HAFSATU MANGA (Yarinyar Kauye)
3
YARIMA ZAIN POV.
A hankali ya kai dayan hannunsa ya cire tsadadden agogon dake hannunsa ya bude drawer ya dauko box din agogon ya saka shi ciki ya mayar, sai kuma yai tsaye a gurin kamar wanda aka dasa a gurin, baya iya tantance yanayin da yake ciki a yanzu shi dai yasan ba farinciki yake ba, kuma ba bakinciki yake ba, indan sabo ya saba da kakkausar lafazi daga bakin Anty Ummi dan haka ko kadan kalaman basu sashi damuwa ba, duk kuwa da kasancewar basu masa dadi ba.
Amman yana jin kamar akwai abunda yake damunsa, yawun bakinsa ya hade ya nufi tagar dake bude yana kallon mutane da ke gudu suna fakewa daga ruwan saman daya fara sauka, hannayensa ya zuba cikin aljihu yana sauke ajiyar zuciya.
Haleema ce ta fado masa a rai, irin rayuwar da suke da zamantakewar aurensu yake tunawa, hakika ta nuna masa so kamar yadda yake nuna mata, bata taba musa masa akan wani abun ba ko da kuwa shine mai laifi, ta kanyi kokarin ganin ta gusar masa da duk wani bacin rai, ko da wasa bata taba daukaka muryarta akan tasa ba, idan yana gida kullum tana manne da shi.
“Ya Rabbi... ”
Ya furta yana busarda iskar bakinsa. Mafita yake nema mafitar da ba zai taba samu ba har abada!
‘Taya zai rayu da wata maccen wacce ba Haleema ba? Taya zai sabu da ita?’
Shine abunda ya tsaya masa rai, ya rasa ta yadda zai fahimtar da Mai Martaba da kuma Anty Ummi su fahimci halin da yake ciki, shi dai be san so ba sai a Haleema ya zurfafa irin zurfafawar nan da har yanzu da bata raye yake jinta a kusa da shi saboda tasirantuwarta a zuciyarsa.
Dada Yalwa ce kadai mace da har yanzu take tayashi jimamin rashin Haleema saboda ita kadai ce macen da take masa dukan gatan da yake so a duniyar har gobe, sam bata daukarsa Babban mutum kamar yadda sauran suke kallonsa ita a kullum kallon karamin yaro take masa saboda rayuwar maraici daya taso a cikinta. Shi kansa babu macen da take jin dadin sakewa da ita kamar ita da Anty Ummi, sai dai baya taba yardar yai sirri da ita saboda yasan Hameeda tana rabarta, kuma tana ma Hameeda kwatankwacin irin son da take masa kasancewarsu duka marayu, a zamanin yanzu babu wacce Yarima Zain ya tsana kamar Hameeda dan ko kallonta baya son yi.
Wayarsa ce tai kara hakan yasa shi dauke dubansa daga waje ya maida gurin da wayar take, yai second uku yana kallonta tana da ringing sannan ya soma takawa a hankali ya karasa inda take, irin takun nan da zaka za ci wayar zata tsinke kamin ya karasa. Ganin mai kiran bashi da muhimmanci sosai a gurinsa yasa yaki daukar wayar har ta tsinke daman yau baya cikin yanayi mai dadi. Daukar wayar yai ya saka a aljihu ya nufi kofar fita da irin takunsa na da ba zaka zaci na dagawa ne da nuna isa ko kuma tausayin kasar yake ji.
Bangaren Dada Yalwa ya nufa domin a can ne kadai yake samun ya sake a duk lokacin da yake cikin bacin rai da damuwa. Tunda ya doso sashenta hadimanta suke ta gaidashi sai dai ko daga kai be yi ya kallesu ba balle har ya amsa su.
A falonta Babu kowa sai sayin ac da kuma kamshim turaren wuta dake tashi, kai tsaye ya nufi Bedroom dinta daman yasan irin lokacin nan bata zama falo da zarar anyi magariba take shigewa Bedroom dinta sai kuma gobe. Yana dora hannunsa a kofar dakin da zimmar turawa ya bude, sai gabansa ya fadi for no reason, hakan yasa shi janye hannunsa ya juya.
“Yarima...”
Cak ya tsaya jin an kirashi da muryar da yafi tsana fiye da komai a duniyar nan. Be juyo ba kuma be amsa ta ba, daman tasan ba zai amsata ba, dan amsawa tana masa wahala, a duk fadin gidan Mai Martaba ne sai Dada kawai zasu masa magana ya amsa musu ba tare da bata lokaci ba, sukan wani lokacin ko kallon basu ishe shi ba.
“Dada tana ciki....”
Ta fada kamar mai shirin yin kuka, zuciyarta cike da son ya dawo ya shiga dakin na Dada Yalwa, amman sai ya cigaba da tafiyarsa kamar ba dashi take ba. Tsaye tai tana kallonshi har sai da ya fice daga falon gaba daya sannan ta juya ta koma dakin na Dada.
“Ya tafi...?”
Dada Yalwa ta tambaya.
“Ai daman ba zai shigo ba, tun da yaji muryata”
“Dan yaji muryarki sai yaki shigowa?”
