FreeArewaPen original
Rumasa'u
- 1views
- 35chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I'm a humble woman, I like interaction with people from different environment and it's a honor and privilege to make new friends with exposure for me to get a lots of experience, I'm one of novel reader since I was young and my dream is to be a great writer (author).
Sample · Part 1
*RUMASA'U* (The Innocent girl).Page 01.Allahumma salli ala sayyidina Muhammadun wa sallim S.A.W.*Note.* RUMASA'U k'agaggen labari ne dan haka ban yarda ajuyamin shi ta wani sigar ba. Idan anci karo da wani abu yazo dai-dai da naki ko naka wannan salon rubutu ne kawai amma ba'ayisa dan cin zarafi ko farantama kowa ba.*Shimfid'a*Uwa da d'iyar rayuwarsu cike ta ke da k'alubale, sun shak'u da juna ainun ta yarda suka zamo ko wani sashi jigon rayuwar d'an uwansar ne, hakan shi ne silar haifar da dank'on k'aunar tasu mai sosa ruhi sannan tafiyar nasa cike ta ke da tausayi. Kowa yasan Soyayya irin ta uwa da d'iyoyinta shi ne ake kira da dashen Allah S.W.A wanda Ubangiji ke sanyawa a zukatan kowani sha-shi na halittar amma dik da hakan gwanin iko da baiwan kan kuma juya lamuran a bisa yarda ya rubuta cikin k'udirarsa wanda babu mai iya sauyashi dik kuwa k'i ko so da bawa ke yiwa al'amarin. Tabbas yabo da dikkan godiya tabbatattu ne a garesa, Ya Rabbi muna rok'onka da ka k'aramana tsoronka a dikkan halin da muka tsinci kanmu, Amin. Bari dai ku mu tsunduma cikin labarin RUMASA'U.*A k'asar busas-shiyar itaciyar d'orawa wacce tabushe k'ayau babu alamar tohon ganye a samanta. A nan ta ke kwance cikin turb'aya ta yi matashin kai da jijiyar itaciyar sai shak'ar barci ta ke yi abinta hankali kwance, hak'ik'a dik wanda ya gitto ya ganta kwance cikin rashin galihu sai lamarin ya tab'a masa zuciya amma ga mai wadatuwar imani.Hasken ne na wayewar gari daga duhun subahi ya takurata ga k'udaje sun soma hanata sukuni sai kai masu duka takeyi idanunta kulle amma da zarar ta sauke hannu zasu dawo suna cigaba da yi mata ihu cikin kunni. A kan dole ta tashi daga barcin badan ya isheta ba, mik'a ta yi tare da sauke hannunta gefen damarta dan lalibo d'iyarta kamar yarda ta saba dik in ta tashi barci ita ta ke soma tab'awa kafin komi, sai dai maimakon ta tab'o d'iyar sai k'ullin kayansu ta kamo, a zabure ta kalli wurin idanuwa nan nata masu razana jama'a a waje, shiru ta yi na 'yan second sai kuma ta soma kaima k'ullin kayan bugu da iya kacin k'arfinta, ganin hakan baiyi mata ba sai ta mik'e tsaye ta k'walla ihu ta d'iba a guje ta nausa cikin unguwa.Gudun ta keyi cikin ihu sai ta kai k'arshen layin sai ta dawo farkonsa dik cikin ihun kuru-ruwan mai tada hankali wanda da kaji kasan bana lafiya ba ne. Dik wanda ta had'u da shi babba ko yaro sai ta kama hannunsa ta zube saman kneel nata tana d'aga hannaye sama alaman rok'o,wasu su tureta ya yin da wasu kuma d'auketa da mari sukeyi, masu tausayi ne ke janye jikinsu subarta batare da sun hantareta ba, yara kuwa in ta rik'e sai su fashe da kuka sabida tsoro dan gani su ke dukansu zatayi dubi da halin da ta ke ciki na tab'in hankali. Haka ta kasance cikin wannan hali tsawon lokaci amma ba wanda ya kula da ita alhalin al'umma sun fa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.