Part 6
by @kwalisa
**
Washe gari xaukacin al’umar musulmi suka tashi da murnar qaramar sallah, sai da suka qare kacaniyar gama girki sallah da rarrabawa, sannan Fauziyya ta je ta feso wankanta ta zuba atamfarta Holland da Malam ya yi musu, atamfar ta fito da kyawun sigarta da kyawun dirinta mai tsari da yake gashinta baqi ne sixik kamar tana dyen, gashi da yawa sosai irin me aka kai har gaban goshi, hakan yasa ta yi kitso qanana zig-zag yiri-yiri gashi ya harhaxe ko tsagar ba a iya gani, gaba xaya ya yi baya sai sheqi yake yi, fuskarta ta fito sosai a ranar ta qara yin kyau fiye da kullum duk da yake ba wata kwalliya ta cava a fuskarta ba, farar powder kawai ta saka, sai wetlips mai qamshi, da yake kuma haqoranta a jere suke reras farare tas ga kuma ‘yar siririyar wishirya hakan ya saka data yi ‘yar dariya sai ta bada sha’awa da xauke hankali da wuya qwayar ido ta dubeta sau xaya tak ba tare da ta sake kallonta ba. Ta shafa turare das aka role one sannan ta yi xaurin daya dace da ita, ta kama can qarshen jelinan kitsonta tax an tufke abinta ta saka takalmi da gyalenta iri xaya ta fito xas-xas, Maimuna ta zo ta tsaya tana kallonta sama da qasa. Fauziyya ta yi murmushi tace “Me ye haka kamar yau ne kika tava ganina?” Maimuna ta yi dariya tace “Ni kullum sai in ga kina qara kyau sosai, kalli idonki ma ba ki sa kajol ba kuma baki sa jan baki 24 hours da jagira kajol amma kullum sai naga ke da ba kya yi kin fini kyau sosai, kuma idan muna tafiya sai naga mutane suna ta kallonki har su kixima da Aunty Maimuna da wannan qawayen naku su Habiba sai in ga kamar duk abinda kike yi sai sonata kallonki kawai”.
Fauziyya ta yi ‘yar dariya ta girgiza kanta tace “Ke ma in kin girma kin kai kamar ni za ki zama mai kyau” Maimuna ta tsale tace “Allah yaya Fauziyya Allah ya kai mu musha biki” tayi murmushi.
“Maimuna kenan sarkin shiririta ‘yar umma taso muje mu kai abincin gidan Hajiya” Maimuna ta xauko abincin suka fita suka shiga gidan da sallama Humaira tana jin sallamar su ta gangaro daga saman bene da gudu tana sanye da wata shadda tasha sirfani xinkin senagal tasha retouching, duk da bata da gashi sosai ya yi mata kyau ta zo ta rungume Fauziyya suna dariya sannan ta saketa tana qare mata kallo “Wai ubangiji ya yi baiwa a wajen nan Gimbiya kenan” ta doki kafaxarta tana faxin.
“Kin fara ko?” Duka suka kwashe da dariya Humaira tace “Ina tuwon Umma, ko karyawa ban yi ba wallahi ina jiran abincin Umma” Ta tafi da sauri ta buxa qaton flask xin miya tace “Woo! Fantastic daga buxewa har qamshin ya buge ni” Ta saka hannu zata xauki qatuwar cinyar kaza sai ga Hajiya nan ta fito daga kicin ta xauke flask xin Humaira kuwa sai ta bita cikin ‘yar tsokana wai zata qwace duka suka saka dariya Hajiya tace “Wato qarfi da Yaji kin maida ni kakarki, to yau ba za ki ci abincin nan ba don kin san wanda zan ajiye wa ga abinci nan kala-kala ki zavi wanda kike so” Humaira ta vata rai.
