Chapter-13
by @maidambu41
_....ZAYN MALIK....✿_
*EXQUISITE WRITERS FORUM*
Mai_Dambu
Chapter-13
*Ina muku Barka da Sallah yan uwan musulmai baki daya Allahbya maimaita mana❤️🥰*
Da wannan tunanin ta zuba musu ido, taga iya gudun ruwan su, shima ta bangaren Abdul Ganiyu yana kokarin kamanta adalci, amma ina Iyabo bata gani,domin haka bai mata ba. Dan haka daga nan U.S ta kira yayarta ta gaya mata a dauki dan tauren ta, a kai wurin boka ya raba tsakanin Erica da Abdul Ganiyu, haka kuwa aka yi ta bangaren Abdul Ganiyu aikin bai tab'a shi ba, sai ta bangaren Erica, domin kiri kiri ta kai Abdul Ganiyu kotu lokacin Titilopemi tana da wata sha biyar, Haka aka raba basu ba tare da wani kwakwaran hujja ba, ta badab'a yarta a kafada ta bar kasar, bai yi azancin kira Baba, sai bayan tafiyar ta anan ne ya kira Baba ya gaya mishi.
Abinka da wanda suka san kan duniya da al'amarin kai tsaye ya gaya mishi ya bincika Iyabo, koda ya bincike ta ya samu haka ne,bai yi kasa a gwiwa ba, itama ya korata ya hanata Yaran ta, tana ji tana gani ya rabu da ita,Sannan ya kwace yaran shi, haka yabi Erica har Ethiopia amma fir taki dawowa kuma babu abinda ya mata, tana son shi yana son shi aka shiga tsakaninsu, wannan dalilin yasa yabar mata Titilopemi wato Aisha, a wurin ta, tare da sharadin tana cika shekaru bakwai zai zo ya dauke ta taga dangin shi.
Sannan ya kuma dauki alkawarin duk shekara zai kawo mata yan uwanta maza, haka kuwa ya kasance sannan tsakanin Abdul da Erica, basu iya rabuwa da junan su ba, ta hanyar aure suka rabu amma a zahirin gaskiya suna watsewar su sosai a waje, aure ne dai aka raba tsakanin su.
Haka Titilopemi ta taso bata da kawa sai Yan uwanta, burin ta a duniya yayunta, daga U.S zasu zo musu hutu, su gama kwanakin da zasu yi su koma amma a bisa al'adar Uban su, yana kai su Edo bikin Voodoo festival duk Shekara, dan haka lokacin da Titilopemi tazo Nigeria na farko a shekaran da za ayi festival din ne suka zo da Uwarta dan gani take kamar Abdul zai rike mata yarta ne ba zai bata ba,.dan haka suka tawo tare, haka suka gama taron bikin al'adun sannan suka koma Ethiopia da.
Bayan shekara goma.
Alhaji Abdul Ganiyu ya dauko Titilopemi ya dawo da ita Edo wurin Baban shi domin ta gaji da zaman da suke na sheke ayar su, ya nime su dawo da auren su, Erica taki shi kuma ya amso yar shi da karfin tsiya, kasancewar gidan su babban gidana dan haka suka saka shi a gaba da magana dole ya auri wata yar Kanwar Baban shi, me suna Tiwa Allah da ikon shi kuwa ta kama yaran shi baki daya ta rike, anan Titih ta hadu da Ustaz Ali, wanda a lokacin yana shigowa karanta da Yayunta ne ya lura da yarinyar Addinin Kirista ya shige ta, dakyar ya samu ta dawo kan hanya.
Kasancewar makota suke da Ustaz Ali, sai ya zama wani lokaci suna shiga gidan su karatu. A cikin gidan da kuma irin babban gidan hayan nan ne, yana dauke da mutane mabanbanta yare da al'ada, yawan shiga gidan nan ma suka hadu Aanuoluwakilishi, Allah ya daura mata sanyi irin yaran nan ne masu sanyi a waje amma a cikin ta irin yara marasa jin magana ne, duk da tafi Titilopemi wayo, gashi tana da girman jiki, da farko Ustaz Ali yaki tarayyar su, amma ganin yadda ta makale a jikin Titilopemi, dan haka ya saka idanu akan ta, kasancewar Titilopemi ita ɗaya ce mace a cikin gidan su, Yayunta da mahaifinta sun dauki soyayyar duniya sun daura mata, ganin yadda ta janyo Aina'u yasa suma suka saka ta a jikin su, sai dai ita Aina'u tayi fatan da ita ce a matsayin Yar gidan ba Titih ba, domin ita Titih babu abinda ya dame ta na jin dadin rayuwa, a haka duk shekara Alhaji Abdul Ganiyu zai kaita Ethiopia Christmas da new year, wurin uwarta a irin wannan zuwan Mahafiyar ta san yadda take kaunar Aina'u irin mahaukacin son nan take mata, karku manta an ce me d'a wawa ne, ita kan ta Madam Erica matuƙar Titilopemi tazo Ethiopia sai ta haɗa kayan Aina'u, daga Aina'u har Uwarta basu tab'a godiya ba, ita babban Burin Maman Aina'u shine yarinyar ta girma baban Titilopemi ya aure ta, ta shiga cikin gidan dan tana ganin matukar ba auren Baban Titilopemi tayi ba, ba zata huce haushin arzikin da take hangowa a dankare a cikin gidan ba.
