UNAISA

P

by @takwalam

*P*





Bayan watanni nayi tunanin zancen Alhaji Yahai da Anna ya mutu Ashe shi Yana can Yana hada wasu abubuwan, sede komai dake faruwa Allah shi ne yake tsarawa Kuma Babu abinda Rai zaiyi face da yarjewar ubangiji. Kafin wannan muka koma makaranta, watanni wajen biyu suka shude muka tafi posting dinmu na farko asibiti, anan aka banbanta Mana ward ni da Zuhra,ni Ina female ward yayinda take children's ward. 10am na Gama abinda aka sakani a allocation na dauka excuse zanje gurinnta muyi breakfast, ni kadai Ina yawo kan dogon corridor din asibitin nayi nisa cikin tunanin da baa rasaawa, da kullum nake cikin yi Kuma da zaka tambayeni I can swear bazan iya fadar tunanin me nakeyi ba ma in the first place, ji nayi nayi bumping mutum hakan yasa nayi saurin dago kaina Ina Sosa goshi na na dubi da Wanda nayi Karo, ok! Na ayyana a zuwana asibitin na ganshi a lokuta da bazasu irguwa ba Kuma duk lokacin da zamu hadu ya dinga kallo na kenan, Kuma irin kallon da yake min Wanda bana so ne Dan kallon kurilla da Kuma rashin kunya, to rashin kunya Mana ya kamata idan ana kallonka ka hada idanu da mutum to ya dauke kanshi ko Kuma ya Dan nuna alamar Jin kunya, Banda wannan mahalukin dalilin da yasa nake jin haushin shi kenan, gashi Kuma fate se hada mu take, ko Dan ai asibitin yake aiki I dunno ko likita ne ko Kuma Lab scientist tunda Lab coat na gani sanye jikin shi for lokuta har uku da muka hadu. Yau din baya sanye da labcoat hasali ma kaftan ne na wani farin yadi a jikin shi, kanshi sanye da bakar hula minister, ya zuba kyau, nayi saurin dauke kaina tunawa da cewar kallon da bana so irin shi nake Masa, kallona yake sosae sannan yace


" Tunanin me kike Haka?"


Na Dan kalleshi sannan nace


" I'm sorry please"


Na fada Ina gebare gefen shi Zan wuce


" Dan Allah Zan iya sanin sunanki?"


Na juyo na kalleshi se Naga ya min kwarjini, bazan iya Masa banza ba, cikin sanyin murya nace


" Unaisa"


Yayi shiru bansan tunanin me yake ba ni dai nan na barshi tsaye sede ya juyo yaga bana gurin. Na danyi nisa se naji muryar shi Yana fadin


" Please Unaisa!"


Na danja na tsaya, ya tsaya shima sannan yace


" Ya hakuri na takura ki"


Nayi rolling idanuna Ina fadin me shegen kallo, shi wannan lower your gaze Bai shiga kanshi ba


" Ehen! Are you in any way related to hadejia ko katsina?"


Na girgiza Kai se naga ya Dan canja fuska sannan yace


" I'm sorry!"


Ya juya ya tafi, na Dan Jima tsaye Ina tunanin me ye maanar maganar shi, Amma se na dage kafada na wuce abuna. Ranar da daddare Ina Kan sallayya Ina waya da Yaya khulthum naji Zuhra na fadin


" Wallahi rabuwa zanyi dashi yama Raina min hankali"


Nayi sallama da ita sannan na dubi Zuhra nace


" Ke da waye Wai?"


Ta zauna bakin gado na tana Kara Bata fuska tace


" Nida wancan wawan ne Mana"


Nasan Nafiu take nufi, nayi murmushi nace


" Nafiu ne Wawa Wai?"


