FARAR MACE KO MAYYA CE

Episode 17&18

by @babybintuu

๐Ÿ‚ *FARAR MACE* ๐Ÿ‚


        *BY*


 *Ummu Sumayya*

```Vote me on wattpad ```

    *#Bintubaby*


*Elegant Online Writer's*


         *PAGE NINE*


Haka taci gaba da renon soyayyar sa azuciyar ta tun tana d'aure wa har abun yafara fitowa fili mahaifiyar ta tasani dake mahaifiyar ta y'ar kunga kunga ce nan take ta lallashe ta takuma ce "Muneef d'in me aiko Alhaji Omar kike so kamar kin same shine balle d'an sa kamar ma kin same sa kin gama ne sha kurumin ki kinji Autar Mom d'inta"

Ajiyar zuciya tasauke tofa tundaga ranar tafara koyar da ita y'an dabarun da zatayi tajanyo hankalin sa sannan tadinga amso mata wani jan kendir awajen wani bokan ta yace kullun idan dare yaraba takira sunan shi sau ashirin da biyar bayan ta kunna kyandir d'in idan tagama takwanta karta kashe kendir d'in domin tsaffen kendir ne, hakan zai zama kamar tana mai kiranye saida tajera kwanaki bakwai tanayi aiko nanfa Muneef yadinga mata hauka kiran waya kan kira ga kyautan kud'i da credit card dayake mata kullun zai tura mata 5k hakan ba k'aramin sake dilmiya ta akogin k'aunar sa yayiba,

Shiko Muneef gaba d'aya ji yayi duk duniya babu wacce yakeso irin Khalisat hakan yasa yabaro aikin sa yazo yafara fafutukar samun ta duk dacewa ak'ark'ashin zuciyar sa yana tsananin sha'awar Mufeeda da begen kasancewa da ita amma kuma atsarin shi bayason ba'kin mutun hakan yasa yake nuna k'yama agareta kwatsam kuma wannan abu yazo yasake faruwa agaresa tundaga ranar baya barci mai dad'i kullun da ciwon ciki yake kwana hakan yasa yamatsa ma Abba akan aje anema mai auren Khalisat koyaji sau'kin abunda ke damun shi.



      *Wannan kenan! Cigaban labari*



Tun daga ranar Samraat bata sake kwanciya koda ciwon kai ba kullun saita futa kuma duka ta aiwatar da aikin Durwanu binni ragon ne kawai yarage shima suna ta fafutukar neman d'an shekara d'aya ne ba'ki hakan yakawo musu tsaikon aikin,

Kusan kullun idan Fahad yazo takan lek'a shi ta window d'in sama sosai ganin shi da Mufeeda kesake tadar mata da hankali amma daga tatuna yakusa zama nata saitayi murmushi tsakanin ta Mufeeda kuwa ba sau'ki aiki take sata kamar jaka daga tadawo makaranta zatai ta tsiro da tsirfa iri iri har Fahad yazo wani lokacin sai Mom tanuna mata b'acin ranta take k'yale Mufeeda taje wajen shi dakuma tadawo zata cigaba damata aiki yanzu har tausa take sata kuma dole tayi ga duka abu kad'an zatayi takai hannu tadake ta,

Sosai Mufeeda tasake fad'awa cikin damuwa amma ita aganin ta gwamma azabtarwar Samraat fiye da akuyancin da Muneef yake k'ok'arin yi agareta,

Ak'arshe satin aka kawo kud'in auren ta da Fahad inda Abba yadam'ka ma Mom kud'in gaba d'aya naira dubu d'ari biyu wanda ya amsa na sadaki da komai da komai domin yace shi albarkar auren yake bu'kata haka suka rabu da iyayen Fahad d'in cikin sam barka kowa nayaba dattakon kowa,

Bayan yaba Mom dubu d'ari biyun ne ya'kara mata naira dubu d'ari biyar yace tahad'a tama Mufee order kayan kitchen sauran kayan furniture d'in kuma shida Mufee zasuje Dubai su zab'o ak'arshe yace ma Mom

"Sannan Samraat itama kice tafito da miji inkuma tana da wanda ta tsayar saiki ce tagaya mai yaturo iyayen shi kinga sai ayi komai tare wata d'aya da sati d'aya a'kasa saimuji sau'kin hidimar"

