HAFSATU MANGA (Yarinyar Kauye)

5

by @khadeejacandy

Tsaye Anty Ummi ta samu Farhat kamar mai tunanin abunda zatai, kallo daya tai mata ta fahimci ba lafiya ba. Saman gadon Anty Ummi ta zauna ta cigaba da kallonta irin serious look din nan. 


“Miya faru?”


Zaunawa tai tana murza yatsun hannunta kamar ba zata ce komai ba. 


“Farhat kina tunanin aje wannan sirrin a cikinki zai miki amfani? Haka zaki yi tai zama ga ki da wata makama sai kokarin boya ko guduwa? Ranar da babu gurin guduwa kuma ya zaki yi?”


Hawaye ne suka fara mata zuba. 


“Anty idan na bayyana wannan sirrin kaina na tonawa asiri, babu wanda zai fahimce ni, kuma na san yaya bashir zai yi iya yadda zai yi ya wanke kanshi ni ya barni, kowa zai ce na masa butulci”


“Shikenan dan gudun kar a zageki sai ki zauna ki cutar da kanki? Kokarin lalata miki rayuwa yake Farhat? Wannan ba dan uwan kwarai ba ne, ya kamata Rukaiya ta san da wannan....”


Farhat tai saurin rika hannun Anty Ummi cike da tashin hankali. 


“A a Anty dan Allah karki fada mata, Wallahi ba zata fahimta ba, zata ce na yi ma mijinta kazafi ne kawai, kuma shi ma ya fada min duk na kuskura na fada sai ya wulakanta ni, Anty ina jin tsoro ya ce zai maidani kauye idan ban amince ba, kuma kin san ba ni da kowa a nan sai shi da Anty Rukaiya...”


“To ki fitar da miji ki yi aure mana, ki bar masa gidan”


“Anty ina kokarin haka, amman Auwal kullum na masa magana da kalar uzurin da yake kawo min, wai shi ya fi son sai ya shirya komai”


Ta karasa cikin kuka. 


“Wane irin shiri ne wannan? Shekara hudu yana neman aurenki ace be shirya ba har yanzu? Sai yaushe zai shirya?” 


Shiru tai sai kuka take rerawa a hankali. Anty Ummi ta kawar da fuskarta wani gefen tana tunanin yadda zata bullowa lamarin, sam bata ganin yin shiru zai magance matsalar dake tsakaninta da yayanta kuma mijin yar'uwata, sai dai kuma idan ta bayyana me zai biyo baya? Ta san duk yadda zata lurarda ita alfanun fadawa Anty Rukaiya ba zata gani ba a yanzu saboda tana tsoronta kamar yunwar cikinta kuma bata san wani irin kallo zata mata ba. 


“Yi hakuri, komai zai wuce insha-Allah”


Hannu tasa ta share hawayenta ta kwanta saman gadon Anty Ummi tana tunanin lamarin yayan nata, taya zata tonawa kanta asiri bayan tasan ita duniya zata zaga ace duk dawainiyar da yai da ita ta saka masa da wannan? A fuska ba kace zai aikata abu makamancin wannan ba, gashi yana nuna mata kulawa irin ta uba da da a gaban mutune to taya za a yarda da wannan? Anty Ummi ce kawai ta san wannan sirrin shima kuma saboda shakuwar dake tsakaninsu kamar ta yaya da kanwarta, ta kan zauna tai fira da Anty Ummi ba tai da Anty Rukaiya ba. 


 Tashi Anty Ummi tai ta fito falo zuciyarta cike da bachin rai, haka ta ke a duk lokacin da ta tuna da lamarin. Plate din abinci kawai ta hango a tsakiyar falon gurin da Hafsat ta zauna amman babu ta, Zain kuma na can karshen falon makkale da waya a kunnensa da alama waya yake da wani. Kamar zata tambaya ina yarinyar tai sai kuma ta share ta karasa gurin plate din zata dauka ta hango Hafsatu rabe gefen cushion tana lasar ragowar toothpaste din data zuba mata dazu ta aje ragowar saman kujera. Tsawa Anty Ummi ta saka mata har sai da ta razana ta jefar da shi ta mike tsaye. 


“Wai ke wace irin yarinya ce miye abun dadi da zaki dauki man goge baki kina sha, daga wane kauye kika fito??”


Juyowa Zain yai tare da wayar a kunnensa yana kallonsu hankalinsa ya dauku sosai akansu. 


