Chapter 5
by @autarmama
👬ABUL-KHAIR👬
(the identical twins)
TSARAWA DA RUBUTAWA DAGA SALMEERT SANI SALMAN TRIPLE S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️🧚♀️)
*WANNAN LITTAFIN NA KUDINE ,KUMA WANDA SUKA FARA BIYA KAFIN A GAMA FREE PAGES TO ZAI BIYA #300 NE, WANDA KUMA BASU BIYA BA HAR AKA GAMA TO ZAI BIYA #400, IN KUMA BAKA DA RA'AYIN SIYA TA NAN, TO SAI KAJE CHAN AREWABOOKS KA BIYA KASHA KARANTUNKA CIN FARASHI MAI SAUKI KUMA CIKIN KWANCIYAR HANKALI*
https://arewabooks.com
*yi a Amfani da wannan 👆 link din domin shiga cikin manhajar kai tsaye*
*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
***
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alƙalaminmu ƴancinmu*
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ,DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI,ALLAH INA ROƘONƘA YARDA NA FARA LITTAFIN NAN RANAR 6 GA WATAN ZUL-HAJJ, ALLAH KASA NA GAMA LAFIYA, ALLAH KA DAFAMIN A CIKIN DUKKAN LAMURANA, ALLAH KA CIKAMUN DUK BURIKANA NA ALKHAIRI , WANDA BANA ALKHAIRI BA ALLAH KA CHANJAMIN SHI ZUWA NA ALKHAIRI*
PAGE 5
"""""""""""""""""""""""""""""Masarautar Nri, Yarima Agulu ne tsaye, rike da kan Wata jaririya wadda da gani ma sabuwar haihuwa ce, dan ga Ciɓi nan ko yankewa ba'ayi ba.
sosai take tsanyara ihu gaba daya gurin sautin Ansakuwar kukanta yake tashi, kafin daga bisani na fara juyo kukan wata mata dake durkushe tana kuka tare da roko, cikin murya mai ban tausayi da naiman a tausaya mata, take cewa.
"kayimin rai Mai girma Agulu, ka bani Yarinyar nan dan Abun Bauta Kal'ana ka taimakamin, it itace kawai sanyin idaniyata a duniyar nan, idan har ka mata wani abu to tabbas zaka lalatamin tawa rayyuwar nan'' , ta fada tana cigaba da rushewa da kuka.
shi kuwait tsaye yake kiiikam, ba alamar damuwa kwata-kwata akan fuskarshi.
wani dan icce aka samo masa mai tudu sosai, sai cikinshi an dan fafa , anyi kamar kwarya.
jaririyar da take, fara tas da ita mai kyau, ya daura kanta kan abun , kuka sosai Yarinyar take, kamar tasan a dai-dai lokacin ake shirin daukar ranta, muryarta har shaƙewa take saboda kuka.
smma shi sam hakan bai dameshi ba dan ya riga da ya saba, da rarrafe matar da ban taɓa ganinta cikin Masarautar ba, ta rarrafo ta kama kafarshi tana bashi hakuri amma, inaaaa.
gatarin dake hannunshi mai kaifin bala'i ya daga wanda da ka kalleshi kasan datsa daya zai balla koma menene saboda har kana ina hango fuskarka ciki dan kyallin da takeyi
na wasuwa.
dagawa ya yi, tare da saita kan jaririya, datseeee kakeji, ya datse da azabar sauri matar ta dago kwayar idanunta , chan ta hangi gangar jikin kan kuma ya fado kan jikinta.
wata gigittaceyar ƙara ta saki, sai kuma ta babbake da wata iriyar dariya, kafin daga bisani ta fara wasu surutai, wanda basu da kai, da tayi magana tayi magana, sai ta saki ihu sai kuma ta gaggaɓe da dariya.
dadai ka kalleta kasan ta fita daga hayyacinta , dan har gashin kanta ya barbuzu, tashi tayi ta nufi waya hanya da gudu tana surutai.
shi kuwa Agulu, ko a jikinshi dan baiji komai ba, abun ya bude, kwaryar ciki ya dauka, tare da yin cikin Masarautar da ita.
kan Jaririyar kuwa da gangar jikin Alade aka tulamawa.
