5 to 9
[12/8/2021, 4:41 PM] Rahma Kabir: LUBABATU
05
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
*Bayan shekara d'aya*
Zuwa wannan lokacin mun shiga cikin wani irin mawuyacin hali sakamakon gobara da muka yi, dukkan shanun Baffa sun kare rabi a ciki muka cinye saboda siyan abinci rabi kuma a zaryar kaini asibiti ya tafi tare da siyan wasu kayan amfanin gida, wannan lokacin mun gama tagayyara saukinmu kanin Baffanmu yana taimaka mana da wasu abubuwa, shima dai ba wani karfi ke gareshi ba sai rufin asirin Allah. Har mun cire rai da sake ganin Adda Jidda saboda har lokacin basu zo ba, Baffa shima ya sare tare da gasgata zancen mutanen gari cewar yabi son duniya ya saida Jidda.
Muna cikin wannan yanayin ne sai ga su Adda Jidda sun zo, rigar ardo suka fara sauka, a nan ne aka sanar dasu mun bar gari, ganin Jidda cikin shiga ta alfarma da kyawun kamala yasa mutanen gari jin kunyar abinda sukawa su Baffa, Haruna ya yi musu alkhairi suka tawo cikin Baihari, muna zaune da Umma muna gyaran dawa da Baffa Iro ya kawo mana zamu nika a injin dutse mu samu garin tuwo, sai muka ji kugin tsayuwar mota a kofar gida bamu kawo wajenmu aka zo ba, ganin Baffa cikin sauri kamar zai kifa ya shigo bakinsa a wangale yana dariya yasa muka bishi da kallon mamaki, dan rabon da mu ganshi a irin wannan yanayin mun mance ranar, Ganin Jidda na biye da shi a baya tare da Haruna yana na mike da sauri tire din dawar dake ciki ya watse a kasa na mance sam yana kan cinyata, na ruga a guje ina murna da kuka a lokaci guda naje na rungumeta, itama ta kamani tana kukan murna sai da muka dauki minti biyar a haka kafin muka saki juna muna sharewa juna hawaye, Jidda ta kamo hannuna muka dawo kan tabarman dana tashi muka zauna kana duk suma Baffa suka zauna a wata tabarman, aka gaisa da juna tare da nuna tsantsar jimamin rashin ganinsu, Haruna ya bada hakuri tare da fadin.
Baffa kuyi hakuri wallahi ayyuka ne suka min yawa ban cika zama ba, itama Jidda sai ta yi kusan wata bata ganni ba in na fita kasar waje. Amma insha Allah ba zamu sake yin shuru haka ba, yanzu haka ma Ilori zamu je wani aiki, kuma zamu kwana biyu a can shiyasa nace bari muzo mu gaisa.
Ka kyauta amma dan Allah kar ku kuma yin shuru irin haka, dan babu irin abinda ba ace mana ba akan shurunku, shiyasa ma muka dawo nan da zama.
Insha Allah Baffa ba zamu kuma ba.
Yace haka cike da biyayya. Ni da Jidda muka shiga dakin da yake mallaki na muka dasa hira. A wannan ranar ba karamin farin ciki muka kwana cikinsa ba, munyi hira munyi wasa tare da tuno baya. Adda Jidda ta fada min b'arinta uku basa zama ciki harda yan biyu, Kuma cikin duk sai sun haura wata uku take barinsu, likita ya tabbatar mata da mahaifarta ba tada kwari, kuma duk b'ari sai anyi mata karin ruwa da jini, tare da shan kayan marmari na karin jini, tabani labarin daular da take ciki dan gidanta na kaduna yafi wanda ta fara zama a Yola sau uku, sai dai ta ce min.
Lubabatu wlh Abu guda ne baya min dadi zaman kad'aici da nake fama ga shegen kulle da Haruna yake min, yaki bari nayi sabo da kowa a unguwarmu, ke in takaice miki ban taba fita a kafa ba sai a mota, kuma bama fita da rana sai dare, Kuma bamai zuwa min nima ban zuwa wajen kowa, sau daya ya taba kaini wajen yayarsa a abuja, suma basu taba zuwa ba har na gaji da naci, nayi masa korafi harna gaji yace shi haka tsarinsa yake in ina son zama da shi to sai dai nayi hakuri mu tafi a haka.
Na jinjina lamarin kuma hakan ya dameni, amma saboda in kwantar Mata da hankali sai na nuna Mata hakan ba komai ba ne.
Karki damu da haka Adda tunda yana sonki kuma baki rasa komai ba ki cigaba da hakuri watarana sai labari. Amma banda wannan damuwar ba kya fuskantar wata matsala ko?
A'a gaskiya Ina cikin kwanciyar hankali da farin ciki.
Allhamdulillah burina kenan naji haka daga bakinki saboda zuciyata ta samu natsuwa.
Adda Jidda ta rungume ni tana dariya, haka ta sakeni tana kallona tare da yimin addu'a Allah ya bani miji irin nata domin tayi dace da miji nagari, haka muka yi barci cike da natsuwa mara misaltuwa.
Sun kawo mana tsaraba irin iri, washe gari aka kwance, Baffa Iro da iyalinsa suka zo aka yini tare dasu cike da kwanciyar hankali da farin cikin sake haduwarmu. Su Adda Jidda basu tafi ba saida suka wadata mu da kayan abinci Wanda zai jima Mana tare da makudan kudi saboda dawainiyar asibiti da ake dani, sannan sun siya mana waya Nokia gaba dayanmu, har Baffa Iro ya samu nashi, Adda ta koya mana yadda za muyi amfani da wayar, cikin kankanin lokaci na iya tayi saving mana numbobinsu, da yake ya sama mata malami da yake koya mata yaki da jahilci a gida, Kuma cikin kankanin lokaci ta iya abubuwa masu yawa har ta soma gane turanci kadan kadan, a gaskiya munyi farin ciki da sauyin rayuwar da muka samu akan zuwansu Jidda. Satinsu guda suka wuce Ilori da cewar in sun gama abinda suke yi zasu biyo tanan su sake yi mana kwana biyu sai su wuce gida, da zasu wuce harda kukanmu da nuna jin tsantsar kewar juna, hatta Baffa sai da yayi hawaye haka ma Umma ta kasa dannewa, suka tafi tare da barinmu cikin kewarsu.
Ashe wannan tafiyar ita ce ta bankwana a garemu tafiyar da ba zamu sake haduwa ba, tun bayan tafiyarsu basu sake zuwa ba tsawo shekara guda, sunata wakar zasu zo amma Allah bai nufa ba, sai dai muna waya akai akai wannan ne ma tasa muka samu natsuwa cewar tana cikin koshin lafiya kuma Haruna yana yo mana aiken kudi masu tsoka. Ashe tsawo shakarar da muka dauka Jidda tana cikin damuwa wanda ta danne a zuciyarta saboda mugun zurfin ciki sai gabda rasuwarta Allah ya bata ikon fayyace min komai wadda ta sanya ni cikin tsantsar rudani.
*****
*Cigaban labari*
Wasu zafafan hawaye suka sauka a idon Lubabatu tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, ta duba taga cewar dare ya yi nisa sosai bata san iya tsawon lokacin data bata ba cikin wannan yanayin tunanin, ta ce cikin raunin murya.
Yanzu ba mutuwarki ke damuna ba, domin nasan taki tayi kyau, don kin cika da imani saboda a wajen haihuwa kika rasu, kawai yadda zan zauna da Haruna nake tunani, gashi ina da rauni banda cikakken lafiya sannan gashi zanyi nisa da ahalina, zanje inda ban taba zuwa ba kuma har nayi rayuwa a can wanda bansan iya addin lokacin da zan dauka ba a can, gaskiya na karaya ina tausayin kaina, yau koda na fadawa su Umma labarin da Anty Jidda ta bani ba wanda zai yarda hasalima zasu ce na fake da hakan ne don k'in da nakewa aurensa. Allah kaine kadai masanin dai dai ka shiga lamarina ka zaba min abinda yake alkhairi.
Saita koma ta kwanta a takure taja mayafin rufanta ta rufe jikinta, ta rufe ido da addu'ar Allah yasa barci ya dauketa.
******* *** *******
Kaduna
Tun ranar da Rahima ta kori Hashim bata sake kai dare tana charting ba sai dai kuma ta dauki sarar kallon films na batsa sai takai karfe ukun dare tana aikin abu guda da safe ta tashi ido suyi tulu tulu da kyar take iya zuwa school, in ko ba ranar makaranta bane sai ta kai azahar tana barci, a lokacin data tashi ne zata yi kokarin yin wanka sannan ta karya kafin daga bisani ta gabatar da sallar asubahi da azahar a lokaci guda. Kasantuwar kowa yana rayuwarsa yadda ya ke so shiyasa babu wanda yasan irin abinda Rahima da Umar suke aikatawa.
Yau asabar kowa yana gida hatta Abba baije kasuwa ba yana sashinsa tare da Ummi, Mami kuwa tana dakinta tana barci, haka su Sarah da Ubaidu suna daki suna kallo cikin soyayya da kulawa, Rahima ce kawai ta fita zuwa farfajiyar gidan wajen rumfar shan iska, tana charting da kawayenta a group dinsu na makaranta, kamar ance ta daga kai sama sai ta hango wulkitawar Jamila zuwa cikin falonsu da sauri ta mike tabi bayanta ta iske harta kusa cimma dakin Umar, ta kara sauri ko kafin ta karasa ta shige sun rufe kofa, ta girgiza kai ta isa jikin kofar tare da gyara tsayuwa, bata yi gigin bugawa ba sai ta bude murya da karfi.
Abba! Ummi! Mami! Kuzo kuga abin mamaki.
Bata karasa abinda zata ce ba Umar ya bude kofa a guje yana rike da wandonsa yana gyara zip, idonsa Lamar zasu fado kasa dan tsananin tsoro da tashin hankali, yace cikin rawar murya.
Ya zaki min haka? Don Allah ki rufa min asiri, kuma ai na baki kudin da kike ce kina bukata.
Rahima ta yatsine fuska tare da turo baki.
Ka mance abinda kamin last week akan zuwan Hashim? ai dama nace saina rama abinda kamin. Abba! Ummi! Wlh kuzo kuga Yaya Umar…
Da sauri ya yi yunkiri ya isa gabanta ya toshe mata baki da hannunsa, dai dai isowar iyayensa wajen suna tambayar dalilin kwala musu kira da take yi, Umar yayi saurin saketa ya yi tsuru tsuru kamar mage a kwali yau yasan dubunsa ta cika, jikinsa har rawa yake yi tsabar tashin hankali daya shiga, ya kasa cewa kowai sai ya kafe Rahima da ido kamar zai sauya mata halitta. Cikin kunkuni Rahima ta soma magana.
Um um ba ya Umar bane.
Sai ta dakata tana son fara yin kuka, Umar cikinsa yayi mugun kadawa ya dafe cikinsa da kai ya jingina na bango saboda kafafunsa ba zasu iya daukarsa. Ganin irin halin da ya shiga na tsananin rudewa sai Rahima ta sha kwana a maganarta ta dafe kuncinta ta soma matsar kwalla. Ummi ta daka mata tsawa.
Wai ba zaki yi magana ba? Kin tsaidamu sai kace abokan wasanki.
Haba Hajiya ki mata a hankali. Mama zonan me yayanki ya miki yanzun nan in hukunta shi.
CewarAbba ya jawota kusa dashi ya dafa kanta, tace cikin shagwaba.
Abba marina fa yayi dan nace ya aramin wayarsa.
Amma anyi babban banza, bansan me yasa ba kake kokarin gallazawa Autan Umminku, gaskiya zan bata maka rai in baka shiga hankalinka ba akanta.
