Chapter -11
by @maidambu41
_....ZAYN MALIK....✿_
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
Mai_Dambu
CHAPTER-11
KADUNA
Yana zaune yana me mika dogayen sawun shi a saman kujeran falon Hajiya na can gefe akan abin sallah aka shigo da sallama.
Samir ne da wasu abokan shi suka shigo.
"Assalamu alaikum Hajiya bar da warhaka" juyawa tayi ta zuba musu ido. Kafin yayi sallama daga lazumin da take ta ce musu.
"Ban kanku mutanen Habuja. Samiru"
"Na'am Hajiya" ya Zubawa Zayn idanu.
"Soldier wurin ka muka zo fa!" Juyowa yayi yana me kallon su kafin ya mai da idanun shi tv.
"Samir AbdulMalik anya zai duba al'amarin nan kuwa?"
Juyawa yayi ya kuma kallon Zayn.
"Zayn wurin ka muka zo fa please ka bamu lokacin ka mana"
Tashi yayi kafin ya nufi hanyar waje kamar dai kullum da gajeren wandon shi.
"Anya zai yarda?"
"Me zai hana, taso muje" haka suka fito yana zaune a balcony na part din shi, domin an yi masu part din kowa a gidan har Abdulrahman dan Baba Uwaisu, shima yana da nashi part din dan filin babban fagi ne. Yana ganin su ya daura daya akan daya ya shiga murza mandular shi, kunnata yayi da shana, sannan ya zuba musu idanu.
"Kar ka kuma min maganar wata deal a gaban hajiya na, domin zan karya kashin wuyar ka, ina jin ku"
"Allah ya huci zuciyar ka, dama wani kuskure aka samu, mun yi odar wiwi daga India, tare da wasu kwayoyin shine aka samu matsala hukumar mu ta hana shige da fice na kasar nan kasan snan muke aiki, toh wallahi sun kama kayan. Kuma mun ji labarin chief of Army staff da shugaban custum zasu duba kayan ana samun nawa za a iya koran mu a aikin ne."
Zuba gwiwar shi yai su suka yi a kasa suna faɗin.
"Mun san akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin ku da chief ne muka zo shima kuma shugaban custum din mun sani please domin kai ne sojan da yayi nasaran aikin da aka kasa yi kuma ko gobe suna bukatar ka a hukumance "
"Shi yasa zaku yi amfani da wannan kusancin na zalinci kasata?" Ya basu amsa.
"Please Zayn kai ke kawai zaka iya mana aikin don Allah zamu rasa aikin mu kuma kasan iyali muke da shi, don Allah ka rufa mana asiri "
Tab'e baki yayi sannan ya kai wiwin bakin shi ya mata zuka daya sai da ya gama da ita sannan ya juya gare su.
"Ba zan shiga maganar ku sai nayi bincike "
Mikewa suka yi dukkan su, tare da cewa.
"Mun gode"
"Ku rike godiyar muga abinda hali yayi " ya fada yana me lumshe idanun shi.
Juyawa Samir yayi yana kallon shi, yana tuna tun yarantar su, Zayn bai tab'a barin wani abu ya same su ba, gashi Allah ya mishi kamar kamar shara'a, baya daukar reni duk da shine kasa da su, sai Muhideen da yake bin shi, amma bai tab'a barin wani mugun abu ya sa me su ba, amma su a wurin mahaifiyar su kamar ta kashe Zayn take ji.
Bude idanu Zayn yayi kalli yadda Samir yayi zuru zuru ya fahimci baya cikin kwanciyar hankali.
Dauke kai yayi yana me jan tsaki babban tashin hankalin shi a duniya yaga daya daga cikin family member din shi cikin tashin hankali.
Ya jima yana sakawa da kwancewa kafin ya fita daga cikin gidan. Cafe ya nufa a can ya yi binciken abinda yake ganin zai taimaka mishi. kafin ya fito hango yan mata yayi suna hoto a jikin motar shi, ya koma gefe ya tsaya.
"Inayat wancan kamar Zayn?"
Dawowa yayi tana me leka plat number motar shi.
"Shine, me ya kawo shi nan har ake daukar hoto a jikin motar shi?" Ta tambayi Kawarta, hango shi tayi yana tsaye yana kallon yan matan.
