LUBABATU

10 to 13 last free page

by @rahmakabir13

[12/8/2021, 4:43 PM] Rahma Kabir: LUBABATU


10


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir


EWF.


_Masoya Ina matukar godiya da comment dinku tare da addu'anku gareni jazakallah khair_



Lubabatu wajen karfe biyar na yamma ta farka, ta tashi zaune bisa gadon tana me yin hamma tare da shafa cikinta alamar jin yunwa, ta daga kai tare da duba agogon bango dake dakin taga babban sanda akan 5 hakan ne ya bata cewar biyar ne na yamma saboda bata iya agogo ba, ko a gida a haka take ganewa sai kuma agogon waya dake nuna lokaci baro baro, ta sauke nishi a hankali sai ta sauka daga gadon ta shiga bayi ta gabatar da alwala kana ta fito ta rama sallar azahar da la'asar, bayan ta idar sai ta fito falo ta hangi tiren abinci akan center table sai ta yi sauri taje ta bude taga tuwon shinkafa miyar kulewa danya sai kamshin manshanu ke tashi, ta sauke tiren kasa ta shiga cin abincin jikinta yana rawa. Can kasar zuciyarta tana mamakin yadda take cin abinci babu fargaba sannan kuma hartake mance matsayin halin da take ciki, ta rasa gane yadda bata iya sarrafata zuciyarta akan ta hana kanta faruwar wasu abubuwan, tana cikin tashin hankali da tsoro amma kuma wani lokaci tana mance komai, tana cin abinci hawaye yana sauka mata sai dai be hana ta fasa ci ba, sai da ta cinye tas kana ta wanke hannu a cikin kwanan ta sha ruwa ta koma gefe tana mayar da numfashi, takai kusan minti sha biyar a haka kafin daga bisani ta mike tana zaga falon tare da bude duk dakin data gani tayi sa'a duk a bude suke, ko wani daki abin kallo ne domin an kashe masa kudi kamar ba za a mutu ba, dakuna biyar ne a saman Kuma duk da kaya a ciki, sai dakin motsa jiki wanda yaji kaya masu tsada daga gani kayan kasar waje ne, sai karamin kitchen shima da komai a ciki, sai ta ga wata kofa tana budewa taci karo da barandar dake sama ta zaro Ido tana kallon gidajen mutane dake makotaka dasu ga mutane dake wucewa akan layi ga motatoci suna wuce, hakan ya tabbatar mata da suna cikin mutane ba daji suke ba, sai taji dadi a ranta, ta zauna a daya daga kujeru da suke mallakin wajen domin shan iska, ta shagala da kallon cikin gidan wanda yakeda mugun girma ba zata iya cewa ga iyakarsa ba, ta mike iska yana kadata sanyin yana ratsata ga kamshin furanni suna dukan hancinta ta lumshe Ido cikin jin dadin yanayin.


Gida har gida amma ba wajen zama ba.


Tace a zuciyarta tare jin saukar siraran hawaye a kuncinta, ta hango wani matakalan karfe siriri wanda yake a markwade har kasa zai kai mutum zuwa wani bangare, cikin karfin hali ta isa gun ta hau matakalan a tsorace ta kama karfen da duka hannunta tana sauka a hankali tare da binsa duk yadda yake har ta sauka, ta tsinci kanta a bayan gidan cikin wata katuwar lambu wanda yake dauke da kayan marmari, duk da akwai tsoro a tare da ita amma wajen ya bata sha'awa ta shiga ciki sosai iska yana kadata tare da shagala da kallon wajen, ta jima tana aikin kallo domin har saida magriba ta kawo jiki kafin ta farga da duhun wajen tayi sauri tabi wannan matakalan tahau ta koma inda ta fito, ta shiga falon ta rufe ta ciki ta koma dakinta tayi alwala kana ta gabatar da sallah ta zauna a wajen tana istigfari. A dai dai wannan lokacin kewar iyayenta ya dirar mata.


Koya su Umma zasuji in suka ji labarin na mutu?


Tace a ranta tare da tausayinsu dake bin jikinta. Ta shiga tinaninsu da yadda suka rabu, daga karshe sai ta tuno da yadda suka isa Zaria da lokacin da wa inda suka kawota suka wuce yola, ta tuna lallai suma tayi a lokacin.


Kenan ina Sume ya kawo ni nan gidan? To wai nan wani gari nake? Haka zan cigaba da rayuwa? Meye makomar aurena?


Tayi tambayoyin a fili sai ta fashe da kuka, tayi me isarta ba me lallashi a haka har aka kira sallar isha'i ta mike ta gabatar tare da shafa'i da wutri tayi addu'a ta shafa kana ta fita falo, nan ta taga tire din abinci tasan an kawo na dare, aiko ta bude ta samu shinkafa da miya taji nama sai ruwa, sun dena kawo mata drink saboda bata sha. Ta zauna ta cika ciki ta koshi kana ta mike ta sauka falon kasa ta samu tv a kunne ta rashe a kujera ta soma kallo tana zancen zuci.


Su kullun da wuta ba'a daukewa kila ba a kasarmu nake ba.


Abinda bata sani ba wutar gidan yana hade da inverter da an dauke inverter take fara aiki ana kawo wuta ta kashe kanta ta cigaba da chargi, shiyasa ko da yaushe wutan gidan baya yankewa. Haruna karfe tare da rabi ya shigo gidan, ya sameta kwance a kujera tayi barci sai ya wuce dakinsa ya yi wanka kana ya sanya kananun kayan barci ya sauko kasa ya shiga wani daki dake dauke da kayan cctv na gidan ya zauna kan kujera ya soma kallon duk tv guda hudu dake jera a haka yaga duk abinda ya guda a gidan da bayanan, ciki harda fitan Lubabatu cikin lambu, yayi mamakin yadda take da karfin halin yin abu duk da akwai tsoronsa a tare da ita, amma bai hanata fita ba, sannan ma ta lanbun gidan katangar dake baya ba tada tsawo zata iya bi ta gurin ta nima guduwa, duk da yasan ya kafeta a gidan amma yau da gobe karyata boka, asirin zai iya ya dena tasiri a kanta. Ya sauke a jiyar zuciya.


Lallai dole na dauki mataki na sanya miki jin tsorona a zuciyarki, a zahiri in Ina nan da kuma bana nan, idan na barki haka watarana nine zan sha wuyarki.


Sai ya mike a fusace ya dauki wani wayar charger ya fita zuwa falo ya risketa inda take kwance ya soma zuba mata a jiki iya karfinsa. A gigice ta farka tare da tsandara ihu saboda tayi mugun tsorata,Haruna yana zuba mata duka tana ihu tare da kururuwan aceceta, sai da ya yi mata mugun duka tayi ligi ligi kafin ya kyaleta ya tsaya ya sharce gumi yana maida numfashi, Lubabatu ta cigaba da kuka tana sosa jiknta da ya ji mata ciwo shashin bulala rudu rudu yayi ja har fuskarta, ya koma ya zauna ya ce cikin daka tsawa.


Dan uwarki zo nan.


Lubabatu ta isa gabanta ta tsuguna tare da sunne kai kasa ya cigaba da cewa.


Ki bude kunne ki saurare ni wannan shine gargadin da zan Miki na farko kuma na karshe. Daga yau kar ki gara gigin fita waje har kije lambu, rayuwa za kiyi cikin falon sama dana kasa, duk abinda za kiyi kifara sanar dani kafin ki kaiga aikata shi in ba haka ba wlh saina yi ajalinki da duka.


Gyada masa kai take cike da tashin hankali sai malalan hawaye take, ya mike tare da damko gashin kanta ta kama hannunsa saboda azaba amma yaki saki, haka ya jata har zuwa dakinsa ya jefata gado ya shige rabata da kayan jikinta in taki tsayawa ya koda mata Mari, a haka harya ciresu duka, yaje ya kashe wutar dakin ya auka mata da karfin tsiya ya kusanceta, sai da yaji Mata ciwo har jini yana fita kafin ya sarara mata ya mike ya shige bayi ya yi wanka, ya fito ya koreta zuwa dakinta, saboda tsananin azaba ta kasa tsayawa tafiya da kafafunta da rarrafe ta kai kanta daki ta samu da kyar ta yi wanka, da bin bango ta fito ta kwanta gado ko kaya bata iya sawa ba ta rufe da bargo, ba jimawa barcin wahala ya dauketa. 


