ABUL-KHAIR

chapter 6

by @autarmama

👬ABUL-KHAIR👬



(the identical twins)



TSARAWA DA RUBUTAWA DAGA SALMEERT SANI SALMAN TRIPLE S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️)




*WANNAN  LITTAFIN NA KUDINE ,KUMA WANDA SUKA FARA BIYA KAFIN A GAMA FREE PAGES TO ZAI BIYA #300 NE, WANDA KUMA BASU BIYA BA HAR AKA GAMA TO ZAI BIYA #400, IN KUMA BAKA DA RA'AYIN SIYA TA NAN, TO SAI KAJE CHAN AREWABOOKS KA BIYA KASHA KARANTUNKA CIN FARASHI MAI SAUKI KUMA CIKIN KWANCIYAR HANKALI* 



https://arewabooks.com


           

*yi a Amfani da wannan 👆 link din domin shiga cikin manhajar kai tsaye*





*BARAKAN MU DA SALLAH ƳAN UWA, ALLAH YA MAIMAITA MANA TA BAƊIN BA ƊAƊA*





*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*

    {R.S.W.A}


***

 *_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_


*Alƙalaminmu ƴancinmu*





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ,DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN ƘAI,ALLAH INA ROƘONƘA YARDA NA FARA LITTAFIN NAN RANAR 6 GA WATAN ZUL-HAJJ, ALLAH KASA NA GAMA LAFIYA, ALLAH KA DAFAMIN A CIKIN DUKKAN LAMURANA, ALLAH KA CIKAMUN DUK BURIKANA NA ALKHAIRI , WANDA BANA ALKHAIRI BA ALLAH KA CHANJAMIN SHI ZUWA NA ALKHAIRI*      




PAGE 6







"""""""""""""""""""""""""""""""Ta gurin ba, da Sallama dauke a bakinsu, suka shiga cikin parlourn da ya gaji da hayaƙuwa, ya haɗu iya haɗuwa ga set din kujeru kusan set 3, masu azabar kyau wanda kana ganinsu ma kasan ba yan 9ja, bane yan waje ne, yan wajen ma wa'inda suka amsa sunnansu .




Sallamar naji an Ansa, rarraba ido na farayi dan ganin ta ina ake ansa Sallamar.



Masha Allah, wata Hamshaƙiyar macece, kan wata haɗaɗiyar kujera mai kyan gaske, fara ce sol matar, mai matukar kama da wani , wanda na sani , tunani na shiga yi amma , shaf ban tuna wanda suke kamar da shi ba.



wasu ƙayatattun kayane a jikinta , masu kyan gaske , wanda da ka kalleta ma kasan matar Sarkice dan sanye take da Alkyabba mai kyan gaske Maroon, gaba daya jikin Alkyabbar duwatsune masu matukar sheƙi tare da daukar ido.



murmushi ne ya suɓuce mata na ganin Zaratan Mazajanta, dake tunkaro inda take.



murmushi ne kuma ya fallasa jerarun Haƙoranta farare tarr masu azabar kyau, jeraru dasu sai wasu Haƙoran Makkah kwara biyu da ya karawa Haƙorantan kyau sosai .




kafin ta su karaso, Mai martaba, ya zame tare da zama kan 3 site, yana kallon kyawawan Samarin Yaranshi tare da Gimbiyarshi abin kaunarshi.




saida sukaje gab da ita, kafin suka sulale gaba dayansu, suka zauna a gabanta.



hakan ne ya bata damar daura, hannunta mai masifar kyau da taushi, ga wasu Zobba na zinari da ya karawa hannun kyau, a kansu ta sauke hannunta tare da shafa sumar.




Abul ne ya buɗi bakinshi a hankali ya fara gaisheta, a natse ta ansa gaisuwar tashi tana kallon Khair, da yake ta motsa baki da yatsina fuska Alamar magana yakeson yi amma, ya kasa, saboda tsabar Miskilancin shi, da Izza.




gaisheta ya yi dakyar, jijina kai kawai tayi, dan ta fuskanci shine Khair din tun daga, yarda taga yana yatsina ya kasa magana.




Fira suka fara su Ukkun, amma shi tun daga gaisuwar da ya yiwa, Momman tasu Uffan, bai sake furtawa ba saima kanshi da ya sauke kasa yanajin Surutun da sukeyi kamar suna zuba mishi darma a kai, saboda tsabar yarda surutun yake shiga kanshi.



shiyasa gaba daya zaman gurin ya gundureshi, dan wani azababben ciwon kai ma, yaji ya fara sauko mishi, hakan yasa ya kara rabewa kamar Maraya.