Jinjina kai Mom tayi kafun cikin damuwa tace "na tuntu'bi Samraat tafito da miji domin nikaina burina kenan amma saita ce ita yanzu bata da tsayayyen saurayi duk sunyi fad'a dasu dana matsa mata ma saita samin kuka wai dannaga Abban ta baya da raine zan matsa mata data fito da miji dole nak'yale ta naxuba mata idanu inata mata addu'a saboda gaba d'aya yanzu takoma kamar me aljanu"

Kai yagyad'a cikin jimami yace "ki k'yale ta Allah yafito mata da nagari yamata zab'in alkhairi"

Asanyaye Mom tace

"Amin ya hayyu ya qayyum" 

D'an tattauna wa sukayi akan investment products d'in nasu dake ta samun cigaba kullun anata dad'a sanin su afad'in Nigeria da kewayan ta sai dare yamusu sallama yatafi. 


Lokacin da Samraat da Muneef suka samu labarin kud'in auren Mufeeda da aka kawo ba'karamin tashin hankali suka shiga ba duk kanin su sun gigice har Mom taso fahimtar wani abu Muneef yayi pretending itako Samraat kuka tafashe dashi tana ri'ke saitin zuciyar ta tana wani shegen tari daya sar'ke ta, cikin tsananin tashin hankali sukai kanta

Dak'yar tarin yatsaya idanun ta sunyi mugun ja kamar wacce tajima tana kuka sannu sukai ta mata Mufeeda kuwa ruwa tami'ka mata amma saita kauda kanta gefe kamar bata ganta ba Muneef ne ya amsa yakafa mata bottle d'in take tafara sha saida tasha fiye da rabi sannan takauda kanta talumshe idanu kamar me barci nazarin ta Muneef yakeyi sosai tabbas amatsayin shi na likitan zuciya yafara fahintar wani abu agame da Samraat d'in k'yale ta yayi zuwa gobe su tattauna anatse haka sukai tajin tajin har dare suna palourn kafun Mom tace sutafi ita zata tsaya da Samraat d'in harta tashi haka kowannen su yatafi yakwanta.


Ahaka kwanaki sukaci gaba da tafiya bikin Muneef da Khalisat nata karatowa kowane fanni sai shirye shirye ake Abba shi yad'auki nauyin had'a mai kayan lefe Mom kuma tabashi wani had'add'en gida dake kusa dasu tace yagyara yazauna aciki gidan ma ba wani gyara penti kawai zai sake mai amma gidan yayi mugun had'uwa ba raini,

Sosai Mom take ma Mufeeda gyara na musamman ciki da wajen ta kuwa tayi order kayan gyara irin su tsumi cukui gumba tukud'i da sauran garurrukan magunguna masu k'arfin gaske datai order tundaga sudan harda turarruka masu shegen k'amshi tundaga kan humra fara ba'ka da ja gana tsigunno gana wanka ga dafe dafen tantabaru da kaji adafa wannan adafa wancan atasa ta dole taci ga dilka ana mata tayi wani fresh sai walkiya da wani sihirtaccen k'amshin turaren da aka had'a mata na wanka dana shafawa ga na hayak'i gaba d'aya tacanza tayi wani mugun kyau kamar kasace ga uwa uba k'amshin datake zubawa KO mace taji sai tasake kallon ta ita kanta saita ta ta'ba jikinta tanajin kamar ba nata ba sometimes har shinshina kanta take saboda k'amshin jikinta ba k'aramin dad'i yake mata ba,

B'angaren Maamin ta ma ba'a barta abaya ba sosai take gyarata da kaya masu kyau duk da tasan Mom na mata amma itama tana m mata sabida bata so mijin yaraina mata y'a gwara idan yashiga yaji komai zam xam ba raini kenan, dake itama Maamin yanzu takama shago tana saida abinci kala kala kamar restaurant haka wajen nata yake har ma'aikata tazuba masu girki da masu kaiwa kuma Alhamdulillah komai yana tafiya yanda yakamata yanzu kud'i sun fara zaman mata,



