HAFSATU MANGA (Yarinyar Kauye)

8

by @khadeejacandy

HAMEEDA POV.


Kamar kullum yau ma gaban window take tsaye tana kallon harabar gidan da kuma masu kai da kawo a harabar. 

 A zahiri harabar gidan take kallo, amman a badini, hankalinta yana wani gurin ne daban, dalilin da ya sanya Zain ya juya mata baya take nema, irin rayuwar da suka yi a gidan take tunawa, ta yi marmarin irin kulawar da yake bata a baya, tana kaunar zaunawa da suke suna fira da juna. 

 Amman komai da canja mata? Mutumen da a duniya yafi kowa tsanar ganin hawayenta a yau shine yake kwadaituwa da saka ta kuka, mutumen dake kokarin yaye mata damuwarta a yau shine damuwarta take sashi farinciki. 

 Ta kasa yarda da komai, yau gobe burinta ya kasa ciki, ta kasa samun natsuwar aure kamar yadda ko wace mace take samun natsuwa a gidan mijinta, saboda ta hana kanta haihuwa, a yanzu kuma tada fito tana jiransa sai ya dauki kiyayya ya dora mata? Har gobe ganin take Anty Ummi ce ta shiga tsakaninta da shi, domin a da ba haka yake mata ba, gani take kamar itace ta saka ya auri Yayarta a maimakonta, bayan kuma ita tafi dacewa da shi, ta kasa yarda cewa Zain baya sonta. 

 Juyowa tai tana fuskarta cikin dakinta, but still jikinta na jingine da ginin gurin, a hankali ta sauke numfashi.


“Wannan ce kadai damar da nake da ita a rayuwata, itace kawai hanyar da zan iya gusar da kiyayyata a zuciyar Zain, ina son mu koma kamar baya, ina kwadayin ka zama abokin rayuwata na har a bada Zain”


Ta furta a hankali sannan ta tako cike da kasaita ta karaso gaban kujerarta dake gefen godonta, har zata zauna sai kuma tai tsaye tana ta tunani. 

 Yadda zata gyara alakarta da Zain take tunani, a ganinta har gobe Zain yana kaunarta kawai dai an shiga tsakaninsu ne. 

  Kwankwasa kofar dakin akai, hakan yasa ta dago kai ta kalli kofar, bayan wasu yan seconds Abida ta turo kofar dakin ta shigo bakinta kumshe da sallama, kanta a kasa karasawa tai gaban Hameeda ta risina.


“Allah ya taimakeki Mai Martaba yana nemanki”


Kallon rashin fahimta da mamaki tai mata.


“Kin san dalilin kiran?”


“Ban san komai akai ba ya shugabata”


Yawun bakinta ta hade, ta soma takawa a hankali har ta isa gaban wardrobe dinta ta bude ta dauko mayafi ya rufe kanta sannan ta nufi kofar fita, zuciyarta na zillon rigan kafafunta. A iya saninta Mai Martaba baya fada a yanzu, kuma idan har wani hukunci zai yanke ko wata magana data shafi iyalinsa a falonsa na cikin gida yake zartarda komai. Kai tsaye part dinsa ta nufa tana kai hannu ta bude kofar falon farko sai gabanta ya soma faduwa.


“Assalamu Alaikum”


Tayi sallamar ne tana kokarin danne zuciyarta, yan matan Mai Martaba ne suka amsa mata, wato Sisters din Zain, cikin falon ta tana karewa duk wanda yakr cikin falon kallo kasa kasa, Hajiya Hadiza ce a kujerar dake kusa da ta Mai Martaba, sai Hajiya Maryam na binta, da Hajiya Zarah dukansu Matan Mai Martaba ne, Dada Yalwa na zaune a kujerar data saba zama a duk lokacin da irin hakan ya samu. 

 Tun da ta zauna bata sake dago kai ta kalli kowa ba, wannan dabi'ar na daya daga cikin dabi'un da Mai Martaba yake so, yana cikin dabi'un da ake yabon Hameeda da su har ake ganin tafi duka yaran sarkin kunya. 

 Gyara muryar Mai Martaba yai, wannan yasa hankalin kowa ya koma kansa kenan, ciki har da Zain da zuciyarsa take can asibiti. 

  

“Zain...”


Mai Martaba ya kira sunansa, a natse ya dago ya kalli Mai Martaba. 


“Mi Hameeda tai maka?”


Kallon Hameeda yai yaga kanta kasa, sai ya kalli Dada Yalwa kamin ya maida dubansa gurin Mai Martaba. 