“Dan Allah kiyi hakuri Wallahi ba zan kara ba” 


Ta fada cikin kuka jikinta har rawa yake.


“Wuce ga bandaki can ki wanke hannunki wawuya kawai”


Da sauri Hafsatu ta nufi bathroom din data shiga dazu tana dingishi, jikinta sai bari yake tana waigen Anty Ummi, abunka da mai shegen tsoro. Dukawa Anty tai ta dauke plate din ta kai kitchen. Zain ya bi bayanta bayan ya saka wayar dake hannunsa aljihu.


“Anty ban san ki da wannan zafin ran, duk kin firgita yarinyar nan” 


“Baka ga abunda tai ba ne”


“Na gani amman idan kin lura yar kauye ce kuma bakin san iya kauyen data fito ba, beside hari aka kai musu bakinsan iya yawan mutane da aka kashe musu ba, maybe duka iyayenta sun mutu, you're working with Human Rights, you know the rules ba haka ya kamata kiyi treating dinta ba, yarinya ce karama”


Iskar dake bakinta ta busar tana wanke hannunta a fonfo.


“Na sani kawai dai raina ne a bace?”


Ya mata wani kallo mai alamar tambaya. Ta rage muryarta sosai gurin fadin. 


“Zain yarinyar nan tana cikin matsala, ban san yadda zaka fahimta ba, amman ya zaka ji idan aka ce maka yaya yana neman kanwarsa?”


Kafadunsa biyu ya daga irin be sani ba. 


“Farhat nake magana, mijin yayarta yake nemanta...”


Ya dan tabe baki kadan yana kallon wani gurin kamar mai nazari, ya saba jin abubuwa kala kala like uba ya nemi yarsa da yai ma uwarsa fyade so wannan be wami bashi mamaki ba. 


“Muna cikin wani yanayi da komai aka ce zai faru ba ba zai ba da mamaki ba, kuma kin san mutum shi yake bada damar a nemesa din”


“Ban gane ba?”


“Anty ki dube ta mana, tun daga kan suturarta ai kin san bata da tarbiya, akan me zata rika saka matsetse kaya bayan tasan tana zama gidan ko da yayarta bata nan? Look at her gashin doki fake eyelashes all in the name of wayewa, yarinyar nan ban taba ganinta da hijabi ba duk zuwan da take gidan nan”


“Saka Hijab ba shine har a zuci ba Zain, akwai mata da yawa masu saka Hijab amman zuciyarsu babu komai sai cuta da kasanta, zan iya maka rantsuwa Farhat ba yar iska ba ce kawai dai zaman abuja ne ya maida ita haka bata daukar Hijabi da daraja ko kuma ta rufe jikinta ko da da Veil ne, saka matsentsen kaya yanxu kuma ai ya zama ruwan dare, so karka zargi yar mutane akan wannan”


“Amman yayarta ta sani? Miyasa bata fada mata ba ita kanta akwai abunda ta kullafa a zuciyarta”


“Kawai dai tana tunanin yadda yayarta zata kalli abun ne, kuma tasan za a ce ta ci amanarta ta dauko ta tun tana primary school har ta gama Jami'a a hannunta, amman ni zan samu yayarta a yau na fada mata za ayi tai ta kare, idan ma ya kama a kai shi kotu am willing to do it”


Zain be sake cewa uffan ba, ya juyo yana kallon agogon hannunsa ya fito daga kitchen din, bathroom din da hafsatu ta shiga ya nufa ganin har yanzu bata fito ba. Sai dai yai knocking sannan ya tura kofar bathroom din, zaune ya sameta kasa ta hada kai da guiwa sai kuka take. 


“Ke... ”


Ta dago ta kalleshi hancinta da majina shabeshabe. 


“Ban ga ruwan wanke hannun ba”


Ta fada cikin kuka kamar zata shide, be ce mata komai ba ya kai hannunsa ya kunna mata fanfon bathroom din sai ga ruwa ya zubo da karfi, tasowa tai ta tara hannunta ta wanke, tissue paper ya zara ya mika mata, ta kai yai mata alamar ta share majinar dake hancinta. Ba musu ta karba ta share sai ta jefar da ita inda ta hango ruwa na wuce, shi dai baya jin zai iya mata magana dan haka ya juyo ya fito sai ta biyo bayanshi. 


“Zaka kai ni gida?”


Ta tambaya cikin kuka tana ta rabon ido ala ala take kar idonta ya hango Anty Ummi dan ta tsorata da ita sosai. Bata ma tsaya jiran abunda zai ce mata ba ta nufi kofa da sauri tana dingishi, kokarin budewa ta shiga yi amman ta kasa sai kawai ta saka kuka. 