Cewar Abba cikin fada da daure fuska, Ummi ta daura da nata.
Kai babban kabo ne, ka yada girma ta raina ka, kun zama kamar kaji kullun fada Allah ya kyauta.
Sai ta juya ta wuce abinda Abba ya kalleshi.
Karka sake dukanmin 'ya in ba haka ba wlh da kaina zan rama mata sha Sha Sha. Auta kiyi hakuri ko in ya kuma dukan ki kizo ki fadamin da kaina zan dauki mataki.
Ta gyada kai alamar to sai ya wuce ya bi bayan Ummi, Rahima sai da ta tabbatar sun bar sashin gaba daya ta kwashe da muguwar dariya harda rike ciki, sai da ta yi mai isarta kana ta tsagaita tana kallonsa ya cika yayi makil da tsananin bacin rai wanda yasanya fuskarsa yin ja, tsabar bakin ciki ya kasa cewa komai sai hadiye yawu yake kamar wanda ya kware, Rahima tayi masa gwalo.
Kadan kenan ka gani, Allah tsakaninmu babu yafiya duk abinda kamin saina rama ehe, Kuma ka kara.
Sai ta wuce tana murguda masa baki cike da shakiyanci har sai da ta kule kana ya samu damar sauke nannauyar ajiyar zuciya, yaja kafarsa zuwa cikin daki saboda gaba daya ya rasa kuzarinsa, ya zauna sharaf a gefen gado kamar kayan wanki ya cije lebensa na kasa.
Lallai dole in san hanyar da zan bi saboda yarinyar nan karta fasa min bomb.
Yace a zuciyarsa, Jamila ta fito daga bayi wajen buyarta duk ta jike da guma kamar wacce tayi uban gudun ceton rai, kafin ta karaso kusa da shi ya daga mata hannu alamar ta tsaya.
Jamcy kije kawai zamu hadu anjima yanzu bana cikin yanayi na.
Bata iya furta komai ba domin itama hukuncin da ya yanke yafi yi mata dadi, ta wuce suf suf ta fice cikin sauri, ta leka falon ba kowa sai ta wuce waje zuwa dakin kwananta da aka ware mata.
Haka dai Rahima ta sanya Umar a gaba sai da ya yi ta bata hakuri da lallashi kafin ta sauko suka daidaita, sannan ta shafa masa lafiya ya samu sukuni.
*****
Bayan mako guda.
Lahadi
Gidan sun tashi da hidima sosai sakamon kanin Ummi da zai zo Wanda ya dauki tsawon lokaci baya kasar, Ummi da kanta ta shiga kitchen ta shirya masa abinci mai rai da motsi tare da Mai aikinsu da Kuma Rahima, bayan sun gama Jamila ta gyara kitchen din da falon gidan, ko Ina ya dauki kamshi, Ummi taje ta tsala wanka ta shirya cikin doguwar rigar shadda brawn wanda tasha aiki ta yi ado kyanta ya fito sosai, duk da tsufa ya nuna amma bai hana cikar zatinta bayyana ba, saboda Ummi irin matan nan ne masu kyawun jiki kamar bata kai shekaru arba'in da biyar ba. Ta fito ta zauna a falo tana taunar cingwam da gani yadda fuskarta ke sheki da walwala tana cikin tsantsar farin ciki, Bayan minti goma sauran mutanen gidan suka fito ko wannan cikin kyakkyawar shiga, Ubaidu, Sara, Rahima, Umar, harda Abba shima ya fito suka soma hira cikin ba'a gwanin sha'awa, saida suka dauki minti Sha biyar a haka kafin Mami ta fito ta zauna sanye take cikin atamfa riga da zani cikin murmushi tace musu sannunsu da hutawa, suka amsa kana ta kai kallonta ga Ummi.
Hajiya karama irin wannan wanka haka sai ka ce me ganin gomna, gaskiya da alamu kina ji da wannan d'an uwan naki, saboda rabon dana ganki a cikin irin wannan kwalliyar Allah na manta.
To uwar tsugudidi, Allah ya wadaran me sa ido, Ina ruwanki da kwalliyata? dan Allah ki fita lamarina karki bata min farin cikin dana ke ciki yau. Haba dole ne sai kin sa kanki akan abinda ba asa da ke ba.
Haba Hajiya daga wasa sai abin ya zama rikici to Allah ya baki hakuri.
Cewar Mami cikin sanyin jiki inda sabo ta saba da irin cin kashin da Ummi ke yi mata, itama rabon ayi ne ta tanka mata. Ummi taja tsaki bata sake cewa komai ba Abba yace cikin jan kunne.
Kema Hajiya tunda kinsan halinta bata so kina shiga sabgarta ki hakura Mana bana son tashin hankali, muna zaune kalau zaki dama mana lissafi, in ba zaki yi hirar ba ki koma daki ban son shisshigi ba kwarjini.
Mami ta kalli Abba cikin damuwa ta mike tana cewa.
To ayi hakuri yallabai
Saita wuce sashinta tana jin wani irin tukukin bakin ciki yana taso mata, hawaye mai dumi ya saukar mata tare da sauke ajiyar zuciya ta ce a zuciyarta.
Bakomai akwai Allah.
Ta saba da wulakancin da suke Mata sai dai a duk lokacin da suka yi Mata a gaban 'ya'yansu yana yi mata zafi sosai. Ubaidu ganin abinda suka yiwa Maminsa sai ya mike zaibar falon, cikin fada Abba ya dakatar da shi.
Wallahi kana barin falon nan saina saba maka, fada ne Kuma bazan fasa yiwa Maminka ba tunda ba tada hankali, sai dai ka hadiyi rai ka mutu ko kazo kasa zabori ka zane ni shine nasan ranka ya baci.
Bai ce komai ba ya dawo ya zauna duk yadda yaso ya danne bacin ransa ya kasa, sai da ambaton Allah ne ya samu sassauci ya sunne kai ya cigaba da danne danne a waya. Suma kansu Umar da Rahima ba suji dadi ba saboda basa son abinda Ummi ke yiwa Mami, tunda suka taso basu taba ganin Mami tayi mata abu na muzgubawa ba amma ita Ummi kusan kullun saita takura mata da mugayen kalami, kuma Abbansu ya biye mata in dai anyi a gabansa. Haka itama Sarah tana jin haushin haka sai dai ba tada yadda zata yi ta sauya lamarin duba da Ummi yar uwar mahaifarta ce. Zaman gurin sai duk ya gunduresu amma ganin irin abinda Abba ya yiwa Ubaidu shi ne yasa suka cigaba da zama a falon, Ummi ce ta katse shurun da cewar.
Ubaidu! Umar! Kuje ku dauki mota ku tafi airport ina ganin jirginsu Hydar yana gabda sauka.
Da to suka mike suka fita tare, Rahima ta mike da sauri.
Ummi nima zan bisu.
To jeki amma banda rawar kai ki natsu. Sarah ko kema zaki je ne?
A'a sai sun dawo.
Sarah tace a takaice ta mike zuwa dakinta, tuni dama Rahima ta fita da sauri suka bar Abba da Ummi su kadai a falon.
#Rahmace
#MamanSultan
#share
#comments
#vote
___________
Talla
*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*
-Yana ciko breast suyi kyau.
-In sun fadi zasu ciko su tashi.
-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.
-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.
-And finally yana karin ni'ima sosai.
Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.
Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free
Price:N4,000
Location: Kaduna State
WhatsApp: ***.
UMMU SULTAN
100% NATURAL HERBS.
[12/8/2021, 4:41 PM] Rahma Kabir: LUBABATU
06
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
Bayan sun isa airport ba bata lokaci jirginsu ya sauka aka gama duk wani bincike da akewa kayan matafiya kana Hydar ya fito ya kira numbern Umar sai ya hango shi ya daga wayar yana helo, da haka ya gane shi ne sai ya karasa gunsu, suka gaishe shi cikin mutuntawa cike da fara'a, Umar ya sanya trolley a bayan mota kana duk suka shiga ciki, Ubaidu ke tuki Umar yana gefensa sai Rahima a baya tare da Uncle Hydar, haka suka kamo hanya suna hira cikin nishadi.
Lokacin da suka isa gida motarsu tayi parking duk suka fito, mai gadi ya rugo da gudu ya kwashi gaisuwa kana ya isa bayan boot da nufin ya dauki trolley, Umar ya dakatar da shi yayi masa nuni daya wuce, shine ya dauki jakar suka kama hanyar falo su duka. Ummi dake cike da zumudi ta mike da sauri dan ta riskesu a tsakar gida saboda ta gaza hakurin su shigo.
Alhaji sun iso fa, bari naje.
Haba Hajiya wannan irin sauri haka? Ki bari su karaso ciki mana.
Abba ya katseta da sauri, sai ta koma ta zauna badan taso ba amma saboda makirci sam fuskarta bai nuna bacin rai ba sai ma washe baki da ta yi tana cewa.
Wlh zumudi ke fizgata, kasan jini ba wasa ba, na kosa naga d'an uwana.
Kafin ya bata amsa sun shigo falon da sallama. Ummi ta mike da sauri fuskarta fal farin ciki sai washe baki take tana zubawa Hydar sannu da zuwa, shima murmushi kawai yake mayar mata annurin fuskarsa ya bayyana sosai, har suka zauna gaba daya, nan suka kwashi gaisuwa ya gaishe da Abba cikin tsantsar mutuntawa da nuna farin cikin ganinsa, hakan yasa Abba yaji kaunarsa a ransa ya saki masa fuska sosai, haka ya gaisa da Ummi cikin nuna kulawa, suna cikin wannan yanayi sai ga Mami ta fito falon fuskarta wasai kamar dazun basu bata mata rai ba, ta zauna kusa da Ummi tana cewa.
Lale da bak'onmu mutanen turai, da fatan ka sauka lafiya ya hanya?
Lafiya lau Hajiya, na sameku lafiya?
Allhamdulillah duk kalau, ai mun ji dadin zuwanka domin zamu huta da maganar da Hajiya take akan zancenka
Hydar ya sunne kai yana murmushi bai ce komai ba, Ummi taja guntun tsaki ta mike tana cewa.
Hydar muje na nuna maka masaukinka kayi wanka sai kazo ka karya, abinci na jiranka.
Ok yace sai ya mike, Rahima ta dauki jakarsa zata bisu Ummi ta amshe.
Bani nan, yau ku barni na sada zumunci, da kaina zan bawa dan uwana kulawa ta musamman, domin jini yafi ruwa kauri.
Sai duk suka sanya dariya Abba yace cikin zolaya.
Auta samu guri ki zauna yau ummanki idonta a rufe yake, kaunar zumunci ne ya motsa, iyeka namu ido.
Sai duk suka sanya dariya suka mayar da abin ba'a, Abba ya mike shima ya wuce sashinsa yabar su Rahima zaune, Ubaidu shima ya mike zuwa wajen matarsa, su Mami suka cigaba da hira tare da kallon tv. Ummi suna isa dakin data baiwa Hydar bangaren sashin da dakin Umar yake, ta ajiye trolley a gefe ta isa inda yake a tsaye gefen gado yana kokarin cire rigarsa ta rungume shi ta baya tare da sauke gauron numfashi.
Nayi tsantsar kewarka sosai Hydar, hop zamanka a gidan nan zaka sanya ni farin ciki.
Nima nayi kewarki fiye da tsammaninki, shiyasa na kasa hakuri nazo gareki, sai dai nazo na iske gidanki cike yake da al'umma hop ba zasu bani matsala ba.
Karka ji komai ka saki jikinka tamkar gidanka, domin nice ke da ikon komai a gidan nan babu wanda ya isa yaja dani.
