DANGINMU NE SILA

DANGINMU NE SILA 001

by @jameey123

*_DANGINMU NE SILAR KOMAI_*



    Na


JAMEEY❣️


*MANAZARTA WRITER'S ASSOC.*


 *_BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM._*

_________________

Spreme Court Kaduna shiru ne ya gauraye illahirin wajen baka jin motsin komai sai  shashsheƙar kukan wata baiwar Allah,ga dukan alamu tasha kuka ta koshi dan ajiyar zuciyar ta kawai ke tashi a cikin Kotun,inda take shiɗe numfashi a rarrabe gami da sauke wata irij nauyayyar ajiyar zuciya ta ƴan sakanni kafin ta kalli Alqali tace."Ranka shidaɗe dan girman Allah kasa mijina ya SAKENI." 

  tunda ta faɗi wannan kalma ga Alkali bata sake cewa komai ba saima zubama Alkali rikitartun idanuwanta da tayi wa'anda basu da mararraba da garwa shi,Jira kawai take ya ba mijinta order ya saketa kamar yanda ta buƙata, shima Alkalin zuba mata ido yayi yana nazarinta dan baya tunanin tana cikin hankalin ta idan kuwa tana da hankali to ta samu taɓin kwalkwalwa na ɗan wani lokaci dan ba yanda za'ayi mai hankali ya aikata abunda tayi,furzar da iskan bakin shi Alkali yayi a hankali yace."Baiwar Allah ko zaki iya gayamani dalilin da yasa kike son mijinki ya baki takardar SAKI."? Murmushi tayi mai ciwo tana ɗan rausayar da kanta kaɗan,dan ta lura Alkali yana mata kallon sakara kuma marar hankali,maida dubanta tayi ga mijin nata wanda yake tsaye kamar gunki yana mamakin abunda take aikatawa yayin da idanun su ke cikin na juna kowa da kallan kallon da yakema ɗan uwan sa a hankali ta sauke nata idon tareda wurga mashi kallon tsana."Saboda na tsane shi." Wannan karon kuwa zuface ta keto ma Alkali dan kalaman ta sun girgiza shi sosai,a hankali ya cire tubaron dake makale fuskar shi ya goge zufar dake keto mashi sannan ya maida tubaron,a hankali ya maida duban sa kanta yace."Ko saboda mi yasa kika tsani mijinki."?cikeda kosawa da tambayar da Alkali ke mata saboda ta lura yana son ya wuce gona da iri,akan case dinta ita tazo ne dam.kawao yaba mijin order akan ya saketa bawai ya dimga jefonmata tambayoyi ba kamar wadda tayi wani laifi cikeda takaici tace."Na tsane shi kawai kuma bani ra'ayin ci gaba da rayuwar aure da shi."wannan karan ba Alqali ba hatta mutanen dake zaune a Kotun saida kalamanta ya girgizasu."keko mi zaisa hakanan kice kin tsani mijin ki ko akwai wata cutarwa da yake maki wadda tasa har kika tsane shi."?ajiyar zuciya ta muka saukewa tace."Aa ko kaɗan mijina bai taba cutata ba natsane shi ne saboda *DANGINMU*."


