3
by @phartybb
"A taimaka a duba min me ke faruwa da rayuwata da dukiyataa cikin shekarar nan."
Faɗin Alhaji Mamman, bayan ya gama zubawa Malam Kalla bayanin abubuwan da suke faruwa dashi kwanan nan.
Shuru ɗakin ya ɗauka, Mallam Kalla ya ja carbi kamar sau goma ya ajiye yace Alhaji Mamman ya ɗauka da yatsa ɗaya. Da bismillah ya ɗauka ya miƙa masa ya karɓa yana dubawa.
"Karayar arziki yanzu ka sa gaba Alhaji."
"Kamar ya?" Alhaji Mamman yace cike da tashin hankali.
"Wato kana ji ba, akwai wani abu da zai shigo rayuwarka da duk dukiya da abin da kasa a gaba ba za ka samu ba, dukiyarka kuma sai ya ƙare tas. Ko kasan farar ƙafa da ake faɗa?"
Cewar Mallam Kalla yana duban Alhaji Mamman da gumi kawai yake sharewa.
"Na..na.. na sani."
Ya faɗa da kyar yana haɗiye wani yawu mai zafi.
"To shine zai shigo rayuwarka, kuma kayi gaggawar ɗaukar mataki."
"Ta yaya Mallam?"
Alhaji Mamman ya faɗa yana tunanin neman mafita.
Nan Mallam Kalla ya ja carbi ya ajiye yace ya ɗauka da wani yatsar bana ɗazu ba. Hannu na rawa Alhaji Mamman ya ɗauka ya miƙa masa.
"Matarka tana ɗauke da juna biyu?"
Mallam Kalla ya tambayi Alhaji Mamman.
Gada kai yayi yace Eh.
"To abinda zata haifa kayi nisa da ita ko shi, in kuma ba haka ba za kayi kuka da idanuwan ka. Shine kawai mafita."
'Innah lillahi wa innah ilaihin rajiun.'
Kawai Alhaji Mamman yake furtawa jin abinda Mallam Kalla ya sanar dashi, yama rasa wani irin tunani zai yi.
Godiya suka mishi ya cika shi da alheri kafin su tafi.
Suna isa wajen aikinsu Alhaji Tukur ya dubi Alhaji Mamman da ya faɗa tunani.
"Shawarar mai ka yanke?"
"Na rasa mafita Alhaji Tukur. Ina son Sadiya ina son ƴaƴan mu, amma dubi abinda yake faruwa dani, kuma zai ci gaba da faruwa in har ta haifi abin cikinta."
"To in baka shawara mana."
Cewar Alhaji Tukur.
Jin haka ya saka Alhaji Mamman juyowa yana dubanshi da kyau.
"Ina jin ka?"
"Ku zubar da cikin kawai ku huta."
Girgiza kai yayi da sauri.
"Ina son ƴaƴa na, ba zan iya bari Sadiya ta zubar da cikinta ba."
"Dama shawara ce na baka, in kuma baku zubar ba to sai dai ku rabu. Ma'ana ka saketa kawai."
Wani kallo Alhaji Mamman ya watsa masa.
"Kai ma zancen ka ke, kasan dai ba zan iya sakinta ba."
Kafaɗa Alhaji Tukur ya ɗaga alamar ko a jikinshi.
"Shikenan dama Shawara ce. Yanzu dabara ya rage maka."
Daga haka kowa yayi shuru, Alhaji Mamman ya ɗauki motarshi yana wucewa gida.
A filin gidan ya samu yaranshi suna wasa, Rahma tana koyawa Hasiya keke, Muhsin yana gefe yana kallonsu yana musu tafi shima yana so. Suna ganin mahaifinsu da gudu suka mishi oyoyo ya ɗauki wannan ya sauƙe karshe suka wuce ciki yana ɗauke da Muhsin, Rahma da Hasiya suka bi bayan su.
A falo ya tarar Hajiya Sadiya zaune taci kwalliya tana jiran shi, idon shi kai tsaye cikin jikinta ya kai ɗan wata biyar. Abin da bai taɓa faruwa a rayuwar shi ba yaji ya tsani cikin tun kafin a haifa. Idonshi ya kawar gefe yana zama.
Rukayya data ganshi tayi ta miƙa hannu ya ɗauketa yana mata wasa. Lokacin ɗaya yaji yafi son dukkan sauran yaran akan abin da za'a haifa.
Har dare Hajiya Sadiya ta kasa gane kan mijinta dan ko kallonta baya juran yi. Baccin kirki ya kasa dan nema kanshi mafita.
Da safe yace ta shirya za suje asibiti bayan yara sun wuce makaranta. Tayi mamaki amma ba tayi magana ba ta shirya suka fita.
Shawarar da Alhaji Tukur ya faɗa mishi na farko kawai zai ɗauka, ya saka a zubar da cikin duk da ya girma, dan yana son Sadiya ba zai iya rabuwa da ita ba. Ciki ne in ta zubar zata samu wani.