Naji dadin jin haka yanzu hadamin ruwa na watsa.
Angama my kani.
Tace tana sakinsa tare da yin guntun dariya, shima murmusawa ya yi yana jinjina karfi hali irin nata, ta isa toilet ta hada masa ruwa kana ta fito ta zauna gefen gado dan ta jira ya kimtsa su tafi tare. Minti Sha biyar ya dauka kana ya fito ya shirya cikin kananun kaya riga mai guntun hannu da wando tree quarter ya feshe jikinsa da turare kana ya juyo yana kallonta fuskarsa cike da sheki.
Ya, na hadu kuwa?
Wanka yayi sosai, ka kara kyau Hydar meye sirrin?
Sirrin ganinki dana yi shi ne ya kara fidda asalin kyauna, domin duk lokacin dana kasance tare dake komai nawa yana sauyawa cikin kankanin lokaci.
Uhum banda zaulaya dai.
Da gaske nake ke ce sirrin kyauna, Kinga muje yunwa nake ji sosai.
Ummi ta wuce gaba yana binta a baya suna hira kasa kasa in ba mutum ya matso kusa dasu sosai ba babu me jin abin da suke cewa, a haka suka isa babban falo ta yi masa jagora har dinning, ta kira Rahima ta yi serving dinsa tabasu wuri ya cigaba da cin abincinsa. Sun dauki kusan rabin awa a dinning kafin daga bisani bayan ya kammala suka dawo falo suka yada zango a nan suka cigaba da hira dasu Mami.
____
Bayan Sallar Azahar
Sarah ta fito tare da Ubaidu suna sakale da hannun juna har zuwa babban falo suka cimma Hydar da Umar suna hira, Sarah ta yi masa sannu da zuwa suka wuce danta yiwa Ubaidu rakiya. Hydar ya bita da wani irin kallo yana hasko irin tarin kyawun dirin halittarta har sai da suka fita a falon kana ya maido da hankalinsa wajen Umar.
Son wannan wacece Kuma?
Matar Yaya Ubaidu ce, sunanta Sarah, Amma nayi tunanin ko ka santa dan 'yar kanwar Maminmu ce.
Anya ban wayeta ba.
Amma ai ka wayi Mamanta Inna Hajjo?
Eh eh nasanta, ka mance yar uwata ce taya zan manceta, ban zaci tana da 'ya kamar wannan ba.
Haka dai suka bata lokaci suna hira, Sarah koda ta rabu da Ubaidu ta kofar baya ta koma side dinta, Hydar yaita zuba Ido dan sosai zuciyarsa ta kwadaita masa son kara ganin surarta, sai dai kash bata dawo ba, ya gaza jure hakurinsa ya tambayi Umar, ya bashi amsa ba tare daya kawo komai a ransa ba, ya tabbatar masa data bi kofar baya ne, ok kawai yace amma a ransa baiji dadi ba.
*
Da dare
Ummi ta isa dakin Abba cikin shirin barci ta zauna a kujerar dressing mirro ya tashi zaune daga kwancen da yake ya jingina da filo yace cikin dattako.
Amaryata ya kika zauna a nan? Ya kamata ki hawo gado mu kwanta tun dazu ke nake jira kizo.
Gaskiya Alhaji da fatan ba wani abu kake bukata ba? dan bana tunanin zaka samu komai, gwara ka daina jirana kayi barcinka.
Amma kinsan dai tun kwana biyu kike jamin rai, ya kamata ki bani hadin kai domin ina cikin bukatarki, Dan Allah karki kuma cemin A'a.
Hmmm fadin A'a ya za ma dole dan ba zaka samu komai ba, ni gaka tafiyata domin ina bukatar yin hira da d'an uwana, kayi barci kawai karka tsaya jirana.
Ta mike tare da wucewa fuuu yana kiranta amma taki tsayawa sauraren me zaice mata. Dakinta ta koma ta sauya wasu kayan barcin kana ta daura dogon hijab a sama ta nufi sashin da Hydar yake, tafiya take cikin sauri saboda ta kosa ta isa dakin, dai dai shan kwana da zata yi taci karo da Umar wayar dake hannunta ya daki kansa ya fadi kasa, cikin tashin hankali yayi baya yana dafe da goshinsa saboda zafin bigewar da yayi, sai zare ido yake alamar rashin gaskiya karara ya nuna a fuskarsa. Ummi ta bishi da mugun kallo tare da daka masa tsawa.
Dan ubanka Ina zakaje cikin faren nan?
Um um dama dama abinci nake son d'ibowa a kicin saboda yunwa naji yana taso min.
Yaushe kaci abinci? Ina ce karfe tara yau muka ci abincin dare, yanzu karfe sha daya da mintuna, du du du awa nawa ne tsakani da har zaka ji yunwu.
Allah Ummi ji nayi kamar anyimin yasa, kuma dazun na zaga…
Dakatamin ban son dogon bayani, in dai abinci ne gaka ga kitchen ka cinye wanda ya rage, acici.
Ummi ta fada cikin mita, Umar ya sosa keya yana murmushi, ya mika mata wayarta da ta fadi ya wuce kitchen badan yaso ba, saboda shi ya fito domin yaje ya shigo da Jamila ne, sai kuma ya yi rashin sa'a yaci karo da Ummi, koda ya shiga ruwa kawai ya dauka yasha ya zauna kan kujera ya bata minti biyar kana ya leko ya duba ba kowa sannan ya koma daki cikin rajin jin dadi, saboda yana tsoron kar ya fita ya shigo da Jamila asirin sa ya tonu, karshe kiranta yayi ya shaida mata ta koma daki kawai yau ba harka.
…
Ummi tana shiga dakin Hydar ta sanya key ta rufe ta yaye hijab din dake jikinta ta ajiye a gefe, ta tsaya jikin kofa tana karkada jikinta tare da yauki, Hydar dake kwance yayi sauri tashi zaune yana mayar mata da shu'umin kallo.
Gaskiya kinfi kyau tsirara tsirara, kinga yadda komai ya fito kuwa? Lallai yau zan kwashi lagwada.
Kayi zancen cikin jam'i, wato zamu kwashi lagwada, domin na jima ina tsumayen wannan ranar.
Ummi ta fada tare da isa gadon ta hau, ta yada zango da kanta bisa cinyar Hydar, ya soma wasa da gashin kanta daya sha gyara sai kamshi ke fita, yace cikin muryar shauki.
Da fatan wannan sirrin tsakanin ni da ke ne babu na ukunmu?
Kai da kasan komai, kai kanina ne Kuma masoyina ne abincin ruhina, wato tsuntsu daya na jifa da dutse biyu. Dan haka wannan sirrinmu ne na jima da birne shi a raina.
Gaskiya ne shiyasa nake kara jin sonki a raina, yanzu tashi za kiyi mu samawa zuciyoyinmu abinci domin duk kanmu a yunwace muke.
Ummi ta zauna tare da rausayar da kai gefe tana karkada harshe. Ha suka soma aikawa juna farmaki, irin mayunwacin zaki nan wanda ya jima bai samu abinci ba.
Sai karfe uku da rabi suka sararawa junansu, a lokacin ne suka farga cewar dare yayi sosai domin ga duk kan alamu kowa yayi barci sai wa inda suka raya dare irinsu ne idonsu biyu. Ta mike cikin tsantsar gajiya ta mayar da kayanta ta sanya hijab ta bude kofar a hankali kana ta fice, da sanda ta isa dakinta ta bude ta shige, ta manna jikinta a kofa tana maida numfashi kana ta koma gado ta kwanta tana mai hasko nishadin da suka gama aikatawa yanzu, ji tayi inama yana kusa da ita yanzu su kara komawa ruwa suyi nitso, duk da ta gaji amma zata iya domin Hydar na musamman ne, samun irinsa cikin maza sai an tona.
Tun daga wannan ranar suka soma wannan kazamin rayuwar baji ba gani, sun adana sirrinsu babu wanda ya fahimci akwai boyayyen alaka a tsakaninsu.
****** *******
*Yola*
Bayan sati biyu.
Baffa sunata shirye shiryen bikin Lubabatu, wanda ita kuma sai kara tusa mata kunci suke domin gani take da alama idonsu ya rufe sun fara mance rasuwar Anty Jidda, sun mayar da hankulansu katsokan kan zancen bikin. Lubabatu tana zaune a daki ta rafka tagumi abin duniya ya dameta, ita yanzu bata lalurar da ke jikinta take yi ba, domin ji tayi kamar ta warke saboda tashin hankalin dake tun karota yafi azabar cutar sucklern da take da shi, wayarta ta ne ya dauki kara wanda yadawo da ita duniyar tunanin data shi ga tana dubawa taga Haruna ne, taji gabanta yayi mummunar faduwa da sauri ta ambaci.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun, Allahu Allahu rabbi laaa ushrika bihi shai'a.
Sai da kiran ya kusa katsewa ta daga tare da sallama. Haruna ya amsa yana cewa.
Lubabatu ya jiki? Naji Baffa yace shekaran jiya jikinki ya tashi, amma da fatan kin samu sauki.
Allhamdulillah na warke ma.
Umum warkewa a gunki abune mai wuya domin cutarki baida maganin warkewa sai dai kiji sauki, insha Allah Ina fatan bayan munyi aure zan fita dake kasar waje kiga manyan likitoci su dubaki, wata kila mu dace ki warke.
Uhum kawai ta ce, hawaye masu dumi suna bin kuncinta wanda yake bayyana zuciyarta akwai magana masu tarin yawa wanda bazai iya faduwa a baki ba.
Kinyi shuru baki ce komai ba.
To Hamma Haruna me zance?
To shikenan bari na barki haka, zan kuma kiranki insha Allah domin Ina bukatar mu soma sabawa kafin zuwan ranar aurenmu.
To nagode
Bata jira yayi magana ba ta kashe wayar, tare da jan tsaki ta dangwarar da wayar cike da takaici, ta rasa dalilin da yasa ta amsa masa waya cikin saukin kai, da taso ta zazzaga masa rashin kunya ne sai kuma ta kasa domin gaba daya ta daburce ne. Ta fito tsakar gida ta samu Umma na damawa Baffa fura kafin ya shigo gida, ta zauna tana cewa.
Umma gaskiya bana kaunar Hamma mijin Anty Jidda, Dan Allah kiyi wani abu akai yadda za a fasa auren nan.
Umma dake damun fura ta ajiye kwaryar a gefe tana kallonta cike da mamaki tace cikin daure fuska.
Lubabatu ban sanki da gardama ba, meyasa kike so ki koyi halin da ba naki ba, kina sane auren nan babu fashi tunda Baffanki ya amsa, gwara ki sanyawa ranki dangana in ba haka ba wlh zaki fuskanci fushina, domin na kula lamarin naki ya soma zama iskanci.
Umma wlh in kuka auramin Hamma Haruna ina ganin mutuwa zanyi bazan iya rayuwa da mijin anty Jidda ba, Dan Allah ki fahimce ni.
Bazan fahimceki ba, ke da zai rufawa asiri ya aureki a haka cikin lalurarki, Amma kike nuna baki so bayan kinsan baki taba wani saurayi daya ce Yana sonki ba kowa na gudunki. Daga yanzu bana son na kuma jin wani korafinki a Kan wannan auren, in ba haka ba wlh zanyi mugun bata miki rai.
Umma ta yi maganar cikin fada sosai, Lubabatu ta share kwallar daya zubo mata a kunci tace cikin raunin murya.
Umma ke kadai ce nake tunanin zaki dafa min akan wannan zancen, dan Allah karki juya min baya, wlh ni kadai nasan irin abinda nake hange, da zaku bar batun auren nan wlh zan jure na kare rayuwata a haka ba tare da aure ba.