“Amman Dada ai kin san yadda ya tsaneni ban san abunda na masa ba, ko kallon arziki baya min, yanzu ma dana masa magana ko kallona be yi ba”
“Wai mi yake damun yaron nan ne? Jeki kira min shi”
Har ta bude baki ta cewa Dada Yalwa ta aika wani sai kuma wata zuciyar ta hanata, juyawa tai ta fita tana ta tunanin irin yanayin da zata tararda shi, ba kasafai take son shiga part dinsa ba saboda hotunan da Haleema da take gani a falon wanda take tunanin a halin yanzu ya kamata ace ya manta da ita, tana ganin hotunanta ne suka dace a mazaumin na Yayarta wato margayiya Haleema.
Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka take tafiya har ta isa part din Yarima, ajiyar zuciya ta sauke yafi a kirga kamin ta ta kai hannu ta tura kofar falon ta shiga, kamar ko yaushe yau ma akan hotunan Haleema da suke manne a falon ta sauke idonta, ba shiri ta hadiye yawu da karfi sannan ta karasa cikin falon tana rabon ido, Karaf ta sauke idonta akan Yarima dake tsaye jikin freezer yana kallonta. Daga inda take tsaye ta isar masa da sakon Dada Yalwa ba tare data karasa kusa da shi ba.
“Dada na nemanka yanzu...”
Bata jira tace abunda zai ce ba ta juya daman bata tsammaci zai ce wani abu ba, da kallon tsana ya bita tana daf da ficewa ya kirata kamar wanda be san sunanta ba.
“Ke...”
Da sauri ta juyo tana hade yawu.
“Na'am”
Shiru yai kamar ba shi yai kiran ba, kuma ta san bata isa ta juya fmta fice ba yace ta masa rashin kunya.
“Kar Dada ta sake aikoki ki shigo part dina, bana son ganin abunda ya shafeki a part din nan...”
Ya fada bayan wasu dakiku, ta gyada masa kai idonta na cika da hawaye, sannan ya juya ta fice daga falon. Da gudu ta karasa part din Dada Yalwa saboda kukan dake son subuce mata kuma bata son kowa ya ga kukan sai wacce take shaye mata hawayenta.
A bakin kofar dakin Dada Yalwa sai ta tsaya ta hadiye kukanta hawayen ne kawai suke zirya a fuskarta, sannan ta kai hannu ta tura kofar dakin ta shiga.
“Ke miyasa same ki?”
“Yace ya tsanane baya son ganina karna sake zuwa part dinsa...”
“Zain din ne ya fada miki da bakinsa?”
Cewar Dada Yalwa cike da mamaki har tana gyara zamanta.
“Dada da ace mahaifiyata tana da rai ko? Da ban rayu a gidanan ba, da Zain be isa ya wulakanta ni ba har ya fada min wa ennan maganganun, Dada saboda ina karkashin kulawar mahaifinsa ne shiyasa yake wulakanta ni, yana min kallon kankanci kallon daya yake min da bayin gida nan....!”
Ta rushe da kuka tare da faduwa kasa jikinta na karkarwa kamar an mata mutuwa. Kibar Dada Yalwa be hanata saurin tashi ta nufi inda Hameeda take rusa kuka ba ta kamata, idan akwai abunda Dada tafi tsana a duniya be fi taga kukan Zain da Hameeda ba, ta tsana suyi kuka musamman akan maraici, hakan ba karamin kona mata rai yake ba.
“Akwai wanda ya isa yai ikirarin ke ba yar nan gidan ba ce? Mi kika nema kika rasa a gidan nan da har maganar Zain zata tada miki hankali? Shi kansa be isa ya nuna ya fiki gata a nan gidan nan.....”
Bata karasa ba sai gashi ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta koma kansa da masifar kamar ba dan lelen jikanta ba.
“Yaushe ka lalace har haka Zain? Taya zaka bude baki kayi mummuna furuci ga yar'uwarka? Idan baka sonta ai sai ka kasheta na gani ko? Wai mi yake damunka ne?”
Be ce mata uffanba, duk fadan da take kallonta kawai yake kamin ya maida dubansa gurin Hameeda dake kuka a hankali ganin shigowarsa.
“Ina jin gurin bakar matar nan da kake zuwa wannan Ummi ce take hure maka kunne saboda kazo ka tarwatsa gida nan dan nasan daman can ba son mu take ba, ai da ba haka kuke ba kuna shirinku amman tun da ta fahimci kana so Hameeda ta hure maka kunne tasa ka auro yar'uwarta yanzu kuma ya sake hure maka kunne ka dauki kiyayya ka dora maka ko? To baka isa ba”
Kallon Dada Yalwa Yarima yake idonsa a sake cike da mamankin kalamanta, shi wa taba cewa yana son Hameeda da har Anty Ummi zata shiga tsakaninsu? Ko dai Hameeda ce ta kitsa mata wannan maganar.? Be ankaro ba yaji tana kara wani furuncin cike da bacin rai.