" Ai dama ke Baki ganin laifin shi, bansan da me ya siye ki ba"


Na danyi murmushi nace


" Have I ever talked to him? Ban taba ba Kinga ta Ina zai siye ni, kawai na fahimci tunda wannan doctor din ya shigo picture din komai ya canja, yanzun kome nafiu yayi laifi ne a gurin ki"


Se tayi shiru ba tareda ta Musa ba, se na Dan saki fuska saboda Kar taji Babu dadi nace


" Inason Naga doctor dinnan da ya barar da gwamnatin Nafiu, he must have put in lots of effort"


Tayi dariya ta fara fada min


" Kinsan Ina muka hadu? bafa a asibiti bane, kin tuna time din da naje refilling Mana gas na karshe? Ina tsaye a road side se ya bani lift, ban fada Miki ba Dan nasan masifarki"


Na dinga binta da kallo nace


" Ke kenan munafurta ta kike? See tell me all what you are hiding"


Ta buga kafar ta tace 


" Exactly abinda yasa naki fada Miki. Kinga wallahi tsoron Zaki ki yarda dashi ne"


A lokacin na fahimci goyon baya na take bukata Dan Haka na nuna Mata duk abinda ta zaba ni din Ina tare da ita, Zan Taya ta addua sannan Kuma Zan Bata shawara when necessary. Zuhra example ce ta mutane masu sa'a, akwai mutanen da namiji Bai taba yaudarar su ba, Basu taba dandana menene heartbreak, to Haka Zuhra take Bata San menene bacin ran soyayya ba, saurayi daya, se tambaya se aure! Amma ni Kam baa magana, ita dai ta saka ni na tsunduma a soyayyar Amma wahalar da nasha seda naji dama nayi zamana single. 


" Yace Wai zai zo ku gaisa"


Na Kara mike kafafuna nace


" Se yazo!"


Daga nan se muka bar maganar, se tace min


" Nama manta dazun Anna ta Kira ni akan idan zamu samu dama Wai muzo weekend dinnan"


Nayi shiru Dan ban Jima da waya da Anna ba Amma Bata min maganar ba, nace


" Why not? Amma lafiya?"


Tayi dariya tace


" Gaskiya lafiya from the excitement na muryar ta"


Se na saki ajiyar zuciya nace Allah ya kaimu. Lokacin bacci yayi nazo na kwanta yayinda Zuhra Kuma ta dira waya ita da Dr dinta, dukda a hankali suke maganar Amma Ina iya juyo abinda suke cewa, I find myself thinking ni yaushe zanyi saurayi ne? Se na tuna Zuhra tace min ai ni nake korar su to Amma tambayar da nake ma kaina yaushe m akace ana Sona har nayi korar. A Haka bacci ya daukeni.


Washegari da yamma na Gama dakko ma Zuhra Kaya, tana zaune gefen gado tana shafa powder, ta dauki atamfar ta saka, tayi kyau sosae mashaaa Allah, na dauki wayata na kashe Mata pictures sannan na juye chilled zobon Dana hada Masa cikin jug, se na jera finger food din da mukai order na rufe da cling film. Husna Dana Kira tazo ta dauka muka fita zuwa inda yake kafin ita gimbiyar ta fito. Yana zaune cikin cafeteria school, ya bada baya da waya Kare a kunnen shi, muka cigaba da tafiya har muka Isa seat din, na saki fuska Ina gaishe shi ni da Husna, Yana dagowa idanun shi cikin nawa yace


" Unaisa?"


Nace 


" Sorry! Ba gurinka muka zo ba"


Nasa hannuna Zan dauke basket din, kunma San Wai wa na gani? Wannan mutumin da mukai gware a asibiti me azabar kallo dinnan, Husna ta zungure ni tace


" Shi ne fa dallah!"


Na harareta shi Kuma se kallon mu yake barin ma ni na e


" Wannan din? He doesn't deserve her"


Na juya da niyyar tafiya Se ga Zuhra tana taku daya daya, ni kaina seda na shagala Ina kallonta balle shi Kuma, ta karaso bakinta ya kasa rufuwa, na kalleta na Kuma kalle shi Naga kallon da yake Mata na kauna se naji contemplating da nake akan son da yake Mata ya tafi, na aje basket din ta karaso tace


" Sannu da zuwa"


Ta zauna mu Kuma muka tsaya kamar zakaru, 


" Wannan ce Unaisa Taki? I've finally meet her"


Tayi murmushi, muka gaisa sannan na juya na tafi, Husna tace min


" Wai me yasa Kika Masa abinda kikai dazun?"


Kawai nayi shiru bance komai ba, se yamma ta kirani zai tafi , Nima na fito Amma ban saki jiki ba se tayi tunanin rashin sabo ne tunda dama Haka nake, na karba kayan muka tafi hostel, 


" Unaisa Yaya? Yayi?"