“Mi aka miki na kuka kuma?”


Anty Ummi data fito yanzu ta tambaya tana gyara rikon jakarta. Juyowa tai da sauri


“Gidanmu nake so”


Murmushi Anty Ummi tai mata. 


“Ke kwantar da hankalinki ni ba wani abun zan miki ba, yanzu zan biya dake gurin yan sanda nai report sai mu dawo gida ki zauna kamin ki gane yan'uwanki”


“Dan Allah karki kaini gurin yan sanda ina tsoronsu sosai”


“Ba zasu miki komai ba, kawai dai zan fada ne saboda asan inda kike ko da yan'uwanki sun zo nemanki”


Hafsat ji tai kamar ta dora hannu saman kai ta kurma ihu saboda taji an kira yan sanda, a duniya ko mutuwarta bata tsoro kamar yadda take tsoron police. Hawaye kawai suke mata zuba ta ko'ina duk tayi fuskar tausayi a iya tunaninta idan an kaita gurin police kasheta zasu yi. 

  A hankali take girgizawa Zain kai alamar no bata son zuwa hawaye sai zuba suke mata, tausayinta ne ya kamashi duk da yadda Anty Ummi ba wani abun zat mata ba, amman be da tabbacin da gaske station din kawai zata kaita yasan halin Anty Ummi zata iya kaita can ta barta ko kuma ta kaita sansanin yan gudun hijira dake nan gusau. 


“Anty Ummi da kin barta har zuwa gobe, yarinyar nan ko lafiya bata isheta dubi kafanta ki gani dinshigi take”


“Zain yanzu fa ba a yarda da mutane bamu san ko wacece ba, anjima yarana zasu dawo daga school kuma dole zasu yi hulda da ita kasan they are very friendly, ban san wacece ita ba”


“Ba zata cutar da ke ba, taimakonki ma take nema”


“Taya aka yi ka sani”


“Zuciyata ta natsu da yarinyarnan da ace bata kwarai bace jikina zai bani haka”


“Ni aiki zanje kai ma aiki zaka je wa zai kula da ita?”


“Ba wannan yarinyar tana nan ba” 


Fada yana kallon bedroom din Anty Farhat tasan da ita yake, bata ce masa komai ba, ta ta bude kofar falon ta fita ba dan ranta ya so ba, dan ita sam hankalinta be kwanta da Hafsat hundred percent ba. Bayan ta wuce Zain ya karaso kusa da Hafsat ya risina yana kallon fuskarta dake dauke da hawaye. 


“Mama ba za'a je gurin yan sanda ba, nan zaki zauna har gobe, yanzu kin ga zanje aiki idan na dawo zan duba miki kafarki kinji?”


“Aa ni ban ji ba, ba zan zauna nan ba”


“Ina zaki je?”


“Kin san hanyar gidanku?”


“Aa kai ka kaini mana”


“Kin taba ganina gidanku?”


Ta girgirza kai. 


“To ya za'ayi na san gidanku?”


“Kai ai kato ne zaka iya tambaya amman ni karama ce mutane ba zasu kula ni ba”


“Okay yanzu dai ki zauna nan zanje na dawo sai na kai ki gida”


“Da gaske?”


Ya gyada mata kai


“Ka yi alkawari?”


Nan ma kai ya sake daga mata, ya mike tsaye.


“Je can ki zauna ga tv can kiyi kallo”


Ya nuna mata can tsakiyar falon, kin tafiya tai ta lake kafada tana son fashewa da kuka, be bi ta kanta ba ya bude kofar falon ya fita. Kamar jira take ya fita sai kawai ta rushe da kuka ta zube a gurin tana barar baki. Hakan yasa Farhat fitowa da sauri ta doso inda take tana kallonta. 


“Ke lafiya?”


Sai tai shiru bata ce komai ba, ta koma can bayan kujerar dake kusa da kofa ta labe tana kukanta a hankali. Kitchen Farhat ta nufa zuciyarta a cinkushe, bata samu komai a can ba, hakan yasa ta dawo dinning, ta hada ma kanta tea ta sha tare da plantain, bata wani ci abinci sosai ba sai dai ta shanye tea duka sannan ta tashi ta dawo saman cushion ta zauna.


“Ke matar nan zo ki bude min kofar nan?”