Banga uban da ya isa ya dakatar da wannan auren ba.
Cewar Baffa cikin fushi lokacin da yake shigowa cikin gidan, ya ciro takalminsa daya ya jefi Lubabatu da shi ya daki gefen guskarta ta dafe gun tana matsar kwalla, Baffa ya daura da cewa.
Ina shigowa zaure na tsinkayi maganarki, wlh Lubabatu baki isa kiyi mana bakin ciki ba, domin hadin aurenki da Haruna shine zai share mana hawaye akan rashin Jidda da muka yi sannan ta hakane zamu rika samun abin arziki da yake mana, dama ba zuri'a ke garesu da jiddan ba, yanzu in ba ta hadin aurenki da shi ba a gidan uban waye za mu cigaba da samun makudan kudin da muke samu a hannunsa, bari kiji aurenku kullelle ne ko kin ki ko kin so, sai dai in an kaiki gidansa ki hadiyi zuciya ki mutu. Mai mugun hali, ke dama tun haihuwarki baki gaji arziki ba shiyasa zaki mana mugunta. Tashi ki bani waje na daina ganin bak'in fuskarki a Idona.
Ya kare maganar a tsawace, da sauri Lubabatu ta shige daki har tana cin tuntube saboda tana tsoron kar ya kai mata duka. Umma bata ji dadin zantukansa ba amma ganin yadda ransa yayi mugun baci ya sata danne abin a ranta saita dauki kwaryar furarsa ta cigaba da damu, Baffa kuwa ya cigaba da sababi ta inda yake shiga bata nan yake fita ba sai kumfar baki yake. Lubabatu ta soma kuka da gunji suna jinta har tsakar gida Amma babu wanda ya iya lallashinta har tayi mai isarta tayi shuru dan kanta.
Sai dare Umma ta samu halin shiga dakinta bayan Baffa yai barci Dan ko abinci ya hana ta kaimata yace in ba zata fito ta amsa da kanta ba to ta kwana da yunwa, sai a lokacin Umma ta bata tuwon dare ta zauna kefen katifarta ta dagota ta zauna, jikinta yayi zafi sosai alamar zazzabi ke damunta, cikin damuwa Umma ta soma magana.
Lubabatu Dan Allah ki sanyawa zuciyarta salama, kina sane da ba cikakken lafiya ce dake ba, karki butulcewa Allah duk kaddarar da kika ga ta sameki ubangiji yasan zaki iya jurewa sai dai kiyi gajen hakuri kawai, kuma wannan tuburewar da kike nunawa shi yake tabbatar da kin kasa yadda da Kaddararki, kuma hakan yana daga cikin raunin Imani, kisa a ranki zaki iya jure ko wani irin kalubale da fatan alkhairi a duk lamarin daya tunkaroki, insha Allah zaki ga ribar biyayyar da kika yi mana ba zaki nadama ba, koda mutuwa kika yi a gidan Haruna kiyi fatan samun aljanna, wata kila rabonki na duniya yana lahira.
Umma ta kare maganar cikin fidda kwalla wanda ta kasa danne su, hakika maganganun Umma ya samu matsuguni a zuciyar Lubabatu wanda ya sanya ta zamu karsashi da jin karfi a jikinta.
Lallai zan iya.
Maganar zuciya ta yi ya fito fili, Umma ta kare mata kallo tare da haske tarin maganganu a bakinta.
Lubabatu ko akwai wani abu da kike boye mana ne?
Da sauri ta dago ta kalli Umma sai a lokacin ta gane wancen maganar da ta yi a zuciya ashe a fili tayi, sai ta muskuta ta gyara zama ta soma magana cikin dakiya.
Babu wata magana Umma sai dai maganarki shine ya karamin karfin guiwa da jin Zan iya rayuwar gidan Hamma Haruna, insha Allah ba zan sake kokarin tubure muku ba. Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa.
Ameen Lubabatu Allah ya miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya, yadda kika yi mana biyayya Allah ya cigaba da faranta miki ya baki 'ya'yan da zasu yi miki biyayya.
Ameen Umma, bari naci tuwon nan tun dazu nake jin cikina yana kullewa.
Umma ta jawo mata kwanon ta ajiye a gabanta, Lubabatu taje ta wanke hannu ta dawo ta soma ci, gaba daya ta danne damuwarta ta barwa Allah lamarin.
#Rahmace
#MamanSultan
#share
#comments
#vote
______________
TALLA
*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*
-Yana ciko breast suyi kyau.
-In sun fadi zasu ciko su tashi.
-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.
-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.
-And finally yana karin ni'ima sosai.
Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.
Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free
Price:N4,000
Location: Kaduna State
WhatsApp: ***.
UMMU SULTAN
100% NATURAL HERBS.
[12/8/2021, 4:42 PM] Rahma Kabir: LUBABATU
07
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
EWF.
Kaduna
Bayan mako guda
Da safe misalin karfe tara duk sun hadu a dinning da yake ranar lahadi ne suna gida, Ummi da sun hada Ido da Hydar sai ta sakar masa murmushi shima ya mayar mata, babu wanda ya kula dasu kasantuwar kowa yana harkar gabansa. Bayan gaishe gaishe Rahima to mike tayi serving dinsu, wajen ya yi tsit sai karar cokali da plate ke tashi, Hydar shi ke kallon kujerar da Sarah ke zaune, duk dago kai da zata yi sai sun hada Ido da shi sai kallonta yake kamar ya samu madubi, hakan yasa Sarah taji ta gundura da zaman gurin bata gama karyawa ba ta mike tace ta koshi tare da komawa sashinsu, Ubaidu shima ya mike yabi bayan matarsa, a haka dai suka watse suka koma falo suka kafa wata hirar Amma banda Abba da Ummi domin sashinsa suka wuce tare.
Bayan Sallar la'asar.
Ubaidu ya fita zuwa wajen wani abokin akinsu akan wata matsala daya taso, wutar wani anguwa ce ya lalace har an cire transformer din ta yi bindiga sai an gyara, kuma alhalin hakan yana karkashin office din Ubaidu ne, sannan mutanen anguwar sun matsa musu lamba akan gyaran shiyasa ya fita dan ya samu a daidaita lamarin a maida musu transformern. Umar kuwa ya fice zuwa filin kwallo dan duk yamma yana fita motsa jiki, Rahima tana daki tana barcin asara wanda ta saba zuwa anjima kuma ta raba dare tana kallo, Ummi tana sashinta, Mami tana kitchen tare da Mai aikinsu suna daura tuwon dare. Hydar dake zaune a tsakar gida ganin fitar Ubaidu akan idonsa ya sashi mikewa ya shigo falo, nan ma ba kowa sai kawai ya wuce sashin Ubaidun, ya yi sa'a kofar a bude take dan haka yasa kai ciki ko sallama bubu, Sarah dake kwance bisa kujerar mai zaman mutum uku ta mike da sauri tana kallonsa, Hydar ya bita da Mayan kallo yana kara karantar zubin halittarta, sai a lokacin Sarah ta tuna da irin kayan dake jikinta, vest ce fara da guntun siket brown color sannan ba birezia a jikinta, da sauri ta koma ta zauna ta rungume hannunta a kirji don ta kare kirjinta, tace cikin rawar mirya.
Lafiya? Me ya kawoka side dina? Kuma ya kamata in zaka shigo ka Nima izini in an baka dama sai ka shigo, dan Allah ka fita.
Ni ba wani abu ya kawoni ba sai dan in san dalilin da yasa baki nuna farin ciki da zuwana ba, ke kadai ce a gidan banga kinyi d'okin ganina ba.
Ni babu wani abu a raina, kuma in da bana farin ciki da ganinka ba zan maka magana ba, in da kayi hakuri kajima a gidan zaka fahimci halina haka nake.
Ok naji, bani ruwa mana na sha saina wuce.
Cikin sauri ta mike tare da karamin filon kujera ta rungume a kirjinta ta nufi kitchen dinta, tana shiga ta sauke numfashi tare da dafe kai.
Wannan wani irin mutum ne mara tunani? Ko da yake tashin turai ne ba arabi.
Tace a ranta sai ta ajiye filon a gefe ta fara tunanin abinda zata samu ta sanya, apron ya fado mata a rai sai ta juya da sauri danta dauko ta daura a jikinta, sai kawai taga Hydar tsaye bakin kitchen din yana kallonta, sam bata ji motsinsa ba balle tasan yazo, ta yi baya ta dafe kirjinta saboda mugun tsoron daya ziyarci.
Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun. Meye haka?
Kalau, kawai na jiki shuru ne nace bari nazo na dubaki ko kin manta dani ne.
To ka fita bana son ganinka gaba daya kuma ruwa ne bazan bada ba.
Ta fada tana juya masa baya cike da tsiwa, sai dai cikin zuciyarta cike take da tsoron kar wani yazo ya gansu a haka, musamman Mijinta da take shakka. Hydar ya kutso kai ciki bata yi aune ba taji ya rungumeta ta baya, ta runtse Ido jikinta yana rawa so take tayi ihu amma tasan hakan ba mafita bace sai kawai ta saki kuka tana yi masa magiya daya saketa, Hydar ko sai fidda murmushi yake shaidan yana kara ingisa masa tururin sha'awarta, ya kai bakinsa kusa da kunnenta yace a hankali.
Idan Baki shuru ba to bazan sakeki ba zamu tsaya a haka har mijinki ya dawo ya ganmu. In Kuma kika saurare ni to yanzu zan tafi dan haka ki juyo ki kalleni yanzu saina wuce.
Ya kare maganar yana sakinta, cikin sauri ta juyo sai dai tsoro yasa ta kasa kallonsa, Hydar ya yi murmushi sai ya dago habarta kafin tayi aune ya hada bakinsu gu daya, duk iya turjiyarta sai da yayi nasarar samun abinda yake so domin ya dauki tsawon minti goma yana juya harshensa a bakinta, gaba daya yasa jikinta ya mutu ta kasa hanashi sai ma soma mancewa da halin tsoro da take ciki tayi, ganin ta shagala sai ya kai hannunsa kirjinta ya shiga murza kan Breast dinta, a takaice dai Hydar sai da ya gigita Sarah da zazzafar soyayya wanda bata taba samun irinsa ba a gurin mijinta, sai da suka kwashe minti talatin a haka sun hau na'urar conputer sosai har sun fara yawo a network saura kiris su kaiga zarcewa karar wayar Sarah dake falo ya fargar dasu, da sauri ta ture shi ta dafe kai da duk hannunta biyu tana maida numfashi, Hydar ko second uku bai karaba ya fice daga dakin cikin sauri, Sarah ta kofa falo ta rufe kofa kana ta zauna dirshen a kasa jikin kofa sai ta rushe da kuka, tsoro, sha'awa, da fargaba sun gama dabaibayeta ta rasa Ina zata sanya zuciyarta, da kyar ta iya lallashin kanta ta mike a gajiye ta isa inda wayarta take ta dauka ta duba mai kira, Ubaidu ne saita duba wajen massage daya shigo taga shine ya aiko mata da sako.
Diamond na kira ki baki kusa, dama zan sanar dake cewar yau zanyi dare kafin na dawo saboda aiki ya rikeni, koda su Mami sun tambayi ina nake sai ki fada musu. Ki kula min da kanki bye
Sarah ta sauke ajiyar zuciya sai ta wuce bedroom dinta ta shiga toilet ta hadawa kanta ruwan zafi a baho ta tube ta shige, gaba daya ta kasa samun sukuni shaidan sai kara hasko mata abinda suka da Hydar yake, zuciyarta kuma tana kara kwadaituwa da shi, da kyar ta iya yakicewa kanta tunani ta yi wanka ta fito, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa ta fesa turare kana ta fita zuwa babban falo. Ta samu Ummi na sauke waya alamar ta kammala amsa kira, Sarah ta gaisheta ta amsa kana ta daura da cewa.
