MADUBIN GOBE

2

by @phartybb

Ƙarfe ɗaya da mintuna na rana suka isa garin, tafiyan awanni bakwai suka yi a hanya don tsaye tsaye da suka yi.

Shigarta cikin gidan da yaranta ta samu yayanta wanda take bi ya zo, fuskarsa cike da damuwa da taji zuciyarta ya ƙara karaya.

"Yaya Muhammadu ina kaka tana lafiya?"

Girgiza kai yayi yana duban ƙanwarshi data zama wata Hajiya ga yaranta ƴan gayu.

"Lafiya lau Sadiya ki shiga tana ciki."

Da sauri ta faɗa ciki, yaran zasu bita ya hana su, da Rukayya kawai ta shiga. Wani ɗaki ya kai su ya saka aka kawo musu abinci da ruwa. Rahma ce taci abincin kaɗan Hasiya da Muhsin sun kasa ci sai kindirmo da suka sha.

Hajiya Sadiya da kuka ta fito ganin halin da kakarta take ciki. Tamkar mahaifiyar ta take kallonta.

"Hakuri za muyi Sadiya muyi ta addu'a Allah zai bata lafiya."

Yaya Muhammadu yace dan kwantar mata da hankali.

Hawayenta ta share.

"Yaya Muhammadu ji nake kaka ba zata tashi ba."

Shima yana jin hakan saboda yadda jikinta yayi tsanani.

Daren ranar basu iya runtsawa ba. A cikin gidan aka ba Hajiya Sadiya ɗaki ita da yaranta suka kwana. Kwana tayi tana sallah da rokan Allah ba kaka lafiya.

Yaya Muhammadu a kanta ya kwana, da asuba kaka ta karɓi shahada a bakin jikinta Yaya Muhammadu. Hajiya Sadiya tana yin sallar asuba ta shiga dubata ta samu rasuwarta. Kuka ta dinga yi tana mata addu'a.

Kafin karfe goman safe gidan ya cika da dangi da ƴaƴan Kaka, da suka kasance yayun mamarsu Hajiya Sadiya da yaya Muhammadu.

Ƙarfe sha ɗaya a kayi jana'izar ta aka kaita gidanta na gaskiya suka bita da addu'a. Daga nan gidan ya zama gidan makoki aka fara shigowa musu ta'aziyya.

Alhaji Mamman Bashir bai samu labarin da wuri ba sai washegarin ya taho. Bayan ya musu ta'aziyya washegarin ya koma.

Sai da a kayi sadakan bakwai kafin Hajiya Sadiya ta fara shirin tafiya dan makarantar yaranta. Haka ta taho ta bar su har lokacin yayunsu maza biyu basu zo ba sai waya da su kayi.

...

Bayan wata biyu da faruwar haka Hajiya Sadiya ta fara mance rasuwar kaka sai addu'a da take mata.

Tsakanin ta da mijinta komai lafiya haka yaranta. Rukayya sai girma take tana wayo abinta ta fara tsayawa, cikin jikin Hajiya Sadiya watanshi uku.

***

Cikin fushi ya shigo gidan ranshi ɓace abin da yaron shagon shi ya mishi ya mutuƙar ɓata masa rai.

"Lafiya Abban su?"

Hajiya Sadiya tace tana miƙa masa ruwa a cup ganin ranshi ɓace yayin da suke zaune.

Sai da ya shanye tas ya ajiye cup ɗin alama ta ƙara masa.

"Salisu yana nema ya fara min wasa da dukiya, ganin shi ɗaya ne na yarda dashi."

"Wani abun kuma ya maka?"

"Wai yaron nan aure zai yi. Ya sanar dani in cire kuɗi cikin kuɗin jikina in bashi yaƙi ya ɗauki kuɗin cinikin mu yayi abinda zai yi dashi. Kuɗin da sai mun cinye shekara kafin mu mai da. Zan nemi wani kawai, zan nemi wani yaron."

"A'a Abban su kayi hakuri, ka sanar dashi laifin shi ya kiyaye gaba kuma ya mai da hankali bisa kasuwanci dan dawo da kuɗaɗen."

"Shikenan hakan zan yi dan ɓacin rai na kasa mishi magana wallahi."

"Hakuri za kana yi. Dana mu'amala da mutane haka ya gada komai daɗewarka da mutum."

Maganganun kwantar da hankali Hajiya Sadiya tayi tawa mijinta har ya sauƙo. Kullum yana godiya ga Allah da alfahari da samun mace kamar Sadiya.

...

Bayan sati biyu.

Bayan sati biyu da faruwar haka Alhaji Mamman Bashir ya ma Salisu faɗa akan abinda ya aikata yaron yaji haushi amma bai nuna ba.

***

"Alhaji Mamman I'm sorry about what happen. Babu sunan ka cikin masu tafiya."

"What!."

Yace da ƙarfi yana tashi tsaye sai ya tuna gaban oganshi yake ya koma ya zauna.