“Allah ya taimaki Mai Martaba, bata min komai ba”


Dada Yalwa ta tari numfashinsa. 


“Bata maka komai ba, zaka ce ta daina shiga sasshen ka? Ta daina bi inda zata ganka? Kace ka tsaneta? Ba wannan dalilin yasa tace zata bar gidan ba, saboda kana nuna mata banbance da sauran kannenka, kuma ba kowa ba ne sai wannan Ummi ita take zigashi a komai, har cewa yai ba zai kara kaunar Hameeda ba a rayuwarsa”


Tunda ta fara maganar babu wanda ya saka mata baki sai da ta kai aya, babu wanda ya isa ya karyatata ko da kuwa karya take fadi babu kuma wanda ya isa ya fada ta fada, shi kansa Mai Martaba natsuwa yai yana sauraren Mahaifiyarsa. Bayan wasu yan dakiku ya sake gyaran murya a karo na biyu ya ce


“Zain Hameeda da Ikram duka kanenka ne, a gurina duka daya kuke, Hameeda tsatson mu ce wannan kadai ya isa yasa ka girmamata, zan iya wakiltarta a komai na tsaya mata, kai ban tsaya maka ba, kai da ita duk a daki daya kuka taso wannan kadai ia isa ya yansa ka ganin kimarta, tafi kowa cancantar girmamawa a gurinka, kai ne Babba Zain be kamata ace wasu dabi'un marasa kyau suna tasowa daga gareka ba.

 Komai na rayuwar duniya dan hakuri ne, idan har tai maka laifine sai ka sameta ku tattaunawa, idan kuma abun ya gagara sai ka samu Hajiya ko daya daga cikin uwayenka sai ka fada musu komai”


Yayi shiru na wani lokacin, sannan ya cigaba. 


“Ko kadan bana son naji wata rigima ko rashin jituwa na tasowa tsakanin iyalaina, zuciyata tana sosuwa idan daya daga cikinku ya aikata wani abu marar dadi, idan laifi tai maka ka yafe mata kuma ku shirya tsakaninku bana son jin wani abu ya shiga tsakaninku daga yau”


Tsit falon yai kamar ba kowa, zuwa can Hameeda ta dago fuskarta da hawaye shabe shabe. 


“Ka gafarce ni Mai Martaba, da nasan idan na fadawa Dada abunda Zain ya fada min zai zata fada maka ne da ban fada ba, Allah shine shaidata bana son abunda zai daga maka hankali a yanzu kuma na maka alkawari ba zaka sake jin wata yasassshiyar magana a tsakaninmu ba”


Ta juyo ta kalli Zain da sai a lokacin ta lura da inda yake zaune. 


“Ka gafarta min Yarima, idan akwai abunda nai maka cikin rashin sani ko da gangace, ka taimaki ne ka rika fada min abunda nake maka da yake bata maka tai zan kiyaye, kuma na maka alkawari zan kasance mai biyaya a gareka har a bada”


Ta karasa tana hade hannayenta hawaye na mata zuba kamar gaske. Kallonta Mai Martaba yai zuciyarsa cike da kaunarta, tarbiyarta da tsantsan da kanta da biyayarta suna burgeshi, tafi kowa gudun zuciyarsa a Masarautar. Zain kam be yi mamaki ba daman yasan yadda take narkewa a duk lokacin da irin hakan ta samu, ko a tsakaninta da Haleema ne sai Mai Martaba ya dora laifin akan Haleema ya ba Hameeda gaskiya. 


“Wata matsala ba zata sake tasowa daga gareni ba Insha-Allah”


Ya fada yana maida kallonsa gurin Hajiya Hadiza dake gyada masa kai. Mai Martaba ya daga kai yana kallon sauran yan matan.


“Na taraku ne gaba daya, saboda kar bayan wannan kuma wata maganar ta sake tasowa, kar abunda ya faru tsakanin Zain da Hameeda yasa ku rainata ko kui mata wani kallo dabe dace ba”


“Insha-Allah zamu kasance masu biyayyah a gareka, kuma babu wani banbance da muke nunawa dukanmu, kanmu hade yake kuma za mu cigaba da kasancewa haka insha-Allah”


Cewar Ikram on behalf of them, kasancewar ita ce Babba a cikin yan matan da suke cikin gidan a yanzu. Da hannu yai musu alama sai duk suka tashi tsaye ban da Matansa, bayan sisters dinsa sun fice Zain ya tashi tsaye da zimmar fice daga falon, sai kuma ya koma ya zauna sakamakon kallon da Mai yai masa. 

