UNAISA

T

by @takwalam

*T*




Yadda abubuwan suke tafiya yasa ban wani maida hankalina akan Al'amin ba, se bayan Dana tabbatar komai ya Zama daidai sannan na nutsu na dawo hankalina, munyi magana da Anna tace min Baffa yace taje Masaya ta sanar da Alhaji Yahai cewar zata ma Badi'a aure, ko da Bai Mana komai ba matsayin mahaifin mu to duk da Haka yana da right din yasan me yake faruwa akan mu, Kuma su din basuda ikon daura Mata aure se dangin Alhajin. 


Ranar Monday da wurwuri na Gama shiryawa cikin farin uniform Dina na student nurses, a karshen hannun akwai brown layette wanda yake tabbatar da cewar ni student ce. Na feshe jikina da turarruka masu Dadi sannan na zura abaya a saman uniform din, na kawo black duty shoe Dina na saka na dauki jakata all set. Anna na tsakar gida yayinda Nuzla Dake level one a maitama sule itama ta Gama shiryawa, Badi'a na daki tana bacci se Hunainah da zamu fita tare da ita. 


" Anna yau din Zaki je Masayan?"


Ta girgiza Kai tace


" Na Bari zuwa asabar se mu tafi Dake ko?"


Na danyi murmushi nace


" Allah ya kaimu, to mu zamu wuce"


Ta tashi tsaye tana Mana adduar nasara da Kuma taari tare da tunatar damu muyi addua mu Kuma kula da kanmu, hakanne a kullum se ta maimaita sede idan ba fita zamuyi ba ko Kuma bamuyi waya ba idan Ina hadejia. Ina fita wayata cikin pocket din Abaya ta ya fara ringing, nayi saurin cirowa na duba kamar zuciyata tasan shi ne, Dan Zuhra kawai ke Kirana da sassafe, to Kuma yau tasan ba tare zamu tafi ba.


" Good morning"


" Mhmm! Yau kinyi niyya kin dauka kenan?"


Na Dan harara wayar nace


" Haka ma zakace"


Yayi saurin fadin


" No! Ba Haka nake nufi ba. Ya Kika tashi? How was your night?"


Na Dan yatsina fuska nace


" Alhamdulillah! Naji kamar kana Hanya aiki zaka je?"


" Yeah! Aiki zanje nasan kema kin fita ko, Salis told me you're very punctual and I like that"


Na danyi murmushi bance komai ba, 


" Ba Wai tambayar shi na dinga Yi bafa, kawai Bayan kin fita he commended you"


Nace


" Ayya!"


Se yace


" Zan shigo Kano anjima, can I see you?"


Na danyi shiru Ina ayyana to dama baa Kano yake ba Amma se nace


" Allah ya kaimu"


Se mukai sallama na rike wayar a hannuna, ba laifi Yana da dadin hira Nuzla tace


" Adda waye? Yaya Ahmad ne?"


Nayi saurin kallon ta nace 


" Ahmad Kuma? Haba dai"


Tayi dariya tace


" Meye abin haba dai? Is it a crime?"


Nace 


" Yeah! It's karki Kara"


Se tayi dariya har muka karaso kowa ya Kama hanyar shi. Ina zuwa nayi signing sannan na wuce can ward dinmu, baa fi minti shida ba Sega Zuhra, she looks excited nace


" What's the news? Ban Nasha"


Tace


" Doctor zai zo anjima"


Nayi murmushi nace


" Ok! Ya zaayi kenan?"


Tace


" Na fadawa Anna zamu wuce can kawai, yace Wai dama yana son zuwa kinsan tunda ta dawo Basu hadu ba"


Na gyada Kai Dan lokacin data dawo yaje wani course India shiyasa Bai ga karamar uwar tashi ba. Wajen karfe Sha biyu na Gama dressing Ina wanke hannuna naji chief dinmu tana Kirana, nayi saurin karasawa tace naje preceptor na Kirana, there and then na gane Al'amin yazo kenan, na Dan goge fuskata da face wipe din Dana dakko daga cikin jakata, na saka wayata Ina haskawa har na goge ko Ina, Babu wani datti a jiki, to ta Yaya zaayi aga datti yadda nake bautawa jikina. Balm na lakuto na shafa a lebe na, wata sister Rahma tana zuane tana ta kallona tace


" Unaisa ko dai keda Salis?"


