UNAISA

C

by @takwalam

🧕 UNAISA 🧕


*C*


✍️ Ayshatuuu


Haka na cigaba da Zama da Mamaa a gidan, yanayin zaman ya banbanta da abinda nayi tunanin ganin, na dauka baza mu taba maganar arziki da ita ba, yadda ta dinga fadawa Dada ta tabbatar idan Zan shigo na shigo da wasiyya ta Dan kuwa se ta min azabar dazan bar gidan da kaina, Amma ko kadan ko kallon banza Bata taba min ba, hasalima kallon da take min me dauke da tausayi ne. Har mamakin yadda muke zaune lafiya nake, last time da na sani balai take akan zaa auro ni, to gashi Kuma ta karbe ni hannu bibbiyu, ta hakura ta saduda, Amma akwai abubuwan da bazan manta ba. Ranar da aka Yi kwana bakwai akai addua a karkade, aka cire tampons Dake waje, wasu Suka gyara Mana gida sannan aka baje, Anna, Dada da Zuhra Wanda suka kasance tare dani duk ranar suka tafi, har mutanen hadejia ma, Anty Aisha ta tafi tun ranar uku Amma ana bakwai dinma tazo. Wannan tafiyar tasu yasa nayi ta kuka mussamman da Abba yace anan Zan zauna ba se na koma gida ba, Haka na yini a daki Ina kuka, har Anna ranar se da tayi kuka, Ina ganin rayuwata a garari take, musamman da nazo kwanciya Naga Babu Zuhra da zata raba dare tana lallashi na, da Kuma min Hira Koda bazan amsa ba. Abokan shi Wanda ya kasance Senate president, da sauran senators tunda shima elected senator ne in office. Seda suka saka aka cika Mana store da duk wani nau'in kayan abinci sannan suka shigo suka Kara gaida mu ya aje kudi ya juya ya tafi su Muhammad Suka raka su. Washegari gidan Babu kowa, Jin shirun da gidan yayi yasa na kasa fitowa Bayan na idar da sallah na zauna Ina jin kewar shi a dukkan sassan jikina, kwana uku kawai mukai dashi Amma kwanakin bazan manta dasu ba, sun kasance masu dadin gaske, ya sakani farin cikin da nake mamakin yadda mutum zai iya hakan, Na lumshe idanuna hawaye sun wanke min fuska ta, na saka kaina tsakanin cinyoyina Ina kuka tun karfina, Ina cikin kukan se wayata ta fara ringing, na saki ajiyar zuciya tare da janyo wayar Naga Anna ce me Kiran, cikin sauri na goge hawayena na dauka Ina fadin


" Anna Ina kwana?"


" Lafiya Lau Unaisa! Ya kike Ina fatan bakya kuka"


Na saka hannu na dauke hawayen dake cascading a kuncina, na danyi sniffing nace


" Na daina Anna"


Ta Jima tana min nasiha sannan tace nayi wanka na fita na taya Mamaa aiki. Daga Haka mukai sallama na Mike jikina ba karfi nayi wanka sannan na shirya cikin wata bakar riga wadda Babu ado ko kadan a jiki. Hulata na cire Dan saka sabuwa anan naji yadda kaina ya damkare guri daya. Comb na dauka na taje shi Ina runtse Idanuna saboda yayi tsamu. Na zauna a nutse nayi kitso biyu na hade jelar na saka a hula sannan na dauki katon veil na yafa a jikina na fito parlor. Ba kowa se masu aiki sunata fama, muka gaisa suna kara min gaisuwa, Ina tunanin murya ta Mamaa taji ta fito, idanun ta sunyi jawur Wanda ya tabbatar min kuka tayi, na gaishe ta, ta saki fuskarta tace


" Ya Kika tashi Unaisa?"


Nace 


" Alhamdulillah Mamaa"


Muna zaune shiru, tunda ba sabawa muaki ba balle muyi magana, plus Ina Kama kaina, Ahmad ya shigo ya shirya zai tafi aiki, muka gaisa sannan ya nufi kofa zai fita se na dubi Mamaa nace


" Bazai ci abinci ba"


Tace


" Ahmad abinci fa?"


