Chapter -12
by @maidambu41
ZAYN MALIK....✿_
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
Mai_Dambu
CHAPTER-12
"Me yake tambaya?" Mijin matar ya tambaya,
Daga cikin masu mishi tafinta ya gaya mishi.
"Danyen kwai yake so"
"Toh a kawo mana idan akwai bana son na rasa matata" ya fada a matukar uzirance. A gaggauce aka nimo kwan aka kawo mishi, ya haɗa da magani ya bata tasha, can kamar minti goma ta fara amai sai da tayi aman dafin macijin nan sannan ta koma jikin mijin ta tana ajiyar zuciya, wurin da macijin ya sara ya saka magana sannan ya cire hakoran macijin, kafin ya tattara ya ce musu.
"A kula da bata danyen madara zai taimaka mata wurin dawowa daidai "
Saboda farin cikin baturen ya rike hannun shi.
"Ai ba zaka tafi ba dole na biya ka"
Kallon me tafinta yayi sannan ya ce mishi.
"Nifa na yafe kawai nayi ne don Allah ba sai ya biya ni ba" dake kowa yasan Ire Ademola Ades a kauyen shi kuma mutumin ya mishi bayani, ganin yadda Abdul Ganiyu ya wuce bai ce kome ba, abin ya basu mamaki. Abokin shi Tunde ne ya ce mishi.
"Babanka idan yaji haka ba zai maka fada ba?"
Murmushi yayi yana faɗin.
"Ya hore ni na zama mai taimako shi yasa na taimaka, baba yana da abubuwan da ko ba a biya ni zai rike ni haka yake gaya min, ya ce burin shi na gaje shi a bada magani"
"Zaka gaje shi kuwa"
Bayan tafiyar Abdul Ganiyu baturen ya cewa tafinta.
"Yaron waye baban shi?"
"Baban shi wani me bada magani ne yanzu shakara goma kenan da ya dawo da Yaron bayan uwar Yaron ta rasu."
Ya gaya mishi kome akan Abdul Ganiyu.
"Zan biya abinda yaron ya min ta hanyar inganta mishi rayuwar shi da ilimin zamani, an jima zaka raka ni wurin baban shi."
"Ranka ya dade ba fa zai yarda ba, domin tsannanin son da yakewa Uwar Yaron yasa ya bar gari ya dawo nan kauyen da Yaron "
"Inganta rayuwar shi zan yi ba wani abu ba, sai dai idan ba a mishi bayani yadda zai fahimta ba."
Haka kuwa aka yi suka samu ire Ademola Ades, akan Abdul Ganiyu sai da ya basu kwanaki yana nazarin akan Yaron ya kuma tambayar shi ko yana son tafiya, amma ya ce mishi a'a ba zai tafi ya bar shi ba, babu me taimaka mishi, sai ta fahimci abu daya dan shi yana da tsananin biyayya da nutsuwa, haka yasa ya amince akan tafiyar shi karatu kasar Poland.
Domin ya fahimci wani abu daya dole Abdul Ganiyu ya fadada ilimin shi, domin shi ne zai gaje shi. Da wannan ya amince, ya kuma roke Mr Drone, akan kar ya bar shi ta fada wata addinin bayan na Musulunci da yake, kuma suka amince da wannan aka tafiya da Abdul Ganiyu kasar Poland.
Shi kuma Ire ya cigaba da kula da harkokin shi nan, har tsawon shekaru goma bai kuma san ya Abdul Ganiyu a idanun ba, sai da aka samu shekara goma sha daya, sannan ya tawo da Mr Drone. Ya kawo shi yaga mahaifin shi.
Farin cikin da murna babu wanda Baba bai yi ba, kafin suka dawo birni gidan Baba da yake Edo, anan ya gafarar da shi ga Yan uwan shi, sannan suka yi farin cikin ganin su, watan Abdul Ganiyu biyu ya gayawa Baban zai koma, domin a lokacin zai fara jami'a, inda zai karanci magani. Uban yayi farin ciki ya kuma godewa Allah da ya kawo mishi bodd'i har ta haifa mishi Yaro irin Abdul Ganiyu, dan haka ba tare da ja ba, ya amince sai dai ya ce kar ya dade kamar yayi na farko, kuma ya amince.