“Bana so bayan ke ba za ki girka ba sai dai a xauko wasu banzayen masu aiki su riqa yi mana abinci babu daxi daxaxawa kullum sai Alhaji ya yi faxa baya iya cin abinci gidan sai dai idan ni ce na je na yi masa, wallahi Hajiya ta iya girki duk ranar data yi sai kowa ya yi santi, Allah sa Alhaji ya auro ‘yar jami’a ai Hajiya kya riqa yi idan kika ga zata kwace miki miji” Duka suka kwashe da dariya Hajiya tace.
“Ai ina jinki aniyarki ta biki, kishiya ba a gidan nan ba” Dukan su suka kuma kwashewa da dariya Fauziyya ta zauna akan step dan ba zata iya jure tsayuwa ba saboda dariya, sai da suka qare dariyar Fauziyya tace “Kai dirama kenan ina son zuwa gidan kodan na yi dariya, a dole Hajiya tace kin maida ita kakarki” Humaira tace.
“A to ai ni da Hajiya sai Allah bari naje na sake tsokanarta” Fauziyya ta riqota tana dariya tace “Don Allah ki bari ki qyaleta haka nan...” Kafin ta rufe baki sai suka ji ihu da sowar yara suna oyoyo Mukhtar, oyoyo Mukhtar suka zubawa qofar shigowa ido sai ga yaya Mukhtar ya shigo duk yaran sun qanqame shi Fauziyya ta saki dariya tace “Yaya Mukhtar” Humaira kuwa sai taje da gudu ta faxa jikinsa tana dariya, Fauziyya ta fito ido tana kallon sakarcin Humaira tun yaushe suka daina wannan shirmen tun da quruciyarsu ta sake ido qasa tana wasa da gyallenta Hajiya ta leqo tana faxa tace “Ke Humaira wai sai yaushe za ki yi hankali ne sai kace wata qaramar yarinya?” Humaira bata ma san tana yi ba Mukhtar ya zuba idon shi akan Fauziyya cikin wani irin salon kallo Fauziyya ta kalleshi tana murmushi yana cikin wani xanyen boyal brown color ya fito da shi sosai duk qamshinsa ya cika musu gida, ganin irin salon kallon da yake yi mata ya saka ta sunkuyar da kanta qasa. Humaira ta kai hannunta daidai fuskarsa tana karkaxa hannu sai ya qifta idanu,sannan ya yi dariya haxe da shafa sumarsa da hannunsa, duk suka yi dariya ganin haka ya sa Fauziyya ta miqe zata tafi ya gano manufarta dan haka ya zo daf da ita ya tsaya yana kallonta cikin idonta fuskarsa taf cike da wani sirrin so da qauna, cikin murya qasa-qasa yace “Madam you look pretty today nice to see you” Ya yi shiru yana kallonta ita kuma sai ta dube shi tana murmushi tace ‘Yaya Mukhtar ka sauka lafiya?” Cikin kwaiwakyon muryarta yace “Na sauka lafiya” Har ya sata dariya ya bi ta gefenta yah aye sama ita kuma sai ta yi kasaqe kamar bata da kuzari, suna haxa ido da Humaira sai suka yi dariya su Humaira da qanenta suka bishi can sama suna hayaniya don sunsan Mukhtara ya dawo musu da tsaraba, Mukhtar akwai kyauta tamkar baya son abin hannunshi baya qaramar kyauta sam.
Fauziyya dai ko sallama ba ta yi musu ba ta nufi gida tana zuwa ta fara arba da Abdul da wani abokinshi sun zo har an kawo musu abinci na musamman sun gama ci suna shirin zuwa can su sameta.
Anan suka shiga hira yau Abdul ya qara yi mata kyau sosai yana sanye cikin shadda mirrow blue xinki tazarce ga takalminsa baqi cover shoe sabo fil yana sheqi, Abdul ya dameta da sambatun bege, saboda yadda Fauziyya ta qara yi mishi kyau da Annuri suna hira tasu taga yana neman zarewa da sambatu na shi,wanda ya yi nisa ba ya jin kira don haka tace zata je gida bacci take ji ‘Mu je na ga naki, ki yi kwanciyar ki anan” Ya nuna qirjinsa da hannu, Fauziyya ta rufe fuskarta da tafin hannunta ta fice da xan gudunta tana dariya.