Da wannan burin yarinyar take nanne da Titilopemi, a haka titi tasa aka mai da ita makarantar su, suna tafiya tare, sannu-sannu Aina'u ta koma gidan su Titi baki daya, ya zama uwar ta, bata da wani abu da zata mata, sai yadda zata ja hankali Alhaji Abdul Ganiyu,
Bayan sheraka shida suka gama secondary school, a lokacin Ita Aina'u ta ki nutsuwa tayi jarabawar ta yayi kyau, karshe ita kuma titi sakamakon ta yayi kyau da taimakon Yayunta da Ustaz Ali, a wannan lokacin Mamarta ta bukaci ta koma Ethiopia tayi karatun ta a addis Ababa, abin yabawa Aina'u haushi, domin bata zataci haka ba, sai ma ana jibi tafiyar aka gaya mata, dan haka ta dauki fushi da Titilopemi. Sai da Titilopemi ta gayawa Yayanta Taye ya kira Aina'u ya tambaye ta, amma dake tana da wayo sai ta nuna mishi babu kome, haka ya shirya su, karshe ba zata suka yiwa Aina'u da za a tafi a tare suka tafi ta raka Titilopemi, su Yayu da Baban ta, suna bayyana hakan ne domin yadda ita, amma su kansu ba son yarinyar musamman yadda take karya tana rintomo magana a gari, sai ayi ta tunanin Titilopemi ce, shi yasa lokacin da Maman Titih tace ta sama mata makarantar a can basu ki ba, dan dama ko uwr bata bukaci haka ba, zasu tura ta ƙasar waje, idan na gaya muku irin kaunar da suke mata da gatar da suke mata sai ka rike baki, gashi kowa yasa Maman Taye ce ta raba tsakanin su, duk haka suka dauki soyayyar duniya suka daura mata, babu sama da Baba Ademola Ades, domin son yarinyar yake yana mata kallon Bodd'i, gani yake kamar ita ce ta dawo mishi.
Allah da ikon shi Titi ta kama karatun ta, na likitanci a bangaren ƙwaƙwalwa a Ethiopia private university,
**
Tunda suka koma Aina'u ta shiga kokarin ganin ta nime Alhaji Abdul Ganiyu, sai dai daga ita har Uwarta an gaya musu basu da wannan sa'ar, sai dai su kare akan Titilopemi, ai kuwa suka sunkuya kanta, a haka ma ɗan tana wasa da Ibada ne, yasa wani abun ya same ta.
Ita kuma Aina'u ta fara polytechnic Edo inda ta fara karanta mass Communication, inda zata yi diploma din ta a wurin, da katon buri ta fara karatun.
A haka ta zama karamar yar iska a cikin makarantar, musamman take son shiga harkan miss world, ganin haka kuwa ta zama babbar yar iska a hannun mutane, dakyar ta samu damar shiga cikin jerin yan mata kyawawan makarantar, karshe har ta samu shiga na jaha, a cikin shekaraá hudu. Ta samu abinda take so, aka cikin shekaru hudun nan basu hadu da Titih, sai lokacin Auren Taye , ita Titih tana shekarun ta na karshe a jami'a,
A lokacin da Aina'u ta ga Titih, sai da ta kusan suma domin ita a ya d ta ai Titih bata kai wannan wayewar ba, sai gashi kome nata gwanin ban sha'awa ne, bata gama jami'a ba, amma ganin ta da abokan Yayunta suka yi sai da guda biyu suka nime auren ta, Baban su ya ce musu, su nime soyayyar ta, Allah da ikon shi ta amince da Dan gwamna Osun ta amince shi, haka manyan suka shiga maganar.