Haka Lubabatu ta cigaba da rayuwa cikin kunci, babu rashin ci ko sha amma tana rayuwa cikin mawuyacin hali, Haruna tunda ya kawota gidan bai taba sarara mata na kwana guda ba ba tare da ya kusanceta cikin zalinci ba, kullun sai ya ji mata ciwo ya maidata sex machine ba control har tsawon wata guda da aurensa, a hankali harta soma sabawa da azabarsa Wanda kullun sai ya gana mata shi, zuwa lokacin zuciyarta ta bushe domin ta daina kukan fili saina zucci duk yadda zata so kwalla ya fita mata bata iyawa sai dai yawan ajiyar zuciya tare da wani abu mai nauyi daya danne mata kirji wanda ba zata iya tantance menene ba.


_____


 YOLA


Cikin sanyin la'asar Umma ke tafiya a wani yankin jeji mai yawan sahara, tun tana hango cikin gari har ta fice bata iya ganin komai sai tsilli tsillin mutane, a hankali ta daina ganin kowa sai ita kadai ke aikin tafiya wanda da ganin alamu ta gaji tare da sarewar da wuya takai inda take son isa ga yamma tayi sosai alamun gari ya soma duhu hakan ya bata cewar magariba ta kawo jiki, ta tsaya tana hutawa tare da mai da numfashi, ta shiga kalle kalle sai ta hango wata Mata can nesa zaune da sauri ta yanke shawarar isa gareta domin ta tambayeta ko ta kusa kaiwa yankin Sammani? ta isa da sauri ta cimmata ta sameta sai maida numfashi take ga kafafunta sun kumbura sai zubda jini yake, idon matar kamar zasu fado kasa a razane take, ganin da Umma ta yi Mata a wannan halin yasa ta kasa tambayarta sai tayi gaba, tafiyarta ba nisa ta kuma risken wata mata ita kuma kayan cikinta a waje tsutsotsi sai bi suke da kuda, Umma tayi tsananin firgita ta toshe hanci ta wuce cikin sauri tana waigenta, haka ta yi ta wuce Mata har kusan biyar ko wacce cikin muguwar kamala, ana shida ne ta samu wata matashiyar yarinya durkushe ta kama cikinta sai murkususu take sannan kuma ga jini yana bin gefen kunnuwanta duk ya wanke mata fuska sai kiran sunaye take barkatai tare da surutai marasa tushe da alama tana niman dauki, Umma ta tsaya nesa da ita cike da tsananin tausayawa sai innalillahi take jerawa hankalinta yayi mugun tashi, a hankali ta cigaba da addu'a yana fita a bakinta ta juya bayanta bata hango komai sai duhu, ta kalli gabanta ta hango hasken wuta naci, ta soma tunanin ta juya baya kota cigaba da tafiya, tana tsaye a gurin aka Kira Sallar Magrib, ta yunkura zata juya tayi tayi ta motsa kafarta Amma kamar an kafeshi a gurin ga wannan yarinyar lamarinta sai kara hauhawa yake, ta fara jan jikinta zuwa wajen Umma, Umma ta Kara rikicewa tana so ta gudu kafa yaki motsi addu'a kawai take jerowa tare da niman tsari, tana kokawar kwace kafarta daga inda ya kafe taji wannan yarinya ta damki kafarta ta saki wani irin kuka tare da dago kanta suka yi Ido biyu da Umma dukansu cikin razana. Umma ta ce cikin tsoro.


Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun Lubabatu me yakawo ki nan?


Bata rufe Baki ba dajin ya dauki kururuwa da amsa kuwa. A firgice Umma ta farka daga barci gumi ya gama wanke fuskarta sai maida ajiyar zuciya take tana ambaton sunan Allah, a daidai lokacin liman ya soma Kiran Sallar asubahi, Umma ta tashi zaune tana juayayin mummunar mafarkin data yi, ta shiga tsananin zullumi da tashin hankali akan rashin samun wayar Lubabatu. Wata guda kenan tun rabuwarsu da ita Basu sake jin muryarta ba sun kira har sun gaji, haka na Haruna shuru baya shiga, Umma tana yawan yiwa Baffa korafi akan rashin samunsu da basa yi a waya Amma yace babu komai in akaji shuru to lafiya ce ta kawo haka, ita ko ta kasa samun kwanciyar hankali gani take kamar Lubabatu tana cikin wani hali duk da bata zargin Haruna, tana yi masa kyakkyawar zato zai rike musu Amana, wannan mafarkin da tayi ya tabbatar Mata da akwai matsala sai dai Bata San ta Ina zata alakanta lamarin ba, sai dai hasashenta lallai Lubabatu tana bukatar addu'a.


Cikin damuwa ta sauko daga gadon ta wuce waje ta dauro alwala ta dawo tazo ta tayar da Sallar asubahi. Ta jima zaune bisa sallaya tana gayawa Allah damuwarta, tuni dama Baffa ya fita masallaci bai dawo ba saida gari yayi haske.


9:00am

Umma ta dama musu koko Baffa ya siyo musu kosai, suna zaune a baranda suna karyawa, Umma ta kalli Baffa hankalinsa kwance sai zuria abinci yake, ta girgiza kai cike da damuwa.


Malam naga sam baka damu ba akan mafarkin da na baka labari. Gaskiya ya kamata mu bincika lamarin Lubabatu domin shurunsu yana daga min hankali.


Nikam bana son wannan korafin naki saboda banga abin da zai dameni ba akan shurunsu, dududu wata guda ne da wannan auren, meye abin tada hankali? Dan Allah ki yi musu zaton alkhairi ki bisu da addu'a.


Hmmm shikenan Allah yasa mu dace.


Ya amsa da amin yana kurban koko ko a jikinsa, Umma ta lumshe Ido ta bude tare da sauke gauron numfashi kana ta cigaba da tsakurar kosai badan zuciyarta nayi mata dadi ba, duk lokacin data rufe Ido fuskar Lubabatu ke mata gizo ta kasa mance fuskarta data gani a mafarki.


_____


KADUNA

Gidan Alhaji Giwa.


Bayan kwana biyu.


Da safe duk sun hallara a dining suna breakfast Abba ne kadai bai fito ba yana sashinsa sai dai yana cikin damuwa ya birkita dakin, da alama akwai abinda yake nima, cike da tashin hankali ya fito falon ya isa wajen dinning ya rungume hannu a kirji ya soma magana cikin kaushin murya.


Jiya na shigo da kudi gidan nan kimanin million Hudu da rabi amma yau wayewa gari banga million biyu ba an dauka, wallahi akan kudin nan bazan ragawa kowannenku ba na gaji da satar da ake yi a gidan nan, ba dama mutum yayi ajiya a boye sai an samu wani shedanin daya tabasu. Tun kafin na shigo da yan sanda cikin wannan lamarin ku fito min da kudina, barayin banza dana wofi.


Gaba dayansu mikewa suka yi cike da tashin hankali domin duk satar da ake a gidan ba a taba yin me yawa irin wannan ba, Ummi cikin damuwa tace.


Lallai barayon gidan nan ya gawurta, Alhaji ina goyon bayanka ka kira Yan sanda kawai nima na gaji da sace sacen da ake a gidanan.


Subhanallahi Hajiya zaifi a fara bincike tunda matsalar cikin gida ne, baidace Yan sanda su shigo ciki ba.


Cewar Mami, Ummi ta balla mata harara tare da jan dogon tsaki.


To ayi chajen mana wake tsoro, kowa dai yasan barauniyar gidan nan sai dai kawai a yi shuru.


Ubaidu zai tanka mata Mami ta daga masa hannu dole ya gimtse maganar da zai yi ya tsaya cike da mugun takaici. Abba yace cikin daga murya.


Ku adana maganganunku ku fito min da kudina dan wlh zanyi rashin mutuncin da ban taba yi ba. Kai Ubaidu da kai Hydar na wakiltaku ki bincika ko wani daki a gidan nan, ku kuma mu hadu mu bincike falon gidan nan.


