Part 7
by @mrsjmoon
Dr. Laylah.
07
'Kina da babban aiki Ramla.' Wani shashi na zuciyarta ya bata amsa.
Tashi ta yi cikin diraba ta matsa ta jingina da jikin gadon yarda zataji dadin zama.
"Bayan dik abin da ya faru sai da Yaya Mahi ya kuma dagula komi, shin wai dama yasan yana... Bata k'arasa ba ta yi shiru cikin tunani tare da tsirawa agogo da mab'allen idanu.
" Shakka babu cikin Yaya Mahi da Yaya Deen wani yasan dalilin tafiyar 'yar uwata Laylah. To amma me sukayi mata? Kar dai a ce dik sun kasan ce da... Nan ma bata k'arasa ba ta girgiza kai " No! hakan bazai faru ba." Ta furta cikin furzar da iska tare da share gumin da ke tsats-tsafo mata a goshinta tamkar wacce ta hadiyi kunama.
'A da ina ganin tafiyata shi ne alkhairi amma yanzu na karyata. Zanyi ne ba dan wani manufa na daban ba.' Kalaman Deen na dazun suka dawo mata a brain ta kuma furzar da iska tare da shafo saitin zuciyarta dake harbawa da sauri da sauri.
Motsin tab'a k'ofa taji ta yi hanzarin zuba tarkacen a pose d'inta tare da daidaita fuskanta. Momy ce ta shigo ta zauna gefenta tana mai nazarin yanayinta.
" Me ke damunki Ramlah?"
" Baya da marata Momy suna matsamin da ciwo."
"Innalillahi! Tun tsawon wani lokaci suka soma?"
"Cikin kwanakin nan ne."
"Dole ki sami hutu dan haka maganar zuwa aiki babu sai kin haihu."
"Momy jama'a suna buk'ata na domin kula da lafiyarsu."
"Mu kuma muna buk'atar lafiyarki dana Baby dan haka bansan gardama dole ki sami hutu kuma zai fara daga yau anjima zansa Mamie ta dauko miki abinda kike buk'ata."
"Momy Allah zan iya aiki rashina a wurin zai iya kawo nakasu tunda kinga Yaya Deen a sati sau biyu ke shigowa ga shi Laylah ta dakatar da Dr. Bilkisu da Dr. Lere, ni ce kad'ai akan komi yanzu."
" Yau she hakan ya faru ban da labari?"
"Anjima da dakatar da Dr. Lere, Dr. Bilkisu ce bai wuce wata biyu ba."
"To akan me hakan ya faru?"
"Dr. Bilkisu dai sabida kanwarta Fatima, ta yi k'ok'arin yi mata rashin kunya a cikin jama'a shi ne ta hukunta kuma hukuncin ya shafi yayarta shi kuwa Dr. Lere ba zance ga abinda ya hadasu ba." Ta kai k'arshen maganar cikin nuna alamun b'oye dalilin.
"Ok in haka ne yazama dole Dr. Bilkisu da dawo bakin aikinta, anjima zanje gidan nasu na sameta shi kuma Dr. Lere idan na samu natsuwa zan bibiye abida ya hadasu sannan dole Saifuddeen ya koma aiki regular, Ishaq ma zai dawo aiki da ku dan ba ruwana da shiriritarsu shi da Saifuddeen abinda na sani ne dole su had'u dan kawowa asibitin ci gaba."
"Hakan ya yi Momy, ba dan ita ma Rahma taki karatun medicine ba da yanzu da ita ake taimakon al'umma."
"Ai ko yanzu tana bakin k'ok'arin ta ki duba irin cigaban da ta ke kawowa a L.L Company, ai ko namiji ke wurin iyakarsa kenan."
"Gaskiya tana k'ok'ari amma bisa jajircewar Yaya Mahi ne har ta zamo hakan." Ta ambata cikin murmushi.
"Da wannan kam kuma hakan ne ma na ke zaton ya burge Laylah har take son samun ilimi akan kasuwanci itama a dama da ita."
"Uhm Momy har yanzu baki gama sanin Laylah ba, tana son samun ilimin kasuwanci ne dan amsar ragamar companin a hannun Yaya Mahi wannan dalilin yasa kikaga Dady ya soma gina new company dan raba gardama dan ya san in har burinta ya cika da rigima."
"Ya Salam amma Laylah anji ja'irar yarinya."
Dariya Ramlah ta sanya ganin yarda momy ta furta maganar cikin zare idanu.