Tun da yasamu labarin auren Mufeeda hankalin shi yayi mummunan tashi gaba d'aya yarasa natsuwar shi a y'an kwanakin musamman yanzu da duk week sai yaje kano sosai Khalisat ke tadar mai da hankali a fakaice tai ta abu kamar yarinya musamman data lura yana son shagwa'ba ga uban perfume datake sa ma jikin ta wanda hakan ke sake narkar dashi a shaukin son ta daure wa kawai yakeyi har biki yarage saura one week inda na Mufeeda yarage sauran three weeks akullun yaga mufee hankalin shi sake tashi yake musamman dayaga kullun k'ara kyau take uwa uba k'amshin datakeyi yana tada mai hankali ayanzu kam ya ayyana saidai Fahad ya auri sauran shi danko baiyi sex da Mufeeda ba zai yi hot romance da ita domin yarage abunda ke damun shi haka yayita sa'ke saken neman mafita kafun lokaci ya k'ure mai yabar gidan.


Samraat ta aiwatar da duk aikin Durwanu kuma sun koma geresa inda agaban su yasaka kaza da ranta yadaka ta aturmi harta mutu saida tadaku sosai yazuba wasu kalan sabulai da garirrikan magunguna aciki yace tadinga wanka da sabulun tatabbatar duk yi Fahad yaji k'amshin hakan zai sake temaka wa yadawo gareta, haka tadawo da sabulu amma cikin rashin sa'a sai taga Fahad yad'auke k'afa da zuwa da bugun ruwan cikin Mufeeda taji yaje wani work shop a Jamaica akan aikin sa haka tafara k'irga kwanaki yadawo shiru har biki yarage saura two weeks aka shiga satin bikin Muneef daya rage two days kwatsam aranar da yamma saiga Fahad kamar yanda Mufeeda suka saba fira a sit room yauma haka amma abunda yad'an d'aure mata kai shine yanda taga yazo yanata mazurai kamar anmai dole yazo data tambaye shi yace lafiya daga haka ma yami'ke yace zai wuce sosai jikinta yayi sanyi ita tad'auka yanzu zaita d'okin tane yana yaba k'yan da k'amshi datake sai taga ba haka ba gaba d'aya yasauya mata gaba d'aya saitaji wani iri amma tashare tasa aranta k'ila gajiya ne haka suka jero dashi domin tasaba indai yayi tafiya yakan kawo mata tsaraba to yauma tayi tunanin zai bata tsaraba shiyasa zata rakashi


yau ba fira suke ba sai wani basar da ita yake gaba d'aya ita saita tsorata dashi har sun kawo parking lot ne har yashiga mota saiga Muneef yayi parking bisa mamaki saitaga Fahad yafito yana washe ma Muneef baki yana fad'in "Allah yatai maki big bros ashe abu yazo? To Allah yanuna mana yasa alkhairi" 

"Uhmm amin ya Allah thanks" yafad'a yana watsa ma Mufee wani shegen kallo gaba d'aya yaga sai wani glowing take tana shining ga wani sihirtaceen k'amshi dake tashi ajikinta, itako bama tasan yanayi ba gaba d'aya hankalin ta ya tafi ga sauyin da tagani daga Fahad tana k'ok'arin juyawa zata tafine saiga Samraat da fara'ar ta da komai tana fad'in "Bokan turai saukan yaushe?"

Dariya Fahad yayi yace "wallahi jiya nadawo ya kike? yajikin?"

Fari tayi da idanun ta ta'karasa kusa dashi har tana bangaje Mufee tana fad'in "Alhamdulillah naji sau'ki sosai yanzu dai tsaraba ta nazo amsa tana ina?"

Dariya Fahad yayi dan tunda yaga Samraat yaji wani maganad'isu najan shi gareta amma d'azun dayake tare da Mufee d'aure wa kawai yayi sabida daya kalle ta zuciyar shi sai tayi ba'kin k'irin taita tafasa  moto yalek'a yad'auko mata wata k'atuwar leda yana fad'in "ga tsarabar ki babu yawa dai" d'an waigowa Mufee tayi taga k'atuwar ledar amma ita bai bata komai ba dasauri ta wuce cikin gidan tana raya abubuwa da yawa aranta.

Itako Samraat cikin murna take mai godiya,

Shiko Muneef Mufee yabi fa wani irin mayen kallo har saida Fahad yakalli inda yake kallo yaga Mufeeda yakema kallon sai baiji dad'i ba kuma sallama sukai da juna yashiga mota yatafi............โœ๐Ÿป



*_How to subscribe ๐Ÿ‘‡๐Ÿป_* 

_200 for normal paid post once a day 400 for VIP group post twince a day, 4210014214 lawal Shamsiyya Eco bank and send the evidence of payment via *** or mtn card with this number ***_