Akan shekaran da zata gama karatu sai ayi auren, haka kuwa manyan suka shiga maganar,har ta koma suna makale da juna a waya.
Wannan sauyi yad'agwa Aina'u hankali kamar zata yi hauka, gashi lokacin tana ta bin Kande yaki kulata sannan tabi Tayo shima da yake bin su Taye amma yaki ko kulata, karshe ta daura jaraba sai ta raba Titi da Ayo, kamar da wasa aka fara shirin bikin su, bayan wata shida da tafiyar ta. Kasancewar suna da suna da sirki da Fulani sun yi kokarin kamanta al'adar Fulani, musamman kayan lefe da suka mata, suka ce ita ma bafulatane.
Sannan Ayo da Taye da Kande da Tayo sun taso daga Nijeriya har Ethiopia suka gaida Madam Erica da dangin ta, sunyi na'am da shi kuwa domin kuwa Titih ce jikar farko da za ayi auren ta a kananun shekarun ta.
Haka akayi ta shiri bayan sun dawo, itama ta mai da hankali akan karatun ta, har suka gama exam dinsu, ta dawo aka fara shirin biki bata da wata kawa sama da Aina'u dan haka da ita suke ta, sai dai ana jibi daurin aure aka turo daga Osun an fasa auren Titih, abin ya bawa kowa mamaki domin sun ki fadar dalilin su, dan haka aka mai da musu kome nasu, ita kanta Titih kamar zata yi hauka duk da lokacin ba wani soyayya take da shi ba, amma da ciwo ace an fasa auren ka.
Haka ta bi Mamanta zuwa Ethiopia, dan ta shiga damuwa, sai da tayi wata bakwai a can ta dawo tazo ta fara Medical school da yake Abuja na cos din watanni uku zuwa hudu, kamar da wasa ta hadu da wani babban Jami'in tsaron yan sanda, rimi -rimi aka gama maganar kome, shi kan ma ba kai da nisa ba, ya fasa auren ta abin yayi d'aga hankalin Mahaifin ta da Yan uwan ta, takanas Baba ya dauke ta zuwa kauyen su aka tabbatar babu kome kawai lokaci ne da saura.
Haka ta cigaba da karatu har ta kuma haduwa da wani Dan majalisa, a lokacin tana aiki a babban asibitin Edo, mutumin yaso ta, shi kan sai ranar daurin auren ya tura da manyan shi ya fasa auren, abin yayi musu ciwo daga karshe sai aka fara fitar da wasu kananan magana akan cewa ai tana bin maza da mata, dalilin da yasa Baban ta haɗa ta da Aina'u kenan suka tawo Denmark ita tayi degree din ta a aikin jarida ita kuma tayi masters dinta a fannin ƙwaƙwalwa da tayi karatu akan shi, wannan abin ya matukar kwantar mata da hankali.
Zaman su A Denmark zama ne na yanci domin gida Ubanta ya saya mata anan ɗin, kuma wani ikon Allah suna zaune zaman lafiya babu tashin hankali, sai daga baya ta fahimci abinda Aina'u take aikatawa wato bin mata domin har tattoos take da shi a bayan ta, sai K'ugunta sai da taso mata magana amma ta kyale ta, yawan shiga damuwa da ganin abinda Aina'u take yi yasa ta fara jin damuwa akan haka, wani zuwan ta hutu a lokacin festival na Voodoo ta hadu da Imaden, da farko taso boye mishi halin da take ciki amma daga baya da suka fara kokarin fahimtar juna ta gaya mishi abinda yake faruwa da ita, Imaden babban dan kasuwa ne kuma malamin Jami'a, sanin ta fito babban gida ne bai yi kasa a gwiwa ba, ya gabatar da kan shi. Duk maneman ta bata tab'a yarda sun yi kazamar soyayya ba sai akan Imaden domin shi ya fara fahimtar tana da karfin sha'awa kuma hakan ya faru ne sakamakon kallon Porn video, da take yi kasancewar babu me saka mata ido yasa har yasa ta fara amfani da Dildo, abin ya matukar bashi mamaki domin bata yi kama da me haka ba, shima a cikin jakarta ya gani dan haka suka yi magana na fahimtar juna tunda shi zai aure ta, zai na taimaka mata yana rage mata zafi, da wannan ya shigo sosai rayuwar ta, sai abin haushi matukar ya samu lalube ta karshe yayi ta mata fada da masifa......