gari Safna bata dawo ba hankalinsu ya kara tashi haka suka tafi gidan Kawunsu, sunyi sa'an samunsa a gida nan suka labarta masa abinda ke faruwa, sosai lamarin ya taba Baffa innalillahi... Kawai yake fada, daga bisani yace su tashi suje su bincika asibitoci mafi kusa ko can suka kaita. Haka suka shiga zata duk asibitin dake cikin badarawa na gomnati dana private, sai dai duk inda suka je babu labarin su Safna har zuwa yamma lis babu nasara haka suka koma gidan baffa, a nan suka ci abinci dare shima saida baffan ya matsa musu, kuma suka kwana a nan saboda dare yayi.
Safna ta kuma kwana a gidan bata ci komai ba sai ruwa da take sha ko sun kawo mata abinci bata ci gani take kamar sun sanya wani abu a ciki, ganin babu sarki sai Allah ya sata dole ta dukufa da addua, da yake dakin akwai bayi sannan akwai dadduma da hijab da suka kawo mata sai ta shiga ta dauro alwala tazo tayi sallolinta kana ta zauna tana fadawa Allah. Haka ta kwana a zaune sai barci barawo ya sace ta.
Washe gari...
Rahma ce
#follow
#vote
#comment
#share
[7/1, 7:14 PM] Rahma Kabir: *ƘADDARARREN AL'AMARI*
© *Rahma Kabir*
Mrs MG
Wattpad @Rahmakabir.
13
Washe gari
Tun misalin karfe shida na safe tun gari bai gama haske ba safna ta gama hada plan din guduwa, toilet ta shiga ta duba window bata san lokacin da murmushin nasara ya kubuce mata ba, windon bayin glass ne da aka jera sai net da aka manna ta baya, tun tsakiyan Daren jiya Safna ta gama cire glass din ta yage net din. Safna ta runtse ido ta karanto Addu'an samun nasara kana tayi bisimilla ta bude abin tuntun kashi ta dare samanta ta taka tuntun da ruwa ke taruwa da ake flushing sai ta kama karfen dake rike gilss din windon ta zura kafarta na dama shima na hagun ta zura shi sai ta rika jan jikinta har Allah ya bata dabar direwa, ta waiga tana kallon tsukukun windon da Allah ya bata sa'an fita, sai ta saki murmushi ta gyara mazaunin dankwalinta dan bata daukar musu hijab ba daga ita sai kayan jikinta, ta nufi gate cike da zullumi, ta samu mai gadi zaune yana sauraren labaren BBC na karfe shida a radio, cikin dakiya da karanto Addu'a a ranta ta tunkareshi, gate man din yayi mamakin ganinta dan bai san da ita a gidan ba tace.
Baba Anty ta aikeni na siyo mata bread
Ok yace bai musa mata ba ganin yanayin ta tayi kama da yar aiki, amma yayi mamakin siyan bread din domin yasan Haj. Najwa komai tana oder ne a kawo mata har gida. Ya bude mata gate ta fita ya maida ya rufe tana jin ya rufe ta ruga a guje tana waige waige sai da ta shanye layin kana ta kutsa kai wani layi sai ta sausauta gudunta tana haki, hawaye ne ya soma kwaranya a kuncinta tana waige waige, ga unguwar ba kowa ihunka banza barinka hofi, bata san ko a ina take ba dan ba sanin manyan unguwanni tayi ba, haka tayi ta tafiya kafa babu takalmi, tayi mamaki ma da mai gadin mai gane ba, koda yake rigar jikinta dugowa ce kuma ta sauka har kasa ta rufe mata kafa, sosai take tafiya tana shiga layi ka ga unguwannin duk titi ne tsoranta karta kara maida kanta layin data fito, sosai take kuka tare da adduan Allah ya kawo mai taikamonta a wannan lokacin.
Haj. Hauwa sai yau ta shirya komawa Abuja, kwana biyu da suka wuce tana ta zarya akan ko zata samu nasarar dauka ka kara akan batun Seema, amma abin yaci tura karshe haka ta hakura ta yanke shawarar komawa Abuja dan cigaba da harkokinta, amma fa Akran yana kahon zuciyarta ta kuma tanadar masa irin mugun hukuncin da zata yi masa. Sanye take da doguwar riga na atamfa sai ta yi dauri da dan kwalinta, ta sanya gyale babba ta yafa a kai sai farin gilashi sisiri data sanya, daka ganta kasan ruwa ya bigi dan zakara har wata yar natsuwa tayi, tayi ramar fargaba sai ta kara haske, sun fito daga hotel din da ta sauka wanda yake a nan malali tana zaune a baya driver yana janta so take su isa Abuja akan lokaci shiyasa suka yi fitan sassafe. Motansu ce tazo ta wuce Safna da gudu ta matsa gefe da sauri dan ta tsorata, kuka sosai take yi domin ta soma sarewa da dogon tafiyar da tayi sai a lokacin yunwa ya taso mata gadan dagan, jikinta ya zama babu karfi sai dai sauri da take yi dan ta samu ta shiga cikin jama'a, Haj. Hauwa ta hango safna ta madubi bayan sun gota ta tana nazarinta duk da bata ga fuskarta ba, har sun yi nisa sai tayi saurin cewa driver.