Kasancewar Baba Ire Ademola Ades yana da Yara kowa kamar ya goya Abdul Ganiyu yake shi yasa da zai tafi sai da ya ce musu ai ba aza'a bar shi ta tafi da tsaraba ba, suka kyale shi. Ya tafi abin shi.
Lokacin da ya koma fara karatun shi a bangaren Phamcy, inda ya samu shekara bakwai amma cikin sharu bakwai din nan yazo Edo sau biyu, sannan ya dawo Nigeria yayi bautar ƙasa, anan ne ya fara taimakawa mahaifin shi da aikin bada magani kuma yana kara inganta maganin sosai, Shekaran shi daya da dawowa Baba ya mishi aure da wata Yarinya me suna Iyabo, duk da shi yana Sallah, Iyabo kan Addinin gargajiya take yi, haka Allah ya azurta su da haihuwa tagwaye.
Dukkan su Maza inda aka samu Taye da Kande.
Farin cikin samun Yaran ba karamin dadi ya musu ba, haka suka cigaba da tafiya har yaran suka samu shakara huɗu, a lokacin ya tafi karatun masters din shi. Ashe ya tafi ya bar ta da karamin ciki, dake Ethiopia ya.tafi a can ya tafi karo karatun.
A can ya hadu da Erica racha, Yarinyar Model ce ga kyau da diri, dan wani hatsari ne ya haɗa su. Kasancewar wani safiyar Laraba zai tafi makaranta, sai ya tsaya a wani gidan cin Abinci. Yana cikin cin abincin ne ya ji wasu yan mata suna ihu a bayan shi, juyawa yayi ya ga ta rike wuyarta tana jan numfashi shi.
Abu daya ya zo mishi a wannan lokacin wanda bai tab'a ji ba, shine bugun zuciyar shi, kamar zai fado ajiye cokalin shi yayi tare da zuwa ya same ta, a hankali ya kai hannun shi bayan ta, yana shafa bayan tare da kai yatsar shi na hannun dama wuyar ta.
Ya tsokalo mata amai, aikuwa take sai ga kwayar masara da take ci ya fado ƙasa, da amai fuskar ta ya b'aci da amai da hawaye tare da gumi, a hankali ya janye ta daga jikin shi yana faɗin.
"Kuna kulawa da abincin da zaku ci idan kuna magana" sannan ya koma ta biya kudin shi da nasu ya koma gida yayi wanka, ya sauya kayan shi. Yana nazarin fuskar ta. Murmushi kawai yayi ya nufi makaranta.
Bai kuma saka ta idanu ba, kuma dai ya kasance yana yawo ziyartan shagon abincin.
Ita kuwa koda suka bar wurin ta samu kanta, sai ta shiga uzurin gabanta.
Sai dai lokaci zuwa lokaci tana yawan tuna shi ya taimaka mata bata mishi godiya ba, karshe haka ta tattara shi ta watsar.
A bangaren shi ba karamin damuwa ya shiga ba, domin itace macen da ya fara jin wani irin yanayi akan ta, har kusan wata uku , wani rana da dadare ya tafi Mall sayayya kawai idanun shi ya kai kanta da saurayin ta, jikin shi yayi sanyi, dan haka ya gama abinda zai yi yazo wucewa ta gaban su.
Har ya wuce ta biyo shi tana cewa.
"Malam ba kai ne ka taimaka min a gidan Abinci ba?"
Kallo daya yayi mata sannan ya kalli saurayin ta, kafin ya dauke kai bai mata magana ba, ya biya abinda zai biya ya bar shagon ai kuwa haka ta biyo shi har waje, yaki sauraren ta.
Karshe ta koma wurin saurayin ta, ta mishi bayani, amma ya share shima domin tayi ta bashi labari, amma bata ji dadin yadda ya share ta ba, bayan ya koma gida yaji damuwa sosai kamar yayi hauka ashe ita tana da nata rayuwar.
Haka ya cigaba da rayuwar shi kwatsam bayan sati biyu yana dakin karatu ta shigo ta zauna a kujeran gaban shi ta ajiye jakarta da ƙarfi. Kallon shi tayi.