Ya girgiza Kai, ta dubeni sanann tace


" No dawo ka zauna, Bari kasha ko tea ne"


Haka ya zauna aka kawo tea din yasha sannan ya tafi ita dama Aseey ta wuce gidan ta tun Daren jiya, Haka Muhammad ma da Bilkisu matar shi sun koma Gombe tun jiya. Se ya rage daga ni se ita, aka hado abinci Wanda naci kadan se naji zuciyata na tashi kawai se na Bari, ta dubeni


" Ko akwai abinda kike so ne?"


Na girgiza Kai Ina Dan murmushi nace


" Kawai bakina daci nake ji"


Ta gyada kanta kawai ba tace min komai ba. A hankali kwanaki suke shudewa, kullum Rana Yana Kara kwanaki a cikin kabarin shi, duk lokacin da na kebe se nayi kuka musamman idan na tuna yadda mukai rayuwa dashi, ranar da muka fara haduwa da irin artabun da akai kafin na aure shi, Amma Ashe Babu ma rabon zaayi doguwar rayuwa tare, kwata kwata kwanaki uku kawai mukai dashi ya tafi ya bar zuciyata da tabon rashin shi. Na goge hawayena Jin muryar Mamaa tana fadin


" Unaisa dakko hijabin ne Haka?"


Na dauki hijab din da wayata na fito, ta dubeni tace


" Kuka Kika Yi ko?" 


Kamar ta zuga ni se wani kukan ya Kara kwace min, ta janyo ni jikin ta tana lallashi har nayi shiru sannan muka nufi asibiti. Ahmad na tsaye sanye da labcoat Yana jiran Karasowar mu. Muna zuwa office din shi muka zauna, da kanshi ya dauka sample sannan ya cike forms ya Kai Lab, seda ya dawo Mamaa tace


" Ahmad dama scan kawai akai ko?"


Se yace Yana shafa Kai 


" Wallahi mantawa nayi. Anty Unaisa sorry na bula ki"


Nayi murmushi ba tare da nace komai ba Dan har lokacin na ksa sakin jikina dashi ba duk yadda yake kokarin ganin na saki jiki, Yana Kuma kokarin wanke laifin shi a gurina, Amma Wanda yasa yayi min laifin ma Baya duniyar, meye abin fushi, kawai dai Ina iya takuna ne, Kuma dama bahaushe yace baa Bari a kwashe daidai. Tare muka fita zuwa scanning room din cikin asibitin, an cika sosae a gurin, ya Shiga Babu jimawa ya fito yace na shiga, Ina Shiga na kwanta dukda naji Babu dadi Ina Kuma ganin hararar da ake wurgo min ta kowanne guri, nasan munyi chancing dinsu. Gel ya shafan a ciki Bayan yayi min gaisuwa sannan ya dauki probe din ya fara gogawa a ciki na zuwa marata, yanayi suna magana da Ahmad da yayiwa screen kuri da idanu. 


" She's pregnant Doctor!"


Nayi saurin duban fuskar Ahmad se Naga ya saki fuska Yana murmushi yace


" Alhamdulillah! Mamaa zata ji dadi. GA din fa?"


Yace fuskar shi a washe 


" 20 days ne"


Shi Kuma a ranar kwanan shi Sha takwas da rasuwar, a raina na ayyana kenan ranar da muka fara having affairs a ranar na samu ciki. Na tuna ranar daurin aure friend Dita tace


" Kina zuwa Zaki samu ciki tunda ovulation kike yau"


Na harareta nace


" Ki gani akan ki, se na huta tukunna"


A hankali hawaye suka gangaro min na sakko daga gadon Bayan ya bani tissue na goge ciki na, na fito ganin hawaye na tsere a fuskata wani na korar wani, Mamaa tayi saurin tasowa tana fadin


" Ya akai Babu cikin ne kike kuka?"


Kaji Mamaa da wata magana, kawai Dan babu cikin se na dinga kuka, na karasa inda take tsaye har lokacin Ina kuka ban Bata amsa ba, Ya fito Yana fadin


" Mamaa akwai Mana"


" To meye abin kukan Unaisa? Kiyi murna Mana"


Na rike hannunta nace


" Haka zaa haife Babyn Bai masan mahaifin shi ba"


Se Naga duk jikin su yayi sanyi suma, Ahmad yace


" Haka Allah ya tsara, Allah ya jikan Abiey!"