Kayi ribas mu koma gurin wancen yarinyar
To yace ya soma yin ribas har suka cimmata, Safna tana ganin haka ta tsandara ihu tana niman fecewa a guje, a tunanin ta ko su Najwa ne suka zo sake dauketa, ganin an zuge gilas din baya taga wata mata ta sayo kai waje yasa ta tsaya tana kuka sosai.
Ke meya sameki kike kuka? Kuma daga ina kike da sassafen nan?
Sace ni wasu yan mata suka yi suka kawo ni nan anguwar, kwana na biyu a gunsu shine Allah ya bani sa'a na samu na gudo, to bansan ko ina nake ba tun dazu nake tafi kuma na gaji sannan ina jin yunwa.
Ayya sannu ko Allah ya kyauta gaba, ina ne unguwarku?
Badarawa nake
Ok ai ba nisa sosai tunda nan malali ne, duk da muna sauri amma shigo mu rage miki hanya sai mu kai ki gida ko
Jikin safna yana rawa ta amsa da to, driver ya bude mata gefenta ta shiga ta zauna tare da rufe kofar ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Nagode hajiya Allah ya saka da Alkhairi
Karki damu, sai ki rika yiwa driver kwatance ko har mu isa gidan baku
Cewar Haj. Hauwa tana gyara zamanta tare da daukar wayarta ta shiga danne danne, tana wasu nazari a zuciyarta domin ba haka kawai ta taimaki safna ba sai dan wasu tunani da tayi akan ta na cikar wani burinta. Safna ta shiga yi masa kwatancen gidan Baffansu domin tana tsoron taje gida su Najwa su je can nimanta, ta san kuma zuwa yanzu Baffa yaji komai, sannan tasan su Muneera suna can gidansa dan ba zai yarda su zauna su kadai ba.
Suna isa suka yi parking a kofar gidan Baffa, Safna ta fito Haj. Hauwa ma haka suka shiga gidan tare, Safna tana sallama Matar baffa ta amsa tare da kwalawa malam kira.
Malam! malam kazo ga Safna ta dawo
Da gudu su Muslim suka fito daga daki baffa yana biye dasu a baya, muneera ta rungume Safna tana matsanancin kuka, Muslim ma kukan yake sosai yace.
Anty mun tsorata sosai gani nake kamar sun sace ki ne sun kai ki gidan yankan kai.
Murmushin karfin hali Safna tayi ta shafa kansa ba tare da tace komai ba, Matar Baffa ta daukowa hajiya tabarma ta shimfida ta zauna, sai duk suka samu guri suka zauna suka gaisa gaba daya. Kana safna ta gabatar da hajiya tare da bayanin sune suka taimaketa, nan ta basu labarin duk abinda ya faru harda yadda ta samu ta gudu, sosai suka jinjina lamarin hatta matar Baffa wannan karan taji tausayinta, Baffa suka yiwa hajiya godiya ta amsa fuska sake tare da nuna musu ai d'a na kowa ne tace.
Ni ina tafe a kan hanya ne zan wuce can gidana dake Abuja, in babu damuwa mai zai hana ku bani Safna tayi min aiki a can insha Allahu zan inganta rayuwarta zan sata a makaranta domin ta samu ilimin zamani Wanda zata taimaki kanta daku duka, insha Allahu zaku sameni da rikon amana, zan siya mata waya kuna gaisawa da ita kuma duk karshen wata zan rika kawota dan nima 'yata tana karatu a garin nan sannan akwai dangina a nan. A gani na dole safna ta bar garin nan in ba haka ba wanda suka sace ta zasu cigaba da farautarta.
Su baffa suka yi shuru suna tunani, Safna ta nisa tace cikin zakuwa.
Baffa wannan shine hanya mafi sauki da zan kubuta daga sharrin su Najwa, dan Allah ka amince na bita koda nan da wata biyu ne sai na dawo kaga komai ya lafa a lokacin
Safna ku marayu ne bana son wani abu sa samu rayuwarki, wannan mata bamu santa ba tayaya zanji karfin guiwar bata ke? ni dai ina jin tsoro domin duniyar nan babu gaskiya.
Gaskiya kam malam duniyar nan sai lahaula
Cewar Matar Baffa, haj. Hauwa ta nisa tace
Kuna da gaskiya domin mutum abin tsoro ne. Ni sunana Haj. Hauwa Matar Abba Turaki ministan kudi da Allah yayi wa rasuwa shekarun baya, kunga babu yadda za ayi na cutar da ita tunda an sanni sosai.