Yauwa Sarah je kitchen ki dauki maltina mai sanyi ki kaiwa Uncle Hydar a daki, yanzu ya kirani yace na aika masa, Rahima tana barci Amma tunda gaki sai ki je.
Gaban Sarah ya buga amma ba tada halin ce mata a'a sai kawai taje ta dauki ta nufi masaukinsa, tana isa ta tsaya a bakin dakin ta tattaro natsuwarta sai ta murda handle ta shiga da sallama, yana ganinta ya mike zumbur daga kwancen da yake, dama tunaninta yake tun dazu da dawainiya da sha'awarta har hakan ya haifar masa da ciwon mara, shiyasa ma yake niman maltina ya sha da wani magani saboda duk in ya tsinci kansa a irin wannan yanayin to dole sai ya sha maltina hade da magani yake samun natsuwa. Sarah ganin yadda ya taso yana kallonta sai ya sata yin baya zuwa jikin kofa jikinta ya shiga rawa gaba daya bukatarsa ya taso mata, Hydar yaje ya amsa maltinan ya ajiye a kan center table ya dawo inda take tsaye ya dago fuskarta ya hura mata iskan bakinsa da sauri ta runtse ido, sai ya matsar da ita jikin kofa ya sanya key ya rufe ya juyo gareta da take kallonsa cikin tsoro, Hydar ya zaro mata Ido cike da wasa.
Ba sace ki zanyi ba kike kallona haka, sai dai don Allah ki tsammin ruwanki dan gaskiya ina cike da mugun k'ishi.
A'a uncle gaskiya bazan iya ba, ka bude min in tafi.
Sarah zaki iya, karki haramtawa kanki abinda zuciyarki ke so, domin dazun kawai ya tabbatar min da kina muradina. Ki bani dama na dan lokacin da zanyi a gidan nan mu jiyar da juna dadi.
Sarah ta girgiza kai ta kasa magana sai hawaye dake bin kuncinta, wanda ta rasa dalilin saukarsu na damuwar cin amanar mijinta ne ko na muradin kasancewa da Hydar din, a haka ya cimmata ya jata har jikin gado ya zaunar da ita amma ta kasa yun kurin hanashi, Hydar ganin ba zata bashi wahala ba ya fara sarrafata ta inda zai gigita tunaninta, Sarah ta kasa hanashi sai ma sauke ajiyar zuciya da take yi, a haka ya ja ra'ayinta sosai har suka fada duniyar cin amana babu ji ba gani. Tun misalin karfe biyar suke abu guda sai wayan Sallar magrib suka kyale juna badan sun kashe kishir ruwan sake damunsu ba sai dan gajiya da suka yi, suka kwanta rigingine suna maida numfashi. Hydar yace cikin zolaya.
Da kin so ki hana mu jin dadin juna, Ashe ke zuma ce dole kiyi min yanga.
Uhum kaima zuman ne domin ka gigitani da dandano mai dadi.
Kafin ya bata amsa Ummi zo tana buga kofa, a zabure Sarah ta jawo kayanta ta rungume su a jiki saita sauka da sauri ta nufi toilet ta rufe, Hydar ya mike tare da gyara kan gadon yadda ba zata gane komai ba yaje ya bude mata kofa yana sakin hamma irin ya tashi daga barci, Ummi ta saki murmushi.
Lallai kana jin dadi barci ma kake yi?
Toya na iya gwauro ba mata, ashe har duhu yayi haka? Kinsan tunda nasha maltina barci ya sace ni, kece kika tashe ni.
Nima nayi zaton barcin kake yi shiyasa nazo na tasheka kayi sallah.
Kin ko kyauta nagode.
Haba babyna babu godiya a tsakaninmu
Ta fada tana Mai Zama a bakin gadon.
Gaban Hydar ya fadi amma da yake Dan bariki ne bai nuna ba ya koma ya zauna kusa da ita ya kamo hannunta.
Kije ki shirya min abinda zanci dan yunwa nake ji.
An kammala abincin dare kai yake jira, Ni kasan me ya kawoni ma wlh can wurin kaikayi yake nace bari nazo kw sosamin.
Haba haba Baby tun yanzu.
Eh, ai yau ina so in fara kalaci da kai tun yanzu har dare muna murzan juna.
Hydar ya runtse ido, saboda yasan Sarah taji duk hirarsu, kuma tabbas taji domin jikinta ya gama jikewa da gumi tare da tsoro hade da mugun mamaki.
Hydar cikin dabara ya mike tsaye yana cewa.
Kema kinsan domin ki yasa nake gidan nan, dan haka bazan tafi ba har sai kin koshi sosai, yanzu kije sai bayan Sallar isha'i sai ki dawo.
To shikenan, amma kayi sauri ka shirya ka fito falo, Ina bukatar ganinka a kusa dani.
Angama hajiyata.
Yana fadan haka ya ja hannunta zuwa kofa, ta fita ya maida ya rufe da key tare da sauke ajiyar zuciya. Ya isa toilet ya bude ya samu Sarah ta maida kayanta sai kallonsa take cikin tsoro, Hydar ya dage mata gira.
Ki fito ta wuce.
Sarah ta fito ta tsaya rike da hannunta, gaba daya a daburce take. Hydar ya zauna a gefen gado ya bude maltina ya kurba kana yace cikin jarumta.
Nasan kinji hirata da Umminku, to ki daukeshi duk yadda yazo miki a zuciyarki, idan kinyi shuru da bakinki tamkar kin birne naki sirrinne, in kuma kika furtawa wani to kin tonawa kanki asiri ne, amma ki sani daga yau alakarmu ta fara kenan har sai ranar dana bar gidan Nan, ko kizo nan ko in biki dakinki. Zaki iya tafiya.
Yana gama magana ya mike ya shige toilet ko ajikinsa, Sarah ta saukar da gauron numfashi tasan cewa ta shiga wani tarko mai fiddata sai Allah, dama shi zina haka yake da dadi amma kuma cike yake hatsari, fargaba da dana sani, jiki a sanyaye ta bude kofar ta leka ta tabbatar da ba kowa sai ta bi da karamar hanya ta fice taje ta shiga side dinta ta baya, tana shiga taga Ubaidu zaune a kujera yana danne danne a waya, gabanta ne yayi mummunar faduwa.
***** *****
Yola
Addu'ar Arba'in
Akwana a tashi ba wuya a gurin Allah yau ya kama addu'ar Arba'in din Jidda, da misalin karfe bakwai na safe aka gabatar da addu'an, anci ansha tare da yin sadakar abinci, mutane sun taru sosai kama daga dangi har mutanen arziki, Haruna shima ya zo tare da 'yan uwansa maza uku, musamman Haruna yasanya aka raba kananun buhun shinkafa wanda yake dauke da sunan Jidda a matsayin sadaka ga al'umma, aiko unguwar ya cika da jama'a kamar zai tsage kowa sai amsar rabonsa yake, duk yawon abincin nan sai da ya kare har wasu basu samu ba, dan babban mota yazo kofar gidan cike da abinci, wannan lamari ba karamin faranta ran Baffa ya yi ba ko ba komai hakan ya samar masa da karin mutunci da girma a idon al'ummar unguwar.
Bayan komai ya lafa karfe goma na safe da minti biyar aka daura auren Haruna da Lubabatu bisa sadaki dubu hamsin, hakan ya yi matukar burge mutanen da basu da labarin hadin auren, sun samu addu'ar fatan alkhairi sosai da yabo, musamman Haruna daya amince da auren duk da tana dauke da lalura. Cikin gida kuwa ya cike da al'umma daga jimamin mutuwa an koma murnar aure, kowa ka ganshi yana cikin farin ciki sabanin Lubabatu data kunshe kanta a daki cikin kunci, saboda yawon kukan da tayi idonta duk sun kumbura ga tsananin ciwon kai daya sata a gaba, babu kowa a dakin ba wanda ya rabeta balle su gane irin halin da take ciki, ba tada kawaye ta taso ita kadai take harkanta babu mutane da suke rabarta illa iyayenta kawai da marigayiya Jidda. Sai bayan sallar azahar Umma ta samu halin shigowa dakin yadda ta sameta yayi matukar tada mata hankali.
Lubabatu kashe kanki za kiyi ne? Dan Allah karki sanya rauni akan kaddararki.
Umma ta fada tana mai dafa goshinta ta ji yayi zafi rau sosai, da sauri ta fita ba jimawa ta shigo mata da ruwan kunu da maganinta da take sha na asibiti.
Tashi kisha ko zazzabin zai sauka.
Umma tace tare da kamata ta zauna, ba musu Lubabatu ta amsa kunun tasha tare da shan maganin, cikin kankanin lokaci gumi ya soma karyo mata, alamar tsananin ciwon ya karu ne saboda yunwar dake dawainiya da ita.
Nasan kina fashin sallah koma ki kwanta, insha Allah kika samu barci azzabin zai sauka.
Lubabatu ta kwanta tana mai sauke numfani.
Nagode Umma, kuma zanyi matukar kewarki, Ina ji a jikina kamar ba zan sake ganinki ba in na tafi.
Karki sake fadin haka Lubabatu kiyi fatan alkhairi, kuma aure ibada ce insha Allah ba zakiyi nadamar biyayyar da kika yi mana ba. Insha Allah aurenki da Haruna alkhairi ne.
Allah yasa.
Tace tana matsar kwalla, Umma ta shafa kanta tana cewa Ameen, bata bar dakin ba sai da barci mai nauyi ya dauketa kafin ta koma wajen mutane suka cigaba da shagalin biki.
*******
Washe gari.
Da misalin karfe takwas na safe an kammala shirya Lubabatu da kayanta wanda zata tafi dasu, tun jiya da daddare su Baffa suka yi mata fada, Dan hakan ba bata lokaci aka fita da ita wajen motar da zata kaisu kaduna, matar Kanin Baffansu da wata gaggwansu sai kawar Umma sune za suyi mata rakiya zuwa gidan aurenta, duk da Haruna bai so haka ba yaso a bashi matarsa su wuce ta jirgin sama, sai dai bai nuna damuwarsa a fili ba sai ya amince tare da nimo musu motar da zai kaisu har can, sannsn ya wuce masaukinsa ya kimtsa kana ya wuce ya samu jirgi ya wuce dashi kaduna.
Bayan su Lubabatu sun shiga mota Baffa da Umma da sauran dangi suka tsaya jikin tagar motar suna yi musu addu'ar fatan sauka lafiya, Lubabatu ta dago kai ta kalli Baffansu.
Baffa ka yafe min ka yi min addu'a a duk lokacin daka tunani.
Insha Allah zan miki, kiyi hakuri da rayuwa kinji.
Yace yana mai jin kwalla ya cika masa Ido, bai san yana kyaunar Lubabatu sosai ba sai yau, hakanan yaji damuwa ya ziyarceshi akan tafiyarta sai kawai yabar jikin tagar yana goge kwallarsa ya shiga gida, Umma ta kalleta sosai cikin kauna.
Lubabatu kiji tsoron Allah a duk inda kike insha Allah zaki dana sani ba.
Nagode Umma.
Ta fada da murmushi a kan fuskarta domin ta karawa Ummansu karfin guiwa, itama murmushi tayi ido cike da kwalla, driver ya tada mota ya soma tafiya suna dagawa juna hannu, Lubabatu kuka ya dauke mata dif gaba daga zuciyarta ta bushe saboda zuwa wannan lokacin ta gama sadakarwa zamanta a gidan Haruna rubutacce ne, dan haka babu sauran kuka sai dai ta shiryawa irin zaman da zata yi a gidansa.
#Rahmace
#MamanSultan
#share
#comments
#vote
__________________
TALLA
*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*
-Yana ciko breast suyi kyau.
-In sun fadi zasu ciko su tashi.
-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.
-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.
-And finally yana karin ni'ima sosai.
Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.
Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free
Price:N4,000
Location: Kaduna State
WhatsApp: ***.
UMMU SULTAN
100% NATURAL HERBS.
[12/8/2021, 4:42 PM] Rahma Kabir: LUBABATU
08
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
_Afwan sisters da jina shuru kwana biyu hakan ya faru ne sanadin jiki da jini. Insha Allah daga yanzu zaku rika samun update akai akai. Nagode da kulawarku gareni_
KADUNA.
Haruna ya isa kaduna da wuri, ba bata lokaci ya kira driver yazo ya dauke shi suka wuce zaria. Bayan sun isa wani gidansa dake can, sun samu komai na gidan a gyare yake saboda akwai mai gadi da me kula da cikin gidan, falo ne madaidaici da daki uku a ciki duk da bayi sai kitchen a falo, akwai komai na bukata a gidan tamkar da macen aure dake rayuwa a ciki. Koda Haruna da yaga babu wani gyara sai ya kira number wata mata ta dauka ya tabbatar mata da sun iso suma su karaso. Minti ashirin wannan matar da ya kira ta iso tare da wasu mata uku wanda suke a matsayin yan uwansa, sun zo tare da kulolin abinci na tarban baki, suka tsara komai tamkar a gidan suka yi girkin. Haruna ya kira driven su Lubabatu ya gaya masa address din gidansa yace in sun karaso ya kira shi koda bai gane ba zai sa azo a dauke su, daga nan sai ya wuce zuwa cikin garin Zaria.
____
4:46pm
Motar amarya ta karaso basu sha wuyar gane gidan ba, wa'innan matan suka fito har wajen motar suka yi musu iso zuwa cikin gidan, suka yada zango a falo cikin gajiya ko wannensu yana wash saboda zaman mota, sunyi saurin isowa saboda babu tsaitsaye a hanya, sun samu kyakkyawar tarba fiye da zatansu, sai suka zama kauyawa sunata raba ido gidan mai dankaren kyau, ga abinci kala kala da nama har sai da suka ture duk kuwa da yunwar da suka kwaso, bayan sun huta sosai sai suka gabatar da sallar azahar da la'asar, kana suka zauna zaman hira da wa'innan matan tare da gabatar da juna. Gabda magrib ne matan suka wuce gida da nufin zasu Zo da safe su kawo musu abin kari kafin su wuce. Lubabatu tunda suka iso fuskarta tana rufe da mayafi, gabatar da sallah shine ya dagata a inda ta zauna, ruwa kadai ta iya kurba ta kasa cin abinci duk yadda su Inna suka matsa Mata data ci Amma taki, dole suka rabu da ita. Da dare yayi suka kwanta a falo kan kafet suka ce Lubabatu ta shiga cikin daya bedroom din ta kwana tunda gidanta ne Amma fir taki dole suka kyaleta. Su dai sun samu barci amma Lubabatu bata runtsa ba har asubahi sai mugun tunani barkatai daya addabi zuciyarta duk yadda taso ta yakicewa kanta ta kasa, sai ma kuka data yi ma'ishinta ba mai lallashi dole tayi shuru dan kanta. Koda aka kira Sallah ita ce ta tashi sauran matan suka gabatar da farali.
***
Da safe
Wa'innan matan sun kawo musu abin kari, bayan gun gama suka yi wanka suka shirya, hatta Lubabatu itama tayi wanka ta shirya cikin wani leshi da matan suka kawo mata, tayi mamakin yadda kayan suka zauna a jikinta ganin basu san girman jikinta ba sai dai tasan kila Haruna ya gaya musu, ba wani kwalliya tayi ba sai mai kawai ta shafa fuskarta ta fayau kamar wcce ta tashi daga cutar shekara idanunta sun firfito waje saboda rama, karfe tara da rabi Haruna ya zo gidan da yake be kwana anan ba, bayan sun gaisane yace su fito mai motarsu yazo, cikin hanzari suka mike dan dama tuni sun gama shiri, su Inna suka dankawa Matan Nan amanar Lubabatu, suka amsa tare da jaddada musu zasu rike amana, sun hada musu sha tara na arziki danginsu atamfofi da kayan abinci sai da suka cikasu da mamaki sosai, suka rakosu har mota suna yi musu godiya, Lubabatu taso fitowa Amma sun hanata, sai kuka take tana gunji, ji take ta rabu dasu kenan ba zata sake ganinsu ba, gaba daya taji ta tsani kanta da rayuwar, mutuwa Jidda ya zame mata sabo, komai gani take kamar a mafarki. Tunani da damuwa sun mata yawa kanta ya yi zafi sosai da tsananin ciwo, wani irin jan numfashi tayi wanda taji kanta yana yawo a sama, nan take jiri ya kwasheta ta fadi a sume, su kuma duk suna waje Haruna ya basu makudan kudi nashan ruwa a hanya suka wuce. Sai da suka daina ganin motarsu kafin suka dawo ciki suka samu Lubabatu a wannan halin, Haruna ya isa gareta da sauri yana cewa daya daga cikin matan.
Hajiya Hindu suma ta yi, ina ga kuje kawai zan tura muku kudi ta account nagode da kokari.
Ok ba damuwa, muke da godiya Allah ya baku zaman lafiya ya sanya alkhairi.
Ya amsa da amin sai suka wuce, shi Kuma ya daukota kamar wata jinjira ya fito da ita ya sanyata a kujerar bayan motarsa, ya koma ciki ya dauko kayanta da sauran nashi kayan ya sanya a boot, yacewa driver su wuce, ba bata lokaci ya shiga motar shi kuma ya zauna a baya ya daura kan Lubabatu a cinyarsa suka wuce zuwa kaduna tana a sume. Haruna yaji dadin suman da ta yi saboda dama baya so ta san inda suka nufa sai dai ta farka ta tsinci kanta a katafaren gidansa dake kaduna wanda ya keso ya cikata da mamaki, sannan kwakwalwarta zata hutu kasantuwar yawan damuwa data sanya kanta ga rashin cikakken barci.
__
KADUNA
Haruna sun isa gidansa dake unguwar Kadaure, can ciki suke inda babu mutane sosai kuma duk gidajen masu hannu da shuni ne a layin kowa naji da kansa da kudi, shiyasa babu wata alakar makotaka a tsakaninsu mazan ma daidaiku ne suka wayi juna shima sanadin haduwa da suke a masallaci lokutan sallah. Bayan sun shigi ciki ma'aikatansa suka tsaya a gefen motan, daya daga ciki ya nude masa suka tsuguna suna kwasar gaisuwa hannu ya daga musu cike da kasaita ba tare daya amsa ba, mulkin ya dawo jikinsa domin ya kasance a masarautar gidansa sai abinda ya gadama zai aiwatar, ya dauki Lubabatu ya sabata a kafada ya juya fuska daure ya nuna musu bayan boot ba tare da yace komai ba, jikinsu yana rawa suka isa boot din domin sun gane abinda yake nufi dasu kwaso kayansu, ya wuce ciki suka bishi da kayan har falo suka ajiye shima ya wuce da ita bedroom din marigayiya Jidda wanda yake dauke da kayan zamani komai tsaf kamar tana raye, hatta hotonta yana manne a jikin bongo kamar za a kirata ta amsa, kullun dakin yana gyara, ya kwantar da ita kan gado sai ya koma dakinsa ya dauko ruwa a gora ya zo ya bude ya zuba ruwan a tafin hannunsa ya shafa Mata a fuska da duk jikinta, nan take ta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da numfashi a hankali ta farfado, ko bude ido bata yi ba barci ya dauketa, Haruna ya cire mata mayafi da dankwali ya gyara mata kwanciya sai ya fice zuwa dakinsa ya yi wanka ya kimtsa kana ya kwanta domin ya rage gajiyar zirga zirgan daya sha na kwana biyu.
____
Dare
Lubabatu sai dare misalin karfe tara da mintuna ta farka, ta mike ta zauna tsakiyar gadon cikin nauyin jiki, a hankali ta dawo cikin natsuwarta sai ta shiga kallon dakin idonta ya sauka a kan hoton Jidda ta kura mata Ido tare da saukar hawaye a kuncinta masu dumi, ta jima a haka kafin ta sauko ta isa jikin wani labule da take zaton windo ne, tana budewa taga garin yayi duhu sai hasken farin wata da wutar lantarki, abinda ya bata mamaki bai wuce yadda ta hango gidajen mutane a kasa ba, da sauri ta saki labulen tana tambayar kanta a zuciya.
A ina nake to?
Kafin ta yi tunanin amsarta an bude kofar an shigo, Haruna ne ya shigo fuskarsa dauke da murmushi.
Amarya kin tashi kenan, nasan zuwa yanzu kin huta sosai. Yanzu ki shiga ban daki ki watsa ruwa sai kizo kici abinci kafin ki rama sallolin da ya wuceki.
Hamma ina ka kawoni? domin naga ba wancen gidan muke ba
Ta mika masa tambaya ba tare da ta amsa masa maganarsa ba.
Wannan shine gidan da zaki rayuwa, wancen gidan zamu rika zuwa lokaci zuwa lokaci Kuma…
Amma me hakan yake nufi?
Ta katse masa maganarsa cikin hanzari.
Bana son yawan tambaya, kije kiyi abinda nace miki.
Yayi maganar cikin tsare gira tare da isowa inda take tsaye ya kama hannunta ya jaka zuwa toilet, ya kunna mata ruwan wanka ya hada mata komai yanayi yana yi mata bayanin yadda zata rika amfani da su, kafin ya fice ya bata wuri, tsayawa tayi kamar gunki tana kallonsa harya gama ya fice, ta sauke guntun ajiyar zuciya ta tube kaya ta samu wani karamin bokiti ta kamfaci ruwan daya hada mata a bahon ta yi wanka a waje domin tana tsoron shiga bahon ji take in ta shiga kamar zai gudu ta ita, a tsorace ta gama ta fito bata sameshi ba ta jawo jakar kayanta ta ciro riga da zani na atamfa ta sanya da sauri gudun karya shigo ta sanya hijab ta shinfida dankwalinta ta kintaci gaban ta zauna tare da gabatar da sallah saboda ba zata iya tsayuwata domin jikinta ba karfi. Sai da ta gama tas kafin ta fito sanye da hijab din, wani wagegen falo ta gani mai dauke da manyan kujeru da kayan zamani a ciki, tsayawa tayi baki kage tana cike da mamaki, taji an motsa kofa da sauri ta kai kallonta gurin sai ga Haruna ya shigo.
Kin kammala kenan sauko muje kici abinci.
Ba um ba um um ta bishi a baya taga sun isa matakala tana hango lafiyayyen falo a kasa, nan take ta gane a gidan sama suke, yadda taga ya sauka da sauri alamun ya saba da hakan, ita kam a hankali take sauka tare da kama karfen matakalan da iya karfinta ta sauka a hankali, ta isa tsakiyar falon ta tsaya ta wangale baki dana kare masa kallo, Haruna yana kallonta be ce mata unfanba sai da ta yi iya kallonta lafin ya yi magana.
In kin gama karence kayan dakin ga abinci kizo kici.
Ajiyar zuciya ta yi ta je ta zauna a kasa kusa da center table, bai hanata ba dan yasan cike take da kauyenci domin tafi Jidda duhun kai, shiyasa yake ganin zaisha fama kafin ya samu ta waye, ya taso ya sauke mata plate din abincin gabanta da ruwan gora hade da drink fanta sai ya koma ya zauna ya cigaba da danne danne a waya. Kamshin abincin yadaki hancinta sai ta somaci ba kakkautawa saboda mugun yunwar dake tare da ita, shinkafa ce jelof data ji kayan hadi ga manyan tsokar naman kaza guda biyu a sama, sai da ta tada abincin kaf da naman sai kashi ta bari a plate din ta shanye ruwan gaba daya kafin tayi gyatsa bata iya shan fanta ba saboda cika da cikinta yayi sai ta ja duwawunta ta isa jikin kujera ta jingina, tayi mugun koshi wanda ita kanta take mamaki yadda ta kwashi abinci haka sai kace mai cikin zani, rabon data ci abinci ta koshi tun kafin faruwar mutuwar Jidda, Haruna ya cigaba da harkokinsa ita kuma ta cigaba da kallon tv wanda ta shagala da kallon tashar arewa24, tana son ta tuno da wasu abubuwa amma ta kasa ita dai ta san bata son auren amma ta kasa tunawa da wasu lamura musamman tun barowarsu garinsu zuwa yanzu da take gidansa, tana son tuno da abinda ya faru da ita a wancen gidan amma ta mance, a yadda take jinta a yanzu kamar ba tada matsala kamar ba tada sauran damuwa, tana jin samuwar cikakken natsuwa a zuciyarta wanda ta kasa gano me ya kawo Mata wannan sauyin harta saki jiki ta ci abincin gidan hankali kwance. Ganin tunanin yana sanya mata ciwon kai sai tayi sauri ta janyeshi ta cigaba da kallonta. Haruna yana kula duk motsinta, Kira ne ya shigo wayarsa sai ya mike da sauri ya shiga wani daki dake nan falon ya rufe ya kara wayar a kunne.
Aliyos komai ya daidaita a yanzu haka harta ci abinci babu gardama.
Hahaha, ai na gaya maka kana shafa mata wannan ruwan anyi an gama dole ta kasance cikin bin umarninka. Sai abu na gaba, karka bari daren amarcinku ya wuce yau domin akwai haske da babban fa'ida idan har ka kusanceta.
Angama Namijin duniya, nasan ba zata taba kiba domin na shiryawa wannan ranar tuntuni.
Dan iskan abokina ba kada wasa, nasan duk abinda ka kudurta sai kayi da alama zuwa yanzu ka kusa ka fini himma a wannan sabgar
Haruna yayi dariya tare da shafa kansa, suka yi sallama sai ya fito ya kalli inda Lubabatu ke zauna har ta fara gyangyadi. Ya isa kanta ya tsaya yana murza zoben azurfansa tare da daure fuska ya ce cikin kakkausar murya.
Ke tashi mu je daki mu kwanta.
Firfigit ta bude ido ta daura kan nasa, sai ta mike cikin sauri saboda kwarjini daya yi mata, ta wuce gaba ta soma tafiya ba tare da musu ba, sai dai can kasan zuciyarta tana jin kunar biyayyar da take masa tana son hana kanta sai dai bata iya aiwatar da haka, tana son tuna wasu abubuwa amma ta kasa, siraran hawaye ne ke bin kuncinta wanda ta kasa tare su, har suka haura sama ganin bata sauri ya shiga gabanta tare da damko hijab dinta ya jata zuwa dakinsa, a gefen gado ya yi mata masauki ya ce ta hau, ba musu ta hau jikinta yana rawa zuciyarta na tsananta bugu.
Tashi ki cire kayanki duka.
Ta mike a kan gadon ta shiga cirewa tana hawaye, hatta pant bata bari ba ta rika boye jikinta da hannu, sanyin ac yana ratsata ta soma jan numfashi da kyar alamun ciwonta ya motsa. Haruna ya kare mata kallo yana wani shu'umin murmushi sai ya isa bedside dirowa ya dauko wani igiya ya hau gadon ya daure mata hannunta duka a jikin gado, tana kuka sosai cike da tashin hankali tasan kila ba zata kwana ba don ta gama karaya da lamarinsa, ya kashe wuta ya zare kayansa kana ya hau gadon a haka ya farwa Lubabatu ba sakonnin wasa ko dan aike har ya rabata da budurcinta, ita dai tunda ya soma komarin shigarta ta tsandara wani ihu to bata sake sanin duniyar da take ciki ba domin ta Suma, a takaice dai Haruna Fyade ya yi mata mafi muni.
***
Gidan Alh. Lukman Giwa
Sarah ta dake tare da tattaro natsuwarta sai ta shiga da sallama, Ubaidu ya amsa yana dago kai.
Diamond Ina kika shiga ne inta Kiran wayarki baki dauka ba, wlh hakan yasa na kasa samun natsuwa gabana yanata faduwa, nayi zaton ko wani abu ya sameki ne fa.
Sarah ta karasa ciki da murmushi a fuskarsa, ta zauna a wani kujerar sabanin da yadda take yi mishi koda daga kicin ta fito tana kaurin girki a kusa da shi zata zauna koda one seater ne, bai kawo wannan tunanin ba shi dai kawai damuwarsa ta fada masa dalilin kin saukar wayarsa.
Diamond wai yaushe ka dawo?
Yanzun nan shigowata, Amma baki amsar tambayata ba.
Kaga yau a garden na yini tun bayan fitarka, na mace sam da wayar a daki, da yake dazu naga sakonka shiyasa koda na tuna ban dauki wayarba ban damu ba.
Ok har naji natsuwa, ko aikin bamu gama ba na dawo fa, sai dai gobe insha Allah Zan fita da wuri mu karasa.
Allah ya taimaka, bari na watsa ruwan zafi na kwaso sanyin waje.
Bari nazo muyi tare.
Ban yarda ba kowa ya yi nashi.
Tace da sauri tana mikewa ta shige bedroom, Ubaidu ya bita da dariya yasan ta gane cewar ba wankan kadai za suyi ba. Gudu gudu tayi wankar tsarki ta fito ta shirya ta daura Sallar magrib, shiko Ubaidu tuni ya fice masallaci dan yin sallar isha'i.
#Rahmace
#MamanSultan
#share
#comments
#vote
___________________
TALLA
*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*
-Yana ciko breast suyi kyau.
-In sun fadi zasu ciko su tashi.
-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.
-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.
-And finally yana karin ni'ima sosai.
Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.
Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free
Price:N4,000
Location: Kaduna State
WhatsApp: ***.
UMMU SULTAN
100% NATURAL HERBS.
[12/8/2021, 4:42 PM] Rahma Kabir: LUBABATU
09
Rahma kabir Mrs MG.
Wattpad@rahmakabir
EWF.
Da Ubaidu ya dawo daga masallaci ya samu Sarah tana drying kanda da hand dryer, cike da mamki ya karasa ciki ita kuma tsoro ya kamata dan ba tayi zaton zai shigo a wannan lokacin ba, dan ya saba in ya dawo masallaci sai ya fara isa sashin Maminsa kafin ya dawo side dinsu, ya zauna gefen gado.
Diamond me ya hadaki da drying kai ke ba janaba ba ko haila? Kuma nasan shekaran jiya kika je saloon.
Um dazun na sakarwa kaina shawa ne da ruwan zafi saboda sanyin dana kwaso a lambu, shiyasa nake tsane sumar da dryer.
Tace cikin in-ina da boye tsoronta a fili.
Ok in kin kammala kije ki dibo mana abinci bana jin zuwa dinning.
Da to ta amsa masa ta cigaba da gyaran cikin sauri tana hamdala a zuciyarta da karyarta ta shiga, ko da yake tasan zai yarda tunda a kwai kyakkyawar aminci a tsakaninsu.
*
Da safe
Ubaidu ya fito zai wuce aiki Sarah tayi masa rakiya ya shiga mota ya tafi sai ta wuce side din Mami ta sameta suka gaisa kana ta zauna suka cigaba da hira, ta kai kusan awa guda a gunta kafin daga bisani ta dawo dakinta tana budewa ta yi arba da Hydar ya daura kafa kan center table yanata danna remote din tv hankalinsa kwance, da sauri ta shiga ciki ta danne kofar da bayanta ta sauke gauron numfashi cike da faruwar gaba, ta kasa yi masa magana tsabar yadda ta firigita da ganinsa, Hydar ya taso cikin tafiyar takama ya iskota har inda take tsaye ya lakaci hancinta da yatsa ya soma magana cikin sanyin murya.
Akan Idona kika raka mijinki, na shigo na budaki ashe kin fita, na jima Ina jiran dawowarki. Sarah na kamu da sonki tare da tsantsar shawararki, dan haka Ina so ki shayar dani irin ruwan koramar da kika bani jiya domin bai kashe min kishin ruwa ba, nayi harka da mata sosai amma ke naki lanbun na musamman ne domin ya kunci kayan alatu iri iri.
Sai ya ja fasali tare da rausayar da kai gefe yana yi mata kallo kasa kasa mai kunshe da sakonni da yawa, Sarah ta sauke numfashi.
Bana tunanin wannan boyayyen alakar zai cigaba, duba da irin kalubalen da zamu muskanta duk da na samu nishadin da ban taba damu ba a jiya, Zan jure iya wanda ka bani ya wadatar dani, zaifi kyau mubar wannan sirrin a haka.
Dako kin yi babban nadama.
Ya fada cikin izza tare da kamo wuyan rigarta ya fincikota ta fada kirjinsa ya maida hannunsa zuwa bayanta ya rungumeta tsam a jikinsa kamar zai maidata ciki, Sarah ta dago kai sai kawai ta hade bakinsu domin bata jin zata iya hakura da shi, haka suka shagala a wajen tare da lulawa wata duniya. Bayan minti sha biyar suka ji ana kokarin bude kofar da sauri suka saki juna tare da danne kofar dukansu su biyun suna danne numfashinsu, da kyar Sarah ta lalubo natsuwarta ta ce cikin sanyin murya.
Waye ne?
Ni ce Anty.
Cewar Rahima da sauri Sarah ta nuna masa ya shiga kitchen da hannu, bai musa ba yaje ya boye a can, sai ta budewa Rahima ta shigo.
Anty dama pink din gyalenki zaki aramin saboda yau muna da birthday din wata friend dina. Daga makaranta zan wuce.
Ok ta ce sai ta wuce daki ta je dauko mata, ita kuma ta zauna akan kujera tana kallon tv, karar waya taji kamar daga kitchen sai ta juya da sauri tabbas daga can taji kara, an kira Hydar ne sai ya yi saurin kashe kiran yana dafe kai. Rahima kamar an ingizata ta mike tana cewa.
Su anty kenan sarkin iyayi harwani sauya ringing tone ta yi, saboda shiririta wayar ma a kitchen ta bari.
Ta isa kitchen din kenan ta kama handle sai ga Sarah ta fito daga bedroom ta ce da karfi.
Keee! Me zaki min a kitchen? Dalla Zo ki amsa ki wuce nasan ki da shegen kodayi kina shiga saikin yi min barna.
Kai anty Sarah ni ba komai zanyi ba wayarki naji tana kara a ciki shiyasa Zan shiga in dauko miki.
To kunnenki bai jiyo miki dai dai ba dan ga wayata a hannuna.
Amma Allah naji ringing din waya daga ciki.
Zoki fice min na gaji da shirmenki.
Tace tana dangware mata gyalen a hannu ta jata zuwa kofar fita, Rahima tayi mamakin yadda tayi mata saboda ba kasafai ma take magana ba balle ta nuna damuwarta akan ta shiga kitchen dinta, sai kawai ta wuce tana cewa.
Su anty Sarah an tashi da masifa yau, to nagode dai tunda kin ban gyalen.
Sarah bata tankata ba ta rufe kofar tare da sanya key, sai ta shiga kitchen din ta sameshi suka sauke ajiyar zuciya tare a lokaci guda.
Zaifi kyau mu rika haduwa a wani wajen ba nan ba saboda tsaro.
Cewar Sarah, Hydar yayi murmushi tare da mika mata wayarsa ta amsa ta sanya numbernta domin tasan abinda yake nufi kenan, sai suka fito falo har ya yi kofa zai fita ya juyo.
Gaskiya bazan iya tafiya ba har sai kin samarmin natsuwa.
Ya fada a shagwaba cike da bukata, Sarah ta murmusa ta iskeshi inda ya tsaya ta kama hannunsa suka shiga bedroom dinta, nan suka yada zango suka cigaba da sabawa Allah babu ji ba gani.
__
Ummee
Wajen karfe Sha daya ta fito cikin Shirin fita domin sun aje magana da Hydar zasu fita, zata zaga da shi wajen dangi, taje kofarsa ta dinga bugawa shuru bai budeba sai Umar ne ya fito cikin yanayin barci yace.
Ummi ina ga fa ya fita dan tun dazu naga gilmawarsa zuwa falo.
Bata tanka masa ba ta fita zuwa farfajiyar gidan ta duba duk inda take tsammanin ganinsa shuru, tun dazu take kiransa a waya baya dauka sai ta yanke zuwa gun me gadi ko ya fita din. Ta iskeshi yana sauraren radio ta tambayeshi ko Hydar ya fita ya tabbatar mata da bai fita ba, sai dai in lokacin baya jikin gate ya fice bai sani ba dan dazun ya zaga bayi. Ummee ta koma ciki cike da facin rai sam bata kawo komai ba a ranta sai haushin ya fita ba tare da ya sanar da ita ba, shida be san gari ba taya ya samu gwanjin fita. Ta zame galenta ta daura kan dressing mirro tabi lafiyar gado cike da tunanin inda Hydar zai nufa.
__
Sai misalin karfe Sha biyu suka Sami halin sakin juna, ya shiga yayi wanka da sauri ganin lokaci ya wuce gashi sunyi alkawarin da Ummi zasu fita sai duk hankalinsa ya tashi dan besan ya zai kare kansa ba, domin baya burin ya bata Mata rai saboda dalilinta gashi ya samu wani wajen hutawan cikin kwanciyar hankali, ya fito ya shirya ya barta a kwance yana cewa.
Zan kiraki anjima.
Gira ta daga masa tana murmushi harya fice, ya isa kofar ya sauke numfashi kana ya tattaro natsuwarsa ya murde key dai dai lokacin Umar ya shiga kitchen na babban falo, Hydar ya fito cikin sanda yana waige waige dan kar wani ya ganshi, sai dai yayi shuka a idon makwarwa domin akan idon Umar ya fito har ya wuce dakinsa, Umar ya cika da tsananin mamaki tare da karanto abubuwa a zuciyarsa game da Hydar da kuma Sarah, ko shakka babu ya hango akwai mummunar alaka tsakaninsu Wanda zuciyarsa ya tabbatar masa, in ba haka ba tun dazu Ummi ke nimansa ashe yana dakin Sarah to me suke aikatawa tsawon wannan lokacin? tambayoyi suka cika masa kai sai yaji ransa ya baci ya fasa diban abincin da zaiyi ya koma daki cike da damuwa, ba zai so ace suna cin amanar D'an uwansa ba, domin Ubaidu mutumin kirki ne duk cikinsu babu wanda ya kaishi jin tsoron Allah, sai tausayinsa ya kama shi yanajin babu dadi a ransa, shi dai ba zai fatan ya tona musu asiri ba ko yayi addu'a akan asirinsu ya tonu domin shima yana da nashi sirrin wanda baya so asirinsa ya tonu, haka yai ta saka yana warwara Amma babu wata mafita, sai dai kawai ya gimtse bakinsa yayi shuru domin nashi boyayyen sirrin.
__
A wannan ranar sai da Ummi suka samu sabani da Hydar saboda ya kasa bata takamaimai amsar inda yaje, sannan da rashin daukar wayarta da yaki yi, ta dauki fushi dashi sosai shiko ko a jikinsa domin ya samu natsuwa sosai da Sarah in tayi fushi abanza yanada inda zai wanke makantar shawarsa.
Haka suka cigaba da gunadar da rayuwa, Hydar yabi Sarah sannan ya bi Ummi. Likafansu Sarah da Hydar taci gaba domin har fita suke su hadu a hotel su yini suna badalarsu, wanda a zuwa lokacin Umar ya san da duk aika aikan da suke aikatawa sai dai ya gimtse komai a ransa domin nashi asirin ya rufu, saboda shima a kullun yana kwana da Jamila wanda Rahima ita ce kadai tasan da nasu sirrin. Sarah tasan Hydar yana aikata tsiya da Ummi sai dai ita batasan cewa Sarah ta sani ba kullun gani take tana cin duniyarta da tsinke cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya fahimci sirrinsu ba. Duk haduwar da suke yi da Ummi sai Hydar ya sanarwa Sarah, tayi tayi ya sanar da ita asalin tsakaninsa da Ummi yaki fada mata yace sai nan gaba zai sanar mata.
Sarah taja baya da bawa Ubaidu hadin kai duk kuwa da mugun sha'awar daya san tanada shi,sai dai duk in ta bashi uzuri ko wani iri ne yana yarda, bai taba kawo wani Abu a ransa ba sai dai ya bayar a zuciyarsa sha'awar mutum yakan iya sauyawa, shiyasa ya samu natsuwar ruhi akanta ya cigaba da al'amuransa.
____
Gidan Haruna.
Sai safiya Lubabatu ta farka cikin matsanancin ciwon mara da kakkarwar sanyi, domin a tsirara ya barta ko rufeta baiyi ba sannan ga sanyin asuba daya shige jikinta, nan da nan ciwonta ya tashi ta shiga zubda kwalla tana hango mutuwarta yazo kusa, tasan ba tada sauran madafa dan da iya azabar da Haruna ya bata na jiya tasan kushewarta ne yazo, ta jawo zanin gadon da duk ya baci da jini ta rufe jikinta har kai tana makerketan sanyi a haka Haruna ya shigo ya sameta sanye da cikin kananun kaya yake, ya daka mata tsawa data sauko daga gadon. Ba shiri ta saki rufan ta jawo jikinta saboda azabar ciwo da kasanta ke mata da mara, ta kasa tsayuwa sai dai ta zauna akan tyles tana fidda sautin ajiyar zuciya da karfi.
Haruna yaja kujerar mirror ya zauna a gabanta ya daure fuska babu digon imani, ya daga hannu ya kifa mata kyakkyawar mari tare da zaro mata ido, Lubabatu tadafe kuncinta tayi suman wucin gadi saboda tsananin gigicewa, ta dago tana kallonsa, ya soma magana cikin daga murya.
Kinsan meyasa na aureki?
Ta girgiza masa kai alamar a'a idonta yana fidda ruwan hawaye.
Saboda Jidda ta sanar dake sirrinmu, na kamata tana fada miki shiyasa na kasheta a ranar, shiyasa na zabi na aureki domin ta hakanne kadai zan cimma burina a kanki. Kuma nasan tsoro ya hanaki ki sanar da kowa labarin data fada miki. Dan haka daga yanzu kisan cewa kinyi sallama da farin ciki kin rabu da iyayenta kenan har abada ba zaki sake ganinsu ba, zaki cigaba da rayuwa dani tare da maimaita duk wani abu dana yiwa Jidda na aikata shi a kanki, domin ki gasgata labarin da ta baki akan azal din dana sanyata ciki. Zan Kara miki azaba fiye da ita domin naso Jidda mun fara rayuwa da ita cikin soyayya da kauna, sabanin ke da ban taba jin digon sonki a raina ba, banda ina da babban dalili akanki babu abinda zaisa na aureki kina dauke da wannan mummunar lalurar da babu warkewa. Tashi ki tafi, kuma ki shirya anjima zan Kara karban hakkin aurensa dan sai kin dauki ciki da gaggawa yadda zanfi cin ubanki da kyau.
Cikin rawar jiki ta mike cike da tashin hankali ta fita daga dakin, tsabar ta rude ko zafin ciwon mara dana HQ dinta bata ji ba, ta shiga dakin da kayanta yake, ta wuce bayi ta hadawa kanta ruwan wanka mai zafi kamar yadda jiya Haruna ya koya mata, sai dai bata shiga bahon ba sai ta dibi ruwan a bokiti ta tsarkake jikinta kana ta rika watsawa a gabanta ruwan zafin, tun tana kukan zugi har taji tana jin dadin watsa ruwan, ta jima a haka kafin daga bisani ta kuma yin wankan sabulu sai ta daura tawul ta fito, ta shiga duba jakan kayanta bata gani ba hakan ya tabbatar mata da Haruna ya kwashe komai data shigo da shi gidan, sai ta girgiza kai ta isa Waldrop din dake dakin ta bude taga kaya makil a ciki wanda takeda yakinin na Jidda ne, ta jawo wata doguwar bakar riga ta sanya ta daura dan kwalinta, sai ta shiga duba hijab bata gani ba sai kawai ta dauki wani babban mayafi a ciki ta yane jikinta dashi sai ta wuce ta gabatar da sallar asubahi, tana idarwa aka yi nokin kofarta, ta isa ta duba sai taga wani saurayi ya miko mata tire cike da abin kari, yana ce mata cikin gwarancin hausa.
Sennu Madam, ga abincinka na safe. Sunana Samuel nine me girka abinci a wannan gidan.
Lubabatu ta gyada masa kai ta amsa tire din bata ce komai ba ya wuce sai ta juya ciki, ta ajiye tiren abincin a gabanta ta bude taga tea ne me kauri da soyayyan arish da wainar kwai, ta hadiye miyau saboda yunwar dake damunta, haka ta soma ci duk da tarin damuwar da take ciki saboda ta riga ta sadakar mutuwa zata yi. Tana gama ci zufa ya rufeta sai ta mike ta isa gado ta kwanta ba jimawa barci ya dauketa.
Bangaren Haruna kuwa ya kwashe kayanta data zo dashi yasa ma'aikatansa sun kona, ya cire sim din wayarta ya karya ya sanya wayar a bola, shima ya cire sim din da su Baffa suka santa da shi ya karya yasa a bola, domin daga ranar ya gama amfani da shi. Ya shirya ya wuce Abuja domin ya halarci taron mitin din da aka kirashi na wurin aikinsa, bai sanar da ita ba domin yasan bazai kwana ba ze dawo shiyasa ma ya bawa Samuel kwayan maganin barci ya sanya mata a tea saboda karta tashi har sai ya dawo. Ya kuma tara ma'aikatansa gaba daya ya ja musu kunne akan su sanya Ido sosai a kanta bai yarda ta fito farfajiyar gidan ba balle taje bakin gate, kana ya sallame su, driver ya jashi zuwa wajen jirgin kasa, ya hau karfe goma jirgunsu ya wuce zuwa Abuja.
#Rahmace
#MamanSultan
#share
#comments
#vote
_____________
TALLA
*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*
-Yana ciko breast suyi kyau.
-In sun fadi zasu ciko su tashi.
-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.
-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.
-And finally yana karin ni'ima sosai.
Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.
Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free
Price:N4,000
Location: Kaduna State
WhatsApp: ***.
UMMU SULTAN
100% NATURAL HERBS.