Nayi saurin rufe fuskata nace


" Ba Haka bane ba fa"


Tayi dariya tace


" Cigaba da kwalliyar ki , Haka ake son mace"


Dole na maida balm din na fita Ina zumbura Baki, ta Yaya ma preceptor da ya kusa ya Dani, tab Allah ya kiyaye min na aure tsoho, nafi son na aura yaro muyi kuruciya tare. Rayuwa kenan, this has always been my dream Amma da na hadu da honorable se na manta abinda nake so da Wanda ba naso, a son shi kaina ne kawai ban manta ba. A kofar office na same shi Yana kallona har na karaso na gaishe shi yace na Shiga ana jirana. I felt ashamed da ban tambayi waye ba kawai na shiga. Yana zaune Yana kallon kofa wayar shi Kare a kunnen shi, sanye yake da wani men lace Blue me haske irin sararin samaniya, plain aka dinka shi Babu wani kwalliyar, Amma believe me ya Yi Masa kyau hade da Kara haskaka fatar shi da take da Dan duhu Amma ya fini haske, kanshi sanye da hula da ta kayatar da shigar tashi. Muna hada idanu ya sakar min murmushi Wanda dama a fuskar tashi yake


" Mummy na samu kina bacci shiyasa ban tashe ki ba, Kuma Amra tace kanki na ciwo shiyasa Baki fita ba"


Ya shagwabe fuska Wanda yasa na kawar da Kai saboda tsaf zai iya charming Dina da hakan


" Haba Mummy, bazan Jima ba Zan dawo Allah"


Ya Dan zaro idanu yace


" Noooo! Mummy haba dai ai Dake Zan fara fadawa."


Se Kuma yayi Mata sallama ya kashe Yana Dan dariya yace min


" My mother kinsan Wai cewa tayi Wai ko wajen budurwata nazo? Na fada Mata?"


Na kalleshi a karkace nace


" Ni budurwar ka ce?"


Yayi murmushi yace


" Hajiya Unaisa zauna Mana"


Na noke kafada nace


" Ni sauri nake, lokacin medication ya kusa"


Na fada Ina kallon wristwatch din hannuna, 


" Zauna na fada Miki relationship din mu"


Na samu na zauna kujerar dake kallon shi Tate da bashi dukkan hankalina, nasan zakuyi tunanin Ina son yace Yana Sona ko? A'a bansan me yasa ba hakan Bai zo kaina ba kawai abinda nake son sani menen ya daukeni.


" You're my best friend, my Buddy"


Na danyi murmushi nace


" Da gaske?"


Yace


" Da gaske fa! Kinga tunda mu kawaye ne zamu dinga fadawa juna komai Babu boye boye. Haka ne?"


Na gyada kaina se yayi dariya tare da mikewa yace


" Bari na gudu, Mummy Kar tayi fushi"


Nima na Mike tsaye nace


" Aikuwa dai ka gaishe ta"


Ya saki murmushi Jin Dadi yace


" Mummy zata ji take care se munyi magana Friend"


Na gyada Kai na muka fito tare, na wuce ward ya wuce wajen SOPD. Ni na fara fitowa wayata a hannuna Ina kokarin dialing number Al'amin, a ganina ya kamata na ji yadda yaje gida, tana fara ringing nayi saurin katsewa Ina tuhumar kaina dalilin da zaisa na kirashi. To Amma ai ni dashi abokai ne Kuma a friend should stand for a friend. Ward dinsu zuhar naje muka taho tare se gida. Muna zuwa gidan ya kacame da aikin tarbar Yaya khalifa, Muna shiga Anna tace


" Karku sake kusa Mana hannu, ku wuce can kuje kuyi wanka Banda warin asibiti Babu abinda kike"


Aseey ta fara dariya, na Harare ta, Zuhra tace


" Ke Kuma yaushe Kika zo?"


