Part 2
by @mrsjmoon
*RUMASA'U.* (The innocent girl).
BY SAFIYYA.
WATTPAD @Mrsjmoon.
Page 02.
"Alhaji da fatan kun kama wanda ya yi aika-aikan? Tambayar da likita yasoma jefo musu kena da shigarsu office d'in.
"Gyara tsayuwa Alhaji Ahmad ya yi ya korowa likita bayanin da ya sani ga me da yariyar tare da mahaifiyarta.
"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, shin wannan wacce irin rashin imani ne tare da d'aukan alhaki? Anya wanda ya yi ma yarinyar nan haka musulmi ne kuwa? Ya rabbi ka gyaramana zukatamu ka tserar damu da ga aikata fasadi."
"Amin domin alfarman Annabi." Baba Liman ya amsa dan Alhaji Ahmad hawaye kawai ya ke sharewa, shi kam lamarin ya gama dagula masa lissafi hakan baisan dalili ba ya ke jin tamkar jininsa aka tab'a.
"Baba a gaskiya ku tsananta bincike akamosa domin ya cukar da ita da dik da baiji mata ciwo mai yawa ba amma dubi da matsayin da ta ke kai na d'iyar mahaukaciya mara galihu sam bai da ce yabi damar ba dan wulak'anta mata rayuwa da wannan k'ananun shekarun na ta. Wajibi ne a nemosa dik inda ya ke domin fuskantan hukunci."
"To likitita zamuyi bakin k'ok'arinmu akai amma ba lalllai ba ne mu samo mai laifin ba tunda yanzu yaran dik sun lalace sannan bazaka buga k'irji ka lik'awa yaro laifi ba batare da shaidu sun baiyana ba kuma iyayen nasu rashin kunya yagama rufe masu ido ko ince rashin tsoron Allah domin suna ganin d'iyoyinsu na aikata b'arna amma basa iya tsawata masu dan kawai son zuciya."
"Tabbas zantukanka haka suke Baba, to sai ince Allah ya saka mata, ya bi mata hakkinta."
"Amin."Baba Liman ya kuma amsawa.
" Ina police d'in da suka rako ku?"
"Alhaji ya sallamesu tunda babu mai laifin a hannu."
"Ok. Yanzu ga wanna takardan a tafi abiya sannan asiyo magun-gunar da aka buk'ata cikin lokaci, sai ku hanzarta sabida jikinta akwai typhoid da maleria dik sai anyi treatments nasu kafin ayi discharge nata."
"Thank you Doctor." Alhaji Ahmad ya ambata a hankali.
Motsa kai Likitan ya yi tare da mik'o masa takardan ya amsa suka fice. A jikin mota suka tsaya Baba Liman nayi masa k'arin baya ni ga me da abinda ya sani akan mahauciyar da d'iyarta.
"Kimanin shekaru goma kenan ta ke zaune a unguwarmu tare muka ganta da d'iyarta wacce batafi shekaru uku. Bata fad'a sam haka bata magana rayuwarta kawai ta ke yi ita da d'iyarta, dik inda taso ta ke kwana ko bakin bola, bakin kasuwa ko cikin kango da zaurikan muta ne. Sannan abinda muka fahimta bata yarda da maza dan ko taimako suka bata bata amsa amma in mace ta bata tana amsa shi yasa in mutum na son bata taimako kamar na abinci sai abawa mace ta kai mata, sadda d'iyarta ta soma wayau ne muka soma ganin dariyar ta haka yarinyar in tanayi mata magana mukanga ta natsu amma bata amsawa. Tabbas uwa da d'iyar sun shak'u fiye da tunanin ka sannan ni dai ban tab'ajin labarin wani ya nemi b'atawa yarinyar rayuwa ba shi yasa na ce samo wanda ya aikata laifin abu ne mai wuya. Sannan ta kan bar unguwar na wasu kwanaki kafin ta dawo, a tak'aice dai bata tab'a yunk'urin cutar da kowa ba karkan gabanta ta keyi cikin gushewar tunanani."
Numfashi Alhaji Ahmad ya ja ya shafo zufar da ya taru a goshinsa ya dubi Baba Liman da ya dasa aya.