Wata muguwar harara Farhat ta watsa mata, sai tai saurin labewa ta fashe da kuka. A dole tasa Farhat ta taso ta bude mata kofar cikin rawar jiki ta ja kafarta mai dingishi ta fice, Farhat ta maida kofar ta rufe. Sauri ta shiga yi kamar zata tashi sama, burinta kawai ta fice daga gidan, tana kawai bakin gate Malam Adamu ya tareta. 


“Ina zakije?”


Tai shiru tana kallonsa. 


“Wannan.... Wannan matar ta gidan can tace na fita waje na dauko kayana”


“Ina kayan ki suke?”


“Suna waje... Can baya”


Be sake ce mata komai ba, ya bude mata gate din ta fita ya maida ya rufe. Kamar wacce ta sato wani abu haka ta rika gudu tana waige waige gani take kamar wani zai biyo bayanta ne, hankalinta be kwanta ba sai da ta fita daga layin gaba daya ta kama hanyar babban titi sannan ta soma tafiya a hankali, hango wani layin da ba mutane sosai yasa ta doshi can dan bata san inda zata je ba, zata karya kwanar layin wata motar data fito daga layin da gudu ta kwasheta sama ta jefar gefen hanya. Cikin tashin hankali mai motar dake sanye da police uniform ya taka burki ya fito da sauri yana fadin. 


“Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un”


Wani irin ihu Hafsat take irin na fita hayyacin nan tana wani kakkafewa kamar zata mutu, kan kace kwabo gurin ya cika da jama'a, a kidime mutumen dake sanye da kayan yan sanda ya dauki Hafsat ya saka ta a motarsa yana tambayar samarin. 


“Dan Allah akwai wanda ya san gidansu a nan?”


Kowa yace be sani ba. 


“Mutum daya ko biyu cikinku dan Allah zai bini muje asibiti”


Ba musu wasu samari biyu yan layin suka shiga motar shi kuma yaja suka nufi wata private hospital. 


FARHAT POV. 


Bayan fitar Hafsat Farhat taji bata da natsuwa abun duniya duk yabi ya isheta, ta rasa abunda yake mata dadi a duniyar, zuciyarta kuma na kwadaituwa da son jin daga sahibinta Auwal gashi kuma wayarta na gida. 


A gogon falonnta kalla sha daya da rabi, ta san a zuwa yanzu Ya Bashir ya wuce gurin aiki, sai dai zai iya rufe gidan ya kyaleta A waje, idan kuma Anty Rukaiya ta dawo bata sameta a gidan ba, bata san abunda zata ce mata ba, har ta mike tsaye sai kuma wani tunanin ya zo mata, sai ta koma ta zauna. 

 Haka ta cusawa kanta tunani kala kala har lokacin dawowar su Amal yai daga makaranta, sannan ta tashi ta nufi dakin Anty Ummi ta dauji aka Hijab din ta saka tana fitowa falo ta samu Zain tsaye rike da hannun Ahmad.


“Ina yarinyar nan take”


Ya tambaya yana kallon Farhat. 


“Kuka tai tace a abude mata kofa na bude mata ta fita”


Wani wawan kallo ya watsa mata, cikin wani irin bacin rai ya katsa mata tsawa. 


“Saboda baki da hankali? Yarinyar da bata san ko ina ba zaki bude mata kofa ta fita? You're very stupid Farhat, ke wace irin wawuya ce”


Kasa daga ido tai ta kalleshi balle ta mayar masa da bakar maganar da yake mata, sai kawai ta nufi kofa ta fice tana rama abunda yace mata a zuciyarta, cikin mugu bacin rai ta nufi nasu gidan, tasan by this time yaran Anty Rukaiya ma sun dawo daga makaranta. Tana isa gidan school bus na aje su a gakin gate.


“Anty Farhat fita kika yi?”


Abdallah ya tambaya yana kama hannunta Faruk kam tuni ya kunna kai harabar gidan.


“Eh gidan Anty Ummi naje”


Ta amsa mishi cikin rashin dadin rai. Dan ita kadai tasan abunda yake damunta. Tare Faruk ya rigasu shiga falon kasancewar yana gabansu ne ita da Abdallah ne a baya. Suka shiga suka cire school bags dinsu suka nufi dakinsu, ita kuma ta nufi nata dakin gabanta sai faduwa yake dan ganin take kamar Ya Bashir na ciki har yanzu. 