Nan take suka bi umarninsa ko wanne yaja inda zai duba su Ubaidu suka fara bincike tunda dakunan dake babban falo, a hankali suke duba duk wani lungu da sako, babu dakin da aka ware hatta na Hydar da yake bako a gidan, Abu kamar wasa karamar magana tana niman zama babba, domun kuwa su Abba sun gama bincika falukan gidan basu samu komai ba, haka su Hydar sun duba dakunan sashin Abba dana Ubaidu amma basu ga komai ba, suna kan sashin Ummi dana Mami, Ubaidu a bangaren Ummi Hydar Kuma Yana bangaren Mami.


#Rahmace

#MamanSultan

#share

#comments

#vote

   

    _____________


TALLA


*HERBAL BREAST ENHANCEMENTS*


-Yana ciko breast suyi kyau.

-In sun fadi zasu ciko su tashi.

-Ga mace me yaye zai gyaru su ciko ba ruwanta da zubewar Breast.

-Ga mata masu rama, in sun sha zasu ciko suyi kumari.

-And finally yana karin ni'ima sosai.


Kawata kin gwada magunguna basu miki aiki ba? to yar uwa kiyi kokarin yin amfani da wannan Breast enhancer din insha Allah kafin sati biyu zaki ga biyan bukata. 100% tested and trusted.


Siyan daya ko sari, muna turawa ko ina. Delivery is not free


Price:N4,000

Location: Kaduna State

WhatsApp: ***.


UMMU SULTAN

100% NATURAL HERBS.

[12/11/2021, 8:54 PM] Rahma Kabir: LUBABATU


11


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir


EWF.


Hydar yana tsaka da binciken dakin Mami ya bude bedside drower yana dubawa da hannu yaji kamar bandir din kudi a leda da sauri ya cirosu ya bude yaga dalar America bandir biyu wanda yake da yakinin ko wani bandir daya dubu dari biyar ne, kenan million guda ya samu a dakin Mami, ya yi matukar mamaki saboda yadda yaga Mami da kamewa baiyi zaton ganin komai a dakinta ba, ya karasa bincike dakin bai samu komai ba banda wannan kudin, sai ya fito rike dasu cikin leda ya isa babban falo jiki a sanyaye, yadda suka ga ya shigo jikinsu ya basu da matsala ya karasa ciki cike da damuwa a fuskarsa ya ciro kudin a leda ya rike, ko wanne cikin tashin hankali da kosawar suji a Ina yaga kudin, Abba ya jefa masa tambaya.


Habawa ni nasan kudin beyi nisa ba saboda jiya da daddare na shigo dasu, haka suke bandir bandir din dubu dari biyar biyar in dollars, lallai da ace nayi sakwa sakwa tabbas da nayi asararsu. Kuma naga bandir biyu ne saura biyu da alama barayon ya raba gurin daya boye kudin. Hydar a wani daki ka samu wannan kudin?


Hydar ya sauke gauron numfashi yace cikin dakiya.


Dakin Mami wato Hajiya babba, a can na samesu cikin bedside drower dinta an sanyasu a leda, na kara bincike ko Ina amma iya su na samu.


Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun


Mami ta ambata da karfi tana dafe kirjinta cike da gigicewa, suma sauran duk salati suka shiga yi ko wanne cike da ban ta'ajibi, a dai dai lokacin Ubaidu ya fito daga dakin Ummi, ya kammala duba ko ina be samu komai ba, ya samesu a tsaitsaye a cikin wannan yanayin mamaki, ya isa da sauri yana tambayar.


Lafiya? Me ke faruwa?


Babu wanda ya iya bashi amsa sai maganar Abba ne ya tsinkayar dashi abinda ke faruwa.


Hajiya kin bani kunya wlh ban taba zaton mugun halinki ya kai haka ba, dama Hajiya karama tasha gayamin kece barauniyar gidan nan bana yarda yau dai asirinki ya tonu, Kuma kiyi maza ki fito min da sauran kudina dan wlh akansu Zan dauki mummunar mataki akanki. Barauniyar banza kawai.


Haba Alhaji yaushe rabon dana je dakinka? Wallahi tallahi bansan da wannan kudin ba, bani ce na sace su ba sai dai in wani ya sata ya kaimin dakina domin ya kulla min sharri.


Cewar Mami ta fashe da matsanancin kuka ta samu kujera ta zauna domin kafafunta sun mata nauyi ba zata iya tsayuwa ba. Ubaidu ya dafe kansa daya ji ya sara masa ya ce cikin matsanancin damuwa.


Mami na ba zata taba satar kudinka ba wlh sharri ne aka kulla mata, haba Abba kafi kowa sanin halinta, don Allah kar ka yanke Mata hukunci cikin fushi yanada kyau ayi bincike sosai insha Allah gaskiya zata yi halinta.


Dalla rufe Mana Baki, in ba ita ce ta dauka ba taya za a samu kudin a dakinta, yau dai anyi walkiya kowa yasan itace barauniyar gidan nan, Dan haka Hajiya babba ki je ki dauko Masa sauran kudinsa ki kawo ehe.


Cewar Ummi cike da hargagi, Rahima ta ce cikin kuka.


Allah Mami ba zata yi sata ba kazafi ne kawai. Barayo dai yasan kanshi.


Ta kare maganar tana kallon Umar, shima ita yake kallo ya waro Ido waje Yana girgiza mata kai alamar bashi ya dauka ba, Ummi ce ta dankaro Mata zagi.


Dan ubanki in kika kuma magana saina karyaki, uban waye zai mata kazafi ga abu a zahiri anga kudi a dakinta.


Abba ya ce cikin fushi.


Hajiya ki tattara kayanki ki barmin gidana, duk lokacin da kika dawo min da sauran kudina saiki dawo dakinki na sakeki daki daya.


Hasbunallahu wa ni'imal wakil Alhaji karka yanke min hukunci akan abinda banda masaniya akai dan Allah.


Na gama magana ki barmin gidana na.


Yace yana kokarin barin falon, Ubaidu ya katse masa hanzari da cewa.


Tabbas Abba zaka yi dana sani nan gaba, Kuma ka sani in dai Mamina ta bar gidan nan to tare zamu barshi Zan dauki matata mu bar kama gidanka muje mu kafa sabon rayuwa Ina tare da mahaifayata.


Yana gama fadar haka ya Kai kallonsa ga Mami.


Mami jeki hada kayanki insha Allah tare zamu bar masa gidan. Sarah zo muje mu hada kayanmu.


Ya kare maganar yana kallon sarah sai ya wuce bangarensu ta bishi a baya, Abba bece komai ba ya wuce sashinsa domin har zuwa lokacin yana cikin dokin zuciya. Hydar yaji damuwa ya dabaibaye zuciyarsa àkan hukuncin Ubaidu saboda sam bayajin shima zai iya cigaba da zaman gidan babu Sarah a ciki, gani yake tamkar in suka bar gidan ba zasu sake ganin juna ba, ya shiga tunanin mafita cikin kankanin lokaci zuciyarsa ta bashi haske ya sauke numfashi ya isa inda Ummi me tsaye yace cikin dakiya.


Matsayinki na mace be kamata ki sanya ido wannan abin ya faru ba, ya kamata kece zaki sanya Baki ki taushi Alhaji, ganin Family dinku be tarwatse ba.


Ummi ta sauke numfashi.


Allah ko? Nima fa banyi zaton lamarin zai kwabe haka ba shiyasa na rasa abin cewa.


Yauwa to kin gani babu dadi ace hakan ta faru, Dan Allah ki sanya baki ko dan Ubaidu saboda yarone me hankali, ke kanki nasan kin sheda haka.


Hmmm gaskiya ne Ubaidu yaron kirki ne, banyi zaton zai yankewa kanshi hukunci har haka ba, sai dai Banga laifinsa ba saboda uwa uwa ce.


Gaskiya ne Ummi koni haka zanyi in haka ya faru dake bazan iya kallo a wulakantaki haka ba, Dan Allah kisa baki Abba ya maido da Mami wlh tausayi take bani, saboda Ina ji a jikina ba ta da masaniya kan kudin nan.


