HAFSATU MANGA (Yarinyar Kauye)
6
Zaunawa yai saman kujera ya dafe kansa, sam be jidadin tafiyar Hafsat ba, yasan bata da gurin zuwa kuma bata san ko ina ba a garin nan bayan haka kuma gata yarinya karama.
“Uncle wacece ta tafi?”
Amal ta tambaya tana kama hannunshi, dagowa yai ya kalleta kamin ya bata amsa Anty Ummi ta turo kofar falon ta shigo tare da sallama.
Yaranta ne suka amsa mata suka je da sauri suna mata oyoyo ita kuma ta rumgume su fuskarta dauke da murmushi.
“My headache an dawo ko?”
Duk suka hada baki gurin cewa
“Yes Anty Ummi”
A hankali Zain ya juyo ya kalleta, sannan ya mike tsaye ya karasa bakin kofar inda take tsaye.
“Wai mahaukaciyar yarinyar nan ta bude mata ta fita”
“Farhat?”
“Ita”
Yana fadar hakan ya kai hannu ya bude kofar falon ya fice ba tare da ya kara cewa komai ba.
“Zain kana son ganin laifin Farhat Wallahi to idan bata bude mata ta fita ba ya zata mata”
Ta fada cikin yanayin damuwa, sannan ta nufi bedroom dinta Amal na biye da ita a baya, Ali da Muhammad kuma suka nufi kitchen dan neman abunda zasu ci.
Ya samu kansa cikin yanayin damuwa sosai, yasan ko ya kansa a neman yarinyar nan be san inda zai ganta ba. Wani haushin Farhat yaji ya karu a ransa, duk ita ya dorawa laifi, kamar marar lafiya haka ya isa Kanwurin Sarki, tun daga bakin babban gate fadawa keta gaisheshi amman be kulasu ba har ya faka motarsa a babban kofar Mai Martaba, ya dade zaune cikin motar sannan ya bude ya fito ya nufi babar hanyar da zata sadashi da fadar mai martaba, a iya saninsa Mai martaba na fada yanzu dan yana shiga fada a duk Monday a daidai wannan lokacin gashi kuma dazu ya fita be gaishe ba da dada, dan haka ya kamata a yanzu ya shiga ya gaishe shi kamin ya karasa sashen Dada, tun da ya hango kofar fadar a kunne abun ya bashi mamaki, kawar da kwankwanto yasa ya kai hannu ya taba kofar fadar, sai ya samu kofar a kulle, hakan ya sashi fitowa gaba daya ya dawo ya zagaya ya mike doguwar hanyar da zata sadashi da cikin gidan.
Duk gaisuwar da ake masa be ji ba saboda hankalinsa baya gurin, ko da ma yana gurin ba zai amsa ba dan be saba amsa gaisuwarsu ba. Tsakar gidan katon tsakar gidane mai cike da shuke shuken fulawoyi, an kawata jikin ginin da fanti fari sai aka kawatar tsakiyar da fenti golden mai haske da sheki, kowa da part dinsa gate ya raba su, daga gefen gate dinsu akwai wani gate na bayi da ma'aikatan gidan, daga bangaren hagu kuma akwai sashen da ake dafa abincin gidan na kowa da kowa, dama da kau kuma babban hanya ce da zata sadaka da sashen mai martaba.
Bangare Hajiya Hadiza ya fara shiga katsancewar ita ce uwargidan mai Martaba, Sisters din ya tarar a cikin falon, cikin girmamawa da mutumci suka gaisheshi, be amsa musu ba kasancewar daya bayan daya suke gaisheshi, sai kawai ya ce
“Ina Hajiya?”
“Bata nan sun fita tare da Mama da kuma Dada Yalwa da Mai Martaba”
Rafila ta amsa masa
“Gurin me?”
“Gurin gaisuwa, wani kauye wai Yayan Hajiya dake sarautar garin aka kashe”
Juyawa kawai yai ya fice, hannayensa zube cikin aljihu, yana takawa a hankali har ya fita daga sashen gaba daya, part dinsa ya nufa kai tsaye yana ciro wayarsa dake ringing a aljihu, yai parking ya kara a kunne amman ya kasa magana kamar ba babban abokinsa ne ya kira shi ba.