Nanni ce ta shigo part din, run kafin ta shigo sukaji karar tahowarta, da masifar da takeyiwa Bayi da Kuyangu , wai ita a dole Uwar Sarki.




tana shigowa Abul ya wulla mata harara, yana taɓe baki , aikuwa akan idonta hakan yasa tace, "Uwarka Muneebatu, kakewa harara, shege mai jan kunne, kai amma anyi Gantalalle, da ka biyo Halin Lele, Wallahi da kaji dadi, amma ka tafi kaje ka koyo bakin hali, duk cikin danginmu bamu da Sallamammu irinka kila acen wani guri, ka tafi ka kwaso wannan halayar, dan mi kuwa babu dangin Iya bana Baba", ta fada tana zama kan shareriyar kujera.



raba ido ta fara dan ganin inda zataga Khair, chan ta hangoshi raɓe kanshi a kasa, yana saurararsu.



"Ni yau na shiga uku ni Salamatu, wane mugun Abun kukayiwa Lele, har ya tafi wani guri ya raɓe, kuko Anya kunason ganin Annabin Rahma kuwa?, dan kunga bananan shine duk zaku tsangwameshi har, ku rabashi da cikinku, dama na sani Duk a cikin, gidan nan, nice kawai ke sonshi, duk makiyanshi ne, shiyasa a kullum nikeyi mishi Addu'ah Allah ya rabashi da, Azzalumai irinku, ", ta fada tana koma kusa da Khair.



wata uwar hararar Abul ya banka mata tare da cewa, "Dan Allah mu kiyi mana shiru, daga zuwa kinzo zaki hargitsa mana wuri, gaskiya bakiyi ba, kuma wallahi ki mana shiru ko yanzu in dauko, bindiga in harbeki", jin Abinda Abul yace ne yasa ta fara kuka tana tsine mishi.



Mai martaba ne, ya daka mishi tsawa daga maganar da yakesonyi, wadda saida tasa Nanni ma shiga taitayinta.



shiru ya yi, ya sunkuyar sa kanshi kasa, ganin hakanne yasa, Nanni cewa, "Gantalalle, Ruɓaɓɓe dakai, shegen hanci kamar na sanmaka,kuma wallahi kaje dan kanka, kuma......", bindigar da ya daga rigarshi ta gani ne yasa, ta dan kara matsawa kusa da Khair tare da rufe bakinta ko motsi ta kasa.



a kunnen Khair ta fara mishi raɗa, amma kamar ba raɗa ba dan kusan kowa naji, "Lele kaga, Wannan dan Uwan naka, bashi da kirki, Bundiga fa ya fiddo, wallahi ka ringa nesa-nesa, dashi kar wata rana ya harɓemin kai ya sani mutuwar da ban shiryaba, ni ko kwananan da kukeyi tare Alkur'an ku daina, dan wallahi na fara zarginshi, karfa yaje ya harɓeka, ya kwashe maka dukiya ya gudu, kawai yanzu ka dawo ɗakina ka ringa kwana tunda akwai ɗakuna da yawa" ta fada tana kallonshi.




wani Sanyayen murmushi ya saki mai wargaza, zuciyoyin Masoya harda ma Abokan gaba...




*****************




saida komai ya lafa lokacin ma wasu Masallatan har an fara kiraye kirayen Sallah, kafin su fito, su koma ɗakinsu cikin ƙunci da bakin cikin tafiyar da akayi da Hajra.




saida sukayi Alwala sukayi sallah kafin su taho su rungumai juna suna sauke ajiyar zuciya, baccine ya sacesu suna rungumai da juna, sosai suke baccin dan daren jiya basuyi bacci ba.




gurin 9, suna bacci basu ankare ba sukaji, saukar ruwan sanyi karara a jikinsu, firgigit suka mike a tare dan yau din, da wani mashahurin sanyi aka tashi ga kuma wani sanyi da aka kara musu...........




ga wanda zasu fara biyan kuɗinsu zasu biya #300 , ga wanda zai bari har a gama free to zai biya #400, ku biya kuɗinku ta wannan account number din👇.





1499884120

Umma salma sani. access bank.




ko katin waya ta wannan number👇.



***.




ku tabbatar kun turo da shaidar biyanku ta hanyar yin screenshot sannan ku turo ta wannan number din👇.




***.




Salmeert Sani Salman triples S° (ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️)