"Toh ki kore su mana"
"Hmm!" Isa wurin motar suka yi.
"Malamai meye haka?"
Cikin isgilanci dayan ta ce.
"Da muka yi uwar me?"
"Ohh ku b'ace kafin na kira muku security"
"Ai ke Yar uban waye? Ba zamu matsa ba"
Dake taji haushin abinda suke kawai ranta ya b'aci kaiwa yarinyar Mari Inayat tayi, yayi maza ya rike hannun ta.
A hankali ya sauke hannun,
"Zagina tayi fa"
"Did I ask you?" Bata rai tayi tana hararan yarinyar.
Zuba musu ido yayi suka matsa a jinin motar. Budewa yayi ya shiga a hankali ya ciro toothpick din bakin shi.
"Ki daina saurin hannu Becareful"
Daga haka ya rufe motar ya ja abin shi yayi gaba.
Yana isa gidan ya hango Motar uncle Bashir.
"Hmm" ya fada, sannan ya nufi cikin gidan. Zai wuce kawai yaji yana son leka Hajiya Umma daga bakin kofar yaji muryan ta cikin sababi.
"Eyyee, wato ga sauna kira mini shashasha idan kin ga sakarai ku tawo tare, idan da ka gaya min ba zan yarda ba inji waye? Bashiru yaushe ka koyi mugun abu? Ikon Allah yau naga abinda ya dame ni, toh maza kasan yadda zaka yi Zainu ya koma aikin sojan shi ina cewa da sanin ka na hana shi! Toh yau ba gobe ba, na saka shi ya kome"
"Allah ya huci zuciyar ki Inshallah idan muka dawo da ga kasar waje zan yi yadda zai koma "
"Kamar ya koma nace da rantalelen kanka a wurin sam ban san lokacin da ka koyi mugun hali ba wanda nasan ba ni na haife ka dashi ba, Auta yanzun irin halin da ka jefa Zainu a cikin shi kenan?"
Fashewa tayi da kuka tana salati.
"Da da iyayen shi amma an mai da shi Maraya kowa na da abin yi shi an mai da shi shakatafi."
"Assalamu alaikum!" Ya shiga da sallama,
"Sannun dan nan, Ayyab bawan Allah mutumin kirki kaf gidan nan babu masoyan mu , nice nan na san zafin ka na san ciwon ka taya ba zan shirya barin gidan nan ba mu kama haya?"
Sauke numfashi yayi sannan ya ce mata.
"Hajiya ki kyale su idan na samu aiki zasu ga abin mamaki"
"Ai dole nasan saka aikata kai da Allah yayiwa gata sai ka ɗauki halina da zuciyata. Ba irin su oo ba mugun halin su yana tare da su"
Ta fada tana hararan uncle Bashir.
Gyara zama tayi sannan ta ce mishi.
"Zainu ya batun aure?"
Kallon ta yayi a ran shi yake jin lallai yau Hajiya rigima take ji na hakika.
"Hajiya ai ban samu sauki ba" ya fada yana had'e rai, tare da daura kafar shi daya akan daya.
"Ina kasamu lafiya dan haka aure babu makawa zaka yi shi ko Hajiya?" Uncle bashir ya saka baki.
"Anyi da kai? An kira sunan ka? Mun kula ka a maganar mu? Bakin halin wasu ya ja musu, Zainu na ina jin ka" ta gwatsile Uncle Bashir.
Sam Uncle bashir baya gajiya da halin su hajiya ne da ko hiran su aka ce ya shiga na zai na shiga ba, domin Hajiya Umma ba kyale shi take ba.
"Zainu ina jin ka, kace baka samu sauki ba?" Yadda ta hade giran sama da na kasa zaka iya rantsuwa Hajiya bata tab'a murmushi ba, dan haka ta cigaba da cewa.
"Yarinyar nan Aniya take ko Inayat toh tace tana sonka dan haka dole kasan nayi domin ni ba sakarya bace a maidani bitalman maza tashi muje wurin Likitan da ya duba ka, sai ya bayani kudina domin ban had'a hanya da mahaukata ba, na gaya maka domin idan na rantse sai ka biya ni kudina."
"Hajiya nifa bana son yarinyar domin yar iska ce" ya fada yana kauda kai.