“Zain kasa muna da tiyata uku da rabi fa kuma ka fita yanzu”
Sauke wayar yai a kunnesa ya katse kiran, a duniya ya tsani a tuna masa abu, ko da kuwa ya manta din ne balle kuma ba kasafai yake yawan mantawa da abubuwa. Keys yasa ya bude kofarsa, idan zai fita baya rufe janyowa kawai yake amman idan ya dawo sai ya bude da keys. Yana saka kafarsa cikin falon wani dadadden kamshi ya daki hancinsa, abun mamaki an gyara komai na falon an cire hotunan matarsa.
Dada ce kawai take da keys din part dinsa, idan ma za a masa gyara a hannunta ake karbar keys a bude dakin, bacin ran dake cikin ransa ne ya karu, har ya soma jin numfashinsa na taushewa.
Freezer ya nufa ya bude ya dauko gorar ruwa ya bude marfin ya kafa gorar a baki be sauke ba sai da ya shanye ruwan cikin gaba daya, sannan ya rufeta ya nufi kitchen ya jefata a kwandon shara.
Miyasa Dada Yalwa zata masa haka? Saboda yai fada da Hameeda ko kuma saboda yau fita be gaisheta ba? Ko kuma tana nunanin ganin hoton Haleema ne ke sakashi yin fada da Hameeda.
“Ban ga dalilin da zaisa ki dauke min hoton Mata ba Dada”
Ya fada a haka kamar mai rada, kana ya sauke ajiyar zuciya kallon windows kitchen din. Ya dade a tsaye kamar sannan ya juyo ya nufo bedroom yana cire yellow T-shirt din dake jikinsa, sannan ya daurawa tawul ya shiga wanka. Be wani dade ba ya fito ya shirya cikin wasu kananan kayan ya fito da sauri dan lokacin shiga tiyarsu ya kusa.
Be shiga wata motar ya shiga wacce ke part dinsa ba wacan ta dazu ba, a gagauce ya fita daga gidan, ko kadan baya son saba dokar aikinsa, yakan kiyayen duk abunda ya shafi aikinsa saboda yasan muhimmancinsa. 3:20 ya isa asibitin, a gurin sa aka tanada ma manyan likitoci su aje motocinsu ya faka motarsa. Sannan ya fito ya nufi cikin asibitin.
“Allah ya taimaki Doctor”
Wani mutun dake fitowa daga Emergency ya fada yana masa irin gaisuwar nan ta girmamawa. Sai a lokacin hankalin Zain ya kai gurinsa.
“Sadiq me kake a nan?”
Ya fada sanin mutumen da yai dan unguwarsu su Anty Ummi.
“Wallahi wata karamar yarinya wani mutum ya kade shine muka raka biyo mutumen nan saboda ba a san kowa nata ba”
“Ayyah Sorry Allah bata lafiya, zan shiga tiyata”
Ya fada yana kokarin wuce, dan hankalinsa gaba daya yanzu yana gun tiyatar da zasu shiga.
“Okay Allah yasa ayi a sa'a”
Ya fada cike da girmamawa.
FARHAT POV.
“Marar mutunci bulutu, ai daman na san ba so na kike ba tunda uwarki ma ba sona take ba, yanxu duk hallacin da Bashir yai miki ki rasa da abunda zaki saka masa sai wannan? Idan ma da gaske ne miyasa baki zo kin same da maganae ba, sai kije xan wani guri kina fadar sirrin gidana, daman haka kuke da Ummi shiyasa baki da gurin zuwa sai can ko?”
Faduwa tai zaune, idonta ya rufe ruf bata ganin komai saboda hawaye. Kalma daya ta Anty rukaiya bata shiga kunnenta bata ganin komai sai pre-wedding picture din Auwal da wannan yarinya.