 Natsuwa yai sosai dan yasan akwai sauran magana. A natse Hajiya Maryam ta fara magana, cike da isa daman haka take masa a gaban a duk lokacin da zatai masa magana. 


“Abu na biyu da yasa muka kiraka Zain zancen aurenka ne, wasa wasa muka kusan shiga shekara ta hudu da rasuwar Haleema amman shiru baka sake maganar aure ba”


Ya dan dago kadan ya kalleta ya maida kansa. 


“Har yanzu ban samu wacce nake so ba ne shiyasa”


“Har yaushe zaka ga wacce kake so, ai kin san halin Zain ko ta farko ai sai da aka matsa masa sannan yai, ni abunda na ga yafi dacewa kawai a hada shi da Hameeda”


Da sauri ya Zain ya dago ya kalli Hajiya Zara wacce itace take maganar a yanzu. 


‘Hameeda..?’


Ya maimaita a ransa, sai kuma ya kalli Hajiya Hadiza kai ta gyarda masa a hankali ta yadda shi kadai zai iya fahimtar abunda take nufi. Sai ya maida kansa kasa zuciyarsa na mugun bugawa da karfi. 

 Hajiya Hadiza ta gyara zamanta tana magana a sanyaye.


“Ba haka ya kamata kui masa ba idan har aure kuke son yai sai ku bashi damar nemo matar da yake so, idan har be samo ba zaku iya bashi duk wacce kuke ganin ta dace da shi, ita kanta Hameeda baku sani ba ko tana da wanda take so”


“Yaushe zai zabo wacce yake so din, kun fi kowa sanin Zain, kuma tabbas yana son Hameeda ita kuma tana son shi ni na sani, Hameeda ita tafi kowa dacewa da ta maye gurbin Haleema”


Wannan karon Dada Yalwa ce take maganar cike da bacin rai.


“Da gangan nasa aka cire hotunan Haleema dan nasan idan ba haka akai masa ba, ba gyaruwa zai yi ba, kuma shi a halin yanzu ai be san wacce yake so ba, mace da matarsa ta mutu ba kamar sabon haihuwa ne komai sai an masa”


Hajiya Hadiza ta ce


“Kuma Hameeda tafi kowa dacewa da shi, saboda halin hakuri da Allah yai mata, da kuma kawaice zata iya jure duk wani abun da zai mata ta zauna da shi lafiya kalau, tunda suna son junansu”


Shi dai be ce komai ba duk da zuciyarsa na cike da abubuwa, yasan ba son gaskiya suke masa kamar Hajiya Hadiza ba, su kullum a cikin neman laifinsa suke, dukan abunda zai kawo rashin jutuwa tsakanisa da Mai Martaba faranta musu rai yake. 


“Shi fa namiji ba a masa auren dole auren dole ma kuma na daya ba na biyu ba, haba abun ai ya zama wani kala, yanzu an daina wannan abun, mai zai hana Mai Martaba ya bashi damar da lokaci na zaben wacce yake so idan har be samo ba sai a yanke masa duk hukunci da ake so”


Dada Yalwa ta tsire baki tana kallon Hajiya Hadiza cike da tsanar dan ita a ganinta bata son Zain ne kuma tana mata katsalandan a abunda ya shafi Zain, bayan kuma ita tana ganin tafi kowa dacewa da ta yanke masa duk hukunci da take ganin ya dace da shi domin tafi kowa son farincikisa.


“Ke dai Allah be rabaki da shisshigi akan maganar Zain ya ba, ana ga gabas kina yamma sai kace baki san halin Zain ba, wani irin a bashi lokaci, shekara uku be ga wacce yake so ba sai cikin kankanen lokaci”


Ta karasa da jan tsaki. Mai Martaba ya gyara zamansa bayan ya gama sauraren abunda yake fita daga bakinsu, ya san halin matansa ya kuma san irin zaman da ko waccensu take yi da Zain, hakan yasa a duk lokacin da zai yanke hukunci abunda ya shafi gidansa ko kuma Zain ya kan saurari abunda zai fito faga garesu. 


“Zain kana da wace kake so ko ta kwanta maka?”


Kamar daga sama Zain yaji tambayar Mai Martaba, sai ya rasa ta inda zai amsa masa, kar yace babu suce zasu hada shi da Hameeda idan kuma ya ce akwai wa zai gabatar? 


“Mai Martaba a yanzu kam babu wacce nake so sai dai a bani damar zan nemo ko da a nan gidan ne”


Maganarsa tai Mai Martaba dadi, daman baya son yanke masa hukuncin abunda baya so, haka ma Hajiya Hadiza, Hajiya Maryam da Dada Yalwa kam sun dauka Hameeda yake nufi ko kuma sauran yan matan da ake riko a gidan jin ya sako maganar gida a ciki. 