"Ta ya hakan zai faru?"

"I don't know. Daga can Thailand suka turo sunan wanda suka zaɓa."

Zai yi magana abokinsa dake gefenshi ya mishi alama da kar yace wani abu. Haka yasa ya hakura ya miƙe.

"Shikenan Sir."

Daga haka ya fice ranshi ɓace. Rayuwar shi ta fara canzawa tsawon watanni biyu kenan. Komai ya nema baya samu sau biyu kenan.

"Alhaji Mamman! Alhaji Mamman!"

Faɗin Alhaji Tukur kenan wanda suke aiki guri ɗaya da shi kuma abokinsa daya yarda dashi.

Dakatawa yayi yana duban shi har ya ƙarasa wajen shi.

"Sorry na tsayar ka, I'm sorry for what happen."

"It's ok ba komai."

Alhaji Mamman yace zai wuce yaji Alhaji Tukur yace.

"Sai dai kamar naga ka shiga damuwa da faruwar hakan."

"Muje office."

Abinda Alhaji Mamman yace yayi gaba da sauri Alhaji Tukur ya bishi.

"Sau biyu ina neman abu cikin Company nan bana samu, na rasa mai yasa hakan yake faruwa dani."

Alhaji Mamman yace kenan ya sanar da Alhaji Tukur abinda yake faruwa dashi.

"Lallai akwai ayar tambaya kan lamuranka, amma ba komai in har ka yarda dani zan taimaka maka?"

"Wani irin taimako kuma Alhaji Tukur?"

Alhaji Mamman ya faɗa cike da ƙaguwa.

"Zan taimaka maka inshaAllah. A weekend mu haɗu zan maka bayani."

"Kai da naji daɗi wallahi, domin abubuwan nan sun fara ishana sosai."

"Kai dai kar ka damu."

Alhaji Tukur yace ya miƙe tare da fita.

Sai lokacin hankalinshi ya kwanta. In har zai taimaka mishi ya samu cigaba a aikin shi yaji daɗi kuma dole ya mishi alheri.

Sati biyu kenan da aka ɗauki sunan masu zuwa ƙasar Thailand dan saro wasu kaya a company nasu ya saka sunansa, yaso zuwa amma yanzu ya samu labarin babu sunanshi cikin wanda aka zaɓa.

Da ya koma gida bai sanar da Hajiya Sadiya ba amma ta lura yana cikin damuwa. Haka yasa tayi ta ƙoƙarin sashi nishaɗi.

An wayi gari da mummunar labari bisa gobara da ya tashi a kasuwa yau ya koma shagunan mutane da dama.

Ciki har dana Alhaji Mamman Bashir da haukane kaɗai bai yi ba da yaga yadda wuta ya masa da kaya.

Rabi da kwata duk kayan abinci ya ƙone ya farfashe.

Gari duk ya kaure da wannan hatsari daya faru. Tuni aka fara ƙira ana mishi jaje wasu har gida.

Hajiya Sadiya ta shiga ruɗu da jin babban shagon mijinta mai faɗinshi babba ga kaya dayawa ya ƙone. Ta mishi jaje da addu'ar Allah yasa wani hau ya tare. Ƴan uwa da suka samu labari har gida suka zo mishi jaje.

Kwana biyu da faruwar haka Alhaji Mamman Bashir ya fara gyaran shagon shi bai jira gomnati ta taimaka musu ba. Cikin satin bai samu zuwa aiki ba kuma basu mishi magana ba dan sun san uzurin shi.

Shagon shi ya gyara ya ƙara buɗa ginin a kayi painting, ya zuba kuɗi aka saro sabin kaya.


***

"Wallahi Alhaji Tukur abin nan ya fara ishana. Ace daga wannan sai wannan cikin lokaci ɗaya. Daga kasuwar da aikin ofishin duka haka."

Alhaji Mamman Bashir kenan yake faɗar haka ga abokinsa Alhaji Tukur bayan gaisuwa da ƙarin jaje da Alhaji Tukur yazo mishi da ganin sabon shago.

"Ai tashi za kayi tsaye abokina. Ba'a zama yanzu, yan sa ido sun yi yawa masu ruwa ana kirgawa, kaga wannan sauran arzikin shima sai ka rasa su in akwai masu mugun ido da baki."

"Allah ko Alhaji Tukur?"

"Sosai ma bana faɗa maka ba. Shawarace dama zan baka muje ka karɓi maganin bakin duniya ka tsare kan ka da dukiyar ka."

"Kamar yaya?"

Alhaji Mamman yace yana neman ƙarin bayani.

Zama Alhaji Tukur ya gyara.

"Akwai wani da yake mini aiki, can za muje. Dubiya kawai zai maka ya baka maganin tsari."

"Anya kuwa?"

Cewar Alhaji Mamman.

"Ba zaka iya ba kenan?"

Shuru yayi kafin yace.

"Zanyi tunani a kai."