Ranar ko sallama ba su yi ba sai kuxi daya aiko mata ‘yan dubu xaya ‘yan naira ashirin sababi da katunan murnar barka da sallah. Tana cikin karatun katunan Abdul masu sanyaya rai sai ga Abdulu qaramin qanin su Humaira, ya shiga da gudu yana haki Fauziyya ta dube shi a tsorace sannan ta xan Harare shit ace “Koma ka yi yo sallama ai Abban Fauziyya ya hanaka shigowa gidan ba sallama bare kuma cikin xaki” Da yake Abban Fauziyya qarami yana xan shakkarta bata sakar masa fuska da yake Hajiya duk ta shagwava shi wai shi auta, gashi nan a sangarce babu ladabi ba tarbiya ba xa’a don Abban Fauziyya ya zage yana tsawatar musu, sai daya koma ya yi sallama sannan ya sake dawowa yace “Wai ki zo inji Mukhtar” Ta sake hararar shi tace “Idan na kuma ji kace Mukhtar direct sai na zaneka, daga yau sunan shi yaya Mukhtar ka ji ko” Yace “To” sannan ya fice da gudu.
Mintina kaxan ta figi gyalenta, ta sa silifas ta nufi gidan tana tunanin dalilin da yasa yake nemanta, tana shiga gidan ba ta ga kowa ba taji hayaniyarsu can saman bene suna kallon talbijin.
Ta wuce can sashensa sai ta tsaya a qofa ta yi sallama sai qarar music da yake tashi a hankali a cikin waqar (maria carey) ta sake qwaqwansa qofar a hankali, can ta ji ya zo ya buxe qofar, ya tsaya yana kallonta yanzu ya sake wata shadda sababbi fil ash colour, xinki tazarce yasha aikin wuyan rigar bai ce mata komai ba, sai ya juya ya koma cikin hakan ya bata damar shigowa, haxe da sallama sanyi ac da qamshin turaren ya sax akin ya yi wani sanyi mai daxi,ta nemi kujera ta zaunashi kuwa sai ya xauki remote ya kashe maganar talbijin da yake kallo channel O sannan ya zauna a xaya kujerar ya dubeta ya saki sannanyar ajiyar zuciyar sannan ya ce “Wall ina son mu yi magana dake gashi ina bala’in jin yunwa kin san sai yanzu na samu kaina yara sun dameni, so shi ne na xan yi wanka”.
“Yaya za a yi kenan?” Ya dubeta a cikin idanu maye kallon da ta tsana kenan ta kalli gefe ta ce “Shi kenan sai in dawo in ka kammala” Ya kalleta ya girgiza kai yace “No, kije wajen Hajiya ki kawo min abinci kaxan” Bata musa masa ba tace “To” ta miqe ta fice ya bita da kallo har ta fice, sannan ya qurawa fuskar talbijin idanu.