Cewar Umar cike da damuwa, Rahima tace cikin kuka.


Wlh Nima binsu zanyi dan in babu su zaman gidan ba zai yi dadi ba.


To iyayen magana naji sai ku yi addu'a Allah yasa Abbanku ya sauko dan yayi fushi sosai.


Cewar Ummi, Hydar yace cikin murmushi a fuskarsa.


Zai sauko in dai kika sanya Baki, haba kece fa tauraruwarsa abin sonsa bana jin zai bijirewa kudurinki.


Ummi ta murmusa domin ya tabo mata inda ke mata kaikayi tana son yabo komin kankantarsa, sanin hakan yada Hydar din ya ce haka. Sai ta wuce sashin Abba su Kuma duk suka zauna jugum jugum da Addu'ar Allah ya daidaita lamarin.


__


Abba koda ya shiga daki ya kasa zaune ya kasa tsaye, karshe komawa yayi jikin window ya bude labule yana kallon waje, zuciyarsa cike da damuwa hade da mamakin Mami, can kasar zuciyarsa ya kasa amincewa da zata iya satar kudinsa, a haka Ummi ta same shi ta ja kujerar dressing miro ta zauna tace cikin sanyin murya.


Alhaji ka sanyawa zuciyarka salama dan Allah, karka yaudari zuciyarka domin bana jin zaka iya rayuwa me kyau in Ubaidu ya bar gidan nan, domin na jima da sanin shine d'an daka fi so a 'ya'yanka, ka dakatar da shi domin muma muji dadin cigaba da rayuwa, ni naji dadin hukuncin daka yiwa hajiya Amma ganin Ubaidu zai barmu naji tashin hankali. Sata dai mun gane meyi, kuma ka samu million daya sai ka dauki na annabawa akan sauran kudin ka yafe, insha Allah Allah zai maida maka da mafificin alkhairi, Kuma karka manta kaine me tausana a duk lokacin da aka satar min kudi karshe rabi kake bani mu raba asara, Dan haka yanzu kaima hakuri nake baka ka maida Hajiya dakinta domin mu cigaba da rayuwa a matsayin falimy guda ba tare da kan gidanka ya tarwatse ba.


Abba ya bar jikin window ya koma ya zauna gefen gado ya sauke numfashi tare da cewa.


Lamarin ne ya sha karfin tunanina banyi zaton haka daga Hajiya ba, amma na fahimci maganarki na hakuri na maidata maganar ta wuce insha Allah. Nagode da koda yaushe kike karamin karfin guiwa hakika ke macece tagari da bana tare dake lallai da Ina cikin kuncin rayuwa, Hajiya ke haske ce a gareni.


Ummi ta murmusa har hakorarta suna bayyana ta mike cikin farin ciki tana cewa.


Kai nawane a koda yaushe Ina tare da kai, yanzu dai tashi zakayi kaje ka dakatar da Ubaidu dan kam suna can suna hada kaya.


Abba ya mike da sauri ko amsa be bata ba ya fice, tabi bayansa da kallo tana sauke shu'umin dariya saita fito zuwa falo ta sanar da Hydar yadda suka yi da Abba, ba karamin farin ciki yaji ba sai dai be nuna akan fuskarsa ba ya mike Yana cewa.


Aikinki yayi kyau Hajiyarmu, bari naje daki na huta dan yau Mijinki ya sani aiki duk ya gajiyar dani.


Se hakuri 


Ummi tace tana dariya, ya wuce itama ta wuce dakinta. Rahima ta shirya ta wuce makaranta Umar ya nufi dakinsa.


___


Gidan Haruna.


Da sassafe Haruna ya shiga dakinta da nufin sanar da ita tashirya za suyi tafiya zuwa enugu, sai dai ya taddata cikin wani irin mawucin Hali, kwance take bisa gado ta rufe da bargo jikinta sai rawar zazzabi take tare da hada gumi, kuka take yi a hankali hade da nishi sama sama, cikin isa ya janye bargon ya tsaya yana kare mata kallo, ita ko sai jawo bargon take domin ta Kara rufe jikinta, yace cikin daga murya.


Ke taso kizo nan.


Lubabatu ta lumshe ido hawaye masu zafi suka saukar mata tabude a hankali tare da mikewa zaune da kyar, saida kashin kugunta yayi kara kas ta saki karamin ihu ta dafe guiwarta na dama dake kwankwatsa da azabar ciwo, ya daka mata tsawa wanda ya sata razana ta dago kai cikin sasshekar kuka tace.


Kayi hakuri banda lafiya ba zan iya saukowa ba.


Ya tsare ta da ido tare da kare Mata kallo sosai kafi daga bisani ya ciro wayarsa a aljihu ya kira Dr. Amiru ya sanar dashi yanada mara lafiya yazo ya dubata, likitan ya tabbatar masa da zai zo cikin Yan mintuna kana suka ajiye wayar, ya zauna kefen gadon yana cewa.


Na kira shi ne ya duba ki badan naji tausayinki ba sai dan ina so ki samu lafiya in cigaba da baki sako har sai kin dauki ciki. Tafiya naso muyi me nisa wacce da nake burin daga can ba zaki dawo ba kin bar arewa kenan domin koda zaki mutu to acan kushewarta take, amma da akwai sauran shan ruwanki a garin nan zan jira ki samu lafiya sosai domin mu tafi kina cikin kuzari.


Ta kare maganar yana murmushin mugunta tare da hura iska me huci, ya mike ya zuba hannunsa duk a aljihu ya fita daga dakin cikin kasaita, Lubabatu tabi bayansa da kallo hawaye cike da idonta tace cikin zuciyarta.


Da Allah na dogara shine me rayawa da kashewa, insha Allah shine majibicin al'amurana koda na mutu a hannuka na tabbatar haka yake cikin kundun kaddarata, fatana Allah yasa nayi kyakkyawar karshe na bar maka duniyar da babu dadi sai tarin kalubale.


Sai ta lumshe Ido hawayen suka sauka a kuncinta ta koma ta kwanta taja bargo ta rufe duka kanta. Minti ashirin Dr. Amiru ya iso ya shigo har ciki Haruna ya mike yana dariya ya isa gareshi ya bashi hannu suka tafa.


Ango ango, kar dai ace harka kunsa mata?


Allah ya amsa bakinka domin abinda nake burin samu kenan, sai dai ita din Sickler ce da alama jikinta ne ya motsa.


Ayya ashe tanada matsala, anya Haruna zaka samu good result akanta kuwa kamar yayarta?


Hahaha fiye da yayarta ma zamu samu abinda muke so kasan ko wani mutum da irin tauraronsa, kafin na aureta an bincike komai.


Ai nasanka ba wasa muje na dubata saboda zan wuce da wuri ina da marasa lafiya da yawa.


Haruna yace ok sai yayi gaba likita na binsa a baya suka shiga cikin dakinta, ba bata lokaci Dr Amiru ya soma dubata tare da yi mata tambayoyi, ya dauki kimanin kusan minti goma yana bincikata kafin daga bisani yayi rubuce rubuce ya dago kansa yana cewa.


Zan diba jininta tana bukatar ayi mata gwajin jini, saboda jikinta yana bukatar a kara mata jini.


Kayi duk abinda ya kamata, kasan ina da karamin asibiti a cikin gidan nan ina ga muje can sai ka aiwatar da komai ba sai ka fita ba.


Shege abokina komai naka special ne, sannan niko nasan kana da asibiti tunda Hajiya Jidda can take jinya. Dauketa muje.


Haruna yayi murmushin kasaita ya janye bargon ya jawota tare da daukarta ya sabata a kafada suka sauko kasa, daga kasan bene akwai wata kofa ya bude ya shiga ciki sai ga katon daki dauke da kayan aikin asibiti da na'urori kala kala da gadon kwanciyar mara lafiya har biyu, ya sauke Lubabatu akan daya ya kwantar kana ya juya kan likita.


Sai ka fara aikinka.