Basu jima ba bayan ya gama ganin shagon suka rabu.

Da Alhaji Mamman ya koma gida ya sanar da Hajiya Sadiya yadda su kayi da Alhaji Tukur.

"Wajen boka zai kai ka Abban su." Mami ta ce.

"Boka dai Sadiya. Maganin bakin duniya kawai zai bani, baki ga yadda aka kasa dukiyar nan gaba ba."

"Ni kam ban amince da wannan duk abubuwan ba, jarabawa ce ko Ƙaddarar Allah dan ya jarabci imaninka, dan Allah kayi hakuri ka cinyewa wannan jarabawar kar ka kai kan ka halaka, duk in da kaji an ce dubiya wallahi shirka ne."

"Ya isa Sadiya, je ki kawai."

Yace yana haɗa rai. Ganin haka ta miƙe ta fita.

Daga faɗa masa gaskiya shine zai nuna ɓacin rai.

Fushi su kayi na kwanaki kafinsu shirya abinda basu taɓa yi ba. Shima sai da yace mata ya fasa kafin ta sauƙo. Ƙasan ranshi kuwa jira yake yaga wani abun zai faru ya nemi hanyar zuwa.


Wata biyu shuru lafiya suka ci gaba da rayuwarsu. Sai lokacin hankalinshi ya kwanta dan ganin babu abun da ya sake faruwa.

...

Tashin hankali da ba'a sa mishi raba.

Daren jiya ne barayi suka ɓalla shaguna suka kwashi kuɗaɗe da wasu abubuwan amfani. Tun asubanin ranar Alhaji Mamman ya samu labarin amma bai bawa labarin muhimmanci ba kasancewar yasan Salisu baya barin kuɗi a shago gida yake wucewa dasu.

Sunyi ta jajantawa mutane a gida da matarshi Hajiya Sadiya har yana cewa Insha Allah babu komai Allah ya taimaka shi dan ya san Salisu.

Sai wajen ƙarfe goma ya fita bai biya office ba ya wuce kasuwa dan jajantawa maƙotan shagon shi.

Mutane turum ya tarar bakin titin da yake shagon shi sai yaji hankalinshi yana neman barin jikin shi yayi sauri ya fito yana shiga cikin mutanen da wasu har sun fara miƙa gaisuwa da bama ji yake ba.

"Salisu mai ya faru?"

Shine kalmar daya faɗa kenan lokacin daya ganshi gaban Salisu.

Salisu da yaji cikinshi ya murɗa kaɗan ya sake fitsari ganin ubangidan shi sai gumi yake ya kasa bashi amsa har sai da ya daka mishi tsawa.

"Na ce maka mai ya faru?"

"Alhaji sun kwashe mu. Jiya na barwa Idris shagon akan in ya rufe ya saka kuɗin a Safe, to sun haɗa da namu."

Salati Alhaji Mamman ya saka yaji hajijiya na neman faɗar dashi har sai da ya dafa abu. Mutanen gurin suna mishi sannu ya bi a hankali.

"Salisu ka gama dani, ka cuce ni. Ina Idris ɗin?"

"Bai samu fitowa ba, labarin jiya ya sauƙar masa da zazzaɓi wallahi."

"Ba laifin ku bane."

Cewar Alhaji Mamman da furucin ya tsorata Salisu, mutanen gurin ya basu mamaki.

"Ba laifin ku bane, Laifi na ne."

Daga haka Alhaji Mamman ya kaɗa babban rigarshi ya fita a shagon ko takan mutanen da suke masa magana bai bi ba.

Motarshi ya shiga ya ja bai tsaya ko ina ba sai Company nasu. Mutanen da suka ganshi suka samu labarin abinda ya faru suna mishi magana bai kulasu ba ya wuce ofishin Alhaji Tukur.

"Yanzu nake shirin zuwa wajen ka. Ya abinda ya faru?"

Cewar Alhaji Tukur ganin Alhaji Mamman ya shigo a hargitse.

Bai iya zama ba dan tashin hankali yace.

"Alhaji Tukur tashi muje. Muje a dubamin wannan abubuwan ba banza aka barni ba, ko ba sa hannun wani to da bakin mutane "

Miƙewa Alhaji Tukur yayi yana ɗaukar mukullin motar shi.

"Muje to."

Daga nan suka fita a ofishin da Company gaba ɗaya, kowa a motar shi suka tafi, Alhaji Tukur a gaba Alhaji Mamman a baya yana binshi.

A wani unguwa ya tsayarsu mai suna AJARI. Unguwar tsofin kanurai malamai da kallo ɗaya ka musu kasan malaman tsubbu ne.

Ƙofar wani gida ya tsaya ya sauƙa shima Alhaji Mamman ya sauƙo suka nufi cikin gidan tare da sallama. A soro suka tsaya aka sanar da wanda suka zo gurin shi kafin ya basu izinin shiga ciki suka shiga.

Vote.

Comments.

Share.