Ko da ta shiga ta samu wayartana ringing, ai dai kamin tai karasa kusa da wayar kiran ya katse, daukar wayar tai ta cire ta key, miss calls din data tarar ya mugun bata mamaki, na Auwal guda biyu sai kuma na kawarta Jawahir da kuma na Fatima. 

 Kiran Auwal yafi ko wane kira a gurinta muhimmanci, dan haka shi ta fara kira tana kokarin gusar da damuwarta dan bata son ya fahimci halin da take ciki. 


“Hello Baby na”


Wani sanyayar ajiyar zuciya ta sauke kana ta amsa cike da jindadi. 


“Na'am Pure heart ya kake?”


“Lafiya amman ba lau ba”


“Lafiya miya faru?”


“Wallahi ina saurin zanzo gidanku na samu accident”


Gabanta ya fadi a take hankalinta ya tashi. 


“Subhanallahi Allah yasa dai ba ka jimu ba kana ina yanzu? Amman babu abunda ya same ka ko?”


“Ni ban yi komai ba amman yarinyar dana kade tana asibiti, itama kuma da sauki”


Lumshe ido tai ta sauke ajiyar zuciya. 


“Al-hamdulillah Allah na gode maka daka tsare min mijina, idan Anty ta dawo zan kiraka sai mu zo dubata wane asibiti ne, amman da gaske ba ka ciwo ba ko dai boye min kake ne?”


“No ba sai kun zo ba, nima anjima kadan zan zo ki ganni saboda hankalinki ya kwanta”


“Da ka barni na zo hankalina zai fi kwanciya”


“Trust me Baby anjima zan zo Wallahi ban ciwo ba”


“Okay take care of yourself for me”


“I will i love you”


“I love you too”


Ta aje wayar ba dan ta so ba, be dace tai masa maganar aurensu a yanzu ba duk kuwa da kasancewar ta so yin haka amman wannan maganar hadarin ya shafe komai. 

  Jawahir ce number ta biyu data kira bayan ta Auwal, ringing daya Jawahir ta daga muryarta a raunane.


“Farhat kina ina? Na zo gidanku aka ce baki nan”


“Ina gida lafiya waya ce bana nan?”


“Mai gadinku, Dan Allah farhat ki kwantar da hankalinki ki dauka haka Allah ya kaddara miki, a rayuwa ba zaka taba samun abunda kake so ba hundred percent dan Allah karki saka abun nan a ranki”


“Miya faru ne ni fa ban gane ba”


Jin hakan yasa Jawahir ta kashe wayar, kiranta na katsewa sai ga na Fatima ya shigo kamar cikin shakku Farhat tai picking call din. 


“Farhat”


“Na'am Fatima”


“Dan Allah Farhat ki kwantar da hankalinki karki taba nuna masa damuwarki, na san duk wani rashin kyautawa Auwal yai miki shi kuma sai Allah ya isar miki, kuma Wallahi wannan auren ba zai yi karko ba tunda akwai cin amana a ciki”


“Ni fa ban gane abunda kike magana akai ba, mi Auwal yai?”


“Baki hau online ba ne? Ki hau online yanzu zaki ga komai”


Cikin sauri Farhat ta kashe wayar, ta kunna data ta shiga whatsapp, sai da sakwanni suka gama shigowa sannan ta samu damar bude wanda Fatima ta turo mata. Pre-wedding picture ta fara cin karo da shi na Auwal shi da wata kyakkyawar budurwa, har kusan guda shida sai kuma iv aurensu. 

 Kallon hoton take kamar ance mata rayuwarta na ciki, hawaye dake zuba a idonta ya jika screen din wayar, jin tai duniya na juya mata kafafuwanta suka kasa daukarta sai gata ta zube kasa zaune ba tare da ta san a kasa take zaune ba. 

  Ta kasa yarda Auwal din ne ko wani mai kamarsa? Amman kuma sunansa ne da na babansa a iv, to ko dai su twins ne? 


“Farhat.... Farhat”


Taji kiran da Anty Rukaiya ke mata kamar daga wata duniyar dan jinta ya soma karanci, mikewa tai tsaye sai ta jita kasa, ta sake mikewa ta jita kasa. Ginin dakinta rika ta mike tsaye a karo na uku ta riko kofar ta samu ta tako rike da wayar ta kawo bakin kofar a daidai lokacin Anty Rukaiya ta kawo bakin kofar. Tassss Anty Rukaiya ta kifa mata kyakkyawan mari a fuska tana huci. Mutuwar tsaye Farhat tai wayar dake hannunta da subuce ta fadi kasa.