Kai tsaye asibiti suka nufa bayan yankan kati suka shiga ganin likita.
"Mai ke tafe daku?"
Likitan yace yana duban su.
"Cikin jikinta za'a zubar mata, tana shan wahala sosai, bayan laulayi mai zafi da take fama dashi."
Baki sake Hajiya Sadiya take jin maganganun mijinta da suka ɗaga mata hankali. Tun da suke bai taɓa nuna rashin son haihuwar da take a kai a kai ba. Hasalima murna yake in ya samu labari. Shi ya hanata planning dan yadda yace yana son ƴaƴa amma yanzu rana tsaka yace a zubar mata da cikin jikinta da ya shiga watanni na biyar.
Likitan kanshi yayi mamaki yana duban Hajiya Sadiya da ita hankalinta yana gurin Alhaji Mamman da ranshi haɗe kamar bai taɓa dariya ba.
"Hajiya wata nawa ne?"
Faɗin likita.
"Wata biyar ne, amma ba zan iya zubar dashi ba likita. Abban su kayi hakuri amma bazan iya aikata haka ba."
Hajiya Sadiya ta faɗa tana miƙewa tare da dafa kujeran da take zaune dan jiri da taji yana ɗibanta.
"Sadiya koma ki zauna."
Alhaji Mamman yace yana miƙewa tsaye.
"Bazan zauna ba, akan me za kace in cire cikin jikina, in baka so ni ina so, kasan zunubin da zamu kwasa ko kasan wahalar da zan sha wajen fitar shi. Wata biyar fa ba kwana biyar ba."
"To sai dai ki haifa a wani gidan ba gidana ba."
Daga haka yasa kai ya fita.
Itama Hajiya Sadiya ta ɗauki Rukayya dake kuka suka fita tama kasa lallashin yarinyar dan haushin ubanta ya shafeta.
Samu tayi ya bar cikin asibitin da motar shi, taxi ta tara ta shiga ta nufi gida.
A filin gida ta samu motarshi ta shiga falon ta same shi zaune da Muhsin saman cinyarshi yana mishi wasa, kasancewar ta barshi wajen mai aikinta. Wato dai cikin jikinta ya tsana ba ƴaƴan ba.
Ko kallon in da yake bata yi ba ta nufi ɗakinta.
"Ga takardar ki yana jiran ki, ki je wani gidan ki haifa sai ki ajiye ki dawo."
Cak Hajiya Sadiya ta dakata da tafiyar da take yi ta juyo a mutuƙar razane dan jin furucin mijinta ta kasa cewa komai balle barin gurin.
Kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kai.
"Kinji mai nace ai, ga takardar ki."
Daga haka ya ɗauki Muhsin suka wuce ɗakin shi.
Hajiya Sadiya da taji kanta yana juyawa ta ɗaga ƙafarta dakyar ta isa gurin da papern yake ajiye, hannu na rawa zuciyarta na bugawa ta ɗauka ta bude.
Saki ɗaya ta gani jiki. Hawayen da bata san yaushe ya taru a idanuwanta ba suka zubo bisa kumatunta.
Linkewa tayi ta wuce ɗakinta cikin zafin rai. Kayanta ta haɗa gaba ɗaya cikin manya manyan akwati biyu da jaka da duk Ƙadaranta da abun buƙata ta jawo ta fito falon.
Rukayya ta ajiye yarinyar sai kuka take ta fice ta barta, itama tana hawayen barin ƴaƴanta. Ta san dai ko dansu zai dawo da ita.
Kukan Rukayya shi ya fito da Alhaji Mamman daga ɗakinshi ga Muhsin na mishi kukan yunwa.
Ganin yarinya ajiye tana kuka ya ɗauketa ya leƙa ɗakin Hajiya Sadiya ya ba babu ita ya duba bathroom bata nan ya fito ya shiga kitchen nan ba bata nan. Nan ya tabbatar ta tafi kenan.
Mai aikinsu ya ƙira ta haɗawa Muhsin cornflakes kafin ta haɗawa Rukayya madaranta a feeder ta fara sha. Ya gwammace yayi wani auren matar ta kula mishi da yaran shi kafin Sadiya ta haihu ya dawo da ita, ya kyautar da abinda zata haifa.
...
Hajiya Sadiya tafiya kawai tana hawaye da ta rasa dame zata ƙirashi. Na bakin ciki ko na barin ƴaƴanta da tayi. Kukan Rukayya na mata yawo a kunnenta har zuciyarta yake ratsawa.
Ƙasar su nisa, gidan da in taje ma zata zauna take tunani, wacce take gabanta ta rasu balle bata jin babba da ita za taje ta zauna a wani gidan dangi ga ciki. Yayanta shima kanshi ta lura lallaɓawa yake da zaman gidan shi da matanshi ba za taje ta ƙara mishi nauyi ba. Waɗan can biyun kuma basa neman su balle tasan takamaiman inda suke.
Gidan ƙawarta ta nufa Zarah. Zarah tayi mamakin ganinta balle da taji abinda yake tafe da ita ta shiga tashin hankali sanin soyayyar da yake tsakanin mata da mijin.