Saida Aqali ya gama yimatu kallo a tsanake kadin ya sauke idon shi akan mijin ta wanda duk zufa tagama keto mashi sai gogewa yakeyi baki ɗaya jikin shi yayi sanyi.tambayar da Alkali ya jefo mashi ce ta dawo dashi cikin hayyacin shi."Bawan Allah kaji abinda matar ka tace tana bukatar takardar SAKI daga gareka zaka iya bata takardar ta."Iskar bakin shi ya fesar mai zafin gaske yace."Ya mai girma mai shari'a gaskia banjin zan iya sakin matata."tunda ya faɗi haka bai kuma cewa komai ba,yayin da take watsa mashi wani irin wulakantaccen kallo mai dauke da tsantsar tsanar shi a cikin kwayar idanin ta."Kai ko miyasa zakace bazaka saki matar kaba bayan tace ta tsane ka."? cikin ɓacin rai yace."Saboda ina son ta kuma ina kaunar matata."jinjina kai Alqali yayi bayan yayi yan rubuce rubucen da zaiyi ya kuma cewa."Ka tabbatar da abinda kake faɗa kuwa."?Gyaɗa mashi kai yayi sannan yace."Kwarai kuwa ina ma matata so na haƙiƙa kuma banji zan iya rabuwa da ita."Baki ɗaya kan Alkali ya gama ɗaurewa duk mamaki ya ishe shi ya rasa ta ina zai fara wannan sarƙarƙiyar shari'ar da zai tunkara ta ma'auratan."Ko minene dalilin da yasa kake sonta bayan ita kuma tace bata son ka,ta tsane ka."? Kalmar da mijin ya tsana yaji Alqali ya ambata wai matar shi ta tsane shi,a hankali ya kuma ɗaura mata rinannun idanun sa ko keftawa baiyi yace."Ranka shi daɗe bakomai bane yasa tace bata sona ba,har take ikirarin ra tsane ni,saidan DANGINMU."Duk wanda ke cikin Kotun saida kanshi ya kulle kowa da kalar tunanin da yakeyi yana mamakin me yasa zatace a sake ta duk saboda Dangin su,da wannan tunanin ne Alqali ya kuma cewa."Baiwar Allah kinji abinda mijin ki yace bazai iya sakin kiba saboda yana sonki,ko zaki iya janye wannan kudurin naki."?wannan karan hawaye masu zafi sukai nasarar ziraro mata tace."Aa ya mai girma mai shari'a dan Allah kataimaka kasa ya sakeni."sosai take kuka marar sauti duk ta rikice."har ta gama magana Alqali na kallan ta kafin ya zare glass din idon sa yace."yau Talata Biyar ga watan July Shekara da dubu biyu da Ashirin da biyu (5/6/2022) Kotu zata ɗage wannan zaman zuwa watan gobe iwar haka biyar ga watan takwas shekara ta dubu biyu da Ashirin da biyu (5/8/2022) insha Allahu. Dan gaka kafin lokacin Kotu ta umurci ma'auratan da suje su sasanta kansu kafin zuwan lokacin da zamu sake zama."Alqali ya buga Court stick yana tashi kowa ya mike tsaye bayan Alqali ya fita daga Kotu kowa ya fita.banda kananun maganganu ba abinda sukeyi wasu na ganin rashin kyautawar wannan matar ta tace mijinta ya sake ta bayan kuma yana sonta yayin da wasu kuma ke ganin cewa tana da nata dalilin na neman saki a wajen mijin ta,wanda wasu tawaga suka tafi wajen ta wasu kuma sukayi wajen mijin nata.banda kallon hadarin kaji ba abinda sukema junan su da tsantsar ƙiyayya dake fita a cikin idanun su,da haka kowa ya kama gaban shi.

  Tafiya sukeyi baki ɗayan su,saidai wuri ɗaya motocin su suka nufa daga dangin nata har nashi suna isa bakin wani katafaren gate da sauri mai gadi ya buɗe masu gate take suka kutsa hancin motocin su cikin wata katafariyar katuwar Estate da gani ta kwashi naira saboda ta gaji da haɗuwa ga titina da suka bi ta kowa ce santa dake cikin Estate ɗin.wanda akaima inkiya da Maikaba Family Housing Estate Kaduna.suna shiga kowa yakama hanyar tafiya gida,gani nayi wannan matashiyar matar tayi parking motar ta cikin wani katafaren gida ita da wasu yan uwan ta,shima mijin nata wani katafaren katon gida naga yayi parking motar shi kusa da ta matar shi saidai da alama kowa gidan iyayen shi ya shiga tareda tawagar su.da alama baki ɗaya Estate din ba bare a cikin ta dagani duk dangi ne na jini.Koda ta shiga gidan su iske mahaifiyar ta tayi a falo zaune ita kaɗai gaida ta sukayi saidai ko kallon inda suke batayi ba jiki sanyaye suka zauna ita da kannen ta.sai magana sukeyi a kan taurin kai irin na mijin ta daya yaƙi sakin ta.takaici duk ya cika mahaifiyar su inda take masu kallan ta yaro kyau take bata ƙarƙo,faɗa tafara yi masu akan sun dameta da surutan banza da wofi ba shiri sukayi shiru,sallamar da mahaifin su yayi cikin falorn yasa kowa naba'a inda yake aikama ya'yan nasa wani irin kallon dayasa jikin su yakara sanyi ba ɗayan su,bayan ya zauna ya aikama ƴar tashi wani irin matsiyacin kallo har saida cikin ta ya katsa tsabar ruɗewa ba shiri ta mike tsaye tanansadda kanta ƙasa bata kuma yarda ta sake haɗa ido da mahaifin nata.Hanyar fita ya nuna mata ba alamun wasa a cikin kwayar idon shi,take hawaye suka fara tsere a saman fuskar ta batasan lokacin da zube guiwar taba tace."Abba dan Allah kayi hakuri kada ka koreni kabarni in zauna gida."cikeda da rauni ta ida maganar.wata muguwar tsawa ya daka mata wadda ta kara ruɗar da ita yace"nan ba gidan ku bane muddin baki koma ɗakin mijin ki ba,saina saɓa maki!."tsoro da razana suka dirar mata tasan kwanan zance kuma tasan halin mahaifin ta ba shiri ta juya zata fita daga falorn sai kuka takeyi daidai kofar fita falorn sukayi karo da mijin nata.hakan yai sanadiyar nugawar zuciyoyin su atare,da kyal ya matsa daga bakin kofar yabata hanya banda kallan tsana data wurga mashi,murmushi yayi mata wanda ke dauke da tsantsar so kaunar da yakeyi mata.Maganar Abban su tadawo da shi duniyar shagala da ya lula."maza ku koma gida bansan kara ganin ku gidan nan."To Abba."yace batareda ya karaso wajen surukan nashi ba,juyawa yayi ya fita cikin katon compound din gidan kowa ya nufi lot din suka aje motocin su kusa da juna tana bude kofa zata shiga baisan lokacin daya riko hannun ta ba yace."Ummin Sadiq meyasa kika tsaneni miyasa kika daina sona dan Allah kada ki janye wannan kudurin naki kinji matata."bawan Allah kana ganin shi kasan yana cikin matsananciyar damuwa.Fizge hannun ta tayi daga rikon da yayi mata a zafafe tace."Kada ka kuma tabani kuma kasa a zuciyar ka bazan sake zaman aure dakai ba dole saika sakeni Abban Sadiq."tana gama faɗar haka ta shige mota tayi mata key ta tafi.