Nace Amin, bamu koma office din ba muka koma gida, da kanta ta Kira Anna ta fada mata, Anna tace Mata


" Kinga rabo"


Mamaa tace


" Wallahi kuwa, ni kaina abinda nake fada kenan. Allah ya inganta"


Ta Kira Abba ta fada Masa da daddare kuwa se gashi yazo shi da Dada ya duba mu, Asiya ma ta kirani tana fadin


" Nasan nayi Miki laifi Unaisa kiyi hakuri"


Ina zaune dirshan akan gado na Gama Shan kunun tsamiyar da Mamaa ta dama min Kiran nata ya shigo wayata, na dauka ko gaisawa bamuyi ba, na danyi murmushi kadan Dan a kwanakinnan Murmushin ba sosae nakeyi ba. Nace


" Asiya magana ai ta wuce, komai ya wuce tunda Wanda akai komai Dan shi dinma ya rasu"


Se ta danyi shiru kafin tace


" Dan Allah Unaisa, ba Haka zakice ba, nasan baki manta abinda ya faru ba"


Na sauke ajiyar zuciya nace


" Asiya ya wuce wallahi, nasan fushi yasa kikai komai, Amma yanzun Ina fata kin fahimci dalilin da yasa Allah ya tsara na aura Baban ki ko? Rabo ne Asiya. Wanann cikin Dake jikina"


Ta jinjina Kai tace 


" Na fahimta Unaisa, Dan Allah find a place in your soft heart and forgive me"


Nayi murmushi nace 


" Ya wuce na yafe miki kada ki Kara tada maganar, mu fuskanci abinda ke gaban mu"


Ina jin dariyar ta saboda Jin Dadi ta Dan tsokane ni kamar yadda muke da sannan mukai sallama kowa yayi nashi wajen. 


Kwanaki suka cigaba da tafiya, har Rana ta zago mukai Masa sadakar arbain, a wañnan lokacin annual leave Dina da na dauka ya Kare haka Kuma na Mamaa. Dan Haka na fara hada kayana Dan komawa aiki. Da yamma ranar asabar na Gama komai na fito daga toilet se na tsaya gaban madubi Ina kallon fuskata, na rame Rama ta ban mamaki, idanuna sun tashi daga asalin farare sun rine saboda yadda kullum se nayi kuka, Haka lips dina duk sunyi cracking kamar bani bace wannan Unaisar da kowa yake kwatancen gayunta, kaina tun wannan kitson biyun da nayi ban Kara ba. Ya kamata na gyara jikina na ayyana. Na cire kayana na dakko shaving cream, da shampoo na shga wanka, seda na wanke jikina da kaina tas sannan na fito, wata ajiyar zuciya na sauke Jin wata iska na shigata ta ko Ina, na zauna na gyara kaina sannan na shafa Mai, na saka turare me sanyin kamshi Wanda nasan bazaa ji ba, na zura wani bakin material dinkin A shaped gown. Anan na Kara tabbatar da ramar da nayi. Na daura dankwali na yafa katon veil na fito parlor. Suka suna zaune, Aarif din Asiya nata tsalle tsalle, Bilkisu na ma yarinyar ta magana. Ko rasuwar nan Bata min gaisuwa ba, Bata taba min magana ba Haka Nima ban taba Mata ba, ko abubuwan aurennmu Yaya Muhammad Bai taba shiga ba, Amma ita tafi Mamaa kishi, Muka gaisa da Muhammad sannan na koma daki Dan Mamaa da Asiya sun fita. Se yamma Mamaa ta dawo, Asiya ta fara shigowa tana fadin


" Kin nane a daki kamar me takaba"


Na tashi na zauna daga kwancen da nake nace


" Da me nakeyi idan ba takaba ba"


Se ta rufe bakinta tana dariya ta shigo, muka gaisa sosae tac e


" Da nazo ai Mamaa tace bacci kikeyi"


" Bana iya bacci da daddare"


Se Naga fuskarta ta Dan canja tace


" Me yasa? Wani gurin nayi Miki ciwo ne?"


Na girgiza Kai na nace


" Kawai abin duniya!"


Se ta Bata fuska tace


" Ya kamata ki Dan sararawa zuciyar ki Unaisa, mutuwa ba yadda zamuyi, we so much missed him wallahi"


Na gyada Kai na ba tareda nace Mata komai ba, se ta kawar da wannan hirar ta dakko wata.


Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First Bank of Nigeria, send evidence of payment to ***.