“Zaka iya tafiya Zain, Allah yai zaba maka abunda yafi zama alheri a rayuwarka”


Cewar Mai Martaba yana kallonsa. 


“A tashi lafiya, Allah ya kara maka lafiya”


Cewar Zain yana kokarin tashi tsaye. Sannan ya taka a natse ya fice daga falon yana ta mamakin yadda suke kokarin yi masa abunda aka daina yayi tun kaka da kakanni, kuma a aure na biyu bama na daya ba.


“A shekarunan nawa”


Ya furta yana duba jikinsa, sai kuma yai murmushi, kamin murmushin dake fuskarsa ya gushe tunawa da makircin Hameeda. And now yayi alkwarin wa Mai Martaba ba zasu sake yin wani abu makamancin wannan ba. After that baya tunanin zaibiya ganin wata mace da har zai iya aurenta. Tunani kala kala a ransa har ya iso part dinsa wanda can kusa da part din Dada Yalwa. Sai da ya duba agogon hannunsa kamin ya tura kofar falon ya shiga. 


Dare yayi yace zai fita a yanxu zuwa asibiti bayan ba aikin yake da shi ba, idan kuma har ya fita a yanxu be san yaushe zai dawo ba, beside yarinyar da zaije a akanta yasan yanxu ma bachi take, ya tabbatar Dr Ibrahim zai mata duk abunda ya bukata dan haka baya bukatar tada hankalinsa akai. 


FARHAT POV. 


Allahumma inni aj'aluka fee nuhurihim wa'a uzuu bika min shururihim. Ita ce addu'ar da take ta maimaitawa tunda suka kawo ta gurin, addu'ar mai muhimmanci da tasiri a halin yanxu, matukar ka karanta wannan addu'ar idan ka hadu da yan fashi ko masu satar mutane ko mai binka bashi ba zai tambaye ka insha-Allah sai dai ma ya kara maka, ko kuma wani mutum da kake tsoron sherinsa Allah xai kareka daga garesu, sai dai tun kana nesa da su ake karantawa. 

 Kadan kadan take maimaitawa har ta isa gaban wanda ya kirata din jikinta sai rawa yake kamar mazari. 

Da yaren fulatanci yai mata magana ta sakar masa ido ta kasa amsawa balle ma har ta mayar masa da amsa, shikan a tunaninsa yaga yar'uwa ganinta fara kuma ga gashi har gadon baya, besan attachment ba ne.


“Kai ba fulani ba?”


“Fulani ce amman bana jin komai”


Ya kalli dan'uwansa sai suka yi fulatancin sannan ya sake kallonta ya ce 


“Dige wane garee kake?”


“Gusau”


Ta amsa jiki na rawa sosai, a ranta kuma tana da maimaita addu'ar. 


“Kana gane hanyan geeda kouu?”


“Ee ina ganewa”


Cikin barkatacciyar hausa yake mata maganar, irin hausar nan ta fulanin daji bakinsa cike da goro, kayan jikinsa sun yi datti sosai kamar wanda ya shekara be yi wanka ba, hasken fatarsa ma dishe kamar an shafa masa laka, ban da hasken fitila da wutar karar da suka kunna na haskashi ba kai kace ma wani dodo a cikin duhu.


“Amman kasan idan be ka san hanya ba zaka hadu da wani gungu kou? Dan haka in beka san hanya ba ka beri jauro shi kai ka, mun yi maka haka ne saboda hanyar fullanci”


Ta duka kasa da sauri tana masa godiya har da kukanta. Daya daga cikinsu ne ya tashi dauko AK47 dinsa ya rataya, ya dauki rawani ya nade fuskarsa da shi sannan ya hau babur dinsa mai kama da dan 50 ta kuma ta hau baya ya soma keta dajin da ita, tayi zaton wani gurin za a kara kaita ganin kasurgumin dajin da suke fitowa cikinsa wani gurin ma kamar ba daji ba, wani gurin kai kace dan adam ba zai iya rayuwa a ciki ba, sam ba ta lura da hakan ba sai yau, shigar da suka yi da su dazu da rana bata lura da hakan ba saboda hankalinta kwata kwata baya jikinta balle har ta iya gane ta inda suka biyo sai a yanxu ne take ganin ikon Allah gaba daji baya daji, duhu kam ya yi musu kamar mutum na cikin daki. 