“Wato iya gogaggiyar yar duniya ko? Sai ta koma can gefe ta rika zuga ka kana zuwa kana fada da yar uwarka ba gwaira ba dalili wato gata Professor gogaggiya”
Rumtse ido yai cike da jin dacin kalamanta sannan ya bude ya kalleta idanuwansa har sun soma sauya kala.
“Dada ki sassauta kalamanki akan Anty Ummi, bata wani buri a kan gidannan balle kuma har tai unkurin zige ni, Anty Ummi ba zata so abunda zai cutar da gidan nan ba ma balle kuma ni, Anty Ummi uwace a gareni kuma ita kadaice yar'uwata da na san zata fada min gaskiya komai dacinta kuma ba zata taba son na lalace ba ya kamata ki san da wannan Dada...”
Ya juyo gurin Hameeda yana nunata da yatsa.
“This is the best reason da zai sa na tsana abada, Dada ta aibanta min yar'uwa saboda ke, haka kike ma Haleema ko ki zo ki ce tayi abunda ba tai ba tana da kyaukawar mu'amala da kowa ban da ke...”
Yana kaiwa nan ya juya ya fice cike da bacin rai.
“Ee kasan ita wannan ba yar'uwanka ba ce daga sama ta fado, ko kuma tsintarta muka yi, kaji min yaro duk ita ce take hure masa kunne ita take kitsa masa komai annamimiya, ita ko damuwa bata yi da irin zaman da Zain yake yi tana nan ta kullafemu cikin ranta to Allah ya fita Wallahi, kinji har da kitsa masa wani munafurcin Haleema duk ita ce take hada ku...”
Cewar Dada Yalwa cikin fushi daman can Dada ta tsani Anty Ummi saboda gani take komai da Zain ke yi ita take saka shi.
*** *** ***
Cike da bacin rai Yarima ya kwanta saboda abunda ya faru, daman duk abunda ya aikata Anty Ummi Dada Yalwa take blaming saboda be da gurin zuwa sai can kuma be da abokiyar shawara sai ita. Wannan dalilin ne yasa be farka cikin walwala ba, as usual Masallacin fadar yai sallah asuba, sannan ya dawo part dinsa yai azkar din safe.
Around nine o'clock Abida ta kawo masa abincin safe wato breakfast, sai da ya shiga yai wanka ya shirya cikin kananan kaya ya shefe jikinsa da turare mai kamshin sannan ya nufi falon dan karyawa.
Dinning room ya zauna yana bude abinci, it's his favorite indomie da kwai da kuma kifi sai ginger tea da. Spoon ya dauka ya soma cin indomie sai kawai yarinyar daya gani jiya ta fado masa a rai, ya tuna jiya gaba daya a mafarkinsa yarinyar nan ce har ruwa yana dukanta, kuma yasan jiyan anyi ruwa maybe bata samu gurin fakewa ba tun da yaga gurin da take zaune ba inda zata fake har tana kukan yunwa.
Da sauri ya tashi daga cin abincin da yake ya koma bedroom ya dauki wayarsa da keys ya fice daga part din.
A al'adarsa baya fita daga gidan har sai yaje ya gaishe da Mai Martaba da kuma Dada amman yau saboda hankalinsa ya dauko yana fitowa ya nufi parking space, motarsa ya shiga yai mata key tun kan ya karasa Babban Gate ya soma horn, cikin rawar jiki masu gadin suka bude masa suna gaisheshi.
@360 ya hau titi, daga kan wurin sarkin zuwa gada biyu tafiyar 32 minute ce sai gashi ya isa cikin 18 minute saboda gudun da yai, a gurin ya fara tsayawa da motar ya bude ya fito hankalinsa duk a tashe sai a yanzu yake jin rashin kyautawar barinta a nan duk da be san ko wacece ba. Hangota kwance kamar matacciya yasa gabansa faduwa cike da sanyin jiki ya karasa kusa da ita.
Ba a jin tafiyarsa dan haka bata san da mutum ba sai da ta ganshi tsaye a kanta, cikin rashin kuzari ta tashi zaune tana shirin fashewa da kuka jikinta sai rawa yake. Dukawa yai yana kallonta kamar yadda itama ta sako masa manyan idanuwanta tana masa kallon tsoro, a hankali ya kai hannu ya taba ta so yake ya tabbatar idan mutum dince da gaske. Sai akwai ta gantsara masa cizo, da sauri ya janye hannunsa yana dan bude ido tare da kare mata kallo, yarinya ce karama da ba zata wuce shakara takwas zuwa tara ba, gashin kanta yai bujibuji kamar mahaukaciya.
Baya baya ta soma yi cike da tsoronsa.
“Ke ke ke ba cutar da ke zan yi ba”
“Ni ban yarda da kai ba...”
Ta furta cikin shagwaba da son fashewa da kuka.
“Ke listen....”
“Ni ba lesa ne sunana ba, kai mugu ne...”
“No no nono...”
Be karasa ba ta zaro ido.
“Kai dan iska ne ko? Ni bani da Nono”
Ta dafe kirjinta tare da fasa wani uban ihu, aiko ba shiri ya tashi tsaye da sauri ya bar gurin har yana shirin faduwa...