"Baba wannan lamari da d'aure kai ya ke amma a d'an bayanan da kayimin yanzu na fahimci kome ya sami matar bazai rasa alak'a da namiji ba dubi da yarda kace bata yarda da su."
"To Allah masani dai."
"Allah ya warware musu lamarin cikin salama."
"Amin Alhaji, kaima Allah yabiyaka bisa taimakon musulinci."
"Amin, ya biyamu tare dan kaima ka taimaka."
"Amin. Alhaji zan wuce amma zuwa yamma zan taho da iyalina dan su zauna da ita sannan ya kamata kasanya likitoci su kauda mahaifiyarta a wurin ka da ta janyo matsala sabida lalurarta."
"Tabbas wannan shawarar abar dubawa ce Baba, zanyi maganar yanzu kuwa. Allah ya basu lafiya baki d'aya."
"Amin."
Shima kud'i mai kauri Alhaji Ahmad ya bashi ya fice cike da alhinin yana mai jan addu'ar Allah ya tona asirin dik wanda ke da sa hannu cikin lamarin.
Pharmacy Alhaji Ahmad ya wuce ya siyo magani sannan ya biya kudad'e da suka buk'ata. Magana ya yi da Doctors cikin dibara suka yiwa mahaukaciyar alluran barci aka sanyata cikin wani d'aki na daban.
Tsaye ya ya ke gaban gadon kyaky-kyawan yarinyar wacce ke ta sharan barci, tausayinta yagama nashe k'irjinsa. 'D'iya mai kyau tamkar ba 'yar Nigeria ba.' Ya amta cikin ransa. Dik da d'aud'an jikinta ya hango hasken fatarta tare da hasashen jinsin da ta fito. 'Wata k'ila daga Niger suke ko kuma daga cikin jinsin shuwa Arab suka fito' Ya gyara tsayuwa cike da jimamin lamarin 'To wai me ye silar lamarin da suke rayuwa cikin wahala? Uhm lallai ba'arasa sark'ak'iya cikin rayuwarsu. Allah na rok'eta kasa cikin sunnar aure ya samar da wannan d'iya.' Nurce ce ta shigo ta katse masa zancen zuccin da ke yi, ya waiwayo ya mik'o mata leda ta amsa tana kallonsa dan sauraren k'arin bayani.
"Dan Allah in ta tashi kiyi mata wanka ga kayanan ki shirya ta zan dawo anjima. Ki kulamin da ita, kiyi mata dik abinda ya dace zan biyaki kona nawa kike buk'ata."
"Tam Alhaji bakomi, ai d'a na kowa ne sai kadawo d'in."
"Nagode kuma in ba takura ki rik'a lek'a mahaifiyar ta, ka da kiji tsoro bata duka sam."
"Shi kenan Alhaji insha Allah zanyi dik abinda ka buk'ata dama aikinmu ne kula da dika wanda ke k'ark'ashinmu."
"Masha Allah, hakan shi ne cikar nagarta."
Daga haka ya fice yana wai-wayen yarinyar wacce fuskanta ya ke a kubbure da alama sai da tasha maruka kafin asami nasarar keta mata haddin.
*
"Kallonsa ya ke yana ta had'a kayarsa dan komawa makaranta. 'Du besa kamar mutumin kirki sam baida ruwan 'yan iska, wannan basajan yasa ko ya yi abu Abba ke k'in yarda.'Muhsin ya furta cikin zuciyarsa yana aunawa Abid kallon k'yama.
"Yanzu Abid abinda ka aikata shi ne mutuncinka? Wai me yasa baka jin magana ne? me ya kaika aitawa wannan rashin imanin? Kana jikan babban mutum kamar kamar mahaifin Umma jinin malumta gaba da baya amma kake ado da rayuwar banza. Anya ba sanjawa Hajiya kai akayi a asibiti ba?"
"Me na yi kuma ya sheikh? Da zaka cikamin kunni da bayanai barka tai har da son sheganta ni." Ya ambata cikin izgili.