Ajiyar zuciya ta sauke ta dafa kafadun Ramlah ta kwantar da ita tana mai cewa "Bari in debo miki abinci dan har da rashin cin abinci zai iya harfarmiki da matsala irin haka."
Lumshe ido ta yi dan bata da zabin da ya wuce amincewa bukatun Momy sannan a zahiri yunwan ta ke ji amma son samo amsar dalilin barin Laylah gida ya shafe komi.
***
Zaune suke Mahi na cin abinci Saifullah ya zuba masa ido, d'agowa ya yi ya watsa masa harara.
" Malam ka da ka sa na kware."
Murmushi ya yi tare da sauke ajiyar zuciya ya ce "Yanzu brother idan da banzo ba ka sanme zai sameka?"
"A'a amma naso na mutu na huta da wannan rayuwa mai cike da takaici."
"Kayya brother ka da kace haka, ina maiyi maka nasiha da ka zamo cikin bayi masu nuna godiyarsu ga Allah ta hanyar karrama halittar ruhinsu da ya yi cikin addinin gaskiya sannan takaicin da kake ambata a rayuwarka k'arara nuna butulci ne ga Allah domin bayan ya sanyoka a cikin addinin musulinci sai ya yalwataka da lafiya tare da dukiya da mahaifa managarta son dikkan bil'adam a ce sun fito dagatsa-tsonsa irin taka, shin Allah da ya baka wad'an nan abubuwa to da me ya rageka a rayuwa?"
"Mata ta gari." Ya amsa tare da ture plate din abincin gefe.
"Uhm wannan ma son ranka ka fad'a."
"Har yau Saifullah ka kasa fahimta na ko da ya ke hausawa sunce Fahimta fuska, wata gila sai nan gaba zaka fahimci karatun da na ke sanarma."
Shiru Saifullah ya yi masa hakan ya bashi damar sanja cancen da cewa "Wai aina ka sami labarin ina nan kuma ta ina ka shiga bayan na kulle ko ina?"
"Sadda ta iso bakin L.L RESTAURANT muna tare da Dady shi ya nunamin kai kafin mu iso ka gansa ka gudu muka bi bayan ka ina ganin ka d'auki titin shiga cikin Dorayi sai na sa ki hanya kafin Dady ya gane na sanar masa da ka b'ace mana sabida na gano inda ka nufa, na mike kamar mai son gano inda ka nufa a k'arshe dai gida muka koma yana ta mita, bayan sallar isha'i na taho amma sai na samu gidan da kwado mai shagon gefen gidan na tambaya ya sanarmin lallai wanda ya shigo gidan ne ya kulle kansa ciki a take nanemi su bugemin kwadon bayan an buge, sai kuma ba hanyar shida dan ka kulle ta ciki da key sai d'aya cikin su ya haura ya bude k'aramin gate wanda akayi sa'a shi baka sanya key ba, na shigo na sameka a sume na kira twins brother ya zo ya daurama drip tare da allurai sai misalin biyun dare ya bar gidan zuwa asibiti shima dan yana da theatre ne amma da tare zamu kwana. Haka na zauna gadinka har zuwa subahi amma ba ka dawo hayyacinka ba sai lokacin da ka farka ka ganni."
"Ya rabbi wannan wani kalan cuta ne ya sameni kuma?"
"Deen ya sanarmin damuwa ce kuma ya soma tabama zuciya ga ulcer da ka ke da ita wanda sakamakon rashin mai da hankali a cin abinci kan lokaci ya haifar maka, ya ce in baka shawara da ka rage tunani sannan ka kula da lafiyarka ta hanyar cin abinci kafin kaji yunwa domin idan kana bari yunwa na kamaka sanann kaci abinci zaka rik'a fuskantan yawan amai da mugun zazzabi tare da ciwon ciki da na kirji kamar dai yarda suka matsa maka har ka fad'a doguwar suma."
Shiru ya yi cike da bakin ciki a dalilin wacce ke ganin ita din ba kowa bace fa ce abar kyama shi ne har ya shiga wannann halin tare da ciwuka masu wuyar magani.
"Mahi ka taimake mu ka fidda komi aranka ka da mu rasaka."
"Saifullah ta shi muje gida na gaji da b'uya kamkar wanda ya aika laifin kisan kai."
"That's good mutumina, hak'ik'a nayi farin ciki da amincewarka na komawa gida."
"To Saifullah idan na dauki wannan hanyar banjin zata fitar da ni hanya mai b'ullewa ba, gara kawai in fuskancesu ko da bazasu amince da bayanaina ba."