Nayi murmushi nace


" Yayi mana! Karshe ma"


Tayi tsalle hade da fadin


" Na iya zabi"


Na Harare ta nace


" Se ya ganki kina tsalle ai"


The next day bayan karfe goma an Gama rounds na fito zuwa Doctor's common room, Ina Isa na iske Dr ishaq a tsaye da wani guy suna ta dariya, na gaishe shi sannan nace


" Dan Allah Dr Khalifa nake nema"


Yace


" Yana ciki, ayi mishi magana?"


Na gyada kaina, baa Jima ba se gashi ya fito hannun shi da mug din coffee, Muna hada idanu yace


" A'a sister mu ce? Sannu da zuwa?"


Na amsa Masa se mukai shiru se shi yace


"I hope I'm safe?"


To me zance masa? Nace Masa me yasa yake kallona ko Kuma nayi questioning son da yake ma Zuhra, se na ga wauta ta Amma Kuma Zuhra ce, Ina son tayi farin ciki. Kamar yasan abinda ke Raina se Naga ya Ciro wayar shi ya danyi scrolling kadan sannan ya Miko min tare da fadin 


" Nasan kina tunanin me yasa nake kallon ki duk lokacin da muka hadu ko? You look exactly like my sister! Kalla hotin ta"


Na saka hannuna na karba, subhannallah! Shi ne abinda na furta she sure looks like me sosae kuwa, banbanci mu shekaru ne kawai, yace


" Da ace wani zai ganki zaice ita ce, kullum na ganki se Naga kamar ita ce shiyasa nake Miki wannan kallon Amma da gaske Ina son Zuhra Kuma auren ta zanyi"


Na sake ajiyar zuciya na relief na bashi hakuri, yayi dariya yace


" Haka kike son Yar uwarki, naji Dadi. Ya aikin?"


Nayi murmushi nace


" Alhamdulillah"


Daga Haka Kuma se na Masa sallama na tafi, Bayan na tafi hoton yarinyar da bansan sunan ta bane kawai a idanuna, how on Earth zamuyi Kama irin wannan? Ta Yaya? Se Kuma wata zuciyar ta kwabe ni da fada min ba Allah ne ke hallitta ba? Then everything is possible. Banyi magana da Zuhra akan hakan ba se da daddare nake fada Mata tayi dariya kawai Bata ce komai ba. Wannan weekend din kuwa Muna tashi daga asibiti muka daura abaya akan farin uniform dinmu, idan ka ganmu baka ce daga asibiti muke ba bamu jira kowa yazo daukar mu ba, muka ma Kano tsinke. Tun a Hanya munata Hira, danmu dai hirar mu Bata taba karewa, 


" Idan mukaje zanyi ma Anna zancen Doctor, ko ya Kika gani?"


Na gyada kaina nace


" Hakan yayi kuwa, Kinga gwara ace ansan kina tare dashi"


Muka danyi planning yadda zamu samu Anna da maganar Bayan mun Gama nace


" Nikam Zuhra wani abu ya tsaya min a raina"


Ta Dan kalleni kamar me son karanta Rai din nawa tace


" Warris that?"


Nace


" Sister Doctor, have you seen her picture?"


Se ta dakko wayar ta ta Miko min, ya ilahi se yanzun na Kara ganin kamar tamu, na dube ta nace


" Baki jin kamar akwai wani Abu, like irin ko we're related hakan?'


Se tayi shiru kafin Kuma tace


" God! Haka ne fa, Allah na manta, Kuma yace min da kakar su ta gurin Baba take Kama, likely..."


Na gyada kaina, se muka Bari akan zamu Masa magana a hankali, muka fara Jin kanmu kamar wasu legend a cikin family, tunda mu mukai uniting family din wannan kenan.


 Gidan Anna muka sauka Dan anan muka samu Dada, seda muka ci abinci sannan mukaji labarin Ashe sallama zamuyi da Anna zata tafi Dubai, zata fara saro Kaya, nayi ma Allah godiya Babu adadi, tabbas arziki da Kuma daukaka ta Allah ce!


Unaisa is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First Bank of Nigeria, send evidence of payment to ***.