FreeArewaPen original
HAFSATU MANGA (Yarinyar Kauye)
- 1views
- 35chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Official Khadeeja Candy ✍🏻 Author • Entrepreneur CEO, Khadeeja Candy Store ☎️ •- ***
Sample · 1
A hakali ta sauko saman Motar fuskarta ɗauke da damuwa."Na gode"Ta furta murya ƙasa-ƙasa kamar mai shirin yin kuka. Dattijon da ta yi ma godiyar ya ciro wata tsohuwar naira ɗari ya miƙa mata yana faɗin"Karɓi wannan ki siye abinci"Sai da ta share hawayen da suka zubo mata sannan tasa hannu biyu ta karɓa tana masa godiya"Na gode Allah ya saka maka da alheri""Babu komai Allah yayi miki mafita"Cewar Dattijon, mutanen da ke cikin Motar suka amsa da"Amin"Sannan Dattijon ya tashi Motar suka hau titin unguwar Gada biyu, titin da zai sada su da tsakiyar birnin Gusau. Da kallo ta bi Motar itacen, hawaye na bin fuskarta, sai da ta daina hango Motar sannan ta maida dubanta gurin manyan gidajen da suke gabanta, wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da kuka mai ƙarfi, kukan da bata san ta ina yake fito mata ba, kukan da ba ta san ranar tsayawarsa ba, hawayen da babu mai share mata su, sai Ubangiji...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.