"Kafi kowa sa ni kuma wallahi sai Hajiya ta ji dan ba zan sanarwa Abba ba domin ba hukuntaka zaiyi ba sabida halinsa kaf ka gado, na iya d'iban albarka shi yasa baya ganin aibunka."
"Oh Abban ka ke jifa da wannan kalamin na b'atanci?"
"Oh a she kasan baku da hali mai kyau? To ka kyauta wulak'antawa yarinya rayuwa da kayi, idan ta mutu alhaki na wuyarka ga zunubin dattin zina da ka aikata, dan haka sai ka tanadi abin fad'a ranar k'iyama dan bazata tab'a yafe maka ba."
Sukuti Abid ya yi yana sauraren labarin da yabawa suna almara domin shi baima gane me Muhsin ke magana a kai ba.
"Brother me ke faruwa kake aibatani har kana kirana da mazina ci alhalin bantab'a aikata shi ba."
"Kafita ido na Abid, shekaru biyar da na baka ba wata biyar ba ne tam, dan haka na wuce gaban ka rainamin wayau."
"Wai me ka ke magana a kai ne Brother? Wallahi ban fahimce ka ba."
"Fyad'en da kayi wa d'iyar mahaukaciya ko kuwa kurwan ka ne ya je har ya jefar da agogonka a wurin?"
"Ni nayiwa wannan abar tausayin fyad'e!?" Ya ambata cikin tashin hankali.
Dogon tsaki Muhsin ya ja cikin watsa masa harara "D'an rainin hankali sai kayi da wani amma ba Muhsin ba wanda yaga ni a zahiri."
"Brother kada ka d'auki alhakina, wallahi bantab'a aikata zina in dai ta hanyar al'aurana ya shiga jikin mace ce amma ban musa maka ba in ka zargeni da yin romances wanda wannan kuma zamani yazo da hakan."
Wani tsaki Muhsin ya kuma ja tare da ficewa ganin rainin hankali Abid ya isheshi. Bayansa ya biyo yana kwala masa kira amma yak'i juyowa, yana kallo ya shige part d'in mahaifiyarsu, komawa ciki ya yi ya shirya a hanzarce ya fito harabar gidan janye da trolley, ya sanya a back seat d'in wata farar mota ya fice da gudu zuciyarsa kamar wuta sabida k'azafin da d'an uwansa ya yi masa abu ne da ba wanda ya tab'a jifarsa da shi. Dik da yasan baya jin magana yana latsa mata amma ba shi ne zai bashi damar kiransa da mazinaci kai tsaye ba har ya jefesa da bata rayuwar miskiniyar yarinyar da ya kewa kallon tausayi sannan dik iskancinsa baiga abar mora ajikin yarinyar ba da zai lik'a masa cewar ya yi mata fyad'e. Cike da fushi ya ke driving sai motsa kai yakeyi tare da jan tsaki zuwa can ya sakarka steering duka.
*
Allura na sa kin mahaukaciya ta soma ihu dik ta rud'a jama'a, marasa lafiya suka k'ara rikicewa, wani alluran suka k'ara yi mata ta koma barci. Hankulan patients ya tashi sai k'orafi masu jinyarsu keyi lamarin da ya fusata mamallakin asibitin Doctor Adnan Lere, ya koma office ya lalibi number Alhaji Ahmad yana d'auka ba ko sallama yasoma cewa.
"Alhaji kazo ka d'auki mahaukaciyar nan dan zata b'ata mana aiki, kada ta kashe mana kasuwa dan asibitin bana mahaukata ba ne."
"Ganin kan hanya Doctor ayi hak'uri dan Allah."
"Ok sai ka iso." Kafin Alhaji Ahmad ya sa ke magana har ya kashe.
Wayar ya ke bi da kallo ya fesar da iska ya dubi Mahmud "Yi sauri mu isa kana driving kamar mace."
"Dady wai me yasa kai da Momy keyimin wulak'anci ne?"
"To uban 'yan k'orafi me mukayi kuma? Saraki sarai wanda bai tauna magana ke fad'arta."
"Momy kun gaji da ni to na kusa barin muku gidan baki d'aya ku huta."