"Ni yanzu ba wannan ba Zarah, gida nake so mai ko ɗaki ɗaya ko biyu in zauna zuwa nan da wani lokaci."
Hajiya Sadiya tace da Zarah.
"Ki zauna anan mana Sadiya, kin san dai Baban su Ƙasim ba zai hana ba."
"A'a ina son zama ni ɗaya, ina son yin nesa da Abban su, bana son ya san inda nake."
Shuru Zarah tayi can tace.
"Hakane, amma mai zai hana ki bashi lokaci ya gane kuskurenshi, gani nake kamar ba a hankalinshi yayi hakan ba. Rana tsaka kace a zubar da ciki daga cewa a'a ka yanke hukuncin saki."
Idanuwan Hajiya Sadiya ya cika da kwalla ta hanasu zuba.
"Nima haka nake ji Zarah. Ni yanzu ki tashi mu fita nema ko kinsan wata da take bada gidan haya ko wani."
"Na sani, Aisha ƙanwata mijinta yana bayarwa, gidanta yana layin bayan nan kin sani ai, muje in sanar da ita in mun ci sa'a mu sameshi a gida ma yanzu sai in haɗa ku dashi."
To! Hajiya Sadiya tace Zarah ta ɗauki mayafinta bayan ta sanar da mijinta suka fita, a gidanta Hajiya Sadiya ta bar kayanta.
Sun ci sa'a sun same shi yana shirin fita, bayan sun gaisa ta sanar da shi abin da suke so.
"Kin ci sa'a akwai gida ciki da falo da ɗaki biyu a ciki, akwai mai ɗaki biyu daban daban, anjima da yamma sai muje ki gani ko yanzu."
"Muje dai yanzu, in son samu ne, ina son mai ciki da falon." Mami ta faɗa.
"To to shikenan muje."
Daga nan suka fita gidan ba nisa sosai unguwar ba mutane sosai an fara gine gine sabon unguwa ne, gidan sabon gini ne an gina shi sabo anyi paint anyi wearing na wuta da komai. Ɗakuna biyu da falo sai kitchen da bathroom a waje da filin gida wadatacce.
Ta gani ta yaba ya mata kyau, anan ta roƙeshi zuwa gobe zata kawo kuɗin ko yau da yamma. Yace ba komai duk yadda tayi shikenan.
Gidan Zarah suka nufa, Ƙadaranta na ɗan kunne da sarƙa na gwal ta ɗauka da Alhaji Mamman ya bata a haihuwar Rukayya. Tace zata siyar ta biya gidan haya, Zarah bata hanata ba ta goyi bayanta.
Kasuwa ta nufa ta sayar bisa kuɗi mai yawa dubu ɗari da sittin aka bata kuɗin ta dawo bata biya gidan Zarah ba ta wuce gidan ƙanwarta A'isha ta bata dubu tamanin kuɗin shekara ta bawa mijinta in ya dawo zuwa gobe zata zo ta karɓi mukullin gidan ya ajiye mata.
Sai karfe huɗu na yamma ta samu nutsuwa tana zaune cikin ɗakin da Zarah ta saka mata kayanta ta kawo mata abinci da sai lokacin ta samu cin abincin rana. Tana cikin ci tunanin ƴaƴanta ya faɗo mata, tasan Rukayya zuwa yanzu zata nemi abincinta, ta mata yayen lokaci ɗaya. Ga Muhsin ma da duk inda zata shiga a gidan yana binta har sai ta mishi wayo in zata fita, Su Rahma da Hasiya sun dawo a makaranta zuwa yanzu.
Wa zai cire musu kaya ya basu abinci?
"Allah raya min ku."
Tace tana share hawayen daya gangaro a fuskarta.
Ta san mijinta bashi ɗaya bane da zai aikata abubuwan nan cikin ƙanƙanin lokaci.
...
Alhaji Mamman Bashir da yaran shi, bai san raino da wuya ba sai da Rukayya ta fara kukan yunwa tana son abincinta, ga Muhsin, ya shiga ya fita ya rasa ya zai yi da taimakon mai aiki ta samu ta sake bata kunu ta goyata tayi bacci.
Haka Muhsin dawowar su Rahma ya shiga cikin su ya sashi mantawa da komai. Su Rahma da suka tambayi Mami aka ce musu ta tafi unguwa.
Daren fa kasa bacci su kayi dukkansu dakyar suka samu yaran suka yi bacci.
Mai aiki ta kwana da Rukayya da cikin dare ta dinga mata kuka dakyar ta sake bata kunu ta sha ta koma bacci kafin ita ma ta samu bacci.
Alhaji Mamman Bashir da duk yana jin kukanta ya kasa fita, ya tashi ya fara zagaye ɗakin shi yana safa da marwa.
"Aure zan yi."
Shine amsar da zuciyarshi ya ba shi kafin ya zauna bakin gado yana dafe kan shi.
Vote.
Comments.
Share.