Dr. Amiru ya murmusa sai ya isa wani bangare ya duba kayan aiki ya sanya hand glove ya bude sterilizing machine ya dauko kayan aiki yazo ya dibi jininta tana runtse ido kana ta soma hasko labarin da Jidda ta bata akan wannan dakin da take ciki yanzu, hawaye ya soma sauka mata kirjinta yana tsananta bugu, tana kara tabbatar da labarin da Jidda ta bata gaskiya ne. Likita ya isa wani gefe ya soma gwaje gwajensa ya dauki minti asirin yana aikinsa, shi Kuma Haruna yana zaune akan wata farar kujera yana danne danne a waya. Likita ya juyo yana kallonsa fuskarsa cike da annashuwa yayi gyaran murya, Haruna ya dago fuska yana kallonsa.


Ya akayi?


Dr. Amiru ya dage masa gira yana murmushi.


Congratulations angon karni, Matarka tana dauke da sabon shigar ciki Ina ganin rashin lafiyarta ya hadu da laulayi, sannan jininta group A+ ne ba zai yi wahalar samun wanda za a kara mata ba.


Haruna ya mike yana shafa kasunbarsa yana fidda wani shu'umin murmushi.


Ni ba na wasa bane, aikina kullun cikin dai dai yake tafiya, ba zan taba samun gargada ba har abada.


Shege abokina shape shooter kenan aikinka yana kyau. Bari na kira a kawo mana jini.


Kayi hanzari domin bana son bata lokaci.


Likita ya kira wani abokinsa likita suka yi waya kana ya sauke ya cigaba da aikinsa, Lubabatu Banda kuka babu abinda take yi hankalinta in yayi dubu ya tashi tunda taji zancen tanada ciki, tasan lallai mutuwa yana gabda ita tasan cewa Haruna zai aiwatar da duk abinda ya aiwatar akan Yar uwarta akanta. Innalillahi... Kawai take abbata a zuciyarta tare da karonto ayatul kursiyu da duk addu'ar da ta koya wajen Ummansu.


Cikin tsayin minti talatin an kawo ledan jini guda biyar suka sanya a fridge dake dakin, likita yayi arranging komai ya yi mata wani allura kana ya seta komai ya sanya mata jinin, Lubabatu tun tana farke har barci me nauyi yayi awon gaba da ita. Likita ya gama komai ya yi sallama da Haruna da nufin zuwa yamma ko dare zai dawo ya dubata, Haruna yayi masa godiya ya rakashi har mota ya wuce, kana ya dawo ciki yayi wanka ya shirya ya fita yasan yadda take barci ba zata farka da wuri ba, domin komai yana aunashi a ransa ne kamar yadda suka yiwa Jidda.


[12/12/2021, 9:14 PM] Rahma Kabir: LUBABATU


12


Rahma kabir Mrs MG.

Wattpad@rahmakabir



Lubabatu ta farka bayan fitarsa da kusan minti arba'in, ta dinga kallon silin tare da shiga dogon tunani me tsawo, ta dauki kusan minti ashirin a haka kana taji motsin bude kofa da sauri ta maida Ido ta rufe ta yi kamar tana barci, Haruna ne ya shigo yazo kanta ya tsaya yana kare mata kallo ya tabbatar da barci take bata farka sai ya duba ledan jininta yaga yayi rabi sai kawai ya koma ya zauna ya cigaba da danne danne a waya. A takaice dai a ranar sun wuni tare a dakin yana jinyarta, da jinin ya gama shiga jikinta ya cire mata kana ya tasheta ta tashi ta jingina jikin pillow, ya kira aka kawo mata abinci ya bata taci kadan kana ya taimaka mata tayi wanka ya sauya Mata wasu kayan, ya maidata kan gadon jinyar sai taji jikinta yayi mata dadi har wani karfi taji, a zuciyarta tana mamakin irin kirkin da yayi mata yau, shine ya maida mata wani jinin ya cigaba da shiga jikinta, da yake ya iya komai akan Jidda domin likita ya koyar da shi. 


Kwanan Lubabatu biyu tana jinya saida tasha ledan jini hudu kafin taji sauki sosai, a kwana biyu Haruna ya shayar da ita ruwan mamaki yadda yake bata kulawa na musamman har addu'a take a ranta Allah yasa zamansu ya daure a haka wata kila da zata samu farin ciki ko kadan ne a rayuwarta, tasan dai duk yanayi ne domin cikin dake jikinta wanda take da yakinin akwai mugun shirin da yake akanta. Hawaye ya cika mata ido ta shanye su bata bari sun zubo ba, tana zaune jikin pillow shi kuma yana zaune a wannan farar kujerar kamar yadda ya saba, yana jiran likita yazo domin sunyi waya dazun ya bukaci ganinsa. Minti goma sai ga Dr. Amiru yazo suka gaisa yana cewa.


Amarya ta samu sauki sai sallama ya rage.


Yana zancen ya isa jikin gadonta yana dubata tare da yi mata sannu ta amsa tana gyada kai, Haruna ya daura kafa daya kan daya yace cikin murmushi.


Dama saukin nake jira ta samu domin cikin jikinta nake so ka cire, kuma kaga sai ta sosai samu lafiya hakan zai faru.


A cire cikin kuma?


Dr. Amiru yace yana kallonsa, Lubabatu taji gabanta yayi mummunar faduwarsa nan take tsoro ya rufeta ta tashi zaune cikin rikicewa tana kallonsa. Haruna ya mike ya zuba hannunsa a ajihun wando yace cikin dage gira.


Kwarai cirewa nake so ayi doctor, ko ka mance aikinmu na baya ne? To ya kamata ka tuna domin zan daura daga inda na tsaya kamar yadda nayiwa Jidda to ina so itama na aiwatar da komai akanta.


Abokina baka ganin ita wannan tana dauke da lalura, Ina ganin ka bari cikin yayi kwari sai a cire a duk lokacin daka bukata.


Hmmm nifa yanzu nake so a cire shi. Lubabatu Bari na baki labari gutsire yadda aka yi Jidda ta rasa cikinta na farko.


Ya kare maganar Yana kallonta hankalinsa kwance fuskarsa dauke da annashuwa, ita ko idonta sunyo waje ta shiga matsanancin firgici yadda take zaune a kan gadon kamar za a ce mata ket ta ruga a guje. Haruna ya zauna ya cigaba da cewa.


Likita hada kayan aiki domin yau nake so a cire cikin nan.


Angama ranka ya dade.


Cewar Amiru ya isa wani bangare ya soma ciro kayan aiki, Lubabatu fitsari ta saki akan gadon tsabar firgici, wani irin dunkulallen Abu ya tokare mata zuciya ta kasa motsin kirki balle ta samu halin kuka. Haruna ya cigaba da cewa.


Lokacin da Jidda ta samu cikinta na farko wata daya da sati biyu, ta soma matsanancin ciwon ciki dare da mugun laulayi duk abinda taci sai ta amayar da shi, tayi mugun galabaita hakan yasa na kira Dr. Amiru yazo ya bata gado a nan daki wato gadon da kike kwance akai, ya shiga dubata tare da yi mata gwaje gwaje, ya tabbatar mana tanada shigan ciki, hakan yayi matukar faranta min rai domin abinda na jima kenan ina dakon samu a gareta, itama ba karamin farin ciki tayi ba saboda tana sona sosai kullun zancenta Allah yasa ta samu ciki. Nan da nan likita ya daurata a kan magani domin kuwa sai da ya sanya mata ruwa saboda ta samu karfi da kuzari a jikinta, a cikin ruwan ya sanya mata maganin barci domin ta huta sosai, cikin mintuna barci me nauyi ya dauki Jidda dana tabbatar tayi barci sai nake cewa Dr. Amiru, nifa so nake ka cire cikin nan saboda Ina bukatar haka, Likita bai musa ba balle ya tambayi dalili saboda yasan komai game dani, domin duk abinda zanyi kusan tare muke yi, halinmu guda. Nan take ya soma shirya kayan aiki, Jidda tana barci ya yi mata wani alura kana ya sanya mata wani karfe a gabanta ya shiga cire cikin da wasu siringi yana kwashe duk gudan jinin, kamar dai yadda ake wankin ciki, daya gama ya danka min cikin daya cire a hannu, kana ya bula wani jijiya a hannunta ya shiga juye min jinin jikinta a wani leda, ruwan drip yana shiga jikinta, sai da ya cika min leda uku na jinin jikinta kana ya ajiye gefe, ya dauko wani sabon jini ya sanya mata yana shiga jikinta, anyi komai cikin awa biyar Jidda bata san komai da ya faru ba, sai cikin dare ta farka, ni nayi mata wanka ta shirya cikin wasu kayan na bata abinci kana ta samu dan karfi a jikinta, ta koma ta kwanta tana cemin.