Sake baki tayi tana kallon shi, kafin ta kalli Uncle Bashir tana mishi kallon zargi anya bashi ya fadi wani abu akan su ba, da lokaci guda Zainu ce Yarinyar yar iska ce.
"Zainun Hajiya kar ka yarda a zugi min kai, yarinyar tana da kirki wallahi karka ga kayan da ta kawo min"
"Hajiya yaushe kika zama yar rashawa?"
Zaro idanun tayi tare da mishi dakuwa da hannu.
"Ungo naka nace Zainu ungo naka, kaga dan banza me kama da dodanni dube ka sai kace itacce kuka dan kaniyar ka dan ina kyale ka, yanzu na dauki muciya nabi kanka dashi. Bari ka gani ma" ta fadi haka tana me nufar kitchen, bayan taci Uban dammara, kamar zata dambe.
Ko kafin ta fito ta samu dukkan su babu nan, tsaki tayi tana faɗin.
"Da baku gudu ba,da kun ga yadda ake karban rashawa.
Kallon juna suka yi shi da Uncle Bashir, kafin suka tsaya a balcony din Zayn.
"Akwai magana a bakin ka" dan tsaki yayi kafin ya ke bashi labarin abinda suka yi da Samir.
"Gara ya rasa aikin shi ai, uwar shi zata yi hankali ta daina bin yaran wasu da sharri."
"Duk haka bai taso ba, za'a duba al'amarin amma dole idan yana da hannu a ciki zasu dakatar shi domin samun shi cikin al'amarin haka kuma zai tab'a mutuncin Abba ne ."
"Gaskiya domin haka zai shafi matakin shi na tsayawa a takarar da zai yi, yanzu me kake tunani?"
"Zan gwada ganin Chief of army staff da controller general muga ko haka zai bamu nasara " dafa kafadar shi Uncle bashir yayi sannan ya ce mishi.
"I trust you Kuma zaka iya insha Allah "
Shiru yayi kafin ya ce mishi.
"Uncle amma da taimakon ka kome zai tafi." Cike da mamaki yake kallon Zayn.
"Kamar Ya?" Gyara tsayuwa Zayn yayi sannan ya mishi bayanin yadda kome zai tafi.
"Idan aka samu matsala fa?" Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"A rayuwata ban tab'a saka abinda ta shafi ahalina na fadi ba, dan haka saka ido kayi kallo tabbas zamu yi nasara "
Murmushi Uncle bashir yayi mishi irin murmushin ban tausayi,
"Ya kake min wani irin kallo "
Cigaba da kallon kofar waje suka yi daidai shigowar Hajiya Umaima da wasu baki mata.
"Wannan matar tana da matsala ban san meye damuwarka da ita?" Zayn ya tambayi Uncle bashir,
"Kawai niman sunan ta ne yayi yawa "
"Tunda ba akan ka take ba ai da sauki kowa ya dibo da zafi bakin shi ." Daga haka ya shige dakin shi Uncle Bashir yana jin lokcin da yake saka key.
"Banza ba shigowa zan yi ba"
**
Denmark
Mimmikewa take jikin ta yana daukar wani irin rawa, tare da kara murza gaban ta, tana kara mikawa, kafin ta sauka a gadon ta dauki dildo din ta, a tsugune a wurin ta dauki abun tana sakawa a gaban ta, aikuwa bata wani dauki lokaci ba, ta shiga sauke ajiyar zuciya tana shafa gaban ta, jikin ta yayi mugun sakewa, dan haka ta koma saman gadonta, ta kwanta tana jin cinyar ta da mahadar maranta yana ciwo, shi kan shi clitoris din ta zafi yake mata, ga uban ciwon kai da damuwa da ya mata yawa, dakyar ta mike ta nufi ban daki, cika ruwan zafi tayi sannan ta shiga ta wanke jikin ta, tare da wasu sabulai, sannan tayi wankar tsarki duk da bata da wani cikakken sani a cikin addinin musulunci amma tasan wanka ya wajaba akan ta, sannan tana sane da abinda take aikatawa kuskure ne babba. Haramun ne a cikin addini. Wanka tayi sannan tayi alola me kyau, kafin ta fito ta shimfida abin sallah ta fara gabatar da azahar da ta rasa kafin ta daura la'asar, yadda zaka fahimci masifa ce ta fada mata, sallah ta a cike take yin shi, bayan ta idar ta fashe da kuka, ta kasa ko addu'a, sai ma dunkule hannun ta da tayi, shi kan shi Ibadar ta koya ne a wurin wurin Makotan su dake su din yan ilori ne, bayan nan ba zata ce tasan wani abu a da ya shafi Addini ba, sai dai Ustaz Ali ya gaya mata zina, luwadi, madigo, istimina'i, shirka, sata, kisan kai, duk haramun ne a musulunce, dan haka dole bawa ya nisance su, idan ta koma ta gefen Mahaifiyar ta yar addinin Kirista, shima haramun ne a cikin bible, bata san me yasa tafi jin karfi da kaunar musulunci ba kodan shine Addnin mahaifin ta, oho amma bata son wani Addnin,
Wacece ita?