 Tsaye yayi kamar an dasa shi duk jikin shi ya mutu shima motar tashi ya shiga mai gadi ya bude mashi gate ya fita motar ta,na gaba shima yana biye da ita,tana isowa bakin gidan su ta danna horn da karfi,da gudu gate man ya buɗe masu gate yana mata sannu da zuwa ko kallan shi batayi ba ta saka hancin motar ta cikin kamilin gidan nasu daya gaji da haɗuwa har zai rufe gate din kenan yaga dannowar motar mai gidan nashi ta danno kai,da sauri ya ida bude gate jikin shi na rawa ya duƙa ya gaida shi cikeda girmamawa sannan ya rufe gate din,tana fita daga mota da gudu ta shige cikin gidan Upstairs ta haye ta faɗa ɗaki ta rufo kofar daidai ya shigo cikin falorn saida yaji rufe ɗakin har cikin zuciyar shi.hakan yasa ya rufe idanun shi da suka sauya kala cikin kankanin lokaci.A hankali yake haurawa sama har ya isa bakin ɗakin ta yafara knocking duk yanda yaso ta buɗe dakin amman taki budewa."Heart beat come and open the door."cikin sanyayyar muryar shi mai dadin sauraro yake maganar.Kunnen shaggu tayi da shi kamar bada ita yake ba dan dole ya nufi dakin shi yanajin zuciyar shi na mashi masifaffan zafi.

Kwace take saman ƙawataccen gadon ta,ta rufe idanun ta kamar mai bacci ba abinda ke mata yawo akai sai maganar mahaifin ta.A hankali ta ware manyan lulu eyes dinta da suka rine tsabar kukan da ta sha.A hankali ta sauko daga gadon ta nufi Bathroom ta sakarma kanta shower tun daga kanta ruwa ke sauka tana shide ajiyar zuciya ɗai ɗai tana gama wankan ta daura towel sannan ta tayi alwalla duk kamshi shower gel ya gauraye illahirin bathroom din da tsadaddan soap din da tayi wanka dashi,koda ta fita toilet a hankali ta isa bamin Press dinta ta fiddo gownt din material tasa sannan ta kabbara sallah tana gamawa tahau addu'a tana kai kukan ta wajen Allah.  Shima a nashi ɓangaren ya rasa yanda zaiyi da lamarin matar tashi ba Allah yasani yana matukar kaunar ta kuma baiji zai iya rasata saboda itace bugun zuciyar shi,idanun sa sun koma kamar rushi tsabar rikidewa da sukayi kamar zautacce ya fara magana." miyasa zakiyi manj haka? Meyasa zaki tsane ni Ummin Sadiq kawai saboda dangin mu shine zaki ce in sakeki bayan kinsan bazan iya rayuwa idan baki tare dani ba why Heart beat kiji tausayina mana.!"ya ida maganar cikeda damuwa yana kaima iska duka,zama yayi gefen gado yana jin kamar kanshi zai rave gida biyu Wayar shi keta faman ringing yana kallo har tayi miss call.Khalid ya baiyana sakan screen din yana kallo harta kuma tsinkewa dan baiji zai iya picking Call a situation din da yake ciki daga karshe kashe wayar yayi gaba ɗayan ta yai wurgi da ita saman bed din...

____________

*_Is not for free it's 500 via 0777512438 Jamila Abubakar Bello Access Bank and show ur evidence via_* ****/*** thank you.*


Share

Dan lillah

❣️