Tace


" Naje gida Dada tace kina nan ai"


Muka wuce daki, ita ta shiga toilet din Anna no na shiga na dakin mu, kafin wani lokaci mun fito, ta shirya cikin lace me kyau me duhu kasancewar ita fara ce Amma fur Taki yadda na shafa Mata powder. Na kwallawa Anna Kira da ta amsa nace


" Anna Wai ba zata shafa ko powder ba"


" Zuhra karki barni nazo ranki zai baci, Haka Zaki je gaban shi kamar ta bargazuzu"


Me zamuyi Banda dariya, ta Bata Rai ita a Dole ta kulu seda na Mata Yar karamar kwalliyya se tayi kyau. Anna da ta shigo tace


" To ko kefa? Ai idan kana da kyau ka Kara da kwalliyya idan ba Haka ba na bashi Asiya"


Aseey ta kwalalo idanu tare da fadin


" Allah Anna Nima Ina da saurayi na fa"


Mukai dariya, Bai Jima ba yazo bayan munje min gaisa muka barsu tare muka dawo gyaran gida, ko Ina ya koma das sannan muka koma daki muka zauna anan na tarar da call din Al'amin da nayi missing, Kuma lokacin na tuna Ashe na Kira shi


" Unnie! Ina Kika jefar da wayar?"


Shi ne abinda ya fara tambaya Bayan ya dauka nace


" Kasan meye Unnie?"


Yace 


" Menene?"


" Ana nufin sister in Korea"


Ya danyi dariya yace


" Har wani yaren kikeji, you really are amazing. Amma kinsan kawai short din sunanki ne"


Na gyada Kai alamar na fahimta, muka gaisa na tambaye shi Mummy yace tana lafiya sannan nace ya Bari muyi magana anjima Ina da Baki. 


A hankali ba tare da na fahimta ba se Al'amin ya.zama someone very close to me, har ya ture kujerar Ahmad. Dukda ni kaina Ina ayyana ba Wai kawance muke ba ko yanayin wayar mu zai tabbatar maka we're confuse, Amma ni dashi min Bari a kawance muke. Mun kasance komai a kudundune muke yi, a bangare na Babu Wanda ya San shi Dan kumbiy kumbiya kawai nake a buna. Ana Haka posting dinmu ya Kare zamu koma hadejia, kafin zuwan lokacin da zamu koma da daddare Abba da Dada suka zo, ranar ba wuta ga zafi da ake kamar zaka cire kayan ka, damuna ta riga ta wuce kiris ya rage sanyi ya shigo, Ina zaune na kunna lantern Ina saka Mana shawl ni da Zuhra saboda sanyin school. Badi'a na Kan keke tana dinka Abaya Dan ita abinda ta iya kenan dinki, har da ta Gama js3 Anna tasa ta wajen top fashion designers dinnan ta koya dinki, idan ta dinka Abaya se kace ba local made bace. Nuzla na danne danne a waya, idan kana neman matar zuciya ka samu Nuzla kawai ka Gama, donut aka kaita ta koya, physical classes Amma data dawo dukkan kayan se ni ce nake dauka idan Naga wani recipe a ig na gwada, tun Anna na fada har ta rabu da ita, to a hankali Kuma se muka ga tana catching interest a kunshi, tana following yawancin manyan masu zanen kunshi, to shi ne da weekend Anna ta tura ta can wata unguwa take koyo, to ita Bata saka Abu a ranta ba kamar mu ba masu nacin gaske. Tace Mana shi ne kadai abinda zata Mana na gata, Bayan karatu se Kuma Sanaa dogaro da Kai, to hatta Hunainah steps Dina take following tare muke saka da ita. 


Sallamar Dada yasa dukka muka aje abubuwan hannun mu Muna Mata oyoyo, ganin ita kadai yasa nace


" Dada ke kadai Zuhra fa?"


Ta tabe baki tace


" Wai ke da Zuhra Baku gajiya da juna, da yaushe kuka rabu? Ni da Abban ku ne a waje"


Anna tayi saurin mikewa tana fadin


" Kuma se ki bar shi a waje Yayah, Adda jeki shigo da Abban ku"


Na mike na saka hijab na same shi a tsaye jikin mota har kasa na durkusa na gaishe shi, da faraar shi ya amsa yace


" Ya asibitin? Har yanzun ko allura baayi min ba"


Nayi dariya nace


" A'a Abba Dan Allah stay healthy! Wanne irin allura Kuma"


Shima yayi dariya yace


" Wai Dan na tabbatar my kids are doing well"


" Inshaaa Allah we'll make you proud Abba"


Daga Haka na bashi sakon Anna muka shigo tare dukka muka gaishe shi ya zauna kan sallayar da na shimfida Masa, daki muka koma Dan Basu guri sui magana.



Unaisa is not free, pay N300 to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria and send evidence of payment to ***