"Ballema na san zasu amince domin sun san kai din mai gaskiya ne mai fadin abinda ke ransa ne ko da hakan bazaiyiwa kowa dadi ba."
Da sauri ya kalli Saifullah sai kuma ya watsa masa harara ckin tare gira, murmushi ya sakar masa cikin girgiza kai, mik'ewa tsaye sukayi a tare wanda ya yi dai dai da karar wayar Mahi, ya duba ganin sunar da ya bayyana sai ya koma ya zauna yana jan hailala.
"Waye?"
"Fatima ce."
Tsaki Saifullah ya ja tare da barin falon, Mahi ya biyo bayansa da sauri.
"Dan uwa me yasa ka ke min haka?" Ya ambata lokacin da suka hau titi.
"Me na yi?"
"Dan na kira sunar Fatima bai kamata kayi tsaki ba alhalin kasan ita din ruhita ce."
"Har kwanar gobe bazan gaji da sanar maka cewa bana son ta ba, sam tarbiyyarta bai kwantamin ba sannan kai ba ajinta ba ne, rashin sanin ciwon kai ya sa zuciyarka mak'ale ma wacce taba can-canci a kalleta ba balle a furta mata kalmar so."
"Uhm ko?"
"Yes, dan abinda ka gujewa shi ne zai kuma manne mata wata k'ila ma yafi wancan na farko muni."
"Ya isheka Saifullah, ka barni inji da abinda ya dameni."
"Yo me ye nawa ciki? Tambayata fa kayi na baka amsa."
"Ko mi dai mutum zaiyi ya rik'a duba girman da Allah ya bawa halittan dan Adam sannan shi da kansa ya ce ba wanda yafi wani a wurinsa sai wanda yafi tsoronsa, kaga kenan cewa Fatima bata dace da ni ba wannan yiwa Allah shish-shigi ne."
"Ka san da wad'an nan jawaban amma ka ta ke ka aikata abinda muguwar zuciyarka ta d'oraka a kai?"
"Ina da hujja akan dik abinda na aikata."
"Hujjar rashin tabbaci ba."
"Saifullah dan Allah ka sauraramin, na gaji da jin zantukanka."
"To Mahi insha Allah na bar sa ke bari maganar ruhinka ya kuma hadamu balle ta danganta ni da aikin sab'ama mahaliccinmu."
"I beg you brother ka daina sanjamin manufar zancena please."
"Ban sanja maka ba ka manta cemin kayi inayiwa Allah shish-shigi."
"Oh ya rabbi wai yaushe ka koma haka, mai yawan mita?"
"Kai za ka soma amsamin wannan tambayar dan kai ne mafi da cewa da ayima tambayar domin halayyanka na kirki kaso tamanin babu su."
"Enough man!." Ya furta cikin daga Saifullah hannu a fusace.
"Angama Engineer." Ya furta cikin murmushi tamkar bashi akayiwa tsawa ba.
Tsaki Mahi ya ja tare da maida kai gefe yana mai jin ransa na kuma daukan zafi sannan sam bai jin son daukan kiran Fatima dik da yana kallon sai shigowa ya keyi, a karshema sai ya kwashe wayar ya cilla back seat, Saifullah ya kwashe da dariya tare da kunna cassette din begen manzon Allah S.A.W inda akeyi masa kirari cikin sunayensa masu daraja.
Suna isa gate d'in estate daidai ana kiran sallar magrib dan haka masjid suka zarce, bayan idar da sallah ba su fito ba bisa al'adan zuri'ar dik in an idar da sallar magrib basa barin masallacin sai sun sallaci isha'i sai ko bisa lalura babba za ka mutum ya fito bai jira lokacin isha'i ba. Yau ma hakan ta kasance ba wanda ya fita cikin iyaye da yaran sai masu gadi wanda ya zame musu dole su koma bakin aikinsu, kafin zuwar sallar isha'in, sai kuma al'umman da kanzo gabatar da sallah irin masu wucewa da makwafta.
Mahi ne ya tashi ya dauko Qur'ani a inda aka killacesu gefe d'aya cikin cabinet mai kyau. Ya dawo ya zauna kusa da Dady ya bud'e yana kallon Baba Alhaji ta gefen iso wanda bai nuna alamun yasan da zamansa ba, ahankali ya soma karanta suratul Namli cikin zuciyarsa ya yin da sauran suka maida hankali kan neman gafarar Allah batare da sun nuna alamun wani abu ga bayyanar Mahi d'in ba dik kuwa da sun zak'u da su yi ido hud'u da shi.