Titilopemi Abdul Ganiyu Ademola, shine cikakken sunan ta, amma sunan ta na Musulunci.
Azimah Abdul Ganiyu, budurwa ce da bata wuce ashirin da yan kai ba, yar kasar Nigeriya, mahaifin ta Mr Abdul Ganiyu Ademola, dan garin Edo ne attajiri na bugawa a jarida, mazauna garin Abuja, Mr Abdul Ganiyu Ademola ya fito daga babban gida ne kasancewar gidan su, ana bada maganin gargajiya tun daga gidan sarki ake zuwa amsa har zuwa gida sauran mutane, daga sauran garuruwa.
Ire Ademola Ades, dan Addinin gargajiya ne, wanda yake da mata rututu, dayawan su ma sun kasance marasa lafiya ne daga jinya sai ya aure su.
Ana cikin haka ya hadu da wata bafulata da ta samu tabin hankali, iyayen ta suka kawo ta jinya, duk matan da yake aura mata suke haifa mishi sannan dayawan su shawa'a ce take saka shi auren su, lokacin da aka kawo Bodd'i sai Allah ya daura mishi kaunar ta, kamar zai boye ta, dan haka ya samu iyayen ta da rokon su bashi auren ta, zai musulunta, kuma zai mata jinya sadaka.
Shiru mahaifin ta yayi kafin ya samu Yan uwan shi, suka tattauna. Babu musu suka amince baki dayan su, sannan suka bashi auren ta, bayan ya musulunta, sannan ya cigaba da jinyar ta, cikin Ikon Allah sati biyu da fara jinya kuwa ta fara kokarin samun lafiya, shi kan shi bai nime ta ba, domin ya san bata gama warkewa ba, kuma ita ce yarinyar karama sosai a cikin matan shi, dan haka jinyarta yake tare da renon ta, har ta samu watanni kamar bakwai a lokacin ne ya nime ta,, kasancewar shi mutum maji karfi da lafiya ba karamin fama yayi da ita ba, kafin ya samu biyan buƙatar shi.
Tun daga lokacin ya kara manne mata, ta sussuce akan ta, haka suka cigaba da zama har Allah ya bata cikin jikin ta cikin koshin lafiya tayi ta renon cikin tare da taimakon shi. Tana cika wata tara ta haifi dan ta Namiji, sai dai ko kallon abinda ta haifa baya yi ba, Allah ya amshi rayuwar ta, Ademola Ades karamin hauka ne bai yi a garin Edo, wanda daga karshe ya tattara ya bar cikin garin Edo ya koma kauyen su, idan yayi ta renon Abdul Ganiyu wanda ya taso babu uwa sai shi, a haka Abdul ya tashi yaki kuma saka mishi sunan al'adar su ta Yarbawa ya ce shi ba bayarabe bane shi bafulatani ne babu amfanin canja mishi suna.
A haka har Abdul ya kai shekara takwas a lokacin turawa suka shigo garin yawon bude idanu, sai aka samu akasi maciji ya sari daya daga cikin turawan, kamar zata mutu Abdul Ganiyu ne ya bata magani dan shima abokanshi sun ja shi yazo suga turawa, anan ne suka samu jikin ta ya fara kore kore, kasancewar garin babu me magani irin Ire Ademola Ades yasa aka fara batun kaita, sai ga Abdul Ganiyu shi ya duba kafar ya janyo wata yar karamar zabirar shi ya ciro magani kallon su yayi sannan ya ce musu.
"Ina son danyen kwai!....