Mintina kaxan ta dawo da diren silba xauke da flask da filet da jug da qaramin tambulan ta zo kan tebur xin gabanshi ya ajiye, zata zauna sai ya yi kiranta da wata irin siga daban wanda ya sa ta ji gabanta ya xan faxi ras, kaxan ta dawo ta haxa mishi abinci a flat duk yana bin ta da kallo tamkar zai cinyeta hakan ya haddasa mata slow active, ta riqa yin komai a hankali saboda jin kunyarshi, ta koma ta zauna tayi shiru tana yin saqe-saqe a cikin zuciyarta, tana nan a zaune yaje ya wanko hannu a kicin ya dawo ya fara cin abinci a yangance,kamar mai baiwa na goye, ko yaya tax ago kanta sai tag a idanunshi a kanta tsaf, ta ji duk ta takura da qyar take motsawa, ta ji haushi ya kamata kamar ta tashi ta fice daga xakin, gaba xaya duk kasala ta rufeta, saboda sanyin da yake surara a xakin, kuma dama barci take ji saboda jiya bata yi barci da wuri ba, suna ta kacaniyar aiki, sai daya xauki mintina da dama sannan ya kammala cin abinci ya rufe sauran ya je ya wanke hannu ya dawo sannna ya sake kiranta, irin salon maganar da ya yi xa zun yace “Zo ki zuba min lemon” Da qyar ta taso kamar bata so ta zuba mishi ginger drink mai sanyi ta ajiye a gabanshi, zata juya sai ya kamo gefen gyalenta, ta juyo tana kallonshi cike da alamomin tambaya a hankali ya haxe fuska cikin slow voice yace “Me kika fahimta a cikin qwayar idona?”.
“Ba komai” ya sake yin luu da idanun sa kamar zai rufe su a hankali ya furta “Fauziyya ina fama da ciwon qaunarki a cikin zuciyarta, Fauziyya ki amince min domin na zama abokin rayuwarki kuma uban ‘ya ‘yanki insha Allahu” Da hanzari taji gabanta ya faxi das ta fiddo idanunta, tana kallon shi a hankali ta zame jikinta ta dinga girgiza mishi kanta a hankali take furtawa “Haba yaya Mukhtar kar ka yi qoqarin ruguza rayuwata, don Allah kada ka qara furta wannan maganar, don akwai wanda zuciyata ta aminta da shi don Allah...” Mukhtar ya katseta a hasale yace “Impossible” ya taso ya zo kusa da ita ya tsaye cikin faxa-faxa yace “You better control your tongue,(ki san me kike faxa min) kin san yadda qaunarki take a zuciyata, ai duk duniya ba wanda nake tsananin qauna da bege tamkarki ina son ki fahimta b azan iya kwatanta qaunarki a raina ba” Ya sassauta murya cikin raunanniyar murya mai qunshe da salo na nuna tsantsar qauna da nuna mata ita ce gaba xaya rayuwarsa “Fauziyya please help me you are my life totally(kin tafi da dukkan zuciyata da ruhina) Fauziyya don Allah don girman Ubangiji ki ji tausayina, I become mad against your love, Fauziyya qaunarki tana azabtar da ni na shiga ruxani da damuwa da tamvele da buguwa a cikin mayen qaunarki da sallamawa da afkawa cikin haxari, faxawa kogin son ki kuma shi ne rabin rayuwata, please don’t let me down” Fauziyya ta sake ja da baya kaxan zuciyarta tana bugawa da qarfi kamar zata faso qirjinta cikin raunananiyar murya tace “Don girman Allah da darajar zumuncinmu ka qyale ni, akwai wanda nake qauna har abada...” ta yi shiru ya yin da tsohon ciwonta ya motsa gaba xaya a take zuciyarta ta soma narkewa, ta dafe qirjinta sai ga hawaye nan yana fitowa daga idanunta bakinta ya soma yin rawa kamar mai jin sanyi, Mukhtar yana tsaye yana dubanta cikin haushi, a hankali ya kamo hannunta ya riqe sannan ya sassauta murya yace “Please Fauziyya ki riqeni ni mai qaunarki ne har abada” Ta dube shi idanunta cike da hawaye a hankali ta zame hannunta daga cikin nashi jikinta a sanyaye tana hawaye ta bar xakin, Mukhtar yana tsaye yana kallonta har ta fice, ya koma kan kujera ya zauna cikin vacin rai ya xan buga tebur da hannunsa, haxe da rintse ido ya sa hannayenshi ya dafe kanshi ya yi shiru shi ya san abinda yake ji.
**