"Ranar ka mai dani kamar mahaukaciya ina bin ka ina magana"
Mikewa yayi ya haɗa kayan shi, ya bar ta a wurin, abin ya bata mamaki. Kiri-kiri ya shiga bata wahala, ko wurin harkokin ta bata da nutsuwa, baki daya Abdul Ganiyu ya ki bata damar tayi mishi godiya shima kuma da gangan yake haka, kafin ta fahimci abinda yake mata ta fada yadda shima ya fad'a mata, haka dai yayi ta bata ciwon kai.
Sai dai lokaci zuwa lokaci yana bibiyar ta, ta hanyar tura mata da sakonnin rose da wasu kyaututtukan da bata san daga waye ba, ranar da ta cika shekaru ashirin da uku a duniya ya haɗa mata kaya na musamman ya tura aka kai mata, tare da cewa.
*Nasan kina busy amma haka bai hana ki zuwa ki ce zaki min godiya ba. Ki amshi wannan kyautar daga mutumin da kike bi domin godiyar taimakon da ya miki a gidan cin abinci*
Lokacin da ta ga sakon da gudu ta fito ko zata ga wanda ya turo sakon amma babu, sai dai ta hango wani mutum ya juya mata ba, a hankali ta fito daga cikin gidan tana me zuwa inda yake.
"Excuse me!" Juyawa yayi yana kallon ta.
"Kina son wani abu ne?" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce mishi.
"Meye haka? Kullum binka nake ina son na gode maka amma kaki bani fuska "
A hankali ya kalle ta,.tare da kallon bakin ta. Sannan ya juya a hankali yana kallon yadda take tsaye.
"Ok idan kika ce min kin gode shi kenan anan Alakar ta tsaya, toh ya zan yi da zuciya ta?"
Hannun ta takai bakinta, ta rufe jikin ta yana rawa.
"Ban gane ba?"
"Ina son ki " ya fada mata haka, sannan ya rab'a gefen ta zai wuce ta ce mishi.
"Ban gane ba"
"Ai ke ba kurma ba ce kin ji ni "
Daga haka ya wuce abin shi, bai kuma bin ta kanta ba, itama baki daya ta birkice ta rasa Meke mata dad'i. Baki daya ta kasa ganewa kanta, soyayyar shi ne ko damuwa ce, sai da ta fara kokarin ganin ta duba ko yana nan. Koda ta shiga makarantar ta bincika aka ce mata ya koma garin su, sai da tayi kuka dan bakin ciki domin jin labarin tafiyar ya sata kuka.
Shi kuwa Abdul Ganiyu da sanin shi yayi tafiyar, sai dai lokacin da ya koma, Nigeria yayi kokarin boye halin da yake ciki amma Baba ya gano shi, lokacin da ya tirke shi bai boye mishi ba. Dan haka Baba ya ce mishi.
"Ba zan hana ka ba, amma kuma kasani ba zan iya barin ka, ka zauna a can ba."
"Toh ba" daga haka ya bar dakin baban ita kanta Iyabo ta fahimci haka daga gare shi, ta fahimci sauyi me yawa, musamman da yazo mualama ta aure da ita, yadda yake mata kamar ba shi ba, dan haka ta kame kanta ta fita harkan shi har ya koma.
Koda ya koma Ethiopia abokan karatun shi suke gaya mishi yadda tayi ta zuwa, dan haka yana hutawa ya nufi gidan su, daga bakin get ya tsaya, ya tura aka gaya mata yana jiran ta, tana fitowa ta zuba mishi ido.
Bata tab'a sanin tana Masifar son shi ba, sai da yayi tafiyar wata biyu cif ta fahimci haka, dan haka tana isa gaban shi ta ce.
"Me yasa ka tafi?"
"Kina sona ne?"
"Waye ya ce bana son ka dama?"
"Ina saurayin ki?"
"Muje"
Ta nuna mishi kofar gidan, riko hannunta yayi tare da gaya mata waye shi din.
"Ina da mata da Yara biyu da cikin na uku! Ba soyayya zan yi dake na bariki ba, Auren ki nake son yi. Ina bukatar mace a kusa dani ne"
"Ina sonka amma ba zan iya binka ba, sai dai idan zaka aure ni mu zauna na lokacin da xaka bar kasar nan amma ba zan iya binka wani wurin ba. Shine iya abinda zan maka amma bayan nan ba zan iya binka ko airport ba. Shima Auren ajiye shi a sirrace sabida career ta."