To Alhamdulillah lamarin yazo gidan sauki dan na gane Abba Turaki domin Abokin mai gidana ne da nakewa aiki, ga Safna nan ki tafi da ita ko muma hankalinmu zai kwanta, Allah yasa ki rike Amana.
Ameen nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi insha Allahu zan inganta rayuwarta sai kunyi alfahari da ita.
Allah ya baki iko
Cewar Matar Baffa data ji dama a cikin 'ya'yanta ne suka samu wannan damar, nan da nan taji kishin hakan a zuciyarta. Baffa yace suje can gidansu Safnan su kwaso kayanta kafin su wuce, hajiyar tace ba sai sunje ba in suka karasa can Abuja zata siya mata sabbi saboda suna sauri, haka fa suka ran kayo waje gaba daya Muneera ta shiga rera kuka sosai, Muslim ma bai iya dauriya ba kukan yake yi saboda wannan shine karo na farko da zasu rabu da 'yar uwarsu na tsawon lokaci, baffa ne ya shiga lallashinsu safna ko daketa tayi bata yi kuka ba domin ta karfafawa kannenta guiwa, suna kallo suka shiga mota suka wuce, sai a sannan ne Safna ta soma kuka sosai tana jin tsantsar kewar kannenta, babu wanda yace mata uffan haka tayi kukanta ta gaji dan kanta tayi shuru. Haj. Hauwa tasa driver ya tsaya ya shiga wani restaurant ya siyawa Safna abinci ya dawo ya bata ta soma ci suka dauki hanyar Abuja.
***** *****
Bangaren su Akram kuwa, Umma ta samu Abba da zancen Auren Akram da Abida kuma yayi na'am da haka yayi murna sosai, haka ya kira dan uwansa Babansu Abida suka tattauna maganar, daga nan Baba yace ya barwa Abba komai a hannunsa ya yanke ranar biki kawai, nan Kaduna zasu zo ayi shagalin bikin dasu. Abba yaji dadin haka yace zaiyi nazari nan da kwana biyu kafin yaga abinda zai yanke.
Yau Umma da kanta ta kira Akram a waya yazo ya sameta a dakinta tayi masa bayanin komai, cike da rashin jin dadi ya ce.
Amma Ummuna wani irin sauri ne haka? 200level take a matakin karatu sannan a abuja take yi, da an bari ta gama tukuna, ni wlh bana son auren nan a barni kawai duk lokacin da nayi niyya sai na yi.
Lallai Akram ni kake fadawa haka? Ashe ban isa da kai ba? Abida yar uwarka ce wannan abu na zumunci ne, in kace haka ya kake so mu kalli Baban Abuja da ita kanta mahaifiyar Abidan? Yarinyar nan tana sonka kuma ba tada makusa dai dai gwargwado tana da kyau da tarbiyya, dan Allah Akram karka bani kunya kayi hakuri a kulla wannan abu, nan gaba da kanka zaka zo ka yi murna da hakan. Batun karatunta sai ayi mata transfer ta dawo nan inda su Teema suke, kaga komai zai zo cikin sauki tunda muna da hanya. Kuma harda na Humaira za a hada tunda abokinka Auwal ya nuna yana so itama tana so, sannan mun yaba da hankalinsa.
Shikenan Ummuna Allah yasa alkhairi. Bari na wuce gurin aiki sai na dawo.
Ameen Allah yayi maka albarka ka kula da kanka banda zama da yunwa nasan halinka.
Murmushi kawai yayi bai ce komai ba ya wuce zuciyarsa cike da damuwa har ya isa mota ya shiga driver ya jashi, escort suna biye dasu a baya. Akram ya lula duniyar tunani fuskarsa ta nuna damuwa sosai har wasu hawaye ne suke barazanar sauko masa, shi ba auren bane bai so kawai yana ganin in har aka yi hakan kamar lokacin tonan asirinsa ne yazo, amma bai da yadda zai yi dole ya yiwa iyayensa biyayya, tunda har ita Abidan taji ta gani ayi auren. Sai yaja guntun tsaki ya dauko wayarsa, ya kira Amir daya fito su dauke shi su wuce gun aiki ba sai ya dauki motarsa ba.
Bayan sun isa Akram ya sanar masa da abin da ake ciki kan batun aurensu, Amir yayi dariya harda tafi.
Wlh su Umma sunyi min dai dai gwara ka fara bude mana kofa. Shege Auwal wato dai da gaske yake zai dauke mana Humeme. Kai nima fa banda ina da wasu abubuwa a gabana da saina kwanto kura
Mutssss kai ka sani, yanzu mu aje wannan maganar mu yi magana akan aikin dake gabanmu.
Nan Amir ya aje shirmensa suka fara zantawa kan harkokinsu.
***** *****
Abuja....
Rahma ce
#Follow
#Vote
#Comment
#Share