chapter 4
by @autarmama
👬ABUL-KHAIR👬
(the identical twins)
TSARAWA DA RUBUTAWA DAGA SALMEERT SANI SALMAN TRIPLE S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️🧚♀️)
*WANNAN LITTAFIN NA KUDINE ,KUMA WANDA SUKA FARA BIYA KAFIN A GAMA FREE PAGES TO ZAI BIYA #300 NE, WANDA KUMA BASU BIYA BA HAR AKA GAMA TO ZAI BIYA #400, IN KUMA BAKA DA RA'AYIN SIYA TA NAN, TO SAI KAJE CHAN AREWABOOKS KA BIYA KASHA KARANTUNKA CIN FARASHI MAI SAUKI KUMA CIKIN KWANCIYAR HANKALI*
https://arewabooks.com
*yi a Amfani da wannan 👆 link din domin shiga cikin manhajar kai tsaye*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alƙalaminmu ƴancinmu*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ,DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI,ALLAH INA ROƘONƘA YARDA NA FARA LITTAFIN NAN RANAR 6 GA WATAN ZUL-HAJJ, ALLAH KASA NA GAMA LAFIYA, ALLAH KA DAFAMIN A CIKIN DUKKAN LAMURANA, ALLAH KA CIKAMUN DUK BURIKANA NA ALKHAIRI , WANDA BANA ALKHAIRI BA ALLAH KA CHANJAMIN SHI ZUWA NA ALKHAIRI*
PAGE 4
"""""""""""""""""""""""""""Sosai Yaran in ta kallesu wata fargaba take luluɓeta , in kuwa ta kalli cikin idanunsu wani mugun kwarjini ne yake lulubeta.
wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, "lalle dole na nisanta ku daga gareni, domin nasan in banyi hakan ba kune zaku lalatamin rayuwa nan kusa", ta fada cikin zuciyarta , azahiri kuwa girgiza kai tayi kafin tace "lafiya , mai kikeso", ta fada tana kauda kanta daga kallonta domin wasu kibiyoyi da batan ko na menene ba da suke fitowa daga cikin idanunta.
"uhmmmm, dama Tuwo akayi kuma Twin batacin tuwo, shine nazo a bata wani abu", ta fada tana wasa da wani katon littafin da yake kan table din wanda da alama na record ne.
wata ajiyar zuciyar ta kara saki kafin ta tashi, a hankali wasu kwalaye ta nufa, da suke cikin Office din, biscuits da driks ta dauko tare da miko mata, bata bari din hada ido ba ta juya.
"Thanks", kawau tace tare da wucewa , saida takai mata taci sosai kafin , ta tashi tana cewa "Twin bari naje dinning", ta fada tana wucewa, batace komai ba dan tasan tana son tuwo sosai, shiyasa bazata iya hanata zuwa dinning din ba.
a hankali take tafiya amma komai na jikinta motsawa yake musamman hips dinta, fa har sunyiwa jikinta yawa, saboda ita ba wata mai kiba bace sosai sai uban hips, wanda in banda ikon Allah, Yarinya kamarta, da wuya ka ganta da irin halittar nan.
a hanya suka haɗu da Hajra, da plats hakan yasa ta tsaya danvtasan Abincin nata da dauko mata, karasawa sukayi ɗaki, anan suka ci abinci , bayan sun gama suka maida plats din, ɗaki suka dawo wanka sukayi kafin su kara shiryawa cikin kaya iri daya.
fitowa sukayi, suka nufi Class, dan komai da akwai cikin gidan akwai School sannan akwai Hospital ma, karami wanda chan ake kaisu in basa da lafiya.
2 hours suka dauka kafin su tashi, rike da hannun juna suka rankayo dukkansu Ukku suka nufo ɗakinsu.
***********************
Nanni ce, ta karaso kusa da shi, tana cewa "Sannu Lalle", ta fada tana shafa kanshi kai kawai ya girgiza mata, kafin ya wanke hannunshi.
mikewa tsaye ya yi, Abul ma mikewar ya yi, hanyar bari part din sukayi, da sauri Nanni tace "ya haka, baka karaa cinye Abincin ba zaka tafi, to wa kabarwa sauran", ta fada tana wurgawa Abul harara.
tsaki ya yi, tare da jan hannun Khair sukayi waje.
ita kuwa Nanni cewa tayi,"Shege mai idanun Kwaɗo, nasan kaine ma ka tsirawa Lele ido shiyasa ya kware, kana tafiya kamar Agwagwa na tafiya", ta fada tana zama kan kujera, kafin ta kwallawa wata Kunyaga kira "ke Ladiyo, Uwar mai kikeyu, ne ki maza kizo ki dauke wannab, kayan kike wani tafi kamar tsakon da ya fada masai", ta fada tana dalla mata harara.
ita dai Ladiyo, bata ce komai ba sai , wucewa da tayi, da kayan da ta dauka.
********************
Fada suka, nufa direct dan gaishe da Sarki, basu jira ison Sarkin kofa ba, kawai suka wuce, zubewa ya yi kasa yana musu, kirari, amma ko kallonsu basuyi ba.
takun tafiyar Zaratan Samarin nashi yasashi, dago da kanshi, aikuwa akansu ya sauke idanunshi , wani Yalwattacen Murmushi ya saki, yana sauke sanyayiyar ajiyar zuciya.
kusa dashi suka zauna, gaba daya fadawan gurin kasa suka zube suna cewa, "Gaisheeee ku, Ƴan Toron giwa, takawar ku Lafiya gaba Salamun Baya Salamun, Allah ya taimaki, Sarakunan gobe, Ɓalɓelu baku farin banzaba, bangwayen Sikari, kuwa ya jingineku sai ya sala, " suka fada a tare suna wani jinjina hannu.
Abul ne, kawai ya yi, murmushi tare da dago musu hannu, shi kuwa Khair, direct gurin Mai Martaba ya nufa, bai ma ko kalli inda fadawan suke ba.
jikin Mai Martaba ya shiga yana lumshe ido, hakan kuma ya tabbatar mishi da cewa Khair ne, domin shi yakeyi mishi haka, a gaban ko waye, shi kuwa Abul yana da matukar kawaici da hakuri.
ta dayan Side din na Mai Martaba ya zauna ya kasance sun sanyashi tsakiya.
sosai naga matukar kamarsu, dan dai shi, Mai Martaba, ya dan manyanta shima ba wani chan ba.
gaba daya Fadawan waje sukayi duka, fira sukeyi shi da Abul inda shi kuwa Lelen ba abinda yake cewa, dan nauyin bude bakinshi yakeji, sannin hakan yasa Mai Martaba, bai takurasa ba sai ma shafa kanshi da yakeyi, a hankali.
hakan kuma yayi bala'in yiwa Khair dadi da gar yakejin wani Bacci bacci na daukarshi, da yaje idanunshi lumshe suke hakan yasa baka gane komai a tattare dashi.
ga wanda zasu fara biyan kuɗinsu zasu biya #300 , ga wanda zai bari har a gama free to zai biya #400, ku biya kuɗinku ta wannan account number din👇.
1499884120
Umma salma sani. access bank.
ko katin waya ta wannan number👇.
***.
ku tabbatar kun turo da shaidar biyanku ta hanyar yin screenshot sannan ku turo ta wannan number din👇.
***.
Salmeert Sani Salman triples S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️🧚♀️)