Yana sonta yana kuma bukatar ta a lokacin, domin ko zuwan shi Edo bawai ya gamsu da Iyabo bane. Dan haka ya ce mata.
"Na Amince"
Juyawa yayi yana cewa.
"Amma ni musulmi ne"
"Babu matsala"
Ita kanta bata san me yasa ta amince da haka ba, har zai tafi ya ce mata.
"Erica racha!" Kallon shi tayi.
"Gobe kazo muje wani church da yake wajen garin nan" daga haka ta koma cikin gidan shima yayi tafiyar shi ba, yarda kawayen ta da iyayen ta sun sani ba, boye al'amarin tayi. Shima kuma yayi kokarin haka, washi gari ya bi ta har gudai suka shirya suka tafi aka daura musu auren a sirritacce,
Gidan ta da yake wurin ta kai shi, tun daga falon suka fara cinye kan su, har suka dangana da dakin da ta gyara shi ita da masu aikin ta, daga nan aka bude wani shafi na rayuwar aure, wanda kana gani kasan ana cin Uwar Juna, kamar yaya.
Haka suka kasance cikin kaunar juna, kamar zasu kashe junan su, a wannan yanayin taki yarda ta dauki cikin shi gudun kar ya shafi career ta, har tsawon shekaru biyu, suna tare duk wani nasara da take nima ta samu, kuma wani ikon Allah babu wanda ya san da wannan rayuwar da take.
Lokacin da Abdul Ganiyu ya gama.karatu ne ya gaya mata zai kome garin su.
"Ba zan iya binka ba tun farko kasan da haka. Dan haka gashi nan ka sallame ni"
Kallon ta yayi sannan ya ce mata.
"Ba zan iya rabuwa dake ba. Kuma ina rokon ki da karki bawa wani Kanki idan na samu lokaci duk bayan wata shida zan na zuwa duba ki"
Daga haka ya tafi ya bar kasar abin shi, sai dai yana isa Nigeria kasar America suka dauke aikin bai so amma haka ya tafi da Iyayen shi, kasancewar ya san maganin gargajiya da ta zamani sai abin ya kara sawa ya samu mahaukatan nasara ga kudi ga cigaba, ganin haka ya nufi Ethiopia.ya dauko.erica racha, suka kara baje rayuwar su kamar me anan ne ta samu cikin farko, tasha wahalar laulayi kafin ta daina watan cikin bakwai, ta haife shi dole aka saka Yarinyar a kwalba. Na tsawon wata biyu kafin aka sallame su shi ya cigaba da kula da yarinyar da uwar ta.
A lokacin Baba ire yana da telephone ya kira ya gaya mishi, Erica racha ta haihu.
A take yayiwa Yarinyar suna inda aka saka mata A'isha Titilopemi. Sannan ya musu addu'ar fatan Alkhairi, sannan ya gaya mishi zai turo mishi Iyabo itama ta zauna a nan.
Duk da bai so ba, amma ba zai iya musa mishi ba, dan haka ya kama wata apartment ya biya kudin sannan ya gayawa Erica bata damu ba, domin tana son shi zuwa yanzun dan haka ta ce ba damuwa, lokacin da su Iyabo suka zo ya kai su inda zasu zauna ya xuba musu kome .
Sannan ya mata magana baya son tashin hankali, su zauna lafiya da Amaryan shi itama kuma Amaryan babu ruwan ta da ita kowa ya zauna lafiya.
Sai dai a ran Iyabo bata jin zata iya zama da kishiya bayan wahalar da tasha na zaman shi ya mata kishiya dan yayi kudi wallahi sai ta dauki fansa ba zata tab'a barin Erica ba, koda haka na nufin mutuwar ta ce ba zata iya zaman ganin shi da wata mace ba,.sai ta dauki fansar cikin amanar ta da yayi har akan tsinanniyar yar da aka saka mata suna Titilopemi wata har abada ba zan daina godewa Allah ba, ita yaranta uku babu wanda aka saka mishi sunan me alaka da Ubangiji...
ZAYH MALIK ISN'T FREE BOOK...300#