*********************
Cikin dare sosai lokacin 3, ta kusa,Muneebat ta tashi zata sha ruwa da yake Al'adarta ce kullum da dare sai ta tashi shan ruwa.
ɗirarar Motoci taji a gidan, hakan yasa zuciyarta bugawa da mugun Karfi, kofofin Orphans din aka fara bubudewa, dan tafiya dasu, wani luguɗe taji zuciyarta ta karayi.
da sauri ta koma kan bed dinsu, tare da fara cewa "Twin ! , Twin!! , Twin!!!, ki tashi ga mutanan nan suzo, ki tashi mu boye", ta fada a hankali, da wani iriyar zabura ta mike tare da dafe kirji, da sauri ta kama hannun Muneebat din, tana cewa.
"Innalillahi yanzu ya zamuyi da Hajra, saida nace ta kwana anan ta tashi ta tafi", ta fada idanun tab kwallah.
Muneebat dai batace komai ba sai jan hannun Twin din da tayi, da sauri suka fito , lokacin har an kusa zuwa ɗakinsu, a hankali suka fito tare da fara, tafi, ikon Allah ne da taimakonshi yasa har suka, karasa.
wani guri mai a azabar duhu , inda chan suka saba boyewa , duk in mutanan sukazo, gurin bashi da nisa sosai daga ɗakunansu, hakan yasa duk abinda akeyi sunaji, duk da , a hankali akeyi, amma daren da ya riga ya tsala yasa, komai sunaji.
kukan Hajra, sukaji tana cewa, "Allah ka taimakemu, dan girmanka, Twins....., ", sai kuma ta barke da kuka ta kasa fadin maganar da zata fada.
wani kukane ya ciyo zuciyar Muneebat, hakan yasa ta kifa jikin Muɗi'at ta fara kukan , ita kuwa dama a Rayuwarta da mugun wuya, kaga tayi kuka damin tana da mugun taurin zuciya..
ko da akazo kan ɗakinsu, basu shiga bama, wani ɗakin suka wuce.
haka sunaji suna gani , aka tafi da wasu daga cikin mutanan, dake gidan.
saida suka gamajin kurar ta lafa, kafin Muneebat, ta saki wata uwar ajiyar zuciya, tana shafa kan Muɗi'at da yake akan kafarta tana dan dukan bayanta Alamar lallashi.
dan ita tama kasa abinda zatace, saidai idanunta sunyi wani mugun jaa, alamar ran mata ya ɓaci..
**********************
Sun daɗe sosai a Fada, kafin , Mai martaba yace, "kun shiga gurin Momman ku, kuwa?, " ya fada yana kallon Abul.a
girgiza kai Abul ya yi, kafin yace "a'a Abbu, bamu karasa chan din ba, daga part din Nainah sai nan", ya fada yana kallon Tuntun da Khair ya daura kafarshi a kai.
a hankali Mai martaba yace, "to ku tashi mu tafi dan nima chan din zanje", ya fada yana dan dukan kumatun Khair.
a hankali ta fara bude blue eyes, dinshi yarda yake budewar a hankali sai ya bada , wani irin yanayi daban.
ganin Abul har ya mike yasa shima , tashi a hankali ,tafiya suka fara, Mai martaba gaba sai su a baya, ta cikin Fadar sukabi wata hayan wadda ta sadasu da part din Mai martabar, inba ka sani ba bazaka taɓa cewa da akwai hanya ba ta gurin.............
ga wanda zasu fara biyan kuɗinsu zasu biya #300 , ga wanda zai bari har a gama free to zai biya #400, ku biya kuɗinku ta wannan account number din👇.
1499884120
Umma salma sani. access bank.
ko katin waya ta wannan number👇.
***.
ku tabbatar kun turo da shaidar biyanku ta hanyar yin screenshot sannan ku turo ta wannan number din👇.
***.
Salmeert Sani Salman triples S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚♀️🧚♀️🧚♀️)