“Munafuka ai daman ya fada min, komai game da ke duk abunda kike masa yana sanar da ni na zuba miki ido ne kawai naga iya gudun ruwanki, yar iska kawai wato an kawo ki kin sha jar miya kin waye ko? Shine kike son hada ni da miji ni ki kashe min aure ki gina taki rayuwar, to Wallahi bari kiji na fada miki baki isa ba, kuma ki hada komai naki ki bar gidan nan tun kamin ma ya dawo, jaka kawai”
Ta karasa tana jan wani mugun tsaki, ta juya a fusace ta fice. Hannu Farhat takai ta share hawayenta ta dauki wayarta ta saka password ta bude wayar, number Auwal ta lalubo har zata aika masa kira sai kuma ta kasa ta fashe da kuka. Ta kai minti talatin tana ta kuka sannan ta unkura ta tashi tsaye ta dauki Hijab din Anty Ummi da tazo da shi ta saka ta fito falo rike da wayar.
“Gidan uban waye zaki? Ba nace ki hada kayanki ki bar min gida ba? O... Gidan Ummi zaki koma ta sake kullo munafurcin ta sake iskoni office ko? Koma ki hado kayanki koma”
Ta turata da karfin ta koma dakin. Sai a lokacin hankalin Farhat ta fara dawowa jikinta har ta soma tuna maganganun dazu da tai mata, kayanta ta shiga hadawa sai kuma ta kasa, jin tai bata bukatar komai a yanzu , duniyar ma idan za a rabata da ita tana farinciki dan ita yanxu bata san wane irin hali take ciki ba.
“Mama... ”
Ta furta cikin kuka tana jin mugun son mahaifiyarta kusa da ita. Tashi tai da sauri ta dauki jakarta ta ratayawa ta fito daga dakin.
“Ai kin san nan ba gidan ubanki ba ne ko?”
“Tafiya zan yi Anka zanje yanzu Anty”
Ta fada cikin kuka, bata tsaya jiran abunda Anty Rukaiya zata sake ce mata ba, ta nufi kofa hawaye na bin fuskarta kamar ba gobe.
“Kara ma ki zo ki kwashe kayanki dan ni ko an dawo an bani hakuri ba zama zanyi da ke ba, makira kawai tsohuwar yar iska”
Babu irin tambayar da mai gadi be mata ba, amman bata ma kula shi ba balle ta masa shi. Tayi sa'ar samun napep a bakin gate.
“Babbar tasha zaka kai ni”
Ta fada tana kokarin tsagaita hawayenta, sannan ta shiga Napep din.
“Hajiya lafiya dai”
“Ba komai”
Tunda ya kama hanya be tsaya har sai da suka isa Babbar tashar gusau.
“Ina zamu ki je Hajiya”
“Anka”
Ta furta tana hadeye kukanta. Da gudu masu tarbon mutane suka biyo Napep din suna tambayar inda zata je, mai Napep di ya amsa da Anka, sai suka nuna masa inda motar Anka take. Dari biyu ta mika masa bayan ya aje ta kusa da inda zata shiga motar anka din. Gabanta ne ya shiga faduwa tambayoyi nata zuwa mata a rai kala kala, ta samu damar yin kukanta ishasshen a cikin motar kasancewar ita ce ta farko kamin a samu wasu Passengers, sai biyar da rabi suka kama hanya Anka domin direbobin basa son tashi sai mota ta shiga, duk irin kiran da Jawahir take mata sai taki dagawa sai kuka take har passengers din suka fara tsarguwa wasu kuma suna tunanin ko mutuwa aka mata ne.
Tunda suka kama hanyar garin kowa yake ta addu'a saboda sanin matsalar garin ta matsalar tsaro, Farhat kan bata komai sai kuka, har suka kai Mayanci, suna karawa gaba kadan suka ango wasu motocin an tsayar dasu a gefe sun danji tsoro sai dai ganin mutanen sanye da kakin soja yasa hankalinsu ya kwanta. Sai da suka karasa daf da su sannan suka gane cewar ba sojoji ne ba, fulanin nan ne na daji masu kashe mutane suka sanya kayan sojojin suna dauki da mugaye makamai. A take suka fitar da kowa dake cikin motar suka sa su kwanciya a gefen hanya, cikin har da Farhat dake kukan da zame mata na bakar rana.