Be sauketa ko ina ba sai a bakin titi, a titi ma babu wasu motoci masu yawa, saboda dare ya yi sosai, gashi kuma kowa ya san hanyar ba mai binta a wannan lokacin sai wanda ya shirya saida ranshi.


“Karka kuskura shigga kauye a yanzu, ka koma inda ka fito”


“To na gode Allah ya saka da alheri Allah ya biyaku”


Be amsa ta ba ya juya ya koma, ita kuma ta fara gudu tana kuka kamar mahaukaciya, kanta babu dankwali daman bata zo dashi ba, Hijab din Anty Ummi data saka kuma tun a can suka rabata da shi, gashi sun karbe mata waya balle ta kira. 

 Haka ta rika sheka gudu kamar ance mata ga mutuwa nan bayanta, ba tai gudun minti arba'in ba ta hadu da wata motar data dauko katakai. Duka hannayenta biyu ta daga mai motar, amman yaki tsayawa, motoci kusan uku na wuce amman babu wanda ya tsaya sai wani mai motar haki, shima kuma dan an hasken safiya ya fara fitowa ne, har yayi kamar ba zai tsaya ba, sai kuma ya tsaya yana kare mata kallo. 


“Baiwar Allah lafiya”


“Lafiya kalau, yan fashi ne suka tare mu suka shiga da mu daji, sai yanzu na samu dayan ya fitar ni, yace karna koma kauye, dan Allah ka taimaka min ka fitar da ni birni”


“Subhanallahi, to ai yanzu Gusau zan je, ke daga ina kike?”


“Daga gusau nake nima gada biyu”


“Shiga shiga muje”


Cikin sauri ta shiga bugubabbiyar motar a front seat. Bata daina addu'ar da take ba har suka isa cikin gusau, mai motar yai mata karanci ita take kwatanta masa ya kaita har kofar gida, dauke da hakinsa cikin mota. A lokacin bakwai saura na safe, tasan bata da inda yafi mata gidan Anty Rukaiya matukar tana cikin garin gusau, sai dai me zata ce mata bayan ta koreta? Anya ma zata karbeta kuwa? Idan ma ta karbeta Ya Bashir zai yarda ya zauna da ita? Cike da kwankwanto ta kai hannu ta buga gate din, bayan wasu yan mintuna mai gadin ya fito waje, ganin Farhat yasa shi sakin fuska da kuma mamaki.


“Aisha lafiya dai”


Bata amsa shi ya tsaya gaisawa da mai motar ita kuma ta tsaya a waje ta kasa shiga cikin gidan kamar bakonta, zuciyarta na raya mata taje gidan Anty Ummi kawai. 


“Bari na kira Alhaji”


Cewar Mai gadin tare da komawa cikin gidan, Farhat kamar ta hana shi sai kuma wata zuciyarta ta dakatar da ita. Ba a dauki lokaci ba sai ga Ya Bashir da Ahmad a tare sun fito da sauri. 


“Farhat Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un miya same ki”


Ya furta da cike da tashin hankali yana kallonta. Kasa amsawa tai ta noce kanta kasa sai ga Anty Rukaiya ta fito tana mata kallon uku saura kwata. 


“Rukaiya ya akai ta fita? Ba kince Ummi tace ta taya ta bachi ba?”


“Korarta nai yi”


Ta amsa kai tsaye. 


“Korarta kamar ya? Mi tai miki da zaki koreta? Wannan wace irin magana ce, yanzu baki san iya halin da kika sakata ba”


Farhat kam kuka kawai take, ta kasa daga ido ta kalli hararar da Anty Rukaiya take mata. 


HAFSATU MANGA POV. 


Ana kiran sallah asuba Hafsat ta farka, sai taji kanta kamar an dora mata dutse, kafarta kuma da zogi, ga idonta bata ganin daidai dasu dishe dishi take gani, sai dai hakan be hanata karema dakin kallon ba, komai na dakin fari ne tun daga kan labulayen har zuwa fentin dakin ga ac da freezer duka farare kamar dai silin, tashi tai zaune tana kallon ko'ina, hannayenta biyu tasa ta dafe kanta saboda jirin da take ji, ji tai kamar ana ja mata hamnunta na hagu sakamakon robar dake hannun nata. Wani uban ihu ta fasa ta fisge robar hannunta da sauri ta jefar, a take jini ya fara zuba da wanda ake mata karin da kuma na hannunta data fisge. Sauka tai saman gadon ta shige karkashi ta dafe hannun nata tana fadin. 


“Na bani sun shanye min jini, wayyo.... wayyo...”


Idonta duk ya cicciko kamar zai fito waje tsabar tsoro.