"Mahmud me yasa ka ke yawan yi mana barazna da zaka bar gida dik in ka tashi yin k'orafi wofinka?"
"Sabida kun fi son Hamid, komi na ku akansa ke k'arewa yanzu kun biya masa mak'udan kud'ad'e yana turai karatu ni kuwa kun barni a Nigeria ina ta wahala da carryovers abokaina dik sun kammala service ni nakasa samun damar hakan wai kuma sai ace bazanyi magana ba sabida an asirce ni."
"Mahmud stop the car here!" Momy ta daka masa tsawa. Parking ya yi gefen hanya ya fito batare da ya saurari maganar da Dady ke yi masa ba ya tsallaka titi ya yi tafiyarsa.
"Me yasa kike yin haka Aminatu?"
"Ja mu tafi Hubby." Ta ambata fuskanta na kallon hanyar da Mahmud ya bi.
"Aminatu nasha sanar miki ki koyi lallab'ashi wata rana sai labari, bana jin dad'in takun sak'ar da kukeyi."
"Hubby yanzu dan Allah me na yi masa? Daga fa ka ce ya yi hanzari mu isa shi ne yasoma zaro zance wanda daga ji ba tunani ciki."
"Yes da kin kyalesa ya yi ya gama ai da hakan bai faru ba."
"Ba wanda ya haifa cikinmu Hubby dan haka bai isa ya juyamu ba."
"Haka ne to Allah ya shirya mana shi."
"Amin dai amma wallahi na kusa tsame hannuna cikin lamuran Mahmud, in yaso yafi ruwa tafiya k'arshen barin gida, Allah ya gani nayi iya abinda zan iya akansa."
"A'a Dear fushi bana ki ba ne kuma banson sa ke jin irin kalaman nan abakinki, komi ya yi tsanani maganinsa Allah."
"To Allah ya kawo mana d'auki."
"Amin."
Isar su ya yi dai-dai da isowar Baba Liman da iyalinsa. A tare suka shiga d'akin da aka sanja mata bisa jagorancin nurse d'in da ke kula da ita, har lokacin bata farka ba amma ancire drip d'in da aka sanya mata. Momy na ganinta tasoma kuka domin itama raunin zuciya gareta tamkar mijinta.
"Hubby ina son ta dan Allah kada a sa ke barinta tare da mahaifiyarta tunda bata da hankali kada wata rana azo asace ta."
"Nima tunanina kenan Hajiya shi yasa nazo da mai d'akina babban dan ta ganewa idanunta halin da yarinyar ke ciki." Baba Liman ya ambata cike da jimami.
"Yanzu dai dik mujira ganin farkowarta kafin asan abinyi a kai." Nurse ta furta tana gyara mata rufa.
Har bayan magrib bata farka ba zuwa lokacin mahaifiyarta ta farka karo na hud'u. Ganin yarda likitan ke fad'a yasa Alhaji Ahmad neman sallama sai kuma ya nuna mahaukaciyar kawai zai sallama a fusace Alhaji ya d'auke yarinyar tamkar gawa ya sanya a mota, mahaukaciya ta rungume ta tana b'ab'b'aka dariya, suka fice a sibitin batare da ya kula hak'urin da likitan ke ba shi ba.
Wani Private hospital ya kuma kaita a takeyi suka amsheta cikin awa d'aya sukayi nasarar dawowar bugun numfashinta. Mahaukaciyar kuwa sun barta tsaye bakin window tana kallonsu ganin d'iyarta ta motsa yasa ta kwaso da gudu ta shigo ta nufi gadon nurses zasu hanata Doctor Fatima ta d'aga musu hannu suka kyaleta, tana isa sai gani sukayi ta kama hannun yarinyar ta kai bakinta, ita kuma yarinyar ta motsa baki a hankali cikin dushewar murya ta furta "Mamana." Sai kuwa ta sa ke ta daka tsalle ta fice waje da gudu tana kyal-kyala dariya. Kuka yarinyar ta fashe da shi ta juya kai gefe tare da mik'a hannun k'asanta inda takejin rad'ad'i.
*Mrs j moon.*