Baby duhu duhu nake gani, jikina kamar ba nawa ba.


Dole zakiji haka domin kuwa kinyi bari ne ba tare da kina cikin hayyacinki ba, zuban jini kike ta yi har saida likita ya tabbatar da dole an yi miki wankin ciki saboda in ba haka ba zaki iya rasa ranki.


Nace mata hakane saboda bana bukatar ta fahimci komai domin ni ban shirya ganin matata ta haihu ba sai nan da wani lokaci wanda na barwa zuciyata. Ta Soma kuka sosai na lallasheta tare da bata baki da cewar zata kara samun wani komai lokaci ne, a hankali ta hakura ta kuma amince da duk bayanin dana yi mata, ta cigaba da jinya tare da shan kayan fruits domin ta zamu kuzari saboda jinin da aka diba a jikinta. Sati daya ta warke sai dai karfin jiki ne yayi saura, tana gama jini muka cigaba da soyayyarmu da alkawarin samun wani cikin.


To kinji yadda Jidda ta rasa cikinta na farko ba tare da ta sani ba, ba sai na tsaya yi miki bayanin ya nayi da jininta ba da kuma cikin da aka cireba, domin ciki dai bana sonshi ne, jini kuma na bada shi kyauta sadaka ga mabukata. Dan haka kamar yadda nayi alkawari duk abinda na aiwatar a kanta saina yi miki shi, sai ki shirya dan saina rabaki da cikin jikinki.


Sai a lokacin Lubabatu ta saki kuka wiwi harda sassheka, tausayin yayarta dana kanta ya cika mata zuciya, su kuma irin tasu kaddarar kenan, likita ya matso kusa da gadonta da kayan aiki Haruna ya taso ya damkota ya riketa ram tana ji tana gani likita ya tsira mata allura ta saki gigitaccen ihu, wanda yasa ta suma nan take, Haruna ya kwantar da ita likita ya shiga dubata da kyar ya tsawo kan numfashinta ya dawo sannan ta cigaba da fiddashi a hankali cikin nishi, Likita yayi aune aunensa ya juyo ya kalli Haruna.


Gaskiya idan akace dole sai ancire cikin nan to hakika za a iya rasata domin yanzu haka jininta yayi mugun hawa 200/100, bugun zuciyarta yana fita da karfi in aka matsa zuciyarta zata iya bugawa, komai zai iya faruwa. Shawara kawai ka hakura zuwa wani lokaci saboda labarin daka bata yayi matukar tasiri a kanta wanda ya haifar da shigarta wannan halin, sai dai in ka dage dole sai an cire to zan cire amma duk abinda ya faru karka zargeni.


Haruna ya dafe kai tare da sauke ajiyar zuciya.


Bana bukatar ta mutu a yanzu dan haka kabar cirewar zuwa wani lokaci, yanzu dai kayi kokari ka dawo da ita hayyacinta.


Karka damu a yanzu haka ta samu barci domin allurar da nayi mata dazun ta fara aiki bayan dawowar numfashinta.


Ok nagode zaka iya tafiya sai ka jini.


Yauwa yanzu dai zata jima kafin ta farka sai ka yi kokari in ta farka ka sauya mata daki saboda ta samu kwanciyar hankalin da ake nima. Ka Kuma tabbatar Mata ka fasa cire cikin kaga inta saki jiki wani lokaci saika sanya mata maganin barci a drink tasha sai muyi komai cikin natsuwa.


Da kyau likita bokan turai na amince da bayaninka ina godiya.


Karka wani damu domin kasan ba zan yi wasa ba akan cikar burinka.


Haruna ya girgiza kai fuska cike da farin ciki. Haka ya rako likita ya wuce shima ya shiga mota ya fice zuwa cikin gari dan aiwatar da wani sabgarsa, dan yasan har yaje ya dawo bata farka ba. 


Bayan minti talatin Lubabatu ta farko ta tashi zaune a firgice tana waige waige, ta shiga duba jikinta taga babu alamar an cire cikin ta saki ajiyar zuciya me nauyi tare da fashewa da kuka, da sauri ta sauko daga gadon ta fincike drip din dake jikinta, kanta ko dankwali babu burinta ta bar dakin ta koma dakinta ta kulle domin ta tsira da ranta, tunda tasan babu yadda za ayi ta fita daga gidan, dakinta ne kadai mafakarta, ta isa kofa ta murda handle taji a rufe kirjinta ya shiga dukan uku uku, ta shiga duba window ko akwai yadda zata iya dirka ta fice Amma Ina shima akwai karfen bogilari a jiki, ta isa jikin wani kofa da yake kamar da glas tayi sa'a a bude yake, ta kutsa ciki sai ta ganta a wani madaidaicin falo me dauke da kujerun hutawa, ta wuce ciki ta shiga duba kofa sai dai bata ga ni ba se wannan kofar data shigo, sai ta hango wani wuri kamar rami haka tana isa gurin taga matakala da zai sauke mutum kasa, a zatonta inda take sama ne batasan cewa wannan matakalar data gani underground ne zai sadata da kasan gidan wanda yake dauke da dakunan sirri guda uku, babu tsoron komai ta shiga sauka kasan da yake akwai hasken wuta, bayan ta gama sauka sai taga daki jere guda uku, mamaki ya kamata ganin bata san wajen ba hasalima ta gane ba ainahin falon kasa take ba, sai ta yi tunanin kila dakunan ta bayane idan ta bude watakila ta isa cikin falon kasa. Sai ta bude daki na farko, tayi sa'a a bude yake ta shiga sai dai abinda ta gani ya tsoratata, kudi ne bandir bandir dollers da kudinmu na nigeria dubu dai dai a jere a ciki, tun daga kasa har sama jeri jeri iya ganinta, dakin sai kamshin kudi ke tashi da kuma sanyin AC, gefe kuma ga hodar iblis wato cocaine da yawa a cikin fararen leda anyi silin dinsu ita dai bata san ko menene ba, ganin wanan daki yasa tayi sauri fitowa saboda kamshin kudin yana niman hawa kanta, sai da ta yi minti biyar a tsaye ta dawo cikin hanyacinta kafin ta isa daki na biyu shima ta samu a bude yake sai ta Shiga, shi kuma ta samu, gwalagwalai, zinari, azirfa da sauran kayan kalekale na dukiya a zube akan wanin shinfida sai dai yana cikin wani babban farin gilas, mutum yana hango komai. Lubabatu jikinta yayi mugun sanyi ta fito, tasan dai ko ba a fada mata ba tasan kayan kudi ne kunshe a gurin. Ta tsaya a kofar daki na uku gabanta na faduwa da tunanin shi Kuma me zata gani a ciki, haka tayi na maza ta murda handle ta shiga sai dai bata karasa shigan ba ta tsaya a mugun tsorace saboda ta hango katon bakin maciji a cikin wani farin gilas me mugun kama, duk da ta tsorata bata fasa kutsawa ciki ba domin gane ma idonta abin mamaki, sai dai tabar kofar a bude koda abin gudu ya kamata ba sai ta sha wuyar budewa ba, ta shiga kallon dakin tun daga gefen dama, halittun ruwa ne a cikin gilasai da ruwa a ciki su tayi ta gani, waigawar da zatayi gefen hagunta tayi tosali da mummunar abu wanda yasa ta saki mugun kara ta fito da guda kanta ya daki kofa ko kafin ta rufe kofar jini ya barke mata ta fadi kasa sumammiya. A lokacin dai dai dawowar Haruna yayi parking mota ya shiga falo da sauri Dan zuwa dakin jinyar Lubanatun.


LUBABATU


13



Gidan Alhaji Giwa.


Abba ya isa dakinsu Ubaidu abinda be taba yi ba kenan tun auren Ubaidun, ya bude murya yayi sallama da sauri Ubaidu ya fito cike da mamakin ganin Abbansu a side dinsa kafin yayi magana Abba yace ya biyo bayansa. Ba musu ya bishi suka wuce sashin Mami, sun sameta tana sallar walha kanta a kasa tana sujud, sai suka tsaya suna jiran idarwanta, ta jima a sujada kafin ta dago ta zauna zaman tahiya sunyi sa'a raka'ar karshe take, bayan ta sallame sai ta bisu da kallo idanunta sunyi jawur saboda kuka tace cikin dishewar murya.


Wallahi Alhaji ban daukar maka kudi ba kawai dai akwai makarkashiya a cikin wannan lamarin, amma babu komai na bar mutum da Allah.


Nazo nan ba dan mu maida magana ba, sai dan na sanar dake na maida aurenki sannan maganar barin gida babu shi, shiyasa na kira Ubaidu nayi maganar a gabansa domin ya fasa yunkurin barin gidan da yace zai yi, dan haka komai ya wuce batun sauran kudina kuma nabarwa Allah duk wanda ya dauka zai dawo min dasu a ranar kiyama, dan banyafe ba. 


Cewar Abba, yana gama fadar haka ya mike ya fice abinsa suka bi bayansa da kallo, Ubaidu ya girgiza kai.


Mami a gaskiya na gaji da cin kashin da ake miki a gidan nan, ina ganin lokaci yayi da zan daukeki daga gidan nan mu koma wani gurin, in yaso Abba ya rika biyoki can.


Kul naji ka kuma zanen barin gidan nan, tunda shi Alhaji yayi hakuri ya maida aurena ba amfanin mu yafi, kawai ka kara hakuri komai lokaci ne akwai ranar da gaskiya zatayi halinta insha Allah. Yanzu kaje kayi shirin aiki ka tafi Allah yayi maka Albarka.


Ameen Mami, Amma gaskiya…


Nace kabar maganar ya wuce kaje kawai.


Ubaidu ya shanye sauran zancensa ya fice daga dakin zuciyarsa sam babu dadi, yana isa side dinsu ya samu Sarah kwance bisa gado cikin bargo, cike da mamaki ya karasa ciki yana tambayarta.


Diamond lafiya kika kwanta ga kayanmu baki gama gyarawa ba? Ko da yake mun fasa tafiyar Abba ya maida aurensa da Mami yace kar mu tafi, yanzu ma na dawo ne mu maida kayanmu mazauninsu sai na shirya na wuce aiki.


Sarah ta tashi zaune tana cizon lebenta na kasa, can kasan zuciyarta tana jin farin ciki da fasa tafiyarsu, domin dama sam bata so subar gidan saboda Hydar, tace cikin muryar rashin lafiya.


Wlh dazun daka fita jiri naji ya dibeni Allah yasa Ina kusa da gado shine na zauna, daga bisani kuma naji zazzabi ya kamani shiyasa ya kwanta na rufe da bargo.


Ashsha sannu Diamond, Ina ganin tashi ki shirya sai mu fita tare na saukeki asibiti kiga likita, ni saina wuce wajen aiki.


Tace to ta sauko daga gadon shape shape ya gyara kayansu ya maidasu inda suke sai ya sauya kaya dan dama tun dazu sunyi wanka, suka kammala shiri suka fito falo, sun samu babu kowa sai suka wuce abinsu, Ubaidu ya kira Mami a waya ya shaida mata rashin lafiyar Sarah tayi mata Allah ya sauke tare da su dawo lafiya sai suka yi sallama.


Asibiti.


Suna isa Ubaidu ya sauketa ya bata 2k na kidin komawa gida ya wuce, dama tun a hanya ya kira likitansu ya shaida masa zuwan matarsa. Sarah ta shiga ta bada number karamin katinsu aka ciro aka kai dakin likita saita zauna zaman jiran layi ya kawo kanta. Bayan minti asirin da biyar layi yazo kanta ta shiga ta zauna suka gaisa, da yake sun yiwa juna kyakkyawar sani shine likitan gidansu, ya shiga tambayarta abinda ke damunta ta fada masa kana yayi rubuce rubuce ya kira wata nurse ya hadasu yace suje laboratory ayi mata gwajin daya rubuta, sannan a dawo masa da result saiya rubuta mata magani. Sarah tabi bayan nurse din zuwa lab, aka diba jininta ba bata lokaci aka yi Mata gwaje gwajen da likita ya rubuta, suka rubuta komai suka dankawa wannan nurse din sai suka koma wajen likita, nurse ta koma bakin aikinta tabarsu, Likita ya duba sakamon ya rike takardar sai Kara duban abinda ke ciki yake, fuskarsa dauke da mamaki sai dai ya boye hakan dan kar Sarah ta hasko komai, yayi rubuce rubuce ya mika Mata takardar da zata siya magani ta amsa tana cewa.


Likita baka yimin bayanin abinda ke damuna ba. 


Ya dauki tabaronsa daya aje gefe ya maida idonsa ya murmusa kadan.


Naso kafin na sanar miki na fara fadawa Ubaidu.


Saboda me yasa? Kawai ka fada min koma menene zai ji a bakina.


Ok, maleria ke damunki sai kuma kina dauke da yaron ciki.


Dagaske kake likita?


Ta fada tana dafe kirjinta fuskarta cike da tsantsar murna.


Shiyasa nace zan fadawa mijinki first, Kuma kin san nan ba wajen Wasa bane da zan zolayeki.


Wayyo Allah na, Allah na gode maka ashe nima zan haihu? Nagode likita.


Tace cikin tsantsar farin ciki tana mikewa, ta dauki jakarta ta fice ba bata lokaci, Dr. Muhammad ya bi bayanta da kallo zuciyarsa cike da sake sake da rudadden tunani,. Nan take ya kira wayar Abba wato mahaifin Ubaidu, yana dagawa suka gaisa kana likita ya ce.


Alhaji dan Allah in kana kusa kazo asibiti ka sameni akwai wani muhimmin magana da za muyi, in so samu ne ku tawo tare da Ubaidu.


Abba ya jinjina maganar likita yace cikin damuwa.


Da fatan ba wani matsala ne ya taso?


Ku daure kuzo din zaifi.


Ok ni gani nan zuwa, Zan kira Ubaidu a waya na shaida masa dan ya wuce gurin aiki.


Ok likita yace ya kashe wayar, Abba nan take ya kira Ubaidu yace su hadu a asibiti likita yana bukatar ganinsu. Ya tambayi Abba ko lafiya? ya shaida masa shima bai sani ba, haka suka yi sallama, Ubaidu ya jinjina lamarin ya shiga tunanin ko jikin Sarah ne yayi tsanani, kamar zai kirata yaji sai kawai ya fasa ya mike da sauri ya fice ko excuse be dauka ba ya fice.


Abba ya rigashi zuwa saboda dama Bai fita ba yana gida sanda likita ya kirashi, bai fita a mota ba ya jira zuwan Ubaidu domin su shiga tare. Minti Sha biyar da zuwansa Ubaidu ya karaso yayi parking ya isa motar Abbansu, ya fito suka jera zuwa wajen likita. Sun shiga office din suka zauna a kujerun dake fuskantar likita, Dr. Muhammad ya mika musu hannu suka gaisa kana ya cire tabarau dake idonsa ya kallesu da kyau yana tunanin yadda zai fara yi musu bayani, Abba ne ya katse shi da cewa.


Likita gamu mun zo Allah yasa dai lafiya?


Lafiyar kenan.


Yace yana bude family folder dinsu, Ubaidu ya kuma jefa masa tambaya.


Ko jikin Sarah ne yayi tsanani? Dan nasan itace ba tada lafiya.


Tazo harna sallameta ta wuce, dama akan batun lafiyarka na kiraku, in baku manta ba sati biyu kenan da Ubaidu ya ziyarcemu domin kara duba matsalarsa ko an samu nasara akan na baya, sai dai sakamakon iri guda dana bayan ya nuna, cewar Ubaidu ba zai iya bawa mace ciki ba duba da matsalar da yake fama da ita na karancin kwayar halitta, wanda tun yana saurayi muketa fadi tashi da kokarin ko za a shawo kan matsalar, sai dai zancen jiya iyau ne.


Sai ya ja fasali yana kallonsu, Abba da Ubaidu suka nuna jinjinarsu cewar haka maganar take, suka nima da ya warware musu abinda yasa yake nimansu. Likita ya cigaba da cewa.


Na tabbatar cewa wannan matsalar taka Ubaidu Matarka bata sani ba, hasalima wannan maganar daga ni sai kai se Abba muka sani, domin nine na baku shawarar a rufe maganar mu cigaba da kokarin shawo kan matsalar ko za a dace.


Kwarai anyi haka, ko iyayensu mata babu wacce ta san da wannan maganar.


Cewar Abba, Ubaidu ya jinjina kai, likita ya daura da cewa.


To a gaskiya akwai matsalar data taso wanda nake zargin babbace, shiyasa na kiraku domin ku sani sannan ku san ta inda zaku bincika lamarin.


Matsalar menene likita.


Cewar Ubaidu cikin zakuwa.


Matarka Sarah dazun tazo, na sanya anyi mata gwaje gwaje duba da irin bayanin data bani akan yadda take ji a jikinta, hakan yasa na rubuta mata harda gwajin ciki, to da aka kawo result dinta na duba na tabbatar da abinda nake zargi, wato Sarah tana dauke da juna biyu kuma a kalla zaiyi wata guda ko ya wuce haka.


Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun.


Abba da Ubaidu suka hada baki wajen fadar haka dukkansu cikin tsantsar tashin hankali.


Taya Sarah zata samu juna biyu likita? bayan ka tabbatar mana da Ubaidu bazai iya baiwa mace ciki ba, ko yaji sauki ne bamu sani ba?


Hmmm a gaskiya matsalar Ubaidu tana nan bata sauya ba, babu yadda za ayi ya baiwa matarsa ciki. Wannan yasanya ma na kiraku domin ku bincika lamarin. Kuyi hakuri da abinda zan fada, a gaskiya Sarah ta samu ciki ne a wajen wani.


Hasbunallahu wa ni'imal wakil.


Ubaidu yace yana cire hular kansa, Abba kuwa cewa yayi.


Laa haula walaa kuwwata illa billah. Akwai babbar matsala.


Yanzu sai ku bar maganar a nan ku fara binciken inda matsalar take, wannan ne dama dalilin kiran da nayi muku. Zaku iya tafiya.


Kusan tare suka mike ko wanne jikinsa babu kuzari, musamman Ubaidu da duk jikinsa kamar an zare masa lakka, suka yi sallama da likita tare da yi masa godiya sai suka wuce. A jikin motar Abba suka yada zango suka jingina duk fuskokinsu cike da damuwa, Abba yace.


Yanzu Ubaidu dama matarka ba mutumiyar kirki bace? Ina ganinta saliha kamila ashe Hajiya karama tayi maka zabin tumun dare. Yanzu ya zamu yi da wannan matsalar? wallahi na shiga rudani.


Abba wlh nima kaina ya kulle, a sanin da nayiwa Sarah ban taba kamata da wani hali mara kyau ba sai dai in tana boye min ban sani ba. Amma nasan dai tana matukar damuwa akan rashin haihuwa da bata yi ba, kullun cikin koka min take akan kawayenta da sukayi aure bayanta duk sun haihu wasu ma harda yara biyu garesu. To Ina ganin akan kwallafa rai da tayi akan ta samu ciki kila ta fada rayuwar banza.


Allah ya kyauta. Yanzu Ina ganin mu rufe maganar ne ko mu budeshi gudun kar gaba a samu matsala?


Abba mu fara Kai kukanmu wajen Allah tare da niman zabin Alkhairi a gareshi, insha Allah duk shawarar da muka ji tafi kwanta mana a rai saimu yanketa kawai.


Gaskiya ne kayi magana me kyau, Allah ya shige mana gaba, yanzu ka wuce wajen aiki kawai nima daga Nan kasuwa zan wuce anjima in mun dawo zuwa dare saimu kara tattauna maganar.


Allah ya kaimu.


Abba yace Amin kana suka yi sallama da juna cike da tunani barkatai suka shiga motocinsu suka bar asibitin.


__

Sarah tana isa gida ko bangarenta bata shiga ba ta wuce sashin Ummi, ta sameta a falonta tana kallo, ga yadda farin ciki ya bayyana a fuskar Sarah Ummi ta jefa mata tambaya ko Zama batayi ba.


Lafiya na ganki cikin farin ciki haka Sarah?


Ummi daga asibiti nake.


Tace tana zama.


Waye kuma ba lafiya?


Nice dazun zazzabi ya rufeni bayan rikicin daya faru, shine muka fita tare da Ubaidu ya sauke ni a asibiti ya wuce aiki.


Ehen to meya kawo farin ciki a fuskarki keda ba kida lafiya?


Ummi an dubani wai ciki gareni.


Ta fada tana rufe Ido cike da jin kunya. Ummi ta saki guda tare da mikewa tsaye tana rawa.


Kai Allhamdulillah abinda muka dade muna jira yau gashi yazo kusa, Masha Allah da wannan labari, yau kin faranta min rai Sarah. Ashe inada rabon ganin kwanki. Allah ya inganta ya rabaku lafiya, yanzun nan zan kura Mamanki ta shaida wannan abin farin ciki.


Sai ta zauna ta dauki waya ta kira number mahaifiyar Sarah ko gaisawa bata bari sunyi ba ta shiga bata labari. Nan Sarah ta mike ta barta domin sai kwasar dariya duke suna hirar farin ciki, ta wuce sashinsu domin tasan Ummi itace zata yi shelar cikinta hatta Mamin Ubaidu ita ce zata fada mata. Tana shiga daki ta fada gado cike da murna, ta dauki wayarta ta shiga kiran kawayenta tana fada musu ta samu ciki. Kai cikin kankanin lokaci duk wanda ya kamata ya sani to ya samu labarin samun cikin Sarah, Ummi itace taje har dakin Mami ta fada mata Mami ba karamin murna tayi ba, wanda labarin cikin Sarah yasa tasamu yayewar bacin ran da ta samu kanta dazun, ta yi ta zuba addu'a da fatan ta sauka lafiya. Ummi ta Kira Abba ta shaida masa ya nuna murnansa ko kadan bai nuna mata ya sani ba, suna gama magana ta kira Ubaidu, shima murna ya nuna da farin ciki sai dai can kasan zuciyarsa yana cike da kunci da tunanin inda Sarah ta samu ciki.


Hydar daya samu labari ya shiga rudani da kokwanto, akan anya ba cikinsa bane? Cikin wani irin yanayi ya kira Sarah.


_*Last Freepage*_


_Me Lubabatu ta gani wanda ya firgitata harda suma? Gashi ta soma zubar jini shin cikin jikinta yana fita kuwa? Wani hali Haruna zai shiga in yaga Lubabatu a bangaren dakunan sirrinsa? Wani mataki zai dauka? Ya rayuwar Lubabatu zai kare? Tana kubuta daga hannun Haruna kuwa? Ko yana kasheta? Wani hali iyayenta zasu shiga? Shin asirin Haruna zai tonu kuwa?_


_Shin tayaya Ubaidu da Abba zasu bayyana cikin sarah ba dan Sunnah bane? Asirin Ummi, Hydar, Umar da Sarah, Jamila Yar aiki yana tonuwa kuwa? Menene asalin Family Alhaji Giwa? Shin Hashim yana rama wulakancin da Rahima tayi masa? Yaushe za'a warware cakwakiyar dake gidan Alhaji Lukman Giwa?_


*Labarin Lubabatu ku dauke shi tamkar a gabanku komai yake kan faruwa, akwai sauran badakala, rudani da kuma tsantsar rikici, abubuwa da yawa basai na tsaya dogon bayani ba, domin duk wacce ta bibiyi labarin daga farko ta fahimci haka. 


_*Last Freepage*_