FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm a humble woman, I like interaction with people from different environment and it's a honor and privilege to make new friends with exposure for me to get a lots of experience, I'm one of novel reader since I was young and my dream is to be a great writer (author).
Sample · Part 2
Dr. Laylah.BY SAFIYYA (Mrs J Moon).02."Yi barcinki Hasken alkhairi, ke kuma fice kibata wuri ta huta, kina ta dariya kamar sauniya."Da sauri maryama ta fice tana cigaba da dariyar, ta samu kawayenta sun cika k'ofar Mama Zainabu, suna ganinta suka tareta, ta dubesu kamar zatayi magana sai kuma ta yi gaba suka rufa mata baya.Lumshe ido Laylah ta yi tana sauke numfashi amma sam barcin ya ki zuwa. Hannu ta dora saman forehead nata ta yi rigingine tana kallon rufin d'akin, mama da ke kallonta ta tab'e baki ta mike ta dauko wankakken bargo ta rufa mata tana cewa "Daure ki sami barci ko kya daina karanta wasikar jaki da ba zai kareki da komi ba sai janyo ciwon kai."Gyad'a kai ta yi batare da ta bude idanunta da suke lumshe ba."Na tafi in tama uwar Maryama sussukan gyeron yin fura da tuwon gobe." Mama ta furta batare da ta jira amswar Laylah ba ta fice. Ta shi zaune